Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muke bankwana da ku sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. A huta lafiya.

 2. Facebook ya toshe wasu gungun masu kutse ta intanet

  facebook

  Kamfanin Facebook ya bayyana cewa ya toshe wasu gungun masu kutse ta intanet a China waɗanda suka yi ƙoƙarin yin leƙen asiri ga ƴan gwagwarmaya da ƴan jarida ta hanyar saka musu manhajar leƙen asiri a na'urorinsu.

  Kamfanin na Facebook ya ce gungun masu kutsen wanda aka fi sani da Earth Empusa ko kuma Evil Eye.

  A cewar kamfanin sun yi niyyar kutsen ga kusan mutum ɗari biyar kuma akasarinsu waɗanda aka so yi wa kutsen, ƴan ƙabilar Uighur ne daga yankin Xinjiang na China waɗanda suke zama a ƙasashen ƙetare.

  Kamfanin na Facebook ya ce masu kutsen sun ɓullo da wata hanyar yaudara, inda suka fake a matsayin ƴan jarida da ɗalibai da masu kare haƙƙi, inda suka yi ƙoƙarin ƙulla abota da waɗanda suke hari.

 3. An saki fursunonin da ake riƙe da su a Myanmar

  An saki sama da mutum 600 da aka kama aka rufe a gidan yarin Yangon na Myanmar, bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar a watan da ya gabata .

  Babu wani tabbaci kan dalilin da ya sa aka saki mutanen baki ɗaya, sai dai wani ɗan jarida mai ɗaukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AP wanda aka kama a watan na Fabrairu, ya ce an wanke shi daga duka zarge-zargen da ake yi masa.

  Wani lauya kenan yake cewa an ware ɗalibai daban da ƴan jarida a cikin gidan yarin. Kuma ba a azabatar da ɗalibai ba, amma akwai yiwuwar an azabtar da wasu mutane daban.

  Sama da mutum dubu biyu aka kama tun bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamnatin shugaba Aung San Su Chi.

 4. Yadda 'wata uwargida ta kashe' amarya mai kwana 54 a jihar Neja

  POLICE

  Rundunar 'yan sandan jihar Neja a Najeriya ta tabbatar da kisan da wata mata ta yi wa kishiyarta mai suna Fatima wacce ba ta cika watanni biyu da auren ba ta hanyar duka da ƙona ta.

  Kwamishinan 'yan sandan jihar Mohammed Adamu ya shaida wa BBC cewa, sun samu labarin ne bayan da mijin matar mai suna Aliyu Abdullahi ya kai musu rahoto kan faruwar lamarin inda ya ce ya shiga gida ya taras an kashe amaryarsa.

  Kuma in ji shi, binciken da suka gudanar ya nuna cewa an yi ta dukanta da taɓarya ko wani abu mai ƙarfi ne kafin a ƙona ta "don nuna cewa ta mutu ne a sakamakon gobara."

  Tuni dai aka yi jana'izar marigayiyar a gidan iyayenta da ke Katsina.

  Shiga nan don karanta cikakken labarin

 5. Ana samun ƙaruwar fyade da Boko Haram ke yi wa yara mata da manya a Najeriya - Amnesty

  BH

  Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty ta ce ana samun ƙaruwar aikata laifukan fyaɗe da Boko Haram ke yi wa yara mata da manya, kuma hakan abin damuwa ne sosai.

  Amnesty ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan matsalar.

  Ƙungiyar a wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba, ta ce "mayakan Boko Haram sun addabi mata da ƙananan yara suna cin zarafinsu da lalata".

  Sabon binciken da Amnesty ta wallafa ya ce laifukan da mayaƙan ke yi ba shi da maraba da aikata laifukan yaƙi a arewa maso gabashin Najeriya.

  View more on twitter
 6. Tinubu ya bai wa ƴan kasuwar Katsina tallafin N50m bayan sun yi gobara

  TINUBU

  Jagoran jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu ya bai wa ƴan kasuwar Katsina tallafin naira miliyan 50 sakamakon gobarar da suka yi a ranar Litinin.

  Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan wanda ya kai ziyara Katsina a wannan rana ta Laraba ya ƙarfafawa ƴan kasuwar gwiwa kan kada su karaya da gobarar.

  An dai tafka asarar bilyoyin naira baya ga shagunan da suka kone.

  Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da bincike domin gano musababbin gobarar.

 7. Ƴan sanda sun kama mutum 34 da sata a kasuwar da ta yi gobara a Katsina

  kwamishinan yan sandan Katsina

  An kama wani mutum da aka ce malamin Islamiyya ne mai shekara 43, cikin mutum 34 da ƴan sanda suka kama a yammacin Laraba kan laifin sata a kasuwar da aka yi gobara a Katsina.

  Jaridar Punch ta rawaito cewa matar malamin ce ta kai shi ƙara, bayan fuskantar cewa ya wawushe kaya kuma ya ɓoye a ƙarƙashin gado.

  Kakakin ƴan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce hakan ne ya kai ga kama mutumin mai suna Muhammad Abba.

  Sauran mutanen da aka kama tare da malamin ƙananan yara ne da suka wawushe kayayyaki irinsu na sawa da amfanin gida da janereto da dai sauransu.

  Yanzu haka dai suna fuskantar tuhuma a wajen ƴan sanda.

  A ranar Litinin ne dai gobara ta tashi a babbar kasuwar Katsina, abin da ya kai ga tafka asarar dumbin dukiya.

 8. Mutane za su iya sayen motar Tesla da Bitcoin, in ji Elon Musk

  TESLA

  Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, ya ce daga yanzu mutane na iya sayen motar da yake ƙerawa da kuɗin Bitcoin.

  Musk ya sanar da hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  Yana cewa,"Daga yanzu kuna iya sayen Tesla da Bitcoin," a ɗaya daga cikin sakonninsa.

  View more on twitter

  Sannan ya yi ƙarin haske cewa Tesla zai dinga adana kuɗin da ya karba daga kwastamominsa a matsayin Bitcoin, maimakon ajiyar kuɗin a takarda kamar yada ake yi a yanzu a al'adance.

  Wadannan bayanai sun fito ne adaidai lokacin da Mista Musk ke nuna goyon-bayansa kan amfani da kuɗin intanet wato cryptocurrency a watan Janairun da ya gabata, bayan sauya bayanansa na Twitter zuwa “#bitcoin”.

 9. Farashin buhun shinkafa ya sauko a Najeriya saboda matakan CBN - Emefiele

  RICE

  Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce farashin buhun shinkafa ya ragu idan aka kwatanta da yadda aka rinƙa sayarwa a bara lokacin kullen korona.

  Ya ce an samu sauƙi saboda matakai daban-daban da babban bankin wato CBN ya bijiro da su domin daidaita tattalin arzikin ƙasar.

  Ko da yake CBN ya ce tsadar da shinkafar ta yi a bara na da alaƙa da ƙarancinta saboda rububin saye da tanada saboda fargabar zaman gida na tsawon lokaci.

  Yanayin da aka shiga a lokacin kullen korona da yunwa da galibin mutane suka shiga ya haddasa kai hare-hare da wawushe abinci a rumbun ajiyar gwamnati da ke sassa daban-daban na wasu jihohin Najeriya.

 10. Farashin ɗanyen man fetur ya ƙaru a kasuwannin duniya

  Farashin ɗanyen man fetur ya ƙaru a kasuwannin duniya sakamakon fargabar yankewar samar da man, bayan wani ƙaton jirgin dakon mai ya tsaya a mashigar tekun Suez.

  Kusan kashi goma cikin ɗari na kasuwar duniya, ciki har da ɗumbin ɗanyen mai na wucewa ne ta mashigar tekun.

  A yanzu dai jirgin ya kawo cikas ga sauran jirage da za su bi ta mashigar domin babu wata hanyar da za su iya bi su wuce.

  Mashigar dai hanya ce mai muhimmanci ta jigilar kayayyaki ta ruwa daga Turai zuwa nahiyar Asia.

 11. Bola Tinubu ya kai wa sarkin Katsina ziyara

  Tinubu

  Jagoran jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman a wannan Larabar.

  Ya kai ziyarar ce da rakiyar gwamna Bello Masari na Katsinar da wasu manyan jiga-jigan siyasa.

  Daga fadar Katsinar, Tinubu ya ziyarci babbar kasuwar Katsina, inda gobara ta laƙume shaguna 100 a ranar Litinin.

  Ya yiwa ƴan kasuwar jaje da kuma kai musu gudunmawa.

  Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Tinubun ya ziyarci Katsinar ne bayan samun rahotannin saɓanin tsakaninsa da shugaba Buhari.

  Jaridar ta kuma rawaito cewa duk da cewa bai fito ƙarara ya shaida anniyarsa ba, akwai alamomi masu ƙarfi da ke nuna cewa yana son ya gaji shugaba Buhari.

 12. JAMB ta sanar da ranar da za a soma rijistar jarrabawar UTME ta 2021

  Hukumar JAMB ta sanya ranar 1 daga watan Afirilu dan fara yi wa dalibai da ke son samun gurbin karatu a jami'o'in kasar rijista, an kuma tsara yin jarabawar a tsakanin 5 da 19 na watan Yuni.

  Hukumar wadda ke da alhakin tsarawa da shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare, ta dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ranar 22 ga watan Maris.

  Wannan na kunshe a cikin sanarwar da JAMB ta fitar, dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin.

  Sannan hukumar ta ce ya zama wajibi ga dukkan daliban da suke son yin rijista dan zana jarabawar, su tabbatar sun mallaki lambar NIN ta dan kasa.

 13. 'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai da dama a Neja

  Rahotanni daga jihar Niger da arewa ta tsakiyar Najeriya na cewa `yan bindiga sun kashe `yan sa-kai ko `yan banga akalla talatin a wata arangamar da suka yi a yankin Kwatankwaro da ke karamar hukumar Mariga.

  Jami`an tsaro dai ba su tabbatar da maganar harin ba, amma nazauna yankin sun ce an gano gawar mutum ashirin.

  Honourable Ibrahim Iliyasu shi ne mai wakiltar Mariga a majalisar dokokin jihar Niger, ga kuma karin bayani da ya yi wa Ibrahim Isa, kamar yadda za ku ji idan kuka latsa hoton da ke kasa:

  Video content

  Video caption: 'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai da dama a Neja
 14. An zargi sojojin Eritrea da kisan fiye da mutum 100 a yankin Tigray

  Birnin Aksum

  Hukumar kare hakkin dan adam ta Habasha ta zargi sojojin Eritrea da kisan sama da farar hula 100 a birnin Aksum da ke yankin Tigray a karshen watan Nuwambar bara.

  Binciken da aka gudanar tsakanin 27 ga watan Junairu zuwa watan nan, ya biyo bayan kwanaki biyu da aka dauka ana kisan kare-dangi a birnin, wanda mabiya addinin Kirista na gargajiya ke wa kallon tsarkakakke.

  Wani ganau ya shaida wa BBC yadda aka zubar da gawawwaki a kan tituna ba tare da an yi musu sutura ba, yawanci kuraye sun fara cin namansu.

  Hukumar ta ce cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai mazauna birnin Aksum, da masu kawo ziyarar addini da suka je bikin addini na shekara-shekara da ake yi.

  Shi ma wani ganau ya shaida wa hukumar kare hakkin dan adam ta EHRC, yadda wani sojojin Eritrea suka shiga gidan wani tsoho mai shekara 70, suka fito da shi tare da 'ya'yansa maza biyu, suka kai su kusa da wata tankar yaki da ke kusa da wajen, tare da umartar su kwanta a kasa.

  "Sojojin sun kashe su, ta hanyar harbinsu da bindiga a kai," in ji hukumar.

  Shi ma wani mutum na daban, ya bayyana yadda aka kashe wasu magidanta a gaban 'ya'yansu da matansu da kuma iyayensu mata.

  An kuma zargi sojojin kasashen Habasha da Eritrea da sace-sace, da lalata gine-gine ciki har da asibitoci da wuraren ibada.

  Hukumar wadda ta wallafa rahoton a shafinta na Tuwita, ta bukaci a hukunta wadanda suka take hakkin dan adam.

  View more on twitter

  Kawo yanzu hukumomin Eritrea ba su mayar da martani kan wannan zargi ba.

  A lokacin da rahoton hukumar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta fitar da rahoto kan kashe-kashen a ranar 26 ga watan Janairu, gwamnatin Eritrea ta yi watsi da shi tare da cewa ba shi da tushe bare makama.

  Wadanda Amnesty ta zanta da su, sun ba da sunayen sama da mutum 200 da suka san ana kashe su a wannan lokacin, wasu da daga ciki da suka taimaka wajen binne mamatan sun ce sun haura 800.

 15. Ana samun karuwar cin hanci a Somalia

  Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Somali ta ce cin hanci da rashawa na karuwa a kasar.

  Wani sabon rahoto da hukumar mai suna Marqaati ta fitar, ya nuna cewa 50 cikin 100 na mazauna birnin Mogadishu da aka zanta da su, sun ce sun bayar da cin hanci a shekarar da ta wuce.

  Haka kuma kashi 14 cikin 100 a sauran sassan kasar su ma suka bayar da cin hanci, wasu daga ciki kan bayar da na goron akalla sau daya a kowanne mako.

  Yawancin an bai wa sojojin yankin Mogadishu da hukumomin birnin cin hancin.

  Haka kuma, rahoton ya sanya kungiyar al-Shabab da jami'an tsaron kasar a cikin jerin wadanda suka karbi na goron.

  A karshe rahoton na Marqaati, ya nuna an samu karuwar cin hanci da rashawa a wuraren da ayyukan gwamnati a kasar Somalia.

 16. Minti Daya Da BBC Na Rana

  Yusuf Yakasai da Badriyya Kalarawi ne suka karanto Labarai Cikin Minti Daya Da BBC Na Rana 24/03/2021.

  Video content

  Video caption: Minti Daya Da BBC Na Rana 24/03/2021
 17. Gobara ta yi barna a kasuwar Kousseri da ke Kamaru

  Kasuwar Kousseri

  Rahotanni daga birnin Kousseri da ke yankin Arewa Mai Nisa a Jamhuriyar Kamaru sun nuna cewa shaguna 230 ne suka kone sanadin wata gobara da ta tashi a kasuwar birnin ranar Talata.

  Waklin BBC a Yaounde ya ce duk da yake a hukumance ba a bayyana musabbabin abin da ya haddasa wannan gobara ba, amma kuma 'yan kasuwa na zargin maido da wutar lantarki da karfi da kamfanin raba wutan lantarki (ENEO) ya yi ne ya janyo musu wannan asara na kaddarori.

  Kasuwar ita ce mafi girma a yankin.

  Rahotanni sun nuna cewa ba a samu asarar rayuka ba, kodayake sai da hukumomi a birnin Kousseri suka nemi agajin sojojin kasar Chadi da suka shigo suka dafa wa takwarorinsu na Kamaru baya domin kashe ta.

  A karo na 5 kenan cikin shekaru 6 gobara take tashi a cikin babbar kasuwar Kousseri da ke kan iyakar Kamaru da Chadi.

  Kasuwar Kousseri
 18. An bai wa Zulum shawara kan yadda zai bunkasa karatun allo

  Kwamitin da gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta kafa domin ba ta shawara kan sauya tsarin karatun allo ya mika wa Gwamna Babagana Umara Zulum rahoto kan hakan a ranar Talata.

  A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Isa Gusau ya aike wa manema labarai, ya ce Zulum ya karbi rahoton mai shafi 76, wanda ya ba da shawarar samar da kyakkyawan tsari da gyara makarantun Tsangaya.

  Ya ambato shugaban kwamitin Khalifa Aliyu Ahmad Abulfatahi yana mai cewa ya kamata wata hukuma ta aiwatar da shawarwarin da suka bayar ciki har da tsare-tsaren gwamnati kan makarantun allo.

  Tun a watan Nuwambar bara, gwamnatin jihar Borno ta kafa kwamitin da ya kunshi malaman addinin musulunci na dukkan bangarori.

  Gwamna Zulum ya ce gwamanti za ta hada kai da hukumar kula da makarantun gwamnati na fasa, domin ganin an hada tsarin karatun Tsangaya da na Boko, ta yadda dalibai za su jefi tsuntsu biyu da dutse daya.

  Zulum
 19. Sojoji 'sun mamaye birnin Onitsha domin kama bata-gari'

  Rahotanni daga jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya na cewa hankula sun tashi a birnin Onitsha bayan da sojoji suka mamaye wasu sassan birnin domin laluben bata-gari da tabbatar da tsaro.

  Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an aike sojoji wasu garuruwa domin kamo wasu da ake zargi da hannu da garkuwa da mutane da kisan jami'an tsaro da fara hula a baya bayan nan.

  A ranar Lahadin da ta gabata Gwamna Willie Obiano ya bai yi kira ga jami'an tsaro, da matasa da 'yan banga da shugabannin al'umma su tashi tsare domin yaki da karuwar tashe-tashen hankula da matsalar tsaro a jihar.

  A makon jiya ne 'yan bindiga suka kai hare-hare kan ofisoshin 'yan sanda, tare da kashe wasu daga ciki da yin awon gaba da bindigogi da alburusai.

  A baya-bayan nan, an samu ƙaruwar kai wa ƴan sanda hare-hare a yankin jihohin Ibo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

  Sojojin Najeriya
  Image caption: Sojojin Najeriya
 20. Majalisun dokokin Najeriya sun amince a kafa jami`ar aikin gona da fasaha a Funtua

  Majalisun dokokin Najeriya sun zartar da kudurin dokar da ke neman kafa jami`ar aikin gona da fasaha a Funtua dake jihar Katsina. Tuni majalisar dattawa da takwararta ta wakilai sun amince da kudurin. Yanzu bangaren zartarwa ake jira domin tabbatar da kafa jami`ar.

  Senata Bello Mandiya shi ne ya gabatar da kudurin, kuma ya yi wa Ibrahim Isa karin bayani, kamar yadda za ku ji idan kuka latsa hoton da ke kasa:

  Video content

  Video caption: Majalisun dokokin Najeriya sun amince a kafa jami`ar aikin gona da fasaha a Funtua