Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kum gobe idan Allah Ya kai mu

 2. Yadda aka yi wa gwamna Tambuwal allurar rigakafin korona

  An yi wa gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal rigakafin korona.

  Gwamnatin jihar ta ce a ranar Asabar likitan gwamnan ya yii wa gwamna Tambuwal allurar.

  Haka kuma an yi wa mataimakinsa da kuma sauran manyan jami'an gwamnati.

  View more on twitter
 3. Leicester City ta kori Manchester United a FA

  Kelechi Iheanacho
  Image caption: Ƙwallaye biyu Kelechi Iheanacho ya jefa ragar Manchester

  Leicester City ta kai zagayen dab da ƙarshe a gasar FA a karon farko tun kakar 1981-82 bayan ta fitar Manchester United a King Power da ci 3-1

  Yanzu Leicester za ta haɗu ne da Southampton a Wembley a zagayen dab da ƙarshe.

  Ɗan Najeriya Kelechi Iheanacho ne ya taimakawa Leicester doke Manchester United.

  A ranakun 17 da 18 za a yi fafatawar zagayen dab da ƙarshe a Wembley yayin da kuma za a buga wasan ƙarshe a ranar 15 ga Mayu.

 4. Chelsea za ta haɗu da Manchester City a FA zagayen dab da ƙarshe

  Chelsea
  Image caption: Chelsea ta doke Sheffield United 2-0.

  Chelsea da ta lashe kofin FA sau takwas za ta haɗu da Manchester City mai harin lashe kofi huɗu a kakar bana a zagayen dab da na ƙarshe a gasar FA.

  Leicester ko Manchester United za su haɗu ne da Southampton a zagayen dab da ƙarshe na lashe kofin FA na bana.

  Manchester City ta doke Everton ne ci 2-0, yayin da Chelsea ta doke Sheffield United 2-0.

  Leicester suna United suna ci 1-1 a fafatawar da suke a King Power lokacin da aka haɗa ƙungiyoyin da za su fafata a zagayen dab da ƙarshe when the semi-final draw was made at half-time at the King Power Stadium.

  A ranakun 17 da 18 za a yi fafatawar zagayen dab da ƙarshe a Wembley yayin da kuma za a buga wasan ƙarshe a ranar 15 ga Mayu.

  Manchester City ta doke Everton ne ci 2-0
  Image caption: Manchester City ta doke Everton ne ci 2-0
 5. Boko Haram ta kashe wasu sojojin Kamaru da aka turo Najeriya

  Rahotanni sun ce an kashe sojojin Kamaru guda biyu da aka tura Najeriya a wani hari da Boko Haram ta kai a jihar Borno yankin arewa maso gabashin Najeriya.

  Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ce wasu majiyoyin soji da suka tabbatar da harin a ranar Lahadi, sun ce mayakan sun abka wa sojojin ne a wajen garin Wulgo ranar Asabar da dare.

  “Kuma harin ya rutsa da sojojin Kamaru biyu da aka turo domin taimakawa sojojin Najeriya.”

  Majiyoyin sun ce an shafe sama da minti 40 ana musayar wuta tsakanin sojoji da ƴan Boko Haram.

  Harin kuma ya raunana wasu sojojin na Kamaru guda uku da sojan Najeriya ɗaya a artabun.

 6. Ƴan tawayen CAR sun ce tsohon shugaba Bozize ne jagoransu

  François Bozizé

  Ƴan tawayen da ke kokarin hamɓarar da shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ce tsohon shugaban kasar, François Bozizé, ne yanzu jagoransu.

  Wani mai magana da yawun ƴan tawayen na Coalition of Patriots for Change (ko CPC) ya faɗa wa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa Mr Bozizé ya amince ya jagorancitawayen bayan buƙatar da kungiyoyin shida masu dauke da makamai suka gabatar.

  A baya ya musanta zargin cewa shi ne ya haifar da tawayen wanda ya fara a watan Disamba.

  C-A-R ta kasance cikin rashin kwanciyar hankali sosai tun shekara ta 2013, lokacin da aka kifar da gwamnatin Mr Bozizé wanda ya haifar da yakin basasa.

  An hana shi tsayawa a zaben na Janairu saboda an zarge shi da aikata laifukan cin zarafin dan adam kuma yana fuskantar takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.

 7. An tsinci gawarwakin zakuna a gandun daji

  An tsinci gawarwakin zakuna guda shida a gidan kula da namun daji na Queen Elizabeth Park da ke Uganda.

  Jami'ai na zargin cewa an saka wa zakunan guba ne kuma sun ce an gano kawunansu da ƙafafu da aka fille a cikin daji da kuma wasu gawarwakin shaho da aka gani.

  A cikin wata sanarwa hukumomin kula da gandun daji a Uganda sun ce sun ƙaddamar da bincike kan al'amarin wanda suka ce ya nuna girman fataucin namun daji ta haramtacciyar hanya.

  Yawon buɗe ido na ɗaya daga cikin ɓangarorin da ke kawo wa ƙasar Uganda kuɗaɗen shiga.

  Zaki
 8. Yaƙin Boko Haram da ISWAP ya yi ‘ajalin ƴan ta’adda 54’

  Ƴan ta'adda a Najeriya

  Mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ɓangaren Abubakar Shekau sun yi mummunan artabu da juna kan iko da wani yanki a Tafkin Chadi.

  Jaridar PRNigeria ta ce ƴan ta’adda aƙalla 54 aka kashe cikin wata ɗaya a artabu tsakanin mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ƴan ƙabilar Buduma a Jamhuriyyar Nijar.

  A cewar jaridar ƴan Boko Haram daga ƙabilar Buduma suka fara kai wa ISWAP harin ba-zata a ƙauyen Chikka da ISWAP ke iko da shi a ranar 3 ga watan Maris domin kwasar ganima.

  “Mayaƙan daga ɓangaren Shekau sun mamaye ƙauyen inda suka kashe ƴan ISWAP da dama tare da sace matansu guda biyar. Kuma mayaƙan sun saci kayayyakin abinci kafin su gudu a cikin dare.”

  Daga baya kuma ISWAP ta kai harin ramuwar gayya inda suka yi ɓarin wuta da ƴan Boko Haram a yankin Kaduna Ruwa da Kaiga kuma an yi hasarar rayuka daga ɓangarorin biyu, a cewar jaridar.

  Sannan kuma mayaƙan Boko Haram sun kashe wasu makiyaya 22 tare da sace shanunsu saboda sun biya haraji ga ISWAP maimakon ɓangaren Shekau. Sun kuma abka wa wani kwale-kwalen da ke ɗauke da makamai na ISWAP inda suka kashe mayaƙa takwas suka kwashe makaman da ke cikin kwale-kwalen.

 9. An kashe mutum ɗaya a Myanmar

  Myanmar

  An kashe mutum ɗaya sannan an jikkata wasu shida yayin wata hatsaniya a yankin Mandalay na Myanmar.

  Wani mazaunin yankin ya faɗa wa BBC cewa rikici ya ɓarke bayan sojoji da 'yan sanda sun nemi a bi dokokin kariya daga cutar korona.

  Marigayin bai wuce shekara 40 da wani abu ba kuma an harbe shi ne a ka, a cewar rahoton BBC Burmese.

  Daruruwan mutane a Mandalay, birnin na biyu mafi girma a ƙasar, sun gudanar da zanga-zanga a yau da sanyin Asubahi a kan tituna kafin fitowar rana.

  Kusan mutum 100 aka kashe tun bayan fara rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabarairu.

 10. Kamfanin mai na Saudiyya ya yi mummunar faɗuwa

  Man Fetur

  Katafaren kamfanin mai na Saudiyya, Saudi Aramco, ya anar da faɗuwa mai girma a shekarar da ta gabata sakamakon dokar kullen korona da ta taƙaita buƙatar man fetur.

  Ribar da kamfanin ke samu ta faɗi da kashi 45 cikin 100 a 2020 idan aka kwatanta da 2019.

  Duk da haka, Saudi Aramco wanda ke ɗaya daga cikin manyan kamfunnan mai a duniya, ya samu ribar dala biliyan 49 kuma ya ce masu hannun jari a kamfanin za su samu kason dala biliyan 75.

  Gwamnatin Saudiyya ce babbar mai hannun jari a kafanin na Aramco.

  Kamfanin ya ce "2020 na cikin shekaru mafiya tsauri a tarihinsa".

  A shekarar da ta wuce, farashin fetur ya faɗi da kusan ninki biyar saboda ƙasashe sun rufe ma'aikatu sannan suka hana zirga-zirga ta yau da kullum, abin da ya jawo raguwa wajen buƙatar man.

  Sauaran manyan kamfunnan mai na duniya irinsu Royal Dutch Shell da BP da Exxon Mobil, duk sun samu faɗuwa.

 11. Ana bikin sabuwar shekara ta Nowruz a faɗin duniya

  Nowruz

  Miliyoyin mutane a faɗin duniya na bikin Nowruz wato Sabuwar Shekarar Fashiya wadda aka fi gudanarwa a Iran.

  Akasari ana gudanar da bikin Nowruz ne a ƙasashen Iran da Afghanistan da yankin Kurdawa na Iraƙi da Turkiyya da yankin Parsis na Indiya da kuma sauran sassan duniya.

  Wannan shekarar - wadda ita ce ta 1400 a kalandar Fashiya - ana gudanar da bukukuwan ne a gidaje saboda annobar korona.

  Nowruz
  Image caption: Ana iya ganin ma'aikatan lafiya na yin shagali a asibitin Firoozabadi da ke Tehran, babban birnin Iran tare da marasa lafiya ta hanyar jera nau'ukan abinci a teburi
  Nowruz
  Image caption: Dubban Kurdawa ne suka yi bikin a Istanbul, babban birnin Turkiyya
 12. Gwamnonin Najeriya sun koka kan yunƙurin kashe gwamnan Benue

  Gwamnonin Najeriya

  Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana harin da 'yan bindiga suka kai wa gwamnan Jihar Benue a matsayin "abin kiɗimarwa".

  A jiya Asabar ne wasu 'yan bindiga suka kai wa tawagar Gwamna Samuel Ortom hari a gidan gonarsa da ke kan hanyar Makurdi zuwa Gboko.

  Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya fitar a yau Lahadi, NGF ta taya Ortom alhini game da harin da ta ce "na tsoro ne kum na ƙeta".

  Shi ma Sufeto Janar na 'Yan Sanda Mohammed Adamu ya yi Allah-wadai da harin kuma ya umarci a tsaurara tsaro kan gwamnan tare da ƙaddamar da bincike.

  "NGF na faɗa da babbar murya cewa yunƙurin da ake yi na ɗaiɗaita Jihar Benue ba zai yi nasara ba," a cewar sanarwar.

  "A kwanan nan aka kashe ɗaya daga cikin 'yan uwan wani tsohon gwamnan jihar. Wajibi ne a kawo ƙarshen iirin wannan aikin na tashin hankali bisa kowane irin dalili domin kashe mazauna Benue."

 13. Tarihin Sayyada Rabi'atu Haruna da abincin da ya kamata a ci lokacin zafi

  Video content

  Video caption: Danna hoton sama ku saurari shirin Amsoshin Takardunku

  Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambaya game da tarihin Sayyada Rabi'atu Haruna, mawaƙiyar yabon Annabi wadda ta rasu a makon da ya gabata.

  Sai kuma tambaya kan abincin da ya kamata a ci lokacin zafi.

  Fauziyya Kabir Tukur ce ta gabatar da shirin. A yi saurare lafiya.

 14. Turkiyya ta kai hare-hare a Syria

  Rahotanni daga arewacin Syria na cewa wani jirgin saman sojan Turkiya ya kai harin bam kan wuraren da galibin mayakan sa-kai na Kurdawa ke rike da su.

  Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin dan Adam ta Syria ta ce an kai harin ne a wani kauye da ake kira Saida kusa da Ain Issa.

  Wannan ne kutse na farko da sojojin Turkiya suka yi zuwa cikin kasar cikin wata 17.

  Babu wasu rahotannin asarar rayuka kawo yanzu.

  Sumamen ya biyo bayan wasu rikice-rikice a yankin tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Turkiyya.

 15. Kuɗin makamai: Hafsoshin tsaron Najeriya za su bayyana gaban Majalisar Wakilai

  Hafsoshin tsaro

  Kwamitin gaggawa da aka kafa domin bincikar kuɗaɗen sayen makamai da amfani da su na Majalisar Wakilan Najeriya ya gayyaci hafsoshin tsaro da sauran shugabannin tsaron ƙasar.

  Shugabannin tsaron za su yi bayani ne game da sayowa da kuma inda aka kwana wajen rabawa da amfani da makaman da aka sayo ɗin a gobe Litinin.

  Jaridar Punch ta Asabar ta ruwaito cewa Kwamitin Tsaro na Majalisar ya gana da Ma'aikatar Tsaro kan kuɗi dala biliyan ɗaya - naira kusan biliyan 400 - da aka ware don sayo makamai a 2017, waɗanda daga cikinsu ne aka biya kuɗin jiragen Super Tucano guda 12 a Amurka.

  Wannan bincike ya biyo bayan kalaman da mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya yi ne a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce ba su san inda kuɗin makaman suka shiga ba.

  Kalaman nasa sun tayar da muhawara tsakanin 'yan Najeriya, ganin cewa ba wannan ne karon farko da aka zargi shugabannin tsaron da sace biliyoyin kuɗin makaman ba.

  Shugaban kwamitin, Olaide Akinremi, ya faɗa wa Punch cewa bayan zamansu na farko sun yanke shawarar bincikar kuɗaɗen makaman cikin shekara 10 da suka wuce kuma hafsoshin tsaron za su bayyana gaban majalisar a gobe Litinin.

  An bayar da odar makaman ne a ƙarƙashin tsoffin hafsoshin tsaro, waɗanda Buhari ya sauke ranar 26 ga watan Janairu kuma ya maye gurbinsu da wasu.

 16. An ci gaba da zanga-zanga da dukuduku a Myanmar

  Myanmar

  Daruruwan mutane a birni na biyu mafi girma a Myanmar wato Mandalay, sun gudanar da zanga-zanga da sanyin Asubahi a kan tituna kafin fitowar rana.

  Da yawa daga cikinsu na sanye da fararen rigunan likitoci.

  Zanga-zangar ta biyo bayan kunna fitulun nuna alhinin mutuwar mutane sama da 200 da jami'an tsaro suka kashe tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan jiya.

  A babban birnin Yangon, jami'an tsaro sun yi amfani da karfi don tarwatsa masu zanga-zanga, sannan an tsare wasu da dama daga cikinsu.

  Har yanzu dai babu labarin inda aka yi da wakilin BBC Aung Thura, da aka sace a babban birnin kasar.

  Kusan mutum 100 aka kashe tun bayan fara rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabarairu.

 17. Jihar Ekiti za ta kori makiyaya da manoman da ba su yi rajista ba

  Fulani makiyaya

  Gwamnatin Jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya ta bai wa makiyaya da manoma ƙarin mako biyu da su yi rajistar ayyukansu da gwamnati ko kuma ta kore su daga jihar.

  Wa'adin ya fara aiki ne daga yau Lahadi, 21 ga Maris.

  Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa tun a watan Fabarairu aka fara yi wa manoma da makiyayan rajista, sai dai wasu da dama ba su yi ba.

  Kwamishinan Harkokin Noma Dr Olabode Adetoyi ya faɗa cikin wata sanarwa a jiya Asabar cewa ana yin aikin rajistar cikin gaggawa saboda a ƙididdige yawan masu sana'o'in biyu.

  Ya ƙara da cewa an fito da yin rajistar ce saboda a tabbatar da zaman lafiya tsakanin rukunin mutanen biyu, waɗanda ke kashe juna a rikice-rikice.

  Kazalika, kwamishinan ya bayyana cewa rikici tsakanin manoma da makiyaya barazana ce ga wadata jihar da abinci, "kuma abin da ya sa kenan muka ɗauki matakan daƙile shi".

 18. Dubban Turawa na zanga-zangar yaƙi da dokokin kulle

  Turai

  Dubban mutane sun shiga zanga-zanga a fadin Turai don neman a kawo ƙarshen dokokin kullen korona.

  A garin Kassel na Jamus, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da suka taru.

  A Hyde Park da ke Landan, an tilasta wa jami'an 'yan sanda gudu zuwa ga motocinsu, yayin da masu zanga-zangar ke jefan su da kwalabe.

  Sai dai yawancin kasashen Turan na duba yiwuwar kara tsaurara dokar ne maimakon janye ta saboda samun karuwar masu kamuwa da cutar.

  Wakilin BBC ya ce mutane da dama a fadin Turai na ci gaba da nuna damuwa a kan jan kafa wajen yin rigakafin korona a nahiyar, har ta kai ga abin na neman fin karfin gwamnatocin wasu kasashe.

 19. Cutar korona a Najeriya: Mutum 3 sun mutu, 112 sun kamu ranar Asabar

  Korona

  Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 112 da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Asabar.

  Bisa sabbin alkaluman hukumar, cutar ta sake kashe mutum uku.

  Jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohi 35 da mutum 46 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

  Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 22 a Babban Birnin Tarayya Abuja, da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

  A Ondo, an samu mutane 17 da suka kamu, dai Kaduna ma mutum 9, da kuma jihar Ebonyi da aka samu mutum 9, da gwajin da aka yi musu ya tabatar da cewa sun kamu da cutar ta korona.

  Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi:

  • Bauchi-6
  • Kebbi-4
  • Delta-2
  • Osun-2
  • Jigawa-2
  • Borno-1
  • Edo-1
  • Kano-1
  • Nasarawa-1

  Kazalika cikin kwana ɗayan, an sallami masu cutar 70 daga cibiyoyin da suke kwance a Legas.

  Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 161,651, sannan an sallami 147,775jumulla, baya ga mutum 2,030 da suka mutu kawo yanzu.

 20. Assalamu Alaikum

  Maraba da sake haduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da ni Umar Mikail.

  Ku biyo ni domin sanin yadda duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da makotansu.