Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibbiyar mu a wannan makon da haka zamu yi bankwana da ku sai kuma gobe Alhamis da yardar Allah. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.

 2. Shugaban harkokin Turai ya yi alla-wadai da ci gaba da takurawa al'ummar Belarus

  Josep Borell

  Shugaban harkokin wajen Tarrayar Turai, Josep Borrell, ya yi alla-wadai da abin da ya kira ci gaba da takura wa al'ummar ƙasar Belarus.

  Mista Borell ya koka matuƙa kan yadda ake ci gaba da musgunawa masu kare haƙƙin bil adama da kuma ƴan jarida a ƙasar.

  Ana dai ci gaba da kama waɗanda ke caccakar Shugaban Belarusa Alexander Lukashenko a duk lokacin da ƴan adawa suka fito zanga-zanga.

  Sai dai da alamu mutane ba su fito zanga-zangar sosai ba a ranar tunawa da samun ƴancin kan ƙasar, inda aka jibge jami'an tsaro masu ɗumbin yawa a ƙasar.

 3. Sojoji sun ƙaddamar da hari kan mayakan jihadi a Mozambique

  Sojojin Mozambqiue sun ƙaddamar da hari kan mayaƙa masu iƙirarin jihadi a arewacin garin Palma, garin da ake katafaren aikin iskar gas.

  A jiya Laraba ne dai masu iƙirarin jihadin suka kai hari a garin inda suka tilasta wa jama'a guduwa cikin daji.

  Harin da a yanzu sojojin suka kai wa mayaƙan na zuwa ne jim kaɗan bayan kamfanin mai na Total ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da aikin ginin matatar gas da za ta lashe kuɗi har dala biliyan ashirin.

  Tun a watan Janairu aka samu aka tseratar da ma'aikatan kamfanin Total daga yankin sakamakon yawan hare-hare

 4. Jami'in gwamnatin Saudiyya ya musanta zargin Agnes Callamard kan kisa

  AGNES

  Wani Jami'in gwamnatin Saudiyya, ya musanta zargin da ake yi masa da yin barazanar kashe Agnes Callamard- wata ƙwararriya daga Majalisar Dinkin Duniya da ke bincike kan kashe ɗan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi.

  Shugaban hukumar kare haƙƙn bil adama ta Saudiyya Awwad Alawwad, ya bayyana cewa Ms Callamard da kuma jami'an majalisar dinkin duniya sun kafe a kan ya yi wanan barazanar, amma a cewarsa, ba zai iya tuna me suka tattauna ba, amma ko alama bai yi wa wani jami'i barazana ba.

  Ms Callamard ta bayyana cewa wani jami'i a watan Janairun bara ya shaida mata cewa za a yi maganinta idan ba ta janye zarge-zargen da take yi na kisan Jamal Khashoggi ba.

 5. Ganduje zai tilastawa masu hali su rinƙa biyan kuɗin zakka a Kano

  Ganduje

  Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin mutum 11 da zai tabbatar kowanne ɗan jihar mai hali da kamfanoni sun biya kuɗin zakka ga mabuƙata.

  Jaridar Solacebase a Najeriya ta ce an ɗau wannan matakin ne ƙarkashin hukumar zakka da hubusi wanda shugabanta, Sheikh Usman Yusuf, ya ƙaddamar.

  A cewar hukumar ɗaukan wannan mataki ya zama wajibi, la'akari da ƙaratowar lokacin watan Ramadan da buƙatar taimakon mabuƙata.

  Babban darakta a hukumar zakka, Alhaji Safiyanu Abubakar, ya ce matakin zai rage talauci da halin babu da galibi ake fama da shi.

  Sannan ya ƙara da cewa gwamna Abdullahi Ganduje a nashi hubbasar da kawar da talauci a jihar Kano ya aminta da naɗin wannan kwamitin da soma aikinsu cikin gaggawa

 6. Me yake jawo gobara a kasuwannin Najeriya kuma yaya za a magance ta?

  Gobara

  Ƴan Najeriya sun jima suna nuna damuwa kan rashin tsari da ingantaccen kayayyakin kashe gobara a ƙasar, sai dai a yanzu damuwar ta koma kan ƙaruwar da ake samu na tashin gobara a kasuwannin a wasu jihohin da dama da ke jawo asarar ɗumbin dukiyoyi da ƙadarori.

  Masana dai na ganin bai kamata a ce a ko da yaushe ana yawaita samun irin wannan gobarar ba a ƙasar da ake ganin ita ce kan gaba wajen yawan al'umma da ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.

  Kusan kowacce jiha ta fuskanci mummunan iftila'in gobara a kasuwanninta. Kama daga Jihar Legas zuwa Maiduguri da Kano da Onitsha da Sokoto, labarin a ko da yaushe iri guda ne - asarar ɗmbin dukiyoyi da ƙadarori wani lokaci har da rasa rai.

  Karuwar irin wannan gobara na sake hadasa damuwa musamman tsakanin ƴan kasuwa da ke asarar arziki mai tarin yawa. Irin wannan asarar ana jimawa ba a manta ba kuma tasirin na ɗaukar tsawon shekaru.

  Karanta cikakken labarin anan.

 7. Rikicin manoma da mikiyaya ya raba mutum dubu 300 da gidajensu a Najeriya - Bincike

  MAKIYAYA

  Wata ƙungiyar bincike mai zaman kanta Zinariya Consult ta ƙiyasta cewa sama da mutum dubu 300 sun rasa muhallansu a jihohi 4 na ƙasar sakamakon rikicin manoma da makiyaya a faɗin Najeriya.

  Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa ɗaya daga cikin jagororin binciken, Dr Joseph Ochogwu, ne ya shaida hakan a wani taron tattaunawa da manema labarai.

  A cewar Ochogwu in ji jaridar, jihohin da ke fuskantar ƙaruwar irin wannan rikici sun hada da Benue da Plateau da Nasarawa da Taraba da Adamawa da Kaduna.

  Wannan yanayi da ake ciki ya haifar da rasa rayuka da asarar dukiyoyi da raba dubbai da muhallansu.

 8. Jamus na duba yiwuwar mayar wa Najeriya ɗaruruwan kayayyakin tarihinta da aka sace

  BENIN

  Ƙasar Jamus ta ce tana duba yiwuwar mayar wa Najeriya ɗaruruwan kayayyakin tarihi na ƙira da sassaƙa da aka sace tun fiye da shekaru ɗari da suka gabata - daga masarautar Benin wadda a yanzu ke kudancin Najeriya.

  Kayayyakin fasahar al’adun gargajiyar da aka ƙera da tagulla, turawan mulkin mallaka ne suka wawashe su a lokacin da suke ƙoƙarin shimfida mulkinsu a Afirka, amma a shekarun baya-bayan nan ana ta kiraye-kirayen a maida su wurarensu na asali.

  Jamus ta bayar da sanarwar duba yiwuwar mayar da kayayyakin ne yayin da Jami’ar Aberdeen da ke Burtaniya ita ma ta ce za ta mayar da wata sassaƙar tagullar ga Najeriya nan da makwannni.

  Ishaq Khalid ya tuntubi Jakadan Najeriya a Jamus, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar domin jin yadda su ke kallon matakin na gwamnatin Jamus.

  Video content

  Video caption: Ambasada Yusuf Maitama Tuggar
 9. Za a iya janye tallafin man fetur a kowanne lokaci - NNPC

  Mele Kyari

  Shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, Mele Kyari ya ce gwamnatin na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur.

  Kyari ya fadi hakan ne a taro na musamman da ministoci ke yi wa maneman labarai bayani karo na biyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Najeriya a Abuja.

  Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kyari ya ce, a maimakon ƴan ƙasar su dinga sayen mai kan yadda farashin kuɗaɗen shigo da adana shi suke na naira 234 kan kowace lita guda, gwamnati na sayar da man a kan naira 162, don haka ita ke ɗaukan nauyin cikon kuɗin.

  Sai dai ya ƙara da cewa, NNPC ba zai iya ci gaba da asarar waɗanan kuɗaɗe ba, don hakan ƴan Najeriya nan bada jimawa ba za su koma sayen man yada aka samo shi.

  Ya kuma shaida cewa dole ne a bar kasuwa ta ƙayyade yada farashin mai zai kasance a ƙasar.

 10. An ƙayyade yawan mutanen da za su iya zuwa Dubai daga Najeriya a kowanne mako

  DUBAI

  Hadaddiyar Daular Labarawa wato UAE ta gindaya sabbin sharuɗɗa da adadin ƴan Najeriya da za suke shiga ƙasarta kafin jiragenta su ci gaba da jigilar fasinjoji tsakanin Najeriya da Daular.

  Jaridar Punch ta Najeriyar ta rawaito cewa ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja ne ya shaida hakan a wasiƙar da ya aike wa ma'aikatar harkokin wajen Najeriya.

  Daga cikin sabbin sharuɗɗan nata, kamar yadda yake ƙunshe a wasiƙar, ƴan Najeriya 200 kawai za ake bari su shiga ƙasar a kowanne mako biyu.

  A cikin watan Fabrairu UAE ta dakatar da jigilar fasinjoji daga Najeriya zuwa ƙasar bayan samun rashin jituwa a kan tsarin yin gwajin annobar korona a filayen jiragen samanta ga masu shirin shiga ƙasar, saboda ba ta amince da takardun shaidar gwajin da ake yi a Najeriya ba.

  Wannan dalilin ya sanya birnin Dubai haramta wa jiragen Najeriya shiga ƙasar na tsawon makonni.

  UAE dai na karɓar baƙuncin dubban ƴan Najeriya da kan shiga ƙasar don yawon shaƙatawa.

  Ko a watan Janairun da ya gabata hukumomin ƙasar sun tsawaita bizar masu yawon bude ido ciki har da na Najeriya da tsawon wata guda.

 11. An tura likitoci makarantar da kwalara ta bulla bayan kashe daliba ɗaya

  Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta aike da likitoci 10 tare da wasu jami'an lafiya zuwa makarantar gwamnati ta 'yan mata da ke Mabera domin shawo kan cutar kwalara da ta bulla.

  Yarinya ɗaya ta rasu sanadiyyar wannan annoba.

  Kwamishinar kimiyya da fasaha ta jihar, Dakta Kulu Haruna ta ce, ɗaukin gaggawar da aka kai makarantar ya taimaka wajen shawo kan cutar.

  "Tuni aka killace duka daliban da suka kamu da wannan cuta domin daƙile yaɗuwarta," In ji Kulu.

  Yanayin da daliban suke a yanzu ba shi da matsala, in ji ta.

  An yi amannar cewa cutar ta fara ne kwanaki biyu baya, abin da ya tilsatawa makarantar mayar da ɗaya daga cikin dakunan karatunta wurin killace marasa lafiyar.

 12. An kama taba sigari ta sama da biliyan daya da ta lalace a jihar Kano

  Video content

  Video caption: Ga karin bayanin Baffa Babba Dan agundi ya yi wa wakilin BBC

  Gwamnantin Kano da ke arewacin Anjeriya ta ce ta kama taba sigari da wa'adinta ya kare ta sama da naira biliyan 1.

  Shugaban riko na hukumar kare hakkin masu siyen kayan a Kano Baffa Babba Dan Agundi ne ya shaida wa BBC cewa sun shafe kwanki biyu suna kwaso tabar daga inda aka boyeta a anguwar sharada da ke jihar.

  Hakan ya sa suka ta baiwa dukkan ‘yan kasuwar dake jahar mako guda domin su fito da kayan da wa’adin amfaninsu ya kusa karewa, ko kuma su fuskanci fushinta.

  Baffa Babba yace tabar sigarin da suka kama kiyasin kudinta ya kai sama da naira biliyan 1, wanda yanzu haka suna ci gaba da bincike, da gano ainihin mai wannan kaya da aka kama.

  Wanna dai na zuwa ne mako guda bayan samun bullar wata cuta da ba'a kai ga gano ta ba, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane uku, tare da kwamtar da mutane sama da dari 200 a asibiti, bayan shan wani lemo da ake zargin waa’adin amfaninsa ya kare.

 13. 'Yan bindiga sun sace wata matar aure a Abuja

  BBC

  Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun dirarwa wani rukunin gidaje da da keyankin Abaji a Abuja a safiyar yau, tare da sace wata matar aure,

  Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, masu garkuwa da mutanen sun raba kansu kashi biyu ne, wasu suka afka rukunin gidaje da kuma wadanda suka kai hari kan muhallan wasu Fulani da ke yakin Kekeshi.

  Wani mazaunin rukunin gidajen da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce masu garkuwa da mutanen sun kutsa kai cikin yankin ne da misalin karfe 12 na safiyar ranar Alhamis ta jikin wata karamar kofa da yake shiga wurin.

  Yace 'yan bindigar sun raba kansu kashi-kashi ne sannan suka fara harbe-harbe ta ko ina domin su firgita jami'an tsaron da ke wurin wadanda za su iya far musu.

  Ya kara da cewa masu garkuwar sun yi kaca-kaca da tagar gidan kafin su kai ga shiga ciki su sace matar auren da suka tafi da ita.

  Mijinta ya kwashe 'ya'yanta suka boye a cikin wani bandakin gidan.

  Jaridar ta ce an tsinci kwanso harsashi a cikin gidan lokacin da wakilinta ya isa wurin.

  An gano cewa wannan harbe-haben da suka yika yi sama ya hana jami'an DSSS dake kusa da wurin karasa wa domin kai dauki.

  An kuma fahimci cewa maharan sun je ne bayan samun bayanin cewa, 'yan sintirin da ke gadin wajen ba sa nan, saboda gaza biyansu hakkinsu da mazauna rukunin gidajen suka yi.

 14. Kotu ta ɗaure Farfesa a Akwa Ibom kan maguɗin zaɓe

  GETTY IMAGES

  Wata babbar kotu a jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin Najeriya ta aike da wani Farfesa masanin kimiyyar kasa a Jami'ar Calabar, Peter Ogban, gidan yari na tsawon shekara uku kan zargin magudin sakamakon zabe.

  Ogban shi ne baturen zabe a mazabar Arewa maso Yammaci Akwa Ibom a zaben 2019.

  Ana kuma zargin shi da wallafa labarai da kuma sanar da sakamakon karya a kananan hukumomin Oruk Anam da Etim Ekpo.

  Hukumar zabe ce ta gurfanar da shi a gaban babbar kotun jihar da ke Ikot Ekpene.

  An same shi da laifin sauya sakamakon zaben domin taimakawa jam'iyyar APC mai mulki da tankware jam'iyyar PDP ta hamayya.

  A wani zama da akai yi, Farfesan ya shaida wa kotu yadda aka sauya sakamakon zaben ta yadda APC za ta samu nasara kan PDP.

 15. Labarai duniya cikin minti daya

  Video content

  Video caption: Saurari labaran duniya cikin minti daya tare da Badriyya Kalarawi da Buhari Fagge

  Wata babbar kotu a Idah ta jihar Kogi, ta daure Ocholi Edicha a gidan yari na tsawon shekara 12 da wata shidda saboda samun shi da hannu a kisan da aka yi wa shugaban mata a jam'iyyar PDP Salome Abuh.

  Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito cewa, an sami Edicha da laifin hada kai wajen aikata mugun laifi da fashi da makami da kuma laifin kisan kai.

  Jamus na yunkurin dawo wa da Najeriya wasu kayayyakin tarihi da ake kira Benin bronzes, in ji hukumomin kasar.

  An sace kayayyakin tahirin ne tun lokacin turawan mulkin mallaka daga masarautar Benin da ke kudancin Najeriya, kuma duk tsawon lokacin nan suna ajiye a wani gidan tarihi a babban birnin kasar Jamus.

  Ofishin hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da wani bayani da kwararriyar da ke jagorantar binciken kwakwaf kan kisan dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi, na zargin cewa wani babban jami'in Saudiyya ya yi mata barazana ga rayuwarta.

  Kakakin hukumar Rupert Colville ya tabbatar da cewa bayanan da aka wallafa a jaridar Guardian gaskiya ne kan barazanar da aka yi wa Agnes Callamard, cikin wani sakon email da aka turawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

  'Yan bindiga sun kai hari a jihar Tillaberi da ke Jamhuriyar Nijar mai iyaka da kasar Mali.

  Maharan sun kashe mutane da dama tare da kona azuzuwan makarantu da asibiti. Sai dai zuwa yanzu gwamnati ba ta tabbatar da labarin ba.

  Liverpool na sha'awar sake daukar dan wasan Atletico Madrid dan kasar Uruguay Luis Suarez, mai shekara 34.

  Dan wasan Atletico Madrid dan kasar Sifaniya Diego Costa, mai shekara 32, zai koma murza leda a Benfica a kakar wasa mai zuwa bayan ya cimma yarjejeniya da kungiyar ta Portugal

 16. 'Koriya ta Arewa na barazana ga zaman lafiyar duniya'

  REUTERS

  Koriya ta Arewa ta harba wasu makamai masu linzami da suka sauka a tekun Japan bayan shafe daruruwan kilomita.

  Firaministan Japan Suga Yoshihide ya kira lamarin a matsayin barazana ga zaman lafiya da keta ka'idojin Majalisar Dinkin Duniya.

  Kwamitin tsaron kasa na Koriya ta Kudu na gab da zama domin tattauna lamarin.

  Wannan ne gwajin makami mai linzami na farko da Koriya ta Arewa ta yi tun bayan da shugaba Joe Biden ya kama mulki a watan Janairu.

  A makon da ya gabata, manyan jami'an gwamnatin Amurka sun ziyarci jami'an gwamnatin Japan da Koriya ta Kudu inda suka bayyana bukatar kawo karshen shirin Nukiliyar Koriya Ta Arewa abin da Koriya ta Arewan ta bayyana a matsayin magana maras tushe.

 17. An hana buɗa-baki a masallacin Makka a lokacin azumi

  @hsharifain

  Hukumomi a Saudiyya sun ce ba za a rika yin buɗa-baki ba a masallacin maka a lokacin azumi.

  Hakan kuma ya shafi sahur da ake yi cikin jama'a a gidajen cin abinci da otel-otel, lokacin azumin na Ramadana.

  Wannan mataki na zuwa ne bayan wata tattauna wa da hukumomin kasar suka yi kan matakan da za a dauka domin kare kai da kuma mutane daga kamuwa da wannan cuta ta korona a yayin azumi da kuma bikin sallah.

  Bayan amince da wasu ma'aikatu shida suka yi da wannan mataki ne ya sa aka sanar da shi, domin duk masu aikin ibada a lokacin azumin suka kwana da sanin haka.

  Ma'aikatar kula da al'amuran cikin gida ta kasar ta ce ta haramta shan ruwa da sahur a otel, ta kuma haramta taruwar mutane da yawa a wuraren shakatawa, sannan za a kulle kananan wuraren shakatawar,a kuma samar da masu sanya idanu kan tabbatar da cewa ana aiki da wadannan dokoki.

 18. An gano abin da ya kashe sama da giwaye 330 a Botswana

  Reuters

  Hukumomin muhalli a Botswana sun ce sun kara gano gawawakin sama da giwaye 39 tun daga watan Janairu, a ci gaba da binciken da suke yi kan yawatar mutuwar giwayen da ake samu a kasar.

  Wannan karin da aka samu na mutuwar giwayen a Moremi ya sa adadin giwayen da suka mutu ya kai 330, tun daga watan Mayun bara zuwa Yuni kamar yadda rahotanni suka bayyana.

  Ma'aikatar muhallin ta ce daga wani bincike da ta gudanar ta gano cewa wata cuta ce da ke kama dabbobi ce ke janyo mutuwar dabbobin.

  Sai dai har yanzu ba a kai ga gano dalilin mutuwar wasu namun dawan a cikin dazukan kasar.

  A bara an ta yada cewa wata cuta ce da dabbobin ke dauka a ruwan da suke sha ke janyo mutuwar ta su.

 19. Mutumin da ya kashe 'yar siyasar Kogi zai sha daurin shekara 12

  Others

  Wata babbar kotu a Idah ta jihar Kogi, ta daure Ocholi Edicha a gidan yari na tsawon shekara 12 da wata shidda saboda samun shi da hannu a kisan da aka yi wa shugaban mata a jam'iyyar PDP Salome Abuh.

  Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito cewa, an sami Edicha ta laifin hada kai wajen aikata mugun laifi da fashi da makami da kuma laifin kisan kai.

  Masu gabatar da kara sun kira mutum biyar a matsayin shaidu yayin shari'ar.

  Rahotanni sun ce kotun ta amince da shaidar baki da wadanda suka ga faruwar lamarin suka bayar da kuma rahoton 'yan sanda.

  Sai dai wanda ake karar ya musanta wasu bangare na rahotan 'yan sandan, wanda daga baya kotu ta amince da shi.

  A 2019 ne, aka kashe Salome Abuh mai shekaru 60 wadda ita ce shugabar mata ta jam'iyyar PDP a mazabar Ochadamu a karamar hukumar Ofu, na barci a gidanta lokacin da 'yan dabar suka cinna wa gidan wuta daf da magariba.

 20. Jamus za ta mayar wa da Najeriya kayayyakin tarihinta da aka sace

  Getty Images

  Jamus na yunkurin dawo wa da Najeriya wasu kayayyakin tarihi da ake kira Benin bronzes, in ji hukumomin kasar.

  An sace kayayyakin tahirin ne tun lokacin turawan mulkin mallaka daga masarautar Benin da ke kudancin Najeriya, kuma duk tsawon lokacin nan suna ajiye a wani gidan tarihi a babban birnin kasar Jamus.

  Hukumar kula da kayyakin tarihi ta SPK ta ce "an yi tattaunawa mai tsayi tsakanin bangarorin biyu sama da shekaru, kan kayan tarihin".

  Misintan harkokin wajen Jamus Keiko Maas ya ce "Maganar mayar da kayayyakin tarihin na daga cikin tabbatar da amana game da tarihin mulkin mallaka da aka yi a baya. Wannan ita ce magana ta gaskiya".

  Gidan tarihin na dauke da kayayyakin tarihi 530 da aka dauka daga masarautar ta Benin, ciki har da tagulla 440 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya wallafa.