Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

 1. Ban kwana

  Masu bibiyarmu a wannan shafi nan ne muka kawo karshen labaran da muke kawo muku a wannan rana ta Litinin.

  Da fatan zamu sake kasancewa da ku a gobe domin kawo muku wasu sabbin labarai da rahotannin.

 2. Yadda aka kare a sauraren shari'ar Netanyahun

  Reuters

  Wata kotun Isra'ila da ke sauraron karar zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ta shai da cewa yana da damar bagarar da kafafen yada labarai.

  Ilan Yeshua, wanda shi ne shaidar farko da aka kira a yau kan shari'ar, ya ce ya matsawa kafar yada labarai ta Walla kan sai ta rubuta labaran da za su bata abokan hamayyarsa na siyasa.

  Masu gabatar da kara sun ce, kafar yada labaran ta intanet ta wallafa labaran ne kamar yadda aka bukata kuma aka ba ta kyautar miliyoyin kudi.

  Amma duka mutanen sun musanta zargin da ake musu.

 3. Iran ta kama dan leken asirin Isra'ila

  REUTERS

  Kafar yada labaran gamnatin Iran ta rawaito cewa, a ranar Litinin kasar ta cafke wani dan Isra’ila mai leken asiri, da wasu mutane da sukai alaka da jami’an leken asirin wasu kasashe, ba tare da yin karin bayani ba.

  An Ambato jami’in ma’aikatar tsaron kasar na cewa “An cafke dan leken asirin Isra’ila a yankin gabashin Iran da ke gundumar Azerbaijan... da sauran ‘yan leken asiri da ke tuntubar wasu.”

  Kawo yanzu jami’an gwamnatin Isra’ila ba su ce uffan kan wannan batun ba.

  A shekarar da ta wuce ne Iran ta zartar da hukunci akan masu leken asiri ‘yan Isra’ila da Amurka da ta ke tsare da su.

  Harwayau, Iran Iran na zargin Isra’ila da kisan da aka yi wa kwararre kan makaman nukiliya Mohsen Fakhrizadeh, wanda kasashen yammacin duniya ke wa kallon kashin bayan sirin makaman nukiliyar Iran.

  Wanda kasar ta musanta kera sabbin makaman nukiliya, sannan har yanzu Isra’ila ba ta musanta ko amsa ta na da hannu a kisan Fakhrizadeh ba.

 4. 'Yan sandan Dubai sun kama masu daukar fina-finan batsa

  Google

  'Ya sandan hadaddiyar daular larabawa sun kama gungun masu yawon bude ido, kan zargin wallafa bidiyon badala a bainar jama'a a shafukan sada zumunta.

  Bidiyon da masu yawon bude idon da 'yan kasashen ketare suka wallafa a ranar Asabar, ya nuna wasu mata tsrara ana daukarsu hoto.

  Jami'in ofishin jakadancin Ukraine a Dubai, ya shaidawa BBC cewa cikin wadanda aka kama har da mata 11 da aka haifa a Ukraine.

  Ita ma kafar yada labaran kasar Rasha ta rawaito cewa, wadanda aka kama 'yan kasarta ne.

  Wallafa hotuna ko bidiyon badala da gangan babban laifi ne a karkashin dokokin hadaddiyar daular larabawa, da ake yankewa wanda ya aikata hakan zaman kason watanni 6 ko tarar Dirham 5,000, kwaankwacin naira 675,000.

 5. Putin ya sanya hannun kan dokar da za ta bashi damar zama a mulki har 2036

  Reuters

  Kafafen yada labarai na Rasha sun rawaito cewa shugaban kasar Vladimir Putin ya sanya hannu kan wani kudurin doka da zai bashi damar ci gaba da shugabantar kasar wa'adi biyu a nan gaba.

  Wanda hakan zai bashi damar zama kan mulki har shekarar 2036.

  A watan da ya gabata ne majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin a wani bangare na sauye-sauyen da aka yi wa kundun tsarin mulkin kasar da aka saurari ra'ayoyi a bara.

  Putin mai shekaru 68, ya shiga ofis ne a karon farko a shekarar 2000.

 6. An ceto wasu daga cikin daliban Kwalejin Horar da Harkokin Noma ta Kaduna

  KADUNA STATE GOVT

  Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da Gwamnatin Jihar Kaduna cewa an gano biyar daga cikin 30 da suka yi saura a daliban Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Abubuwan da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation da aka sace a watan jiya.

  Cikin wata sanarwa da ma'aikatar tsaron cikin gida ta jihar ta wallafa a shafnta na Twitter tace daliban na hannun jami'an tsaro domin tabbatar da lngancin lafiyarsu.

  Sanarwar ta ce da zarar an samu wani karin bayani game da halin da ake ciki gwamnatin jihar za ta sanar.

  A watan jiya ne aka sace dalibai da dama a wannan kwaleji to amma daga baya aka samu nasarar kubutar da wasu sama da 100 daga ciki.

  Inda Sojojin Najeriyar suka ce sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130. Amma kuma a lokacin ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba, wadanda yanzu aka gano biyar daga cikinsu.

  Hakan dai yana nufin har yanzu akwai sauar dalibai 25 a hannun 'yan fashin dajin.

  Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun daga watan Disambar 2020 .

  BBC
 7. Sojojin Mozambique sun sake karbe iko da garin Palma

  AFP

  Sojojin Mozambique sun karbe iko da garin Palma da ke arewacin kasar wanbda mayakan jihadi suka kai wa hari tare da karbe iko da shi a watan da ya gabata.

  Mai Magana da yawun sojin kasar Birgediya VidigalChongo ya ce baki daya garin Palma na karkashin ikon sojoji da sauran jami’an tsaro.

  Babu wata majiya da ta tabbatar da hakan sakamakon rashin hanyar sadarwar wayar salula, tun watan jiya.

  Za dai a dauki lokaci kafin dubban mazauna garin da suka tsere dan tsira da ransu komawa gida saboda rashin tabbacin tsaron rayukansu.

  A hirar da kafar yada labaran yankin ta yi da tsirarun da suka koma gida, sun bada rahoton samun gidajensu wayam , an sace duk wani abu mai amfani da suka bari lokacin da sukai gudun hijira.

  Kawo yanzu ba bu takamaimai adadin wadanda suka mutu a lokacin da mayakan jihadin suka kai harin.

  Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla farar hula 11,000 ne suka tsere daga yankin yawancinsu mazauna garin Pemba ne.

  A bangare guda kuma, jami’ai sun ce za a tantance duk mazauna garin Palma da suka koma gida, dan tabbatar da babu wani daga cikin mayakan jihadin da ya yi badda kama ya sake komawa garin.

 8. Labarai da dumi-dumiAn sanya dokar hana fita a Umuahia da Aba

  NW

  Gwamnan Jihar Abiya Okezie Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Umuahia da cikin birnin Aba daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

  Yace an dauki wannan mataki ne sakamakon wasu rahotanni da suka samu daga majiyoyi daban-daban.

  Gwamnan bai bayyana wadanne rahotanni ne ba amma ya ce "akwai bukatar kare rayukan 'yan kasar da basu ji ba basu gani ba da sauran mazauna jihar".

  Ana ta fuskantar hare-hare kan jami'an tsaro da kuma wasu kadarorin gwamnati a yankin Kudu Maso Gabas a 'yan makonnin nan.

  A safiyar Litinin ne, aka kubutar da wasu fursinoni daga gidan gyara hali a jihar Imo a wani hari da 'yan bindiga suka kai.

 9. Masarautar Sokoto ta yi nade-nade mafiya yawa cikin shekara 200

  Video content

  Video caption: Saurari rahoton Haruna Tangaza

  Masarautar Daular Usmaniya da ke Sakkwato a Najeriya ta yi nadin sabbin sarautu mafi girma tun kafuwarta fiye da shekara 200 da ta gabata.

  Mutane 20 Mai martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na uku ya nada yayin wani kasaitaccen biki da aka yi a fadarsa jiya Lahadi.

 10. Sojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 11 a Gwoza

  NIGERIA GOVERNMENT

  Dakarun sojin Najeriya sun kashe akalla mayakan Boko Haram 11 a daren Lahadi yayin wata musayar wutar da suka yi tsakaninsu da mayakan kungiyar a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

  Wata majiya ta gayawa jaridar PRNigeria cewa an kashe 'yan Boko Haram din ne lokain da suke yunkurin kai hari ga sojojin Bataliya ta 192.

  "Nan da nan runduna ta 9 suka mayar da martani, suka fara musayar wuta suka samu nasarar kashe wasu tare da tilastawa sauran tserewa.

  "Mun yi musayar wuta da mun kashe 11 daga cikinsu," in ji majiyar.

  Haka zalika sojojin sun samu nasarar kwace bindiga kirar AK-47, da motaci da kuma wasu makamai na aikata muggan abubuwa.

 11. Dubai za ta rage farashin kayan abinci da kashi 75 lokacin Azumi

  Arabnews

  Daukacin kantuna da da wuraren saida kayayyaki da ke hadaddiyar daular larabawa za su rage farashin kayan abinci nau'I 30,000 tun daga kasha 25 zuwa 75 cikin 100 a lokacin watan Ramadan.

  Kamfanin dillancin labaran kasar WAM y ace kayan sun hada da shinkafa, da nama da siga da sauran kayan da aka fi amfani da su a lokacin Azumin.

  Ma'aikatar tattalin arziki ta ce za ta yi zagaye 420, na sa ido dan hukunta wadanda bas u bi dokar ba.

  Jami'an ma'aikatar sun gana da 'yan kasuwa tare da gargadinsu kan karin farashin kayan masarufi a lokacin Azumin, daraktan da ke kula da shige da ficen kayayyaki a ma'aikatar Marwan Al-Sboosi ya bayyana hakan ga manema labarai.

  Harwayau, Al-Sboosi ya kara da cewa jami'an sun kuma gana da wakilan masu saida kayan marmari da na lambu da ke kasuwannin babban birnin kasar domin tabbatar da an samu wadatar kayan marmari da na abinci a lokacin azumin watan Ramadan.

  Akalla a kowacce rana ana amfani da tan din kayan marmari da na lambu 17,000 a cikin Dubai, ya yin da ake amfani da tan 5,000 a birnin Abu Dhabi.

 12. Yan bindiga sun kashe wani fasto bayan sun karbi kudin fansa

  Google

  Yan bindiga sun kashe wani Fasto da ke jihar Legas a Kudancin Najeriya, Frederick Ojo Aramuwa, bayan sun karbi kudin fansar da suka nema naira miliyan 2.

  An tsinci gawar Fasto Aramuwa a kusa da yankin da aka sace shi.

  Wata majiya ta ce an sace shi ne tare da direbansa kwanakin baya lokacin da yake komawa gida zuwa Ifira.

  Majiyar ta ce masu garkuwa da mutanen sun nemi miliyan 10 ne tun da farko amma daga baya suka karbi miliyan 2.

  Amma daga baya wata tawaga ta musamman ce ta nemo gawar tasa.

 13. 'Yan Amotekun sun kama 'masu garkuwa da mutane' a Ondo

  Amotekun

  Jami'an rundunar 'yan banga ta Amotekun sun ce sun kama mutum biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

  Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa 'yan bangar na Amotekun sun kuma ceto mutum uku matafiya daga a kan hanyar Ifira-Akoko/Idoani da ke karamar hukumar Ose daga hannun masu garkuwa da mutanen.

  "Matafiyan su ne Adewale Adebisi, Ahan Mary, da kuma Ladi Bude, wadanda wasu mutane dauke da bindiga suka sace a yayin da suke balaguro tare da wasu mambobin cocinsu daga Benue zuwa Akure, da ke Ondo da safiyar Asabar," a cewar rundunar ta Amotekun.

  Rahotanni sun ce masu garkuwa da mutanen sun tsare hanyar sannan suka umarci mutanen su fito daga motocinsu daga nan suka shiga da su daji.

 14. Gobara ta kashe wasu yara a Suleja

  Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello
  Image caption: Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello

  Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya na cewa wasu yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi a gidansu da ke Anguwar Dawaki a garin Suleja.

  Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yaran - mace da namiji - wadanda da ke suna Suraiya da Habib, ba su wuce shekara tara a duniya ba.

  Rahotanni sun ce mahaifin yaran, Alhassan Jibirin Yanji, ya samu raunuka a lokacin da ya yi yunkurin kubutar da yaran kuma yanzu haka yana kwance a wani asibiti da ke Suleja.

  Hukumomi a karamar hukumar ta Suleja sun tabbatar da tashin gobarar suna masu cewa an kaddamar da bincike domin gano musabbabinta.

 15. Neymar zai sabunta zamansa a PSG, Messi zai yanke shawara kan makomarsa

  Neymar

  Dan wasan gaban Brazil Neymar, mai shekara 29, ya amince ya tsawaita zamansa aParis St-Germainzuwa 2026 - don haka yanzu kungiyar ta Faransa ta mayar da hankali wajen sabunta kwangilar Kylian Mbappe, mai shekara 22.(Telefoot, via AS)

  Kudin sayen dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland zai iya karuwa da euro 40m (£34m), saboda wakilinsa Mino Raiola da mahaifinsa Alf-Inge suna so a bai wa kowannensu euro 20m (£17m) a matsayin la'ada a wani bangare na yarjejeniyar sayar da shi.(RAC1, via Marca)

  Kazalika akwai kudin darajar dan wasan da ke kan Haaland wanda ya kai euro 75m (£64m) da za a titalas wa kungiyar da za ta saye shi ta biya idan ya kai shekara mai zuwa amma zai iya barin Dortmun da bazarar nan a yayin da kungiyar ta kasa katabus a Bundesliga ko kuma idan ta kasa samun gurbin gasar Zakarun Turai.(Sun).

  Karanta cikakken labari kan makomar 'yan kwallon kafa a nan:

 16. Ambaliyar ruwa ta 'kashe mutum 100 a Indonesia da East Timor'

  Gine-Gine sun rufta kan mutane da dama
  Image caption: Gine-Gine sun rufta kan mutane da dama

  Akalla mutum 101 ne suka mutu bayan wata ambaliyar ruwa da zaftarewar laka da suka auka wa Indonesia da East Timor ranar Lahadi.

  Runwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadin rushewar gidaje da dama a makwabciyar kasar da ke Kudu maso Gabashin Asia, inda ruwan ya rika tumbatsa a koguna lamarin da ya ruwan ya malala cikin gidaje ya cinye su.

  Wuraren da ambaliyar ta shafa sun hada tun daga tsibirin Flores da ke gabashin Indonesia zuwa East Timor.

  A kasar Indonesia kadai, mutum 80 sun mutu yayin da da dama suka bata.

  Hukumomi sun yi gargadin cewa alkaluman wadanda suka mutu za su iya fin haka.

  "Taɓo da kuma yanayin maras kyau sun kasance babbar barazana sannan tarkacen da ke yankuna sun sa aikin ceton yana da matukar wahala," a cewar kakakin hukumar takaita hadura ta Indonesia Raditya Djati

  Hukumomi sun ce mutane da dama na binne a kasa sakamakon gine-ginen da suka rufta a kansu kodayake ana kokarin fito da su.

  Ambaliyar ruwa
 17. Yadda Firaiministan Isra'ila ya gurfana a kotu kan cin hanci

  Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

  Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya isa wata kotu da ke birnin Kudus, a yayin da aka bude shari'ar da ake yi masa game da zargin cin hanci da rashawa tare da sauraren shaidu.

  Mr Netanyahu, mai shekara 71, ana zarginsa da cin hanci da zamba da kuma cin amana da ke da alaka da shari'u guda uku.

  A watan Fabrairu ya bayyana cewa ba shi da laifi a kan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

  An jinkirta shari'arsa sau da dama saboda dokokin da aka sanya na takaita zirga-zirga game da annobar korona da kuma zaben da aka yi a watan jiya, wanda ke da muhimanci a kan shari'ar.

  Zaben ya gaza samar da mafita a kan turka-tukar siyasar da aka kwashe shekara biyu ana cikin a kasar, inda jam'iyyar Mr Netanyahu da jam'iyyun adawa suka kasa samun kuri'un da za su ba su rinjiye a majalisar dokokin kasar.

 18. Fatan kun wayi gari lafiya

  Ku biyo ni Nasidi Adamu Yahaya a wannan shafi domin karanta labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya a Nijar da maƙwabtansu.

  Barkanku da wannan lokaci tare da fatan ana hutun Easter lami lafiya.