Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Mun zo ƙarshen rahotannin

  Ta faru ta ƙare an yi wa mai dami ɗaya sata!

  Ƙarshen ayyuka kenan a wannan shafin na labarai kai-tsaye a yau Lahadi.

  Mu haɗu da ku gobe domin kawo wasu labaran.

 2. 'Yan sanda sun ceto mutum 5, sun kashe ɗan fashi a Kaduna

  Makamai

  Jami'an tsaro a Jihar Kaduna sun yi nasarar ceto mutum biyar da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Birnin Gwari.

  Kwamishinan Tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya ce lamarin ya faru ne da tsakar ranar Juma'a bayan dakaru sun samu rahoton cewa wasu 'yan bindiga sun tare hanyar Birnin Gewari zuwa Kaduna.

  A cewar kwamishinan, nan take jami'an tsaro suka isa kuma suka yi nasarar tserar da mutanen bayan fafatwa da 'yan fashin.

  A wata fafatawar ta daban, jami'an sun kashe ɗan fashi ɗaya tare da kama wani bayan sun buɗe wa motar 'yan sanda wuta.

  Aruwan ya ce bincike ya nuna cewa mutanen suna ɗauke ne da makamai domin kai wa 'yan fashin daji a Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja.

  Kazalika, rundunar jami'an tsaron haɗin gwiwa ta yi nasarar ƙwato shanu 32 da tumakai 10, waɗanda 'yan bindigar suka sace a Ƙaramar Hukumar Kachia.

  View more on facebook
 3. Daga yanzu 'yan Sudan za su iya yin duk addinin da suke so

  Gwamnatin Sudan ta saka hannu kan yarjejeniyar bai wa 'yan kasar 'yancin yin addinin da suke so ba tare da muzgunawa ba.

  Wakilin BBC ya ce an ƙulla yarjejeniyar ce da ƙungiyar 'yan tawaye ta SPLM, wadda mafi yawan 'ya'yanta mabiya addinin Kirista ne da ke yankin Nuba.

  A shekarar 1983 ne tsohon Shugaba Omar Al-Bishir ya ƙirkiri Shari'ar Musulunci a Sudan.

  Ƙungiyoyi da dama a ƙasar sun sha fafutikar ganin an dawo kan turbar 'yancin gudanar da addini tun daga wancan loakci.

 4. Kano Pillars ta zama ta biyu bayan ta doke Heartland

  Rabiu Ali

  Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta doke Heartland ta garin Owerri 2-1 a wasan mako na 18 na gasar Firimiyar Najeriya.

  Sakamakon ya bai wa Masu Gida damar hawa mataki na biyu da maki 33, daidai da Kwara United ta saman teburi.

  Chidera Eze na Heartland ne ya fara zira wa Pillars ƙwallo a raga a minti na 39 kafin daga bisani Rabiu Ali ya farke ana gab da tafiya hutun rabin lokaci.

  Ana cikin minti na 9 da aka ƙara a kan 90 ne kuma Ebuka David ya ƙara ta biyu daga bugun finareti.

  Wasan wanda aka buga a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna wato gidan Kano Pillars, ya zama na 10 da ta yi nasara cikin 18 da ta buga a kakar bana ta 2020/2021.

  Sauran wasannin da aka buga a ranar Lahadi:

  • Akwa Utd 3-0 Lobi
  • Rivers Utd 1-0 Sunshine Stars
  • Plateau Utd 2-1 Rangers
  • Nasarawa Utd 5-3 Abia Warriors
  • Katsina Utd 1-2 Kwara Utd
  • Adamawa Utd 0-0 Wikki
  • Kano Pillars 2-1 Heartland
  • Wolves 3-1 FC Ifeanyiubah
  View more on twitter
 5. Jirgin dakon kaya da ya maƙale a Masar na haddasa asarar dala biliyan 9 a kullum

  Jirgin ruwa

  Katafaren jirgin ruwa na dakon kaya da ya maƙale a Tekun Suez na Masar na haddasa asarar kuɗin kayan da suka kai darajar dala biliyan tara da rabi - kwatankwacin naira tiriliyan uku da 600,00.

  Bayanan da aka tattara na dakon kaya sun nuna cewa ana asarar kasuwancin dala miliyan 400 - fiye da naira biliyan 150 - a kowace awa ɗaya bayan da jirgin mai suna Ever Given ya maƙale.

  Hakan ya faru ne sakamakon muhimmancin hanyar ruwan ga kasuwancin duniya, wadda ta haɗa yammaci da gabashin duniya.

  Masanin fiton kaya, Lloyd's List, ya ƙiyasta darajar kayan da ake yin fito zuwa yammacin duniya a kullum kan dala biliyan 5.1, yayin da waɗanda ake kai wa gabashin duniya suka kai 4.5.

  Masana sun ce za a ɗauki tsawon makonni kafin a iya ceto jirgin duk da irin ƙoƙarin da ake yi.

  Jirgin wanda kamfanin ƙasar Taiwan ya mallaka, ya kai tsawon filayen wasan ƙwallon ƙafa huɗu kuma yana ɗaya daga cikin mafiya girman jirage a duniya.

  Jirgin na ɗaukar tan 200,000 na kaya - zai iya ɗaukar kwantena guda 20,000 a lokaci guda.

  Maƙalaewar da ya yi ta sa sauran jirage ke shan wuya kafin su iya ƙetare shi.

 6. Birtaniya na shan matsin lamba daga ƙungiyoyin agaji kan rigakafin korona

  Rigakafin korona

  Manyan kungiyoyin bayar da agaji na Birtaniya sun bukaci gwamnati ta fara rarraba alluran rigakafin korona ga kasashe matalauta.

  Kungiyoyin agajin da suka haɗa da Save The Children sun ce akwai yiwuwar ɓoye allurar a Birtaniya yayin da ma'aikatan lafiya a kasashe masu tasowa ba su da su.

  Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi alkawarin raba rigakafin karkashin shirin Covax da zarar an samar da su.

  Kungiyoyin agajin na son hakan ta faru domin kawo ƙarshen annobar ta korona a duniya baki daya.

  Birtaniya na cikin ƙasashe masu bai wa shirin na Covax tallafi, wanda ya bai wa ƙasashe irinsu Najeriya da Afirka ta Kudu da Ivory Coast alluran a Afirka.

 7. Sojojin mulki sun kashe ƙarin mutum huɗu a Myanmar

  Myanmar

  Sojojin juyin mulki a Myanmar sun kutsa kai cikin wani sansani da ke Tahan a yau Asabar, inda suka kashe mutum aƙalla huɗu.

  Mazauna yankin sun bayyana cewa cikin waɗanda aka kashe har da wata mace.

  Sama da mutum 440 ne suka mutu ciki har da yara a Myanmar tun bayan kashe-kashen da aka yi a watan Fabrairu.

  Da yammacin Lahadi 28 ga Maris, aka harbi Ma Ah Khurin a ƙirji sannan aka kashe Maung San da ɗansa Chit Oo da kuma Thang Liang Han, wanda aka kashe daga baya.

  Mutanen yankin Tahan sun ce an shafe sama da awa uku ana musayar wuta tsakanin sojoji da wasu mutane.

  Wata kafar yaɗa labarai ta yankin ta ce sojojin sun isa wurin ne da manyan makamai sannan suka buɗe wuta.

  Rahotannin da BBC ba ta tabbatar ba sun ce sai wajen 8:00 na yammacin Lahadi aka daina jin ƙarar harbi sannan dakarun suka bar Tahan.

 8. Kamfanin mai na Total ya dakatar da aiki a Mozambique

  Total

  Kamfanin mai na Total ya janye kudirinsa na sake buɗe katafaren aikin samar da iskar gas a arewacin Mozambique saboda fafutukar da masu ikirarin jihadi ke yi ta mamaye yankin.

  Kamfanin na Faransa ya ce babu ɗaya daga cikin ma'aikatansa da yaƙin ya shafa.

  Dakarun kasar na ta kokarin hana 'yan bindigar da ke da alaƙa da IS ƙwace garin Palma.

  A cewar wakilin BBC, maharan sun fara kai hari ne a garin na Palma tun ranar Laraba.

  Shaidu sun ce an lalata wasu ɓangarorin garin, inda gawarwarki ke yashe kan tituna.

  Akwai rahotannin da ba a tabbatar da su ba da ke cewa 'yan bindigar sun ci karfin garin.

  Kimanin mutum 170 ciki har da ma'aikata 'yan kasashen waje ne aka kwashe daga wani otel da suka maƙale tsawon kwana uku.

 9. Jihar Neja ta sake buɗe makarantun gwamnati

  Sakandaren Kagara

  Gwamnatin Jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta yanke shawarar sake buɗe makarantun sakandare na gwamnati bayan shafe mako biyu a rufe.

  Kwamishiniyar Ilimi Hannatu Jibrin Salihu ta ce an rufe makarantun ne domin tantance yanayin tsaro a jihar biyo bayan sace ɗalibai daga sakandaren Kagara a watan Fabarairu.

  Cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, kwamishiniyar ta ce za a buɗe makarantun ne sannu a hankali.

  Sharuɗɗan bude makarantun su ne:

  • Sakandare na je-ka-ka-dawo za su koma daga Litinin, 29 ga Maris
  • Makarantun kwana da ke cikin birni za su koma ranar Talata, 6 ga Afrilu
  • Makarantun kwana waɗanda aka mayar da su na je-ka-ka-dawo da ke wuraren da babu barazanar tsaro za su koma Talata
  • An bai wa dukkan shugabannin makarantun umarnin yin aiki tare da daraktocin yankunansu domin kauce wa matsalar tsaro
  • Za a tura jami'an tsaro makarantun da ke fuskantar barazanar tsaro
  • Wajibi ne kowace makaranta ta kafa majalisar tsaro wadda za ta ƙunshi jami'an tsaro da 'yan banga da iyayen yara
  View more on twitter
 10. Tinubu ya ziyarci Sarkin Kano Aminu

  Twitter

  Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya isa Jihar Kano duk da sukar da ake yi na cewa bai kamata a yi bikin zagayowar haihuwarsa ba a jihar.

  Kungiyar matasan arewa ta nemi kada gwamna Abdullahi Ganduje ya shirya wa Tinubu bikin a Kano.

  A kuma ranar Lahadi ne Ganduje ya jagoranci wata ziyara da shugaban APC din ya kai fadar sarkin Kano.

  Ana sa ran a gobe Litinin Tinubu zai tattauna da masu rike da sarautar gargajiya a Najeriya.

  Wani abu da ke karin haske kan jita-jitar da ake yadawa cewa yana neman takarar shugabn kasa,duk da yake bai fito ya bayyana aniyarsa a fili ba.

  Lokacin da yake bayani a fadar, Tinubu ya amince cewa Najeriya na cikin wani mawuyacin hali a yanzu, wanda babu abin da zai fitar da ita sai hadin kai da kuma kaunar juna.

 11. Abba Kyari ya isa Benue don bincike kan yunkurin kashe Ortom

  Google

  Wata runduna da zata gudanar da bincike na musamman da shugaban 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya hada tare da aike ta Benue ta isa jihar.

  Rundunar da DCP Abba Kyari ke jagoranta za ta ci gaba da bincike ne kan yunkurin kashe gwamnan jihar ta Benue Samuel Ortom.

  Tawagar da ke Makurdi a yanzu ta hadar da mutane daga sassa daban daban na kwararrun 'yan sanda da ke gudanar da bincike kwarewa a aikata manyan laifuka, kamar gano zanen yatsun masu laifi da dai sauransu.

  Ana sa ran tawagar za ta karbi ragamar gudnar da bincike da aka fara kan lamarin.

  Za kuma su gudanar da bincike ta ko wacce fuska domin tabbatar da cewa duk wani mai hannu cikin wannan lamari ya girbi abin da ya shuka.

 12. Zan sauka daga shugabancin EFCC idan aka nemi na karya doka— Abdulrasheed Bawa

  EFCC

  Shugaban Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC, Abdulrasheed Bawa ya ce zai sauka daga mukamunsa idan wani ya nemi ya yi wani abin da ya saba ka'idar aikins shi.

  Ya kuma kara jaddada dokar da ta bai wa EFCC damar binciken kadarorin ma'aikatan banki.

  Bawa ya fara bayyana wannan ra'ayin nasa ne lokacin da ya yi wata tattaunawa da gidan talabijin na kasar NTA.

  An raba wa 'yan jarida rubutaccen bayanin shugaban ta hannun shugaban masu yada labarai na hukumar Mista Wilson Uwujaren.

  Yace zai kasance mai tsoron Allah da bin ka'idojin da doka ta tanada.

  Yace "Zan ci gaba da aiki domin yin abin da ya kamata. wannan hukuma karkashin kulawata za ta zama mai bin doka da oda.

  "Idan wani ya nemi in yi abin da ya ci karo da ka'idar aiki na ko abin da doka ta tanada, zan ajiye wannan aikin ne kawai".

 13. Atiku na son 'yan Najeriya su taimaki gwamnatin Buhari

  BBC

  Tsohon mataimakin shuagaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce ya ce lokaci ya yi da yan Najeriya ya kamata su taimakawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

  Atiku ya bayyana hakan ne cikin wani jerin sakonnin Twitter, kan sanya zama da Najeriya ta yi a matsayi na uku na kasashen da suka fi fama da matsalar rashin aikin yi.

  Rahoton jaridar Bloomberg ya ruwaito cewa Najeriya ce ta uku a duniya cikin jerin kasashen da ake da marasa aikin yi, da kashi 33 cikin 100.

  Atiku ya ce tun kan azo wannan mataki sun yi gargadin haka, shi da wasu makamantansa masu kishin kasa.

  Ya kuma tambaya tayaya Najeriya ta samu kanta a irin wannan matsayi? ya kuma bai wa kansa amsar cewa, Najeriya ta samu kanta ne a nan ta dalilin watsar da shugabancin da ke jin kan mutane, da kuma saukakakken kasuwanci da watsar da wasu manufofi da aka gabatar lokacin mulkin Obasanjo.

  A wancan lokacin in ji Atiku kason da Najeriya take da shi bai fi daga daya zuwa tara ba.

  Matsalar tsaro duk ita ta haifar da wadannan matsaloli da aka samu kai a ciki.

  View more on twitter
 14. Gobara ta tashi a kusa da Masallacin Annabi da ke Madina

  Haramain Sharifain

  Gobara ta tashi a kusa da masallacin Annabi Muhammad SAW da ke birnin Madina da ke kasar Saudiyya.

  A wasu jerin sakon Twitter da shafin Haramain Sharifain ya wallafa dazunnan hotunan bidiyon da aka wallafa sun nuna wani gini na ci da wuta kuma hayaki ya turnuke saman kusa da ginin masallacin mai alfarma.

  Ba dai a bayyana musabbabin tashin wannan gobarar ba, sai dai shafin ya ce an kashe ta cikin gaggawa.

  View more on twitter
  View more on twitter
 15. Shugaban Brazli ya sa a biya wata yar jarida diyya

  EPA

  Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya yi umarnin a biya wata yar jarida dalar Amurka dubu uku da dari biyar saboda furta kalaman kaskanci a kanta.

  Wannan dai ya biyo wani umarni da wata kotu a kasar ta bayar na cewa sai shugabn ya biya yar jaridar diyya.

  Mista Bolsonaro cikin watan Fabrairun bara ya ce yar jaridar, Patricia Campos Mello ta mika kanta ga wani mai ba da rahoto domin ta samu mummunan bayani a kansa.

  Alkalin kotun ya ce Mista Bolsonaro ya ci zarafin yar jaridar.

  A wata Janairu ne yar jaridar ta yi nasara a wata shari'a makamanciyar wannan da ta shafi dan shugaban kasar, Eduardo wanda aka bukaci ya biya ta sama da dalar amurka dubu biyar a matsayin diyya.

 16. An kama ‘mutanen da ke kashe ‘yan sanda’ a Kudancin Najeriya

  NP

  Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta kama mutum16 da ke zargi da kashe jami'anta a kudancin kasar.

  A wata sanarwa da kakakin ta Frank Mba ya fitar, rundunar ta ce ta samu nasarar kama Ugochukwu Samuel da Raphael Idang sai kuma Cletus Nwachukwu Egole wadanda ake zargi da jagorancin wannan mummunan aiki.

  Ta cikin sanarwar Mba ya ce "rundunar 'yan sanda ta yi alkawarin bankado duk wani mai irin wadannan laifuka a duk inda ya boye a cikin kasar."

  NP

  An kama wasu sauran mutum 13 a sauran sassan kasar wadanda ba a bayyana sunayensu ba, tare da makamai irinsu bindiga kirar AK 47 da harsasai da kuma wasu abubuwan fashewa da dama.

  A baya-bayan nan an samu yawaitar kai hare-hare kan yan sanba da ofisoshinsu a kudu maso gabas da kudu maso kudu, lamarin da ake dangantawa da fafutukar ballewa daga Najeriya.

 17. Dole Saudiyya ta rungumi tsarin sauyin yanayi - Yarima Mohammed bin Salman

  Getty Images

  Saudiyya wadda ita ce babbar mai fitar da mai kasuwar duniya ta ce, za ta gaggauta shirinta na rage fitar da gurbatacciyar iska da masana'antu ke yi, tare da sanar da sabbin hanyoyin rage torzarta kasar.

  Yarima mai jiharn gabo Mohammed bin Salman ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce akwai bukatar masarautar Saudiyya ta rungumi tsarin sauyin yanayi cikin gaggawa., tare da fatan za ta koma samar da mafi yawan makamashinta ta wasu sabbin hanyoyi daga nan zuwa 2030.

  Sanarwar ta ce a yanzu an samu raguwar kashi bakwai cikin dari na makamashi a Gabas Ta Tsakiya dalilin amfani da sabbin hanyoyi na zamani, dan haka Saudiyya a shirye take da yi aiki da makotanta domin rage fitar da gurbatacciyar isaka a yankin.

  Saudiyyar ta sanar da shirin samar da bishiyu biliyan goma domin karfafawa kasashen da ke makwabtaka da ita wajen samar da gandun daji mafi girma a duniya.

 18. Mun kama dan shekara 70 da ke kai wa 'yan Boko Haram kwaya - NDLEA

  @ndlea_nigeria

  Hukumar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi NDLEA ta Najeriya ta ce ta kama wani mutum dan shekara 70 da ake zargi dai kai wa 'yan bindiga kwaya.

  Cikin wata sanarwa da ta wallafa a Twitter, hukumar ta ce, mutumin mai suna Muhammad Rabi'u Wada da ke kai wa Boko Haram da 'yan bindiga kwaya an kama shi ne a jihar Neja.

  NDLEA ta ce mutumin na zuwa ne daga jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar ne, ya shigo da kayan Najeriya.

  A wani aikin da hukumar ta yi mai kama da wannan, ta samu nasarar lalata gonar taba a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya wadda girmanta ya kai hekta 95.

  An samu gonar ne a dajin Ogbese, sai dai ba a samu nasarar kama kowa ba yayin samamen, amma ana ci gaba da bincike domin gano mai gonar.

  A jihar Kogi da ke arewacin kasar Hukumar ta samu nasarar kwace tabar da ta kai kilogiram 116.1 wani shingen ababan hawa a yankin Okene-Lokoja.

  Mutumin da aka kama da kayan mai suna Sulaiman Said ya ce ya ɗakko kayan ne daga jihar Edo kuma zai kai su Jihar Kaduna ne.

  View more on twitter
 19. 'Yan bindiga sun ƙara lalata turakun wutar lantarki a kan hanyar Maiduguri

  Google

  Ofishin ministan lantarki na Najeriya ya ce, kasa da kwana guda 'yan tada kayar baya sun kara lalata wasu turakun wutar lantarki biyu da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

  Ofishin ya wallafa haka ne a shafinsa na Twitter, yana cewa an dawo da wutar lantarki a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

  Ya ce lalata turakun ya haifar da daukewar wuta a Maiduguri da kewayenta.

  Ofishin ya ce a wannan karon 'ya bindigar sun sanya bam ne akan turakun biyu wadanda aka lalata a baya kuma suka janyo dauke wuta ta kimanin watanni biyu a Maiduguri da kewayenta.

  Sai dai kamfanin da ke samar da wutar a kasar ya ce za yi iya kokarinsa ya ga yadda za a gyara wannan barna a kan lokaci.

  View more on twitter
 20. Bam ya fashe a wajen wata coci a Indonesia

  Reuters

  An samu fashewar wani abu a wajen cocin katolika da ke birnin Makassar a Indonesia.

  Wani malamin addinin kirista daga cocin, Father Wilhemus Tulak ya ce mutum 10 sun ji rauni bayan da wasu jami'an tsaro suka tunkari mutanen da ya bayyana a matsayin yan kunar bakin wake.

  Ya ce maharan sun isa wajen kan babura inda suka yi kokarin shiga majami'ar.

  Fashewar ta faru ne yayin da mutane ke barin majami'ar bayan kammala bauta yau Lahadi.