Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Bankwana

  A nan ne muka kawo karshen rahotannin da muke kawo muku a wannan shafi a kuma wannan rana.

  Sai mu hadu gobe idan Allah ya kaimu, Buhari Muhammad Fagge da Awwal Ahmad Janyau ke fatan mu kwana lafiya.

 2. An kashe mutum 6 a wani harin kunar bakin wake a Mogadishu

  BBC

  Yan sanda a Somalia sun ce akalla mutum 6 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai gaban wani shagon sayar da shayi a lardin Shangani da ke Mogadishu

  An rawaito jama'a da dama sun jikkata yayin harin.

  Ana kuma shan Shisha a wurin da ake shan shayin wanda ya yi fice a wurin tara matasa.

  Tun da farko Kungiyar al-Shabab ta kai wa wasu sansanonin soji bhari guda biyu, ta kuma hari wani jerin motocin su a kudu maso yammacin Mogadishu.

  Da dama sun raunata a harin da aka kai wa sansanin sojin, amma tuni rundunar sojin kasar ta ce ta kara karbe iko da wuraren nata.

 3. Ana zanga-zangar adawa da dokar karawa yan sanda karfin iko a Burtaniya

  BBC

  Dubbai sun gudanar da zanga zanga a yankunan Ingila da Wales na Burtaniya, inda suke nuna adawa da kudurin majalisa na karawa yan sanda karfin ikon hana bore.

  Tsohon shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya fadawa dandazon al'umma da ke bore a tsakiyar London cewa matakin ba karamin hadari ya ke da shi ba, a don haka dole ne ayi adawa dashi.

  Sauran kungiyoyin da suka shiga zanga zangar sun hada da yan kungiyar da ke yaki da nuna wariya ta Black Lives Matter da kuma ta masu rajin kare muhalli wato Extinction rebellion, wadanda a shekarun bayan suka hana birnin London sakat a dalilin zanga zanga.

 4. Jamus ba ta jajirce yadda yakamata ba kan korona - Frank Walter Steinmeier

  BBC

  Shugaban Jamus Frank Walter Steinmeier ya gargadi yan siyasa da su guji siyasantar da lamarin annobar Korona.

  Mista Steinmeir na magana ne ta kafar talabijin din Jamus, inda ya bukaci da a aje siyasa gefe a hada hannu don sauraren koken al'umma.

  Shugaban ya ce babu tantama kan cewa Jamus ba ta jajirce yadda yakamata ba wurin tunkarar annobar, to amma duk da haka ya bukaci al'umma da su fita ayi musu rigakafi.

 5. Katsina United za ta biya kusan miliyan uku a matsayin tara

  Google

  An ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Katsina United da ke arewacin Najeriya kudi da suka kai naira miliyan daya domin gaza bayar da kariya ga tawagar alkalan wasa.

  Hakan ya biyo rashin da'ar da ake zargin magoya bayan kungiyar da yi a yayin wasanta da Kwara United da aka ci Katsaina har gida 1-2.

  Cikin wani sakon Twitter hukumar shirya gasar ta Najeriya ta bayyana cewa, an kama wani daga cikin manyan kungiyar da ake zargi da jifan alkalin wasa da kujera lokacin da yake shiga dakin sauya kaya.

  Wannan ta sanya aka ci kungiyar tarar naira 250,000 a matsayin diyya ga alkalin wasan.

  An kuma kara cin kungiyar tarar naira miliyan 1 saboda kasa samar da cikakken tsaro ga kulob din da ya ziyarce ta a gida.

  An kara neman ta biya naira 500,000 saboda gaza shawo kan rashin da'ar da aka yi a filin wasa wanda ya janyo tsayar da wasan baki daya.

  Katsina za ta ci gaba da buga wasa ba tare da 'yan kallo ba, wadanda za su shiga filin wasan na Muhammad Dikko daga shugabannin wasa sai na kungiyoyin biyu.

  Wadanda suka jiwa alkalin wasan rauni an kama su kuma za a gabatar da su gaban shari'a.

  Katsina United na da damar daukaka kara cikin kwana biyu kacal kamar yadda sanarwar hukumar ta bayyana.

  Ba dai wannan karon ba ne na farko da ake cin tarar wannan kungiya ba, saboda ya wan tashe-tashen hankula da ake samu a lokacin da ta ke wannninta a gida.

  View more on twitter
 6. Kungiyar ma'aikatan shari'a ta Najeriya za ta fara aikin sai baba ta gani

  BBC

  Kungiyar ma'aikatan shri'a ta Najeriya ta shirya tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 6 ga watan Afrilun da muke ciki.

  Wanann umarni na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar ta JUSUN Isaiah Adetola ya fitar.

  Sanarwar ta ce maganar yajin aikin ta samo asali ne tun a bayanin bayan taron da aka yi da kwamitin zartarwa na kasa da kungiyar a ranar 31 ga watan Maris a Abuja.

  Sanarwar ta ce da an tsara fara yajin aikin ne a ranar 5 ga watan Afrilu amma dole aka matsara da shi zuwa ranar Talata 6 ga watan Afrilun 2021 saboda hutun da aka bayar a kasar.

  Kungiyar dai sai da ta bai wa gwanati wa'adin kwana 21 domin ta biya musu bukatarsu na bai wa bangaren shari'a cin gashin kai a harkokin kudi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya zayyana.

  Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasar ta fara na ta yajin aikin saboda da nata bukatun da ke da alaka da kudade.

 7. 'Duk cikin minti 40 mace daya na kamuwa da kansar mama a Iran'

  BBC

  A iran mace da kamu da kansar mama a cikin ko wanne minti 40, kuma yiwuwar yaduwar cutar tsakanin maza ta karu daga shi 1 cikin dari zuwa kashi biyu.

  A wata tattaunawa da aka yi da shugaban kungiyar wayar da kan game da kansar mama kariya da kuma yadda ake iya gano cutar Afsaneh Iqbalunia, yace yawaita ko kuma karancin samun wannan cutar tsakanin maza da mata ya ta'allaka ne da irin yadda ake musu bayanan yawar da kai game da alamominta.

  "Abin takaicin shi ne gwamnati ba ta hada hannu da masu fafutuka a fagen yaki da kuma kare kai daga kamuwa da kansar mama domin samar musu da magunguna akan lokaci," in ji Afsaneh Iqbalunia.

  Karancin abin da mai fama da wannan cuta zai kashe a ko wanne wata shi ne (Toman) kudin Iran miliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka dubu 42.

 8. Nijar na son a gudanar da bincike kan fyaden da sojojin Chadi ke yi wa 'yara'

  AFP

  Hukumar kare hakkin dan adam ta Nijar ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa bayan zargin da ake yin a cewa sojojin da aka girke daga Chadi domin yaki da ‘yan ta’adda sun yi wa mata da yawa fyade, ciki harda wata yarinya yar shekara 11.

  Cikin wani rahoto da kungiyar ta buga a ranar Juma’a game da bincike da ta gudanar, wanda ya dogara kan wadanda suka ba da shaida da kuma bayanan asibiti tsakanin ranar 31 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afrilu, ta gano an yi wa wasu mata biyu fyade.

  Matan sun hada da wata da ke da ciki wadda aka yi wa fyade a gaban mijinta kamar yadda rahoton ya bayyana.

  “Dayar kuma ta ki bayar da shaida ne saboda tsoron nuna mata kyama,” in ji rahoton.

  Kungiyar ta yi Allah-wadai da wannan mugun aiki, kan mutanen da ba su ji ba ba su gabi ba.

 9. Buhari ya yi tir da harin da aka kai Íshíelu a jihar Ebonyi

  Reuters

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin da aka kai karamar hukumar Íshíelu da ke jihar Ebonyi a kudancin kasar.

  Cikin wasu jerin sakonnin Twitter da mataimaki na musamman kan harkoki yada labarai ga shaugaban Garba shehu ya wallafa, ya ce Shugaba Buhari ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wannan hari tare da tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda aka samu da hannu cikin wannan hari.

  Shugaban ya mika jajensa tare da ta'aziyya ga mutanen gari da iyalai da abokan da suka rasa 'yan uwa da abokan arzikinsu.

  Kazalika ya mika sakon auna arziki da tsohon shugaban babban bankin Najeriya Chukwuma Soludo ya yi, bayan wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai masa, wadanda daga baya aka kama wasu daga cikinsu.

  Buhari ya nuna damuwa kan yadda ake samun shigowar makamai ba bisa ka'ida ba, inda yake yi wa 'yan kasar alkawarin cewa da sannu za a shawo kan wannan matsala.

  View more on twitter
 10. Chelsea ta yi rashin nasara a karon farko tun bayan zuwan Tuchel kungiyar

  BBC Sport

  Chelsea ta yi rashin nasara da ci 5-2 har gida a hannun West Brom, wannan ne karon farko da ta yi rashin nasara tun bayan zuwa Tuchel.

  A ganinku Ina Aguero zai koma?

  BBC Sport

  Ku kasance da Jabir Mustapha Sambo da misalin karfe karfe 4:00 agogon Najeriya da Nijar don bayyana ra'ayinku a filinmu na sharhin wasanni.

 11. Mutum 7 sun mutu bayan an musu rigakafin AstraZeneca a Burtaniya

  Getty Images

  Hukumar da ke kula da magunguna ta Burtaniya ta bayyana mutuwar mutane 7 cikin 30 da wadanda cijinsu ya daskare bayan an musu rigakafin korona ta kamfanin AstraZeneca a watan da ya gabata.

  Amma ta ce babu wani cikakken haske kan cewa akasi aka samu ko kuma rigakafince ta janyo mutuwar tasu.

  Zuwa ranar 24 ga watan Maris, hukumar ta kara da cewa ta samu rahoto 22 na daskarewar jini amma 8 daga ciki suna da alaka da karancin jini a jiki.

  Dakta John Raine shi ne shugaban hukumar ya ce, "Alfanun rigakafin shi ne tana kare mutum daga kamuwa da korona, kuma ya kamata mutane su ci gaba da fitowa suna karbar tasu rigakafin."

  Da yawa daga cikin kasashen Turai sun dakatar da amfani da rigakafin "AstraZeneca" saboda rahoton da aka rika samu na mutanen da aka yi wa suna fuskantar daskarewar jini.

 12. Ga Filin Taɓa Kiɗi taɓa Karatu

  Video content

  Video caption: Taba Kidi Taba Karatu
 13. Ƴan sanda sun ceto mutum 15 da ƴan bindiga suka sace a Kaduna

  Gwamnatin Kaduna ta ce rundunar ƴan sandan jihar ta ceto mutum 15 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Chikun.

  Wata sanarwar da ma'aikatar lamurran tsaro ta jihar Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter mai ɗauke da sa hannun Samuel Aruwan ta ce akwai mata guda uku daga cikin waɗanda aka fara ceto wa Rijiya Uku waɗanda aka sace tun a watan Nuwamban 2020.

  Ƴan sandan kuma sun ceto mutum 12 a dajin Buruku waɗanda aka sace a hanyar Kaduna- Birnin Gwari a

  View more on twitter
 14. Arsenal da Liverpool za su kece raini

  Jurgen Klopp da Mikel Arteta

  Arsenal za ta karɓi bakuncin Liverpool a Emirates wasan mako na 30 a gasar Premier ta Ingila.

  Fafatawar na da muhimmanci da tasiri ga makomar manyan ƙungiyoyin biyu na Premier.

  Idan Arsenal da ke matsayi na 9 a tebur ta yi nasara zai kasance tazarar maki ɗaya ya raba ta da Liverpool.

  Sakamakon wasan kuma zai yi tasiri ga burin Liverpool da ke matsayi na bakwai a tebur na hauro wa zuwa huɗun farko.

  Tazarar maki shida ke tsakanin Liverpool da kuma Chelsea da ke matsayi na huɗu a teburin Premier.

 15. Gane mini Hanya: Matsalar ilimin ƴaƴa mata a jihar Kebbi

  Ilimin ƴa mace wani abu ne da ke da matukar amfani a cikin al’umma, sai dai tsawon lokaci ƙarancin sanya yara makaranta ya kasance ɗaya daga cikin manyan matsaloli a Najeriya.

  Wannan matsala ta fi Kamari ne a Arewacin kasar inda miliyoyin yara mata kan gaza samun ilimi sanadiyyar talauci ko kuma dalilai na ala’ada.

  BBC ta ziyarci jihar Kebbi domin ganin yadda matsalar take.

  Video content

  Video caption: Rahoton Haruna Ibrahim Kakangi
 16. Babban limamin cocin Katolika na Kamaru Christian Tumi ya mutu

  Babban limamin cocin ɗarikar katolika a Kamaru Christian Tumi

  Babban limamin cocin ɗarikar katolika a Kamaru Christian Tumi ya mutu yana da shekara 90.

  Ya kasance mai sukar lamirin gwamnatin Kamaru kuma mai rajin kare haƙƙin mutanen da ake dannewa.

  Tumi ya daɗe yana cewa tsarin tarayya shi ne mafita ga rikici tsakanin yankin renon Ingila tsiraru da kuma yankin da ke magana da harshen Faransanci.

  A shekarar 2019, ya jagoranci tawagar tattauna zaman lafiya a yankin da ke magana da Ingilishi.

  Masu neman ɓallewa daga Kamaru sun taɓa sace shi a bara.

 17. Shugaban ƙasa ya kamu da korona duk da ya yi allurar rigakafi

  Shugaban kasar Argentina, Alberto Fernandez, gwaji ya tabbatar da yana ɗauke da cutar korona duk da an yi masa allurar rigakafin cutar.

  Mista Fernandez, mai shekara 62, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana cikin yanayi mai kyau duk da yana ɗan jin zazzaɓi.

  Amma ya ƙara da cewa gara ce ya gama bikin ranar haihuwarsa ba tare da samun irin wannan labarin ba.

  A watan Janairu aka yi wa Mista Fernandez rigakafin korona ta Sputnik da Rasha ta samar, shugaba na farko daga yankin Latin Amurka da aka yi wa rigakafin.

  View more on twitter
 18. Za a nuna gawar Fir’auna da tsoffin sarakunan Masar

  Masar

  Za a jerin gwanon gawarwakin tsoffin shugabannin Masar 22 a Alkahira a yau Asabar inda za a sauya su zuwa wani sabon gidan adana kayan tarihi da ke kudancin birnin.

  Ana sa ran cincirindon jama'a za su yi jerin gwano kan tituna domin kallo - inda za su ga sarakuna 18 da sarakuna mata huɗu na Masar da za a ɗauka cikin akwatin zinari.

  Za a jera su ne a tsarin tarihin mulkinsu.

  Za a tsaurara matakan tsaro, musamma ɗaukarsu da ake a matsayin masu daraja kuma matsayin dukiyar ƙasa.

  Sarakunan sun ƙunshi har da Sarauniya Hatshepsut ta biyar a Masar da Fir’auna da ake kira Ramses na biyu.

 19. Ƴan bindiga sun kashe shugabannin Miyetti Allah a Nasarawa

  Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ce wasu ƴan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah na jihar da kuma shugaban ƙungiyar na ƙaramar hukumar Toto.

  Rundunar ta tabbatar da kashe su a cikin wata sanarwar da kakakinta Ramham Nansel ya fitar a ranar Asabar.

  Sanarwar ta ce ana tunanin ƴan bindiga makiyaya ne suka kai wa shugaban Miyetti Allah na jihar Mohammed Hussaini hari suka harbe shi.

  Ƴan bindigar sun kuma kashe shugaban ƙngiyar ta Miyetti Allah na ƙaramar hukumarToto a kasuwar Garaku.

  Sanarwar ta ce bayan samun labarin a ranar Juma’a da yamma, kwamishinan ƴan sanda na jihar Bola Longe ya aika da runduna wuraren da aka samu gawawwakin mamatan tare da ɗaukarsu zuwa asibiti.

  shugaban ƴan sandan Najeriya
 20. 'Iƙirarin Boko Haram na harbo jirgin sojin Najeriya ƙarya ce kawai'

  Rundunar sojin sama ta Najeriya ta yi watsi da wani bidiyo da ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin harbo jirgin rundunar sojin saman a jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.

  Rundunar ta ƙaryata Boko Haram ne cikin wata sanarwa da kakakinta Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar inda sanarwar ta ce bidiyon ƙarya ne aka haɗa domin yaɗa farfagandar Boko Haram.

  Rundunar sojin ta ce tana tunanin jirgin ya yi hatsari ne.

  A ranar Laraba ne rundunar sojin saman cikin wata sanarwa ta bayyana bacewar jirgin na ta mai kirar Alfa Jet (NAF 475) mai dauke da mutum biyu.

  Bidiyon ya nuna mayaƙa ɗauke da makaman harbo jirgin sama da masu cin dogon zango, da kuma tarkace da gawar matuƙin jirgin.

  Rundunar sojin ta ce an tsayar da bidiyon aka haɗa yadda jirgin ya kama da wuta daga sama yayin da yake kokarin fadowa.

  Rundunar ta sojin saman Najeriya ta ce ko da yake har yanzu tna nazarin bidiyon, amma a bayyane yake cewa yawancin sassan bidiyon an haɗa ne da gangan don yaɗa ƙaryar cewa an harbo jirgin.

  Rundunar ta yi kira ga ƴan Najeriya su yi watsi da bidiyon da ta kira farfagandar ƙarya da Boko Haram ta shirya.

  View more on twitter