Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail, Nasidi Adamu Yahaya da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. A nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

 2. Buhari ya yi Allah wadai da yunƙurin juyin mulki a Nijar

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

  Tun misalin ƙarfe 3:00 na tsakar dare aka fara jin harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa kuma an ɗauki kusan minti 15 ana yi.

  Gwamnatin Nijar ta ce an ƙaddamar da bincike kan sojojin da suka jagoranci juyin mulki, kwana biyu kafin rantsar da sabuwar gwamnatin Bazoum da aka zaɓa - karon farko a tarihi da wata gwamnatin farar hula za ta miƙa mulki ga wata gwamnatin dimokuradiyya.

  Shugaban Najeriya a cikin wata sanarwar ya ce "duk wani yunƙuri na haramtacciyar hanya don hambarar da gwamnatin da aka zaɓa ta hanyar dimokiradiyya ba abin ƙyama ba ne kawai, abin Allah wadai ne ga gwamnatocin dimokiradiyya a duniya."

  View more on twitter
 3. Ƴan bindiga sun buɗe wuta a taron siyasa na Charles Soludo a Anambra

  Farfesa Charles Soludo tsohon gwamnan babban bankin Najeriya

  Ƴan bindiga sun kai wa Farfesa Charles Soludo tsohon gwamnan babban bankin Najeriya hari, ɗaya daga cikin masu neman kujerar gwamna a zaɓen Anambra da za a yi 6 ga Nuwamban bana.

  Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun kashe jami’an ƴan sanda da ke ba shi tsaro guda uku.

  Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Anambra DSP Ikenga Tochukwu ya tabbatar wa sashen BBC Pidgin da faruwar lamarin.

  Bayanai sun ce ƴan bindigar sun abka gangamin yaƙin neman zaɓensa ne a ranar Laraba inda yake taro da matasa suka buɗe wuta.

  Babu dai wani cikakken bayani game da tsohon gwamnan Babban Bankin na Najeriya.

 4. Aisha Buhari ta ba ƴan Najeriya shawarar amfani da magungunan gargajiya

  Aisha Buhari

  Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta yi kiran rungumar magungunan gargajiya da ta kira wani ɓangare na kula da kiwon lafiya da ke magance cututtuka.

  Aisha Buhari ta yi wannan kiran ne a wani bikin da Hajiya Hajo Sani ta wakilce ta na kaddamar da litattafan da Zainab Sharif ta rubuta babbar daraktar sashen kula da magungunan gargajiya a ma’aikatar lafiya ta Najeriya, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar NAN ya ruwaito.

  “Litattafan suna ƙunshe da bayanai game da ire-iren tsirrai da ake da su a Najeriya,” a cewar NAN.

  Uwargidan shugaban na Najeriya ta kuma jinjinawa marubuciyar tare da cewa litattafanta za su yi amfani ga kiwon lafiyar ƴan Najeriya.

 5. Jami'an tsaron jihar Legas za su fara yawo da kyamarori a jikinsu

  Gwamna Babajide Sanwo-Olu, a ranar Laraba, ya ƙaddamar da wani gagarumin shiri na inganta tsaro a Jihar Legas.

  Gwamnan ya amince da shirin horar jami’an tsaro na jihar kan yadda za su yi amfani da kyamarori a jiki don ayyukan tsaro a fadin jihar.

  Za a fara horar da jami'an ne a watan Mayu, kuma bayan horon za su fara yawo da kyamarorin a jikinsu a lokacin da suka fita aiki.

  Sanwo-Olu ya ce matakin zai tabbatar da gaskiya da amana a ayyukan jami'an tsaron, sannan zai taimakawa Gwamnatin Jiha da kyakkyawan yanayi na tunkarar ƙalubalen tsaro cikin gaggawa.

  Sannan a cewar gwamnan, kymarorin za su taimakawa gwamnati wajen duba yadda ake amfani da ƙarfi da wuce gona da iri daga jami’an tsaro, tare da inganta tsaro da tabbatar da bin diddigin jami’an, waɗanda kuma za su yi amfani da na’urorin don samar da bayanan sirri na sha'anin tsaro.

  View more on twitter
 6. Boko Haram na da alaƙa da ƴan fashin daji – Gwamnatin Najeriya

  Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da rahotannin gano alaƙa tsakanin ƴan fashin daji da ke kai hare-hare da satar mutane don neman fansa da kuma ƙungiyar Boko Haram.

  Ta ce tuni jami’an tsaro sun kama wasu mutane da suke zargi suna da hannu wajen samar da kuɗaɗe tare da tura wa ƙungiyar Boko Haram.

  Gwamnatin ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kamar yadda Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC.

  Video content

  Video caption: Hirar Halima Umar Saleh da Malam Garba Shehu
 7. Madugun adawar Rasha Alexei Navalny ya shiga yajin cin abinci

  Alexei Navalny, madugun adawa kuma babban mai sukar gwamnatin shugaban Rasha Vladimir da ke gidan yari ya ce zai shiga yajin cin abinci.

  Ya nemi ya gana da likitansa.

  "Duk mutumin da aka yanke wa hukunci na da damar zuwa diba lafiyarsa don bincike da kuma ba da shawara. Ni ma. Duk da cewa ba ni da laifi," kamar yadda Mista Navalny ya rubuta a shafinsa na Twitter.

  "Ina buƙatar a amince likita ya duba ni kuma zan shiga yajin cin abinci har sai an amince da buƙata ta."

  Ya sha yin koke kan halin rashin lafiyarsa a gidan yari.

  "Maimakon taimaka wa lafiyata, ana azarbatar da ni da rashin bacci, ana tayar da ni sau takwas," in ji shi.

 8. An ƙara kwaso Ƴan Najeriya da suka maƙale Saudiyya

  Kimanin ƴan Najeriya 418 da suka maƙale a Saudiyya suka sauka Abuja babban birnin tarayyar Najeriya a ranar Laraba.

  Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta ce jirgin kamfanin Saudi Air ne ya kwaso ƴan Najeriyar inda suka sauka da rana.

  Sai dai sai sun yi kwanaki a killace a sansanin hukumar alhazzai kafin su tafi gidajensu.

  View more on twitter
 9. An gurfanar da 'yan kungiyar asiri 60 a kotun Lagos

  Hakeem Odumosu
  Image caption: Kwamishinan 'yan sandan Lagos Hakeem Odumosu ya ce za su kawar da masu tayar da zaune tsaye

  Rundunar 'yan sandan jihar Lagos da ke kudancin Najeriya ta ce ta gurfanar da mutum 60 da take zargi da shiga kungiyar asiri a wata kotun majistiret da ke birnin.

  Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Olumuyiwa Adejobi ya aike wa manema labarai ta ce ana zargin mutanen da aikata laifuka 13 da suka hada da hada baki don aikata laifuka, da kisan kai, da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da sauransu.

  A cewarsa, an kama mutanen ne a yankuna daban-daban na jihar ta Lagos.

  "Kwamishinan 'yan sanda ne ya tsara yadda aka kai wasu daga cikin samamen a fadin jihar, musamman a yankin Ikorodu inda aka farmaki 'yan kungiyar asiri da 'yan daba wadanda suka addabi jihar," in ji sanarwar.

  Ya ce Kwamishina Hakeem Odumosu ya sha alwashin kawar da masu tayar da zaune tsaye a fadin jihar.

 10. 'An sace Kiristoci 'yan kungiyar CAN fiye da 500 a shekara daya'

  Shugaban CAN na Najeriya Reverend Samson Ayokunle
  Image caption: Shugaban CAN na Najeriya Reverend Samson Ayokunle

  Kungiyar Kirista ta Najeriya CAN reshen Arewacin kasar ta ce a shekarar da ta gabata kadai an yi garkuwa da mambobin kungiyar fiye da 500.

  Sakatare Janar na kungiyar reshen arewacin Najeriya, Reverend Joseph Hyap ya ce suna da dukkan shaidun da suke nuna wannan adadi na mambobinta da aka yi garkuwa da su.

  Hyap ya kara da cewa "ita da kanta gwamnatin jihar Kano ta ce an yi garkuwa da sama da mutum 2000 a shekarar da ta wuce, don haka idan muka ce an sace namu mambobin sama da 500 ba mu yi karya ba."

  Ya ce ya tara fastoci 1500 da ya zauna da su domin tattara bayanan mutanen da aka sace da wadanda aka kashe ta haka ne suka gano wadanda lamarin ya rutsa da su, yana mai cewa an biya kudin fansa domin karbo wasu daga cikinsu, wasu kuma babu labarinsu.

  "Ko a makon da ya wuce an sace wani fasto da sakatarensa da wasu mambobi, an sako uku daga ciki amma sauran har yau babu amo babu labari," in ji Hya.

  Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta fito ta karyata ikirarin kungiyar.

 11. Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kafa gidan rediyo

  Mohammed Adamu
  Image caption: Mohammed Adamu ya ce gidan rediyon zai taimaka wajen kawar da laifuka

  Rundunar 'yan andan Najeriya ta kaddamar da gidan rediyo na kanta da zummar inganta dangantakar da ke tsakaninta da jama'a.

  Babban sufeton rundunar 'yan sandan Mohammed, wanda ya kaddamar da gidan rediyon mai suna Nigeria Police 99.1FM Radio ranar Laraba a Abuja, ya ce gidan rediyon zai taimaka wajen rage aikata laifuka ta hanyar watsa labarai game da yadda za a kama masu laifuka da ma hana aikata wasu laifukan.

  "Tuni gidan rediyon The Nigeria Police 99.1FM ya soma gudanar da aiki na gwaji kamar yadda dokar hukumar kula da kafafen watsa labarai ta tanazar. Gidan rediyon zai zama wata hanya da rundunar 'yan sandan Najeriya za ta tattauna da wayar da kai da kuma ilimantar da 'yan kasar game da ayyukanta da kuma sauran lamuran da suka shafi harkokin tsaro," in ji Mohammed Adamu.

  Ya kara da cewa gidan rediyon zai rika gabatar da shiri na kai-tsaye da 'yan kasar za su rika kiran waya game da yanayin tsari a yankunasu musamman kan yadda za su gano masu aikata laifuka da bayar da rahoto a kansu ta yadda jami'an tsaro za su yi saurin kai musu dauki.

  View more on twitter
 12. 'Yan Najeriya sun tare wa Buhari hanyar shiga gidansa na London

  Wasu 'yan Najeriya da ke zaune a Birtaniya sun yi zanga-zanga ranar Laraba inda suka nemi shugaban kasarsu Muhammadu Buhari ya koma gida.

  Yan Najeriyar sun taru ne a kofar gidan Najeriya gwamnatin kasar da ke birnin London inda suka tare hanyar shiga.

  Suna dauke da kwalaye inda suka rika kira ga shugaban da ya koma kasarsa.

  Sun kirkiro maudu'i a shafin Tuwita mai taken #BuhariMustGo, wato dole Buhari ya sauka daga mulki, domin nuna bacin ransu kan abin da suka kira rashin iya gudanar da mulkinsa.

  View more on twitter

  Shugaba Buhari ya isa birnin London ranar Talata domin a duba lafiyarsa.

  A sanarwar da fadar shugaban kasar ta fita ta ce shugaban zai koma kasar a mako na biyu na watan Afrilu bayan an kammala duba lafiyarsa.

  Sai dai mutane da dama ba su ji dadin tafiyar shugaban domin a duba lafiyarsa a London ba musamman ganin yadda ake zargi harkokin lafiyar kasar suna ci gaba da tabarbarewa abin da ya sa likitoci masu neman kwarewa suka sha alwashin shiga yajin aiki.

 13. Kotu ta ɗage shari'ar Zakzaky da matarsa

  Zakzaky

  Wata Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sake ɗage zaman shari'ar shugaban ƙungiyar mabiya Shia ta Islamic Movement in Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim Elzakzaky da matarsa Zeenat zuwa ranar 25 ga watan Mayun 2021.

  Yayin zaman na yau Laraba, lauya mai shigar da ƙara, Dari Bayero, ya kammala gabatar da shaidunsa, a cewar rahoton kafar talabijin ta Channels.

  Kazalika, lauyan ya nemi kotun ta hukunta waɗanda ake zargin bayan ya gabatar da jumillar shaidu guda 15.

  Ana sa ran lauyan da ke kare Zakzaky da Zeenat, Femi Falana wanda Abubakar Marshal ya wakilta, zai fara kare mutanen biyu a zaman kotun na gaba.

  Zakzaky da matarsa na fuskantar tuhuma guda takwas da suka haɗa da kisan kai da taro ba bisa ƙa'ida ba da kuma takura wa al'umma da sauransu.

  Sai dai shugaban da matarsa sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

  Mai Shari'a Gideon Kurada na kotun Jihar Kaduna ya saka yau Laraba domin ci gaba da sauraron ƙarar ce ranar 8 ga watan Maris bayan lauya mai shigar da ƙara ya gabatar da shaidu guda 14.

  An tsare Zakzaky da matarsa tun Disamban 2015 bayan rikici tsakanin mabiyan malamin da sojojin Najeriya, abin da ya jawo kisan ɗaruruwan 'yan ƙungiyar.

 14. Uba 'ya kashe' ɗansa a Kano

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Khalifa Dokaji daga Kano

  Rundunar yan sandan Jihar Kano a Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Auwalu Awaisu mai shekara 19 bayan mahaifinsa ya lakaɗa masa duka a daren ranar Juma’a da ta gabata.

  'Yan sandan sun ce matashin ya mutu ne a ranar Litinin a Asibitin Murtala sakamakon dukan da mahaifin nasa ya yi masa a ka da kuma cikinsa.

  A cewar 'yan sandan, mahaifin Auwalu mai suna Awaisu Auwalu na zargin dan nasa Auwalu Awaisu wato Abba da batan wasu kudadensa a shagonsa.

 15. 'Sojan da ya jagoranci' yunƙurin juyin mulki a Nijar ya tsere

  Birnin Yamai

  Sojan da ake zargi da jagorantar juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a daren Laraba ya tsere, a cewar kafofin yaɗa labaran Faransa.

  "A cewar bayanan farko-farko, wani sojan sama mai suna Kaftin Gourouza, shi ne shugaban maharan waɗanda suka isa a motoci guda huɗu," a cewar AFP yana mai ambato gidan rediyon RFI.

  "Shugaban nasu wanda yanzu haka ake nemansa ruwa a jallo, ya tsere, a cewar majiyoyin tsaro."

  Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kama wasu sojoji biyo bayan yunƙurin juyin mulkin.

  Ya zuwa yanzu gwamnati ba ta tabbatar da yunƙurin juyin mulkin ba yayin da birnin Yamai ya kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

  Tun misalin ƙarfe 3:00 aka fara jin harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa kuma an ɗauki tsawon kusan minti 15 ana yi.

  Jami'an tsaron fadar ne suka daƙile yunƙurin, wanda ya faru ƙasa da kwana biyu kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Mohamed Bazoum.

  Rahotanni dai sun ce al'amura sun dan lafa a yanzu.

 16. Gwamnatin Kamaru ta musanta kisan fararen hula

  Ma'ikatar tsaro a Kamaru ta musanta kashe fararen hula da ake zargin jami'anta da yi a garuruwan Foe Bakundu da Kumbo a yankin renon Ingila.

  Cikin sanarwar da hukumomi suka fitar, sojojin bataliya ta 21 ne ke yin sintiri inda suka yi karo da wasu 'yan aware masu rike da makamai kuma suka fara musayar wuta da su.

  Hakan ya sa suka yi nasara a kan 'yan awaren suka kwantar tare da kashe biyu daga cikinsu.

 17. An rantsar da shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afirka a wa'adi na biyu

  Mousa Faki

  An rantsar da Shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Faustin-Archange Touadéra a wa'adi na biyu.

  An sake zaɓar shugaban ne a watan Disamban 2020.

  Bikin rantsuwar ya gudana ne a majalisar wakilan ƙasar, wanda baƙi daga ƙasashen waje suka halarta.

  Daga cikinsu akwai shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki.

  View more on twitter
 18. 'Yan bindiga sun kashe mutum 27 a Jihar Ebonyi

  'Yan bindiga

  Rahotanni daga Jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kashe mutum kusan 27 a yankuna huɗu na jihar.

  Kafafen yaɗa labarai sun ruwaito Gwamnan Jihar David Umahi na bayyana kaɗuwarsa da harin yayin da ya ziyarci yankin, wanda ake zargin makiyaya ne suka kai shi.

  Kazalika, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan da wasu jami'an gwamnati sun bayyana harin cewa na ramuwar gayya ne, inda ya ce an kashe wasu makiyaya biyu a yankin kusan shekara ɗaya da ta gabata.

  Gwamnan ya ce an kama mutanen da suka kashe makiyayan, abin da ya sa ya kasa gane daliin da ya jawo harin na bayan-bayan nan.

  Harin ya shafi mazauna yankunan Nkalaha da Obegu da Amaezu da Umuhuali da ke Ƙaramar Hukumar Ishielu.

  Sai dai jaridar ta ruwaito shugabannin al'ummar Fulani makiyaya na Ebonyi sun musanta zargin cewa mutanensu ne suka kai harin.

  Duk da cewa rundunar 'yan sandan jihar ba ta ce komai ba game da harin zuwa yanzu, rahotanni sun ce an tura wani babban jami'in rundunar zuwa yankin.

 19. Korona ta kashe mutum kusan 4,000 cikin kwana ɗaya a Brzail

  Brazil

  An samu adadi mafi yawa na mutanen da suka mutu sakamakon cutar korona a Brazil ranar Talataa daidai lokacin da kasar ke tsaka da fama da rikicin siyasa.

  Kimanin mutum 3,800 ne suka mutu, kusan kashi 1 bisa uku na yawan wadanda cutar ta kashe a duniya kenan a ranar.

  Shugaba Jair Bolsonaro na fuskantar matsin lamba matuka game da salon gwamnatinsa na yaki da annobar.

  Wakilin BBC ya ce masu sharhi da dama na jiran shekara mai zuwa, lokacin da ake sa ran shugaba Bolsunaro zai nemi wa'adi na biyu.

 20. Yau Laraba za a ci gaba da shari'ar Zakzaky da matarsa

  Zakzaky

  Yau Laraba za a ci gaba da shari'ar shugaban ƙungiyar mabiya Shia ta Islamic Movement in Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim Elzakzaky da matarsa Zeenat a Kaduna.

  Zakzaky da matarsa na fuskantar tuhuma guda takwas da suka haɗa da kisan kai da taro ba bisa ƙa'ida ba da kuma takura wa al'umma da sauransu.

  Sai dai shugaban da matarsa sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

  Mai Shari'a Gideon Kurada na kotun Jihar Kaduna ya saka yau Laraba domin ci gaba da sauraron ƙarar ce ranar 8 ga watan Maris bayan lauya mai shigar da ƙara ya gabatar da shaidu guda 14.

  An tsare Zakzaky da matarsa tun Disamban 2015 bayan rikici tsakanin mabiyan malamin da sojojin Najeriya, abin da ya jawo kisan ɗaruruwan 'yan ƙungiyar.