Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

 1. Ban kwana

  Nan ne muka kawo karshen rahotannin da muke kawo muku a wannan shafin.

  Buhari Muhammad Fagge ke cewa a kwana lafiya.

 2. An bai wa Neymar jan kati PSG ta sauko daga saman tebur

  Getty Images

  An bai wa dan wasan Brazil da ke taka leda a Paris St-Germain jan kati a wasan da kungiyar ta yi da abokiyar hamayyarta Lille.

  Lille ta doke PSG da ci daya mai ban haushi har gida, kuma nasarar ta ba ta damar darewa saman teburin gasar Ligue 1 tare da sakko da PSG da ke ta daya a baya.

  Jonathan David mai shekara 20 ne ya jefa kwallo dayan da ta bai wa kungiyarsa wannan gagarumar nasara a minti na 20 da fara wasan.

  Dan wasan PSG Neymar da na Lille Tiago Djalo duka sun samu katin gargadi da farkon wasan kafin daga bisani aka ba su jan kati su fita daga filin wasan a mintinan karshe.

 3. Direban da motarsa ta janyo hadarin jirgin kasa a Taiwan ya ba da hakuri

  EPA

  Direban da motarsa ta lalace da hakan ya yi sanadin hadarin jirgin kasa a Taiwan ya ba da hakuri.

  Lee Yihsiang ya fadawa dandazon yan jarida cewa ransa ya yi matukar sosuwa da lamarin, kuma a shirye yake ya taimakawa masu bincike don gano yadda hadarin ya faru.

  A ranar Juma'a ne jirgin ya fita daga tarogansa wanda hakan yayi sanadin mutuwar fasinjoji akalla hamsin tare da jikkata wasu da dama.

 4. Za a kara sanya dokar kulle a Indiya bayan mutum dubu 93 sun kamu da korona

  Reuters

  Hukumomi a jahar Maharashtra da ke yammacin India za su kakaba sabbin dokokin kullen Korona a yankin.

  Hakan ya zo lura da yadda annobar ke yaduwa a yankin ba ji ba gani.

  Dama jahar Maharashtra ce ke da sama da rabin sabbin kamu a India, inda aka samu mutun dubu casa'in da uku dauke da ita a cikin kwana daya, adadin da ba taba ganin irinsa ba a duniya.

  A gobe ne za a rufe dukkan shaguna da gidajen abinci da shakatawa dake jahar.

 5. Jordan ta yi karin haske kan bidiyon da Yarima Hamzah ya saki

  Khalil Mazraawi
  Image caption: Yarima Hamzah da Gimbiya Basmah a 2011

  Mataimakin Firaiministan Jordan Ayman Safadi ya yi karin haske game da zargin da Yarima Hamzah dan uwan sarki Abdallah ya yi.

  Ya ce Yariman da wasu mutane suna da hannu cikin yi wa kasar zagon kasa da bayyana sirrinta ga wasu kasashen ketare.

  Yace an jima ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma dole sai dai a koma kotu da wannan batu.

  A ranar Asabar ne yariman ya saki wani bidiyo inda yake cewa an masa daurin talala a gida.

  Ya kuma zargi shugabannin Jordan da cin hanci da kuma rashin kwarewa.

  A yau Lahadi sarkin Morocco Muhammed na 6 ya tattauna da Sarki Abdallah ta re da nuna masa goyon baya kan matakan da ya dauka na tsaro. kamar yadda fadar masarautar Morocco ta rawaito.

 6. Kisan wasu 'yan kasuwar arewa 7 ya janyo zaman dar-dar a jihar Imo

  Getty Images

  Zaman dar-dar na karuwa a jihar Imo da ke kudancin Najeriya, bayan kisan kan da aka yi wa wasu 'yan kasuwa su 7 daga yankin arewacin kasar.

  Rahotanni sun ce an harbe mutanen ne a lokuta daban-daban a garin Orlu da Umaka da ke karamar hukumar Njaba tsakanin ranar Juma'a da Asabar.

  Wani da abin ya faru a kan idonsa Harisu Umaru Ishiaku, ya ce wadanda suka yi kisan suna sanye ne da kayan sojoji, kuma da misalin karfe 8:30 na dare ne suka shiga kasuwar Afor Umuaka suka farwa mutanen.

  Yace hudu daga cikin wadanda aka kashe da shekarunsu ke tsaknin 30 zuwa 45 sun dade suna rayuwa a yankin na shekaru masu yawa.

  Hakan yasa ya yi zargin maharan baki ne, domin kuwa a cewarsa ba a taba samun wata matsala ba tsakanin wadanda aka kashe da kuma al'umar Umuaka.

  kamar yadda shugaban 'yan kasuwa Hausawa na Imo Mallam Ibrahim Abdulkaddir ya bayyana cewa, harin farko ya faru ne a ranar Juma'a lokacin da wasu masu sayar da nama ke kokarin tashi.

  Kawai sai ga wasu mutane a mota kirar Sienna suka bude musu wuta.

  Ya ce a koma yanayi mai kama da juna aka kashe wasu 'yan kasuwa a Umuaka.

  Abdulkadir ya ce mafi yawan 'yan kasuwar Hausawa da ke Orlu yanzu suna rayuwa ne cikin firgici, wasunsu ma sun gudu sun koma Owerri.

 7. Obasanjo ya nemi a yi wa tubabbun 'yan bingida afuwa

  Getty Images

  Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo da Fitaccen Malamin addinin Sheik Ahmed Gumi sun nemi gwamnatin Buhari ta yi wa tubabbun 'yan bingida afuwa.

  Wannan na zuwa ne bayan wata ziyara da Malamin addinin ya kai wa tsohon shugaban Najeriyan a gidansa da ke jihar Ogun.

  Obasanjo ya ce, "Yan bindigar da suka shirya fita daga daji da kuma daina muggan laifuka, a yi musu ahuwa a gtara halayyarsu a koya musu ayyuka a basu jari ya zama suna da aikin yi".

  Wannan ne karon farko da aka ji Obasanjo na irin wadannan kalamai game da matsalar tsaro da ake ganin ta kusa mamaye yankuna da yawa a kasar.

  Sai dai kuma ba wannan ne karon farko ba da Sheik Gumi ke neman a yi wa 'yan bindigar ahuwa ba.

 8. Sheik Gumi da wasu malaman addini sun kai wa Obasanjo ziyara

  BBC

  Fitaccen Malamin addinin Musulincin nan Sheik Ahmad Gumi na wata ziyara ta musamman ga tsohon shugan Najeriya Olusegun Obasanjo a Abeokuta da ke jihar Ogun ta kudancin kasar.

  Rahotanni sun ce Gumi ya isa gidan tsohon shugaban kasar ne da misalin karfe 11 na safe kuma ya wuce kai tsaye cikin dakin da za su tattauna a yankin da dakin karatun tsohon shugaban yake.

  Getty Images

  Mataimakin shugaban kan harkokin yada labarai Kehinde Akinyemi, ya tabbatarwa da Daily Trust faruwar lamarin inda ya ce "Eh Gumi ya zo wajen Baba domin su tattauna tare da shi kuma akwai wasu malaman addini".

  A baya-bayan nan dai Gumi na ta haduwa da 'yan bindiga daga jihohin Zamfara ga Neja domin ganin yadda za su saki wadanda suka yi garkuwa da su.

  Sai dai kuma wata sanarwa da Gwamnatin jihar Kaduna inda Sheik Gumi ya fito ta fitar ta ce, za ta hukunta duk wanda ta kama yana tattaunawa ko biyan kuɗin fansa a madadinta ga ‘yan fashi ko‘ yan ta’adda a jihar.

  Wanda hakan zai iya zama koma baya ga aikin malamain.

 9. Yan kallo za su shiga wasan karshe na kofin Carabao

  Getty Images

  Za a bar 'yan kallo 8,000 su shiga kallon wasan karshe na kofin Carabao da za a buga tsakanin Tottenham da Manchester City.

  Wannan ne gwajin farko da za a yi na barin 'yan kallo masu yawa tun bayan dakatar da shiga filayen wasa a Ingila.

  Za a raba tikitin shiga wasan tsakanin magoya bayan kungiyoyin biyu a wasan da za a buga a filin kwallo na Wembley a ranar 25 ga watan Afrilu.

  Za kuma a sayar da sauran tikitin ga masu kallo.

 10. Gwamnatin Kaduna ta ce za ta hukunta duk wanda ya tattauna da ƴan fashi

  Gwamna El Rufa'i

  Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta hukunta duk wanda ta kama yana tattaunawa ko biyan kuɗin fansa a madadinta ga ‘yan fashi ko‘ yan ta’adda a jihar.

  Gwamnatin ta faɗi haka ne a wata sanarwa da kwamishin kula da harakokin tsaro ya fiyar yana watsi da rahotannin da ke cewa gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da za su shiga tsakaninta da ƴan fashi.

  Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada cewa babu wani irin wananan kwamitin na masu shiga tsakani.

  Gwamnati ba za taɓatattaunawa ba ko biyan kuɗin fansa ga ’yan fashi. Duk wanda da ya yi ikirarin yin hakan ta kowane hali, idan aka kama shi, za a hukunta shi,” in ji sanarwar.

  Gwamnatin Kaduna kuma ta yi kira ga mutane su bayar da rahotona duk wani da ke ikirarin shi wakilin gwamnati ne da ke tattaunawa da ƴan bindiga.

 11. Muna roƙon Ubangiji ya kawo ƙarshen ƴaki a duniya – Fafaroma

  Fafaroma Francis

  Fafaroma Francis ya yi wa duniya addu’ar kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a saƙonsa na bikin Easter a ranar Lahadi.

  Har yanzu ana fama da yaƙe-yaƙe da dama a duniya ! muna addu’ar Ubangiji wanda shi ne zaman lafiyarmu, ya kawo mana ƙarshen wannan tunanin na yaƙi,” in ji Fafaroma.

  Francis ya ambaci ƙasashe kamar Syria da Lebanon da Iraƙi da Yemen da Libya da Najeriya da ƙasashen Sahel da kuma Isra’ila da Faladinawa da ya yi wa addu’ar samun zaman lafiya.

 12. SERAP ta maka Buhari kotu kan ɓatan kudaden kiwon lafiya

  Shugaba Buhari

  Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta kai ƙarar shugaba Buhari kotu kan abin da ta kira “kasa bincikar ɓacewarnaira biliyan 3.8 da aka ware wa hukumomin kiwon lafiya.”

  Sanarwar ƙungiyar mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta Kolawole Oluwadare ta ce ta shigar da ƙarar ne a babbar kotun Abuja inda take neman kotun ta tilastawa shugaban binciken kuɗaɗen da suka ɓata da kuma magance girman matsalar rashawa a ma’aikatar lafiya da asibitocin Tarayya da kuma Hukumar da ke sa ido a kan abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC.

  SERAP ta kuma yi gargadin cewa, “Rashin binciko zargin da ake yi na ɓatan kuɗaɗen na kiwon lafiya, da gurfanar da wadanda ake zargi da laifi a gaban kotu, ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya marasa ƙarfi cikin mummunan hatsarin kiwon lafiya, wanda ya saɓa wa tsarin mulki da ƴancin dan adam a dokar ƙasa da ƙasa da kuma alƙawalin da aka yi wa ƴan Najeriya yaƙi da rashawa.”

  Ta ce kotu ba ta tsayar da ranar sauraren ƙarar ba.

 13. ISWAP ta yi iƙirarin kashe sojojin Nijar 11

  Ƙungiyar da ke da’awar jihadi reshen Afirka ISWAP ta yi iƙirarin cewa ta kashe sojojin Nijar 11 a wasu hare-hare da ta kai a kudu masu gabashin ƙasar.

  Cikin wata sanarwa da ta wallafa a dandalin RocketChat, ta ce mayaƙanta sun kai hari a barikin sojojin da ke garin Ngagam kusa da Diffa, inda suka kashe sojoji biyar tare da raunata wasu.

  Ƙungiyar kuma ta iƙirarin yin amfani da abubuwan fashewa kan sojojin da ke sintiri inda ta ce ta kashe sojoji shida.

  ISWAP ta kuma ce ta ƙwaci motoci da makamai a harin.

  Sai dai ƙungiyar ta ƴan ta’adda ba ta bayyana lokacin da ta kai harin ba amma ta fitar da sanarwar ne a ranar Asabar 3 ga Afirlu.

 14. Yadda Kiristoci suka yi bikin Easter a duniya

  Fafaroma Francis lokacin da ya jagoranci taron addu'o'i a gaban fadarsa ta Vatican
  Image caption: Fafaroma Francis lokacin da ya jagoranci taron addu'o'i a gaban fadarsa ta Vatican

  A duk shekara mabiya addinin kirista a fadin duniya sukan gudanar da biki da kuma hutu domin Easter, musamman domin tunawa da tashin Yesu Kiristi daga matattu.

  Fasto Yohana Buru limamin kirista a jihar Kaduna a Najeriya, ya ce a ranar Easter ne aka gicciye Yesu Almasihu saboda haka ya kamata duk wani kiristan da ya amsa sunansa ya tuna da wannan ranar kasancewar Yesu ya mutu ne domin fansar zunuban al'ummarsa.

  Wasu kiristoci mabiya mazahabar Katolika da Angilikan sukan kwashe kwana 40 suna yin azumi domin tarbar wannan rana.

  Mabiya Kirista a birnin Kudus suna jerin gwano domin bikin Easter
  Image caption: Mabiya Kirista a birnin Kudus suna jerin gwano domin bikin Easter
  Kiristoci kan yi addu'o'i a ranar Easter
  Image caption: Kiristoci kan yi addu'o'i a ranar Easter
  Kiristoci kan yi addu'o'i a ranar Easter
 15. Saudiyya ta ce mutane da dama za su iya yin umrah lokacin Ramadan

  Masallacin Ka'aba

  Saudiyya na shirin ƙara yawan musulmi da ke son yin Umrah lokacin azumin watan Ramadan wanda ya rage saura kwanaki.

  Tun da farko Saudiyya ta rage yawan mutanen da ta amince su gudanar da Umrah saboda annobar korona.

  Mataimakin ministan kula harakokin aikin hajji Abdulfattah Mashat ya shaida wa kafar talabijin ta Al Arabiyya ta ƙasar cewa za a yi wa dukkanin ma’aikatan da ke kula da masallacin Ka’aba rigakafi.

  Ya ce wannan matakin zai ba musulmi masu yawa damar gudanar da aikin Umrah musamman da aka fi zuwa lokacin azumin watan Ramadan.

  Mashat ya jaddada cewa kwamitoci na musamman da aka kafa za su tabbatar da cewa an yi amfani da matakan kiwon lafiya a masallatan harami biyu na Makka da Madina.

  Annobar korona ta tilastawa wa Saudiyya dakatar da yin Umrah a watan Maris din bara. Kuma an rage yawan mutanen da suka gudanar da aikin hajji sosai a shekarar.

 16. Jarumin Bollywood Akshay Kumar ya kamu da korona

  Tauraron fina-finan Bollywood a Indiya Akshay Kumar ya kamu da cutar korona ɗaya daga cikin shahararrun taurarin finafinan Indiya da ya kamu da cutar.

  Jarumin ya ce ya killace kansa a gidansa a Mumbai.

  A cikin sa’a 24 mutum dubu 93 Indiya ta ce sun kamu da korona, adadi mafi yawa da aka taɓa samu a rana ɗaya a duniya.

  Narendra Modi ya tattauna da jami’an gwamnatinsa domin tattauna bazuwar cutar.

  View more on twitter
 17. Chadi ta kama sojojin da ake zargi sun yi wa ƴan mata fyaɗe a Nijar

  Gwamnatin Chadi ta ce ta kama sojojin da ake zargi da yi wa mata aƙalla uku fyaɗe a Nijar da suka ƙunshi har da ƴar shekara 11.

  Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato ma’aikatar harakokin wajen ƙasar na cewa za a hukunta jami’an bisa laifin da suka aikata da kuma neman ɓata sunan sojin ƙasar.

  Sai dai gwamnatin Chadi ba ta bayyana adadin sojojin da ta ce ta kama ba.

  A ranar Juma’a ne hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Nijar ta buƙaci gudanar da bincike kan zargin fyaɗe da ake yi wa sojojin Chadi da aikatawa bayan fitar da rahoton binciken da ta gudanar.

  Shugaba Idriss Deby
 18. Yariman Jordan ya caccaki Sarki Abdallah

  Yarima Hamzah tsohon Yarima mai jiran gado na Jordan
  Image caption: Yarima Hamzah tsohon Yarima mai jiran gado na Jordan

  Yariman Jordan Hamzah bin Hussein ya caccaki ɗan uwansa Sarki Abdallah inda ya ce ƴan ƙasar sun fara yanke masa ƙauna saboda abin da ya kira rashin shugabanci na gari da na son rai.

  Yariman ya kuma ce an yi masa ɗaurin talala.

  Cikin wani hoton bidiyo da ya aike wa BBC, Yarima Hamzah bn Hussein ya musanta yana da hannu a duk wata makarkashiya da ake yi wa Sarkin amma ya ce an janye masa tsaro da kuma iyalinsa.

  Wata sanarwa da aka fitar tun da farko, babban jami'in sojin Jordan ya musanta rahotannin kama Yarima Hamza amma ya ce an nemi Yariman ya dakatar da duk wani abu da zai shafi tsaro da kuma kwanciyar hankalin kasar.

  Sojojin sun kuma tabbatar da tsare wasu manyan mutane da dama saboda abin da suka kira dalilan tsaro.

 19. Bazoum ya naɗa sabon Firaministan gwamnatinsa

  Sabon Firaministan Nijar Ouhoumoudou Mahamadou
  Image caption: Sabon Firaministan Nijar Ouhoumoudou Mahamadou

  Sabon shugaban Nijar Moamed Bazoum ya naɗa tsohon minista Ouhoumoudou Mahamadou a matsayin Firaministan da zai jagoranci gwamnatinsa.

  Shugaban ya sanar da naɗa Firaministan ne a jawabin da ya gabatar a kafar talabijin ga ƴan ƙasa.

  Kafin zaɓensa Mahamadou shi ne shugaban ma’aikata a fadar tsohon shugaban ƙasa Mahamadou Issoufou.

  Mahamadou, mai shekara 69, ya taɓa riƙe muƙamin ministan ma’adinai da makamashi 1999 da kuma ministan kuɗi tsakanin 2011 zuwa 2012. A 2015 aka naɗa shi shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasa.

 20. Korona ta rage bazuwa a Najeriya

  Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 50 daga jiha shida da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Asabar sannan an sallami mutum 18 bayan sun warke daga cutar.

  Kwana uku a jere kuma babu wanda cutar ta kashe a ƙasar.

  Najeriya na cikin ƙasashen Afirka na farko da suka ƙaddamar da rigakafin korona

  View more on twitter