Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muke bakwana da ku a wannan rana sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.

  Ga kaɗan daga cikin abubuwan da muka wallafa a wannan rana ta Talata

  • Mahamadou Issoufou ya ba Buhari lambar yabo mafi girma a Nijar
  • Ƴan bindiga sun kashe sama da mutum 50 a Nijar
  • Ghana ta shiga makoki bayan mutuwar yara a cikin teku
  • Ƴan Najeriya za su soma biyan harajin sayen katin waya ta banki
  • Gwamnatin Najeriya ta dakatar kamfanin Azman Air
  • Najeriya na fama da 'matsalolin jin-ƙai mafi muni' a duniya
  • Mahara sun kona makaranta da asibiti a jihar Yobe
  • An gano littafin Injila da ya shafe shekara 1,900 a Isra'ila
 2. Masana sun gano abin da ya janyo ruwa ya daina gudana a duniyar Mars

  MARS

  Masana kimiyya sun ce sun gano abin da ya janyo ruwa ya daina gudana a duniyar Mars biliyoyin shekaru da suka gabata.

  A wata maƙala da aka rubuta a mujallar Science, sun ce ruwan mai ɗimbin yawa ya maƙale ne a cikin albarkatun ƙasa a ƙarƙashin ƙasar duniyar ta Mars.

  Masu bincike sun daɗe suna ƙoƙarin gano asalin abin da ya faru.

  Sun samu shaidar gudanar ruwan ne daga butumbutumi mai yawo da aka aika Mars din kuma ya ke aiko da saƙonni.

  Masana kimiyyar na amfani da bayanan da butum-butumin ya aiko don gano yadda duniyar ta rasa wasu sinadaren da ke taimaka wa rayuwa.

 3. Me ya sa ƴan bindiga ke kai hari makarantu da satar ɗalibai?

  Video content

  Video caption: Yadda satar ɗalibai ke barazana ga makomar ilimi a arewacin Najeriya
 4. Ƴan bindiga sun kashe sama da mutum 50 a Nijar

  NIGER

  Gwamnatin Nijar ta ce mutum 55 sun mutu a wani harin bindiga da aka kai yankin Tilleberi da ke kusa da iyakar ƙasar da Mali.

  Rahotanni sun ce an kai harin ne a jiya Litinin, inda ƴan bindiga suka buɗe wuta kan fasinjoji da ke kan hanyar komawa gida daga kasuwa a motar bus. Sannan suka cinnawa motar wuta.

  Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan waɗanɗa suka kai harin a yankin da ke kudu maso yammacin Nijar.

  Sai dai mayakan jihadi sun yaɗu a yankunan Sahel da dama cikin shekarun baya-bayanan.

  Ko a watan Janairu sai da aka kashe aƙalla mazauna wani ƙauye 100 a wani harin Jihadi.

  Gwamnatin Nijar dai ta ayyana zaman makoki na kwana uku daga gobe Laraba,

 5. Amurka ta gargaɗi China kan nuna halin tunzuri

  ANTONY BLINKEN

  Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya gargaɗi China kan ta daina nuna halin tunzurawa don biyan buƙatar kanta.

  A lokacin da ya ke magana a Japan, Mista Blinken ya ce Amurka za ta ja baya idan China ta nuna tursasawa don samun abin da take so.

  Sai dai Mista Blinken bai mayar da martani kan zargin da Koriya ta Arewa ta yi ba, na cewa Amurka na taƙalarta ta hanyar atisaye da sojojinta ke yi tare da dakarun Koriya ta Kudu.

  A sanarwar da ta yi ta kafar yaɗa labaran ƙasar Kim Yo-jung, ta gargaɗi Amurka da ta daina haifar da husuma idan tana so ta zama cikin kwanciyar hankali a shekaru huɗu masu zuwa."

  Kim Yo-jung ƴar uwar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ce kuma mai ƙarfin faɗa-a-ji.

 6. Ghana ta shiga makoki bayan mutuwar yara a cikin teku

  ghana

  An yi jana'izar yara 13 da aka tsinto gawawwakinsu a cikin teku a Ghana a makon da ya gabata.

  Yara 20 ake kyautata zaton sun ɓata bayan zuwa bakin teku Apam domin ninkaya a kudancin Ghana.

  Har yanzu akwai sauran gawawwakin da ba a gano ba.

  An yi jana'izar 12 daga cikin yara 13 da aka tsinto a yau Talata, bayan jana'izar ɗaya daga cikinsu tun Alhamis ɗin makon da ya gabata saboda gawar ta ruɓe.

  Akwai mutum biyu cikin yaran da suka tsira.

 7. CBN ya rage harajin da ake biya idan mutum ya aika da kudi ta sakon waya

  Shugaban Babban Bankin Najeriya

  Babban bankin Najeriya da ma'aikatar sadarwar kasar sun bullo da sabon tsarin haraji kan masu mu'amalar da ta shafi yin amfani da wayar salula wajen aikawa da kudi ko sayen katin waya ko 'data'.

  Bankin ya ce daga wannan Talatar, za ake cire harajin N6.98 kan kowanne kati ko 'data' da aka saye na layin waya ko kuma aikawa da kudi.

  A baya ana cire N20 zuwa sama kan kowacce mmu'amala da ta shafi aikawa da kudi ko sayen katin waya ko 'data' ta wayar salula.

  Ya ce sabon tsarin na cikin yarjejeniyar da aka cimma da bankuna da kamfanonin sadarwa bayan wata tattaunawa a jiya Litinin kan bashin naira biliyan 42 da ake bin kamfanonin sadarwa.

  Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa haɗin-gwiwa da aka fitar tsakanin babban bankin da kamfanonin sadarwar.

  Wannan tsari dai zai soma aiki ne daga wannan Talatar wato 16 ga watan Maris din 2021.

 8. Ana yi wa yara yankan rago a Mozambique

  Wadanan iyalai sun tsere bayan yiwa babban ɗansu yankan rago
  Image caption: Wadanan iyalai sun tsere bayan mayaƙa sun yi wa babban ɗansu yankan rago

  Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce masu iƙirarin jihadi a Mozambique sun yi wa yara ƙanana da shekarunsu ba su haura goma sha ɗaya ba yankan rago.

  Shugaban ƙungiyar a Mozambique ya ce harin ya yi matuƙar kaɗa shi.

  Ƙungiyar ta ce an kashe yara da yawa saboda sun ƙi shiga ƙungiyar masu ta da ƙayar baya.

  Ƙungiyar na gudanar da ayyukanta tun shekarar 2017 kuma tsawon shekaru gwamnati ta yi burus da yankin Cabo Delgado kafin a gano ɗimbin man fetur wanda ya yi sanadiyyar kafuwar ƙungiyoyin masu ta da ƙayar bayan.

  Wata mata ta bayyana yadda aka yi wa ɗanta mai shekara goma sha biyu yankan rago a lokacin da ta ke ɓuya da sauran ƴaƴanta.

 9. Gwamnatin Najeriya ta dakatar kamfanin Azman Air

  Gwamnatin Najeriya ta dakatar sufurin jiragen kamfanin Azman Air kirar Boing 737 nan take.

  Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin tantance lafiyar jiragen.

  Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ta sanar da cewa za ta bude sashen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje na filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal da kuma Enugu.

  Kamfanin Azman ya sanar da soke tashin jiragensa daga ranar Talata zuwa Juma'a bisa matakin da gwamnati ta dauka

  View more on twitter
 10. Mahamadou Issoufou ya ba Buhari lambar yabo mafi girma a Nijar

  Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya ba shugaba Buhari na Najeriya lambar yabo mafi girma ta Nijar da ake kira Grand Croix Des Ordre National Du Niger.

  Shugaba Issoufou ya karrama takwaransa ne a ziyarar da ya kawo masa a Abuja a ranar Talata inda ya ce an ba Buhari lambar yabon ne saboda dangantaka da kishin ƙasa da kuma manufarsa ta ciyar da Afrika gaba.

  A nasa ɓangaren shugaba Buhari ya taya Mahamadou Issoufou, murnar kammala wa'adinsa na biyu cikin nasara, da kuma lashe babbar lambar yabo ta 2020 ta Mo Ibrahim.

  View more on twitter
 11. Najeriya na fama da 'matsalolin jin-ƙai mafi muni' a duniya

  MDD

  Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matsalar jin-ƙai a arewa maso gabashin Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a duniya.

  Ta ce kusan mutum miliyan tara ne ke tsananin buƙatar agaji a yankin.

  Ƙungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare wanda kawo yanzu ta kashe kusan mutum dubu talatin tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu a shekaru goma da suka gabata.

  Majalisar Dinkin Duniyar da Gwamnatin Najeriya sun ce annobar cutar korona ta ƙara dagula lamarin.

  A wani ɓangaren kuma, tashe-tashen hankula da garkuwa da mutane don kuɗin fansa sun janyo dubban mutane sun tsere daga muhallansu a arewa maso yammacin Najeriyar inda wani rikicin ke ruruwa.

 12. Ana ci gaba da yi wa ƴan Afirka allurar AstraZeneca

  WHO

  Galibin ƙasashen Afirka na ci gaba da yiwa al'ummar su allurar rigakafin korona ta AstraZeneca, duk da cewa galibin ƙasashen Turai sun dakatar da yin allurar saboda rahotan da aka rinka samu na daskarewar jini.

  Hukumar Lafiya ta WHO, ta ce babu shaida da ke alaƙanta allurar da daskarewar jini amma dai tana nazari kan lamarin.

  Ƙasashen Afirka sun dogara kan rigakafin tallafin Covax na AstraZeneca domin shawo kan annobar korona.

  Kusan allura miliyan 14.5 na rigakafin aka raba a ƙasashen nahiyar Afirka 23, ƙarƙashin shirin Covax, wanda tuni dama sun soma yiwa al'ummarsu.

  Sai dai a yanzu Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta bi sahun ƙasashen Turai da ɗage soma yi wa ƴan ƙasarta rigakafin.

  WHO dai ta umarci a ci gaba da amfani da allurar, sannan ta ce idan an samu wani sauyi za ta sanar a hukumance bayan ta kammala nazarinta.

  Mahukuntan lafiya a Najeriya da Uganda sun ce suna da yarda akan rigakafin.

 13. Mahara sun kona makaranta da asibiti a jihar Yobe

  Video content

  Video caption: Latsa wajen magana domin sauraron rahoton Zahradden Lawal kan harin da aka kai Jihar Yobe

  A Najeriya mutanen garin Katarko na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar sun ce suna cikin kaɗuwa da fargaba bayan da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai musu hari yau da safe.

  Shaidun sun ce maharan makare a cikin motocin a-kori-kura sun afkawa garin ne da ke yankin karamar hukumar Gujba da asuba lokacin da jama’a ke kokarin yin salla inda suka kona makaranta da wani asibiti, ko da yake babu rahotan rasa rai.

 14. An gano littafin Injila da ya shafe shekara 1,900 a Isra'ila

  Getty Images
  Image caption: Wadancan fatu ne ba takar du ba, an sanya wannan ne domin nuna tsufan da kuma kwatanta yadda wadancan suke

  Masana Ilimin kufai sun ce sun gano wani bangare na littafin Injila da aka yi amfani da shi shekara 1,900 a Isra'ila.

  Sun ce fatun da ke dauke da rubutun Injilar da aka gano a cikin wani kogon da ke tsakiyar sahara sune na farko da aka gano a kudancin birnin Kudus a cikin shekara 60.

  Cikin rubutun da ke kan fatun akwai na yaren Girka wanda aka debo daga littafin Annabi Zakariyya da kuma wani bangare na littafin 12 Minor Prophets.

  An yi amannar an boye fatun ne lokacin guguwar rikicin Yahudwa da masarautar Rumawa da suka mamaye mazaunan Yahudawan a zamanin sarki Hadrian, tsakanin shekarar 132 zuwa 136 da haihuwar annabi Isa.

 15. Yar uwar Kim Jong Un ta ja wa Amurka kunne

  Getty Images

  Yar uwar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un dake da matukar tasiri kan harkokin kasar ta ja kunnen Amurka, game da duk wani yunkuri da ka iya zama wargi ga kasar, yayin da gwamnatin shugaba Joe Biden ke shirin fitar da manufofinta kan Koriya ta arewar.

  Cikin wasu bayanai da kafofin watsa labaran kasar suka rawaito, Kim Yojong ta soki Amurka da Koriya ta Kudu game da shirinsu na yin atisayen soja na hadin gwiwa da suka sabayi shekara shekara, tana mai cewa kada Amurka ta kuskura ta zamanto ummul haba'isin haifar da yaki.

  Kalaman nata dai na zuwa ne kwana guda gabanin ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai kai Koriya ta kudu, tare da rakiyar sakataren harkokin tsaron kasar Lloyd Austin.

  Ita dai sabuwar gwamnatin Amurkar ta ce ta shafe tsawon makwanni tana kokarin yin magana da Koriya ta arewa, amma ta ki amsa kasar ta ki amsa wannan tayi.

 16. El-Rufai yana taro da sarakuna kan rashin tsaro a Kaduna

  @GovKaduna

  Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Nasir el-Rufa'i na jagorantar wani taro kan matsalar tsaro da ta addabi jihar.

  Jami'an gwamnati da wakilan kungiyoyi da malaman addinai da masu sarautar gargajiya da sauran wakilcin daga sassa daban-daban ne ke halartar taron.

  Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, wadda ta ki ci ta ki cinyewa.

  @GovKaduna

  Ko a jiya sai da wasu 'yan bindiga suka kutsa kai cikin wata makarantar Firamari suka dauki dalibai da malamansu.

  @GovKaduna

  Gabanin nan a ranar Asabar, sai da jami'n tsaro a jihar suka dakile wani hari da aka aki wata makaranta, inda aka kusa sace daliban makarantar sai dai harin bai yi nasara ba.

  @GovKaduna
 17. Ahmad Lawan ya bai wa ‘yan kabilar Igbo shawara

  NATIONAL ASSEMBLY

  Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Ahmed Lawal ya shawarci 'yan kabilar Igbo da ke kudu maso gabas, da su zo a dama da su a siyasar kasar.

  Shugaban ya yi wannan bayani ne lokacin da yake bayanin godiya a taron taya gwamnan Imo Hope Uzodimma murnar cika shekara guda kan shugabancin jihar.

  Shugaban Majalisar ya ce gwamna Uzodimma ya samu nasarori da dama cikin shekarar da ya yi a ofis, Dalilin fadada siyasarsa da ya yi a Najeriya.

  "A yau muna taya gwamna murnanr cika shekara daya a ofishinsa, ga mataimakin shugaban kasa ga gwamnoni da yawa, wanda hakan ke nuna kyakkyawar alakar da yake da ita tskaninsa da 'yan siyasar Najeriya.

  Don haka akwai bukatar sauran 'yan kabilar Igbo su yi koyi da shi domin su ma su shigo a dama da su a siyasar kasarsu.

 18. An ceto wasu 'yan mata daga gidan sayar da jarirai a Anambra

  NIGERIA POLICE FORCE

  Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bankado wani gidan sayar da jarirai a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar, wanda ake yi masa bad-da-kama a matsayin gidan shan barasa da mata masu zaman kansu a garin Nnewi.

  Rundunar yan sandan reshen jihar ta Anambra ta ce ta ceto wasu 'yan mata hudu masu juna biyu da ake jira su haihu yayin samamen da ta kai.

  Kakin 'yan sandan jihar Haruna Mohammed ya ce kasuwancin da ake yi na sayar da barasa kawai wani basaja ne, inda daga ciki kuma ake kasuwancin sayar da jarirai.

  Rundunar 'yan sanda ta ce Ikegwuonu wadda itace mai gidan ba ta da aiki sai kamo 'yan mata da gayyatar maza su yi musu ciki sannan a sayar da jariran da suka haifa.

  An kama wasu mata biyu da ke da alaka da gidan, kuma ana ci gaba da neman Gladys Nworie Ikegwuonu domin gurfanar da ita gaban shari'a.

 19. Saddam da Netanyahu 'sun fi kashe Larabawa sama da kowa'

  BBC

  Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce Saddam da Netanyahu sun fi kashe larabawa sama da kowa.

  Javad Zarif ya yi wannan ikirari ne lokacin da ake wata tattaunawa a Tehran ta intanet.

  Ya ce Iran ba ta adawa da duk wani mutum da ke yankin, kuma Saddam ne ya fara bata mata suna sai kuma Firaiministan Isra'ila Natanyahu.

  A zauren taron Mista Javad ya ce wadannan mutanen biyu sun fi kashe Larabawa sama da duk wani mutum a duniya.

  Ba tare da kama sunan wata kasa ba, Ministan harkokin wajen ya ce, "har yanzu wasu kasashe sun ki su sauya halayyarsu domin ganin an samar da sauyi mai kyau a gabas ta tsakiya."

 20. Abin da ya sa Kano ta haramta sayar da lemon dan tsami

  Video content

  Video caption: Hirar Baffa Babba Dan Agundi da BBC kan sinadaran da wa'adinsu ya kare a Kano

  Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar.

  Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.

  Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wannan sinadari da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.

  Ya kara da cewa sakamakon binciken da suke yi sun kama buhu 583 na irin wadannan sinadirai da wa'adinsu ya kare.

  Da ma dai gwamnatin ta ce ta kama mutumin da ke sayar da lemun da ya janyo ɓarkewar baƙuwar cuta a jihar