Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Nan za mu rufe shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

 2. Ana zanga-zangar adawa da kullen korona a Turai

  Ana ci gaba da zanga zangar adawa da kullen Korona a wasu kasashen Turai, duk da tsauraran matakan da ƴan sanda ke ɗauka.

  Hakan ya zo ne bayan da ƙasashe a nahiyar ke fuskantar bazuwar Korona a karo na uku, wadda ta sa suka kara ayyana dokokin kulle da suka shafi miliyoyi.

  A kasashen Holland da Jamus ƴan sanda na amfani da ruwa da kuma hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu boren.

  A Burtaniya batun har ya shiga majalisa, inda ƴan majalisar sama da 60 suka nuna adawa da kudurin da ke son a ƙarawa ƴan sanda ƙarfi da zai ba su damar hana zanga-zanga.

  Shekara ɗaya kenan da ƙaƙaba dokar kulle ta farkoa Turai, kuma a yanzu al'umma sun fara fito na fito da matakin kullen da nufin daƙile bazuwar annobar Korona.

  Masu zanga-zanga a Turai
 3. Tattalin arzikin duniya na farfaɗowa – IMF

  Shugaban IMF Kristalina Georgieva

  Hukumar bada lamuni ta duniya IMF ta ce akwai haske kan haɓakar tattalin arzikin kasashen duniya bayan nakasa tattalin arzikin da annobar Korona ta yi.

  Amma IMF ta ce har yanzu ana ci gaba da samun wagagen gibi tsakanin kasashen masu arziki da kuma matalauta.

  A cewar mataimakin babban daraktan hukumar Geoffrey Okamoto, yayin da kasashe kamar Amurka ke kokarin fitar da ƴan kasarta daga halin matsi da Korona ta jefa su, annobar ta jefa mutun miliyan casa'in cikin tsananin talauci.

  Babbar fargabar IMFa yanzu ita ce yadda cutar ke daɗa canza nau'i tare da sake bazuwa duk da cewa ana samun rigakafi.

 4. Japan ta haramta wa ƴan ƙasashen waje zuwa kallon wasannin Olympics

  Japan ta yanke shawarar cewa babu wani ɗan kasar waje da zai shiga kasar da sunan kallon wasannin Olympics da za a yi a cikin wannan shekara.

  Matakin ya zo ne saboda ci gaba da bazuwar annobar Korona.

  Kwamitin shirya Olympics IOC ya ce matakin bai masa dadi ba, amma ya fahimci cewa Japan ba ta da zaɓi.

  Gwamnatin Japan ta shirya mayar wa duk wanda ya sayi tikitin kallon wasannin da kuɗinsa.

  Haka ma za a duba yiwuwar idan za a iya barin ƴan kasar kallon wasannin.

 5. Buhari zai fara biyan matasa tallafin rage raɗaɗin korona

  Ma’aikatar ƙwadago da ayyukan yi ta Najeriya ta ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin fitar da kuɗi domin soma biyan ƴan Najeriya 774,000 da suka yi rijistar shirin SPW na tallafin korona.

  Ƙaramin ministan ƙwadago Festus Keyamo ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter.

  Ya ce nan ba dadewa ba waɗanda suka yi rijistar shirin za su fara jin alat a asusunsu na banki.

  Kuma a cewarsa, za a yi amfani da lambar BVN ta banki domin kaucewa masu karba har sau biyu musamman waɗanda suka yi rijista da suna biyu.

  Sai dai ministan bai fadi lokacin da gwamnati za ta fara biyan kuɗin ba.

  A watan Janairu ne gwamnatin Buhari ta ƙaddamar da shirin na tallafi ga matasa 750,000 da ke zaman kashe wando yayin da rashin ayyukan yi tsakanin matasan ya yi ƙamari.

  View more on twitter
 6. Mafi ƙarancin albashi a Qatar yanzu ya haura naira dubu 100

  Daga yanzu mafi ƙarancin albashin ma’aikata a Qatar ya kai dala 270 a wata kwatankwacin sama da naira dubu 100, kuɗin Najeriya.

  Amma dole ma’aikata su samar wa kansu abinci da muhalli ƙarƙashin tsarin.

  Ƙarin na kusan kashi 33 ya fi shafar baƙi waɗanda suka fi yawa a cikin mafi yawan ƙananan ma'aikata a Qatar.

  Qatar na bunƙasa ayyukanta musamman na gine-gine yayin da take shirye-shiryen karɓar bakuncin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya da za a yi badi.

  Wata ƙungiyar fafutikar kare ƴan ci-rani ta Migrant Rights ta ce duk da ƙarin amma albashin ya yi kaɗan. Amma Qatar ta musanta inda ta ce zai inganta saka jari.

  Ma'aikata a Qatar
 7. Firaministan Pakistan ya kamu da korona

  Imran Khan

  Hukumomi a Pakistan sun ce gwaji ya tabbatar da Firaministan ƙasar Imran Khan ya kamu da korona – kwana biyu bayan ya karɓi allurar rigakafin korona.

  Yanzu ya killace kansa a gida.

  Mista Khan wanda yanzu shekarunsa 68 ya halarci wani taron jama’a a kwanakin da suka gabata.

  Yawan masu kamuwa da korona na ƙaruwa a Pakistan yayin da cutar ta sake yin ƙamari karo na uku.

 8. Korona ta kashe mutum 3,000 a Brazil cikin kwana ɗaya

  Brazil ta bayar da sanarwar fiye da mutum 90,000 da suka kamu da cutar korona sannan wasu kusan 3,000 suka mutu cikin kwana daya.

  Wannan ne karo na biyu da aka samu karuwar mace-mace cikin sa'a 24 tun bayan da cutar ta barke a ƙasar.

  Yawan marasa lafiya da ke kwance a asibiti ya kai kashi 80 cikin 100 amma a jihar Rio de Janeiro yawan marasa lafiyar ya kai kashi 95 cikin 100.

  Magajin garin ya bayar da umarnin rufe bakin teku amma kuma shugaba Jair Bolsonaro wanda yake adawa da sa dokar kulle, ya soki matakin.

 9. 'Yan bindiga sun kashe mutum 14 a Jihar Neja

  'Yan fashin daji

  Wasu 'yan bindiga sun kai hare-hare a garuruwan Jihar Neja da ke Ƙaramar Hukumar Mariga, inda suka kashe mutum 14 tsakanin Alhamis zuwa Juma'a.

  Maharan sun fara far wa wani gari da ke kusa da Shadadi da yammacin Alhamis tare da kashe mutum takwas sannan suka ƙona gidansu, kamar yadda tsohon ɗan majalisar jiha Honarabul Usman Musa ya shaida wa BBC.

  Usman ya ce biyar daga cikin mutanen da aka kashe 'yan uwansa ne, mata biyu da kuma 'ya'yansu uku, kafin daga baya su kashe maƙotansu uku. Haka nan sun kashe wani mutum ɗaya a garin Marafan Mugumu.

  Mun tuntuɓi kakakin rundunar 'yan sandan JIhar ta Neja, sai dai wayarsa ba ta shiga ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

  A ranar Juma'a kuma, 'yan fashin sun shiga garin Ishanga, inda suka kashe mutum biyu da kuma yaro guda ɗaya.

  "A harin na ranar Juma'a, sun sace shanu sama da 300 da tumakai kusan 200," in ji shi.

  Ya ƙara da cewa maharan sun sake komawa garin Shadadi bayan an yi jana'izar mutanen a ranar Juma'a suka sake raunata mutum huɗu da harbin bindiga.

 10. Faransa da Poland sun sake ƙaƙaba dokokin kulle

  Poland
  Image caption: Babban birnin Poland Warsaw ya kasance fayau

  Faransa da Poland sun sake kakaba dokokin kulle yayin da kasashen ke fama da karuwar masu cutar korona.

  An bukaci kimanin kashi daya bisa uku na al'ummar Faransa, har da birnin Paris, su zauna a gida tsawon wata daya amma matakin bai shafi fita sayayya ko motsa jiki ba.

  A cewar wakiliyar BBC, a Poland ma ana samun karuwar mutanen da suka kamu da cutar korona kuma shaguna da otel-otel da wuraren motsa jiki duka za su kasance a rufe a kasar.

  Jami'an lafiya a Poland sun yi gargadin sabon nau'in cutar da ya bulla a Burtaniya ya bazu a kasar kuma hakan ya sa dole aka sa dokar kullen.

  Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce kasarta za ta zama cikin shirin yin amfani da allurar rigakafin Rasha wato Sputnik da zarar hukumar da ke tabbatar da sahihancin magunguna ta Turai ta amince da ita.

  Markel ta kuma kare matakin dakatar da yin amfani da allurar AstraZeneca na wani lokaci saboda fargabar da ake da ita cewa yin amfani da allurar na iya janyo daskarewar jini.

 11. Mummunan hatsarin mota ya kashe mutum 14 a Sri Lanka

  Sri Lanka

  Wata mota cike da mutane ta yi arangama da wani dutse a ƙasar Sri Lanka, abin da ya jawo mutuwar direban da kuma fasinja 13 da ke cikinta.

  'Yan sanda sun ce wannan shi ne hatsari mafi muni cikin shekara 16.

  Motar na tafiya ne a yankin Passara mai cike da tsaunuka a lokacin da direban ya yi yunƙurin kauce wa wata babbar mota da ke tunkararsa, inda ta sauka daga kan titi kuma ta yi karo da dutsen.

  Biyar daga cikin fasinjojin mata ne, sauran takwas kuma maza, a cewar 'yah n sanda. Wasu mutum 30 sun ji raunuka.

  Kakakin rundunar 'yan sanda, Ajith Rohana, ya ce bidiyon da kyamarar tsaro ta CCTV ta ɗauka ya nuna cewa direban ya yi ganganci kafin faruwar hatsarin.

  Ya ƙara da cewa an fara gudanar da bincike.

 12. Halin da makarantun tsangaya da Jonathan ya gina ke ciki a Sokoto

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Haruna Kakangi a cikin shirin Gane Mani Hanya

  Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya yi duba kan Halin da makarantun tsangaya da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gina suke ciki a Jihar Sokoto.

  Gwamnatin Jonathan ta yi ikirarin gina makarantu akalla 157 a fadin Najeriya a wani yunkuri na kawar da bara da kuma haɗa ilimin zamani da na addini.

  Lamarin ya sa iyaye da dama murna domin kuwa suna ganin wata dama ce da ‘ya’yansu za su samu ilimin addini da na zamani a lokaci guda.

  Sai dai cikin rahoto na musamman da Haruna Ibrahim Kakangi ya haɗa, za ku ji yadda almajiran da ke karatu a makarantar suke fama da bara duk da cewa an gina ta domin tsugunar da su da zummar hana su yawon barar.

 13. Yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya miliyan 6 ne - Ma'aikatar ilimi

  Yara ɗalibai

  Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya ta yi ƙarin haske game da adadin yaran da ba sa zuwa makaranta bayan ƙaramin ministan ilimi da babban minista sun bayar da mabambantan adadi cikin wata biyu.

  Kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Ƙaramin Ministan Ilimi Chukuemeka Nwajiuba na cewa adadin yaran ya kai miliyan 10.1 yayin ƙaddamar da wani shirin Bankin Duniya kan ilimi a Jihar Jigawa ranar Alhamis.

  Sai dai wata biyu kafin haka, Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce yaran guda miliyan 6.95 ne a 2020, inda aka samu raguwa daga miliyan 10.1 da suke a 2019.

  Da yake fayyace batun ga kafar TheCable, mai magana da yawun ma'aikatar, Ben Goong, ya ce adadin da Adamu Adamu ya bayar shi ne daidai, yana mai cewa wanda ƙaramin minista ya faɗa ƙididdigar 2019 ce.

  Ya ƙara da cewa duk da dai adadin da Nwajiuba ya faɗa ba daidai ba ne amma "ba za a ce ya yi kuskure ba, saboda haka abin yake cikin wata 18 da suka wuce".

 14. Tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da amfani - Ganduje

  Umar Ganduje

  Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce yana goyon bayan amfani da ƙarfi da kuma tattaunawa da 'yan fashin daji masu kashe mutane da garkuwa da su don neman kuɗin fansa.

  Ganduje ya ce tattaunawa da tubabbun 'yan fashi na da muhimmanci musamman ga mutanen da aka yi garkuwa 'yan uwansu.

  "Ina ganin waɗanda aka sace musu 'yan uwa za su so a tattauna da masu garkuwar domin sakin mutanensu. Za su so a yi duk abin da za a iya yi domin kuɓutar da su. To idan ba ka tattauna da su ba kuma suka kashe su duka fa?" in ji gwamnan.

  Gwamnan ya bayyana haka ne cikin shirin 'A Faɗa A Cika' na BBC Hausa, wanda aka gabatar a daren jiya Juma'a a matsayin shirin Ra'ayi Riga.

  "Ya kamata a yake su to amma kuma idan an samu yanayin da wasu suka tuba, za su iya zama gada wajen daidaitawa idan an saci wasu."

  Jihar Kano ba ta cikin jihohin da 'yan fashin ke yawan kai hare-hare amma ana ci gaba da nuna fargaba game da ƙaruwar kashe-kashen a maƙotan jihohi kamar Kaduna da Katsina da Jigawa.

 15. Ɗan bindiga ya kuɓutar da ɗan uwansa daga gidan yari a Najeriya

  Bindiga

  Wani fursuna ya tsere daga gidan yari na Aguata Custodial Centre da ke Jihar Anambra ta kudancin Najeriya a jiya Juma'a.

  Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba, ya gudu ne bayan wasu 'yan bindiga sun kai wa motar jami'an tsaron gidan tsararrun hari yayin da take kan hanyar zuwa kotu.

  Wata majiya ta shaida wa kafar labarai ta PR Nigeria cewa ɗan uwan mutumin ne ya shirya harin.

  Majiyar ta ce an kashe 'yan sanda biyu da suka haɗa da mace da namiji yayin harin, sannan kuma ba a ga direban motar ba.

  "Shi ma mai tsaron kotun an jikkata shi kuma har yanzu ba ya cikin hayyacinsa," a cewar majiyar.

  A 'yan kwanakin nan, ana yawan kai wa ofisoshin 'yan sanda hari a jihohin kudu maso gabashin Najeriya, yayin da ƙungiyar IPOB ke fafutikar ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biafra.

 16. Dutse ya yi aman wuta a Iceland

  Aman wutar dutse

  An samu aukuwar aman wutar dutse a kudu maso yammacin Iceland sakamakon motsawar kasa da aka samu a 'yan makonnin da suka gabata.

  A cewar wakilin BBC, lamarin ba ya barazana ga rayuwar jama'a saboda babu mutanen da ke zaune a wajen kuma an sa dokar hana jirage bi ta sararin samaniya yayin da kwararru ke kokarin yin bincike kan lamarin.

  Lamarin ya faru ne a dutsen Fagradalsfjall mai nisan kilomita 30 daga babban birnin Iceland.

  An rufe babban filin jirgin saman kasar na wani dan lokaci a jiya Juma'a.

  Hukumomi sun bukaci jama'ar da ke zaune kusa da wurin da su rufe tagoginsu saboda yiwuwar fitar hayakin gas.

 17. Ƙarin mutum 130 sun kamu da cutar korona a Najeriya

  Korona

  Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 130 da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Juma'a.

  Bisa sabbin alkaluman hukumar, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohi 13 da mutum 46 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

  Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 19 a jihar Ogun da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

  A Kwara, an samu mutane 18 da suma suka kamu da korona sai Abuja, babban birnin ƙasar da aka samu mutum 12, Kaduna mai mutum 10 da Ekiti da aka samu mutum 6.

  Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi:

  • Abia-5
  • Edo-3
  • Sokoto-3
  • Osun-3
  • Niger-2
  • Oyo-2
  • Akwa Ibom-1

  Kazalika cikin kwana ɗayan, an sallami masu cutar 691 daga cibiyoyin da suke kwance a faɗin Najeriya - mutum 242 daga Legas, 193 a Abuja sai 103 a Kwara.

  Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 161,539, sannan an sallami 147,581 jumulla, baya ga mutum 2,027 da suka mutu kawo yanzu.

 18. Assalamu Alaikum

  Barkanmu da hantsin Asabar, da fatan an tashi lafiya.

  Sannunmu da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, inda za mu fi mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar maƙotansu.

  Umar Mikail ke mkuku maraba.