Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibbiyar mu a wannan lokaci da haka muke banƙwana da ku sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu. A huta lafiya

 2. An damka ɗaliban kwalejin Kaduna da aka gano a hannun iyayensu

  A Najeriya an damka daliban kwalejin Kaduna wadanda ‘yan bindiga suka sace kusan wata guda a hannu iyayensu.

  Gwamnatin jihar ce ta mika daliban ga ‘yan uwa da iyayensu bayan da sojojin Najeriya suka gano su sannan suka duba lafiyarsu.

  Har yanzu dai akwai dalibai fiye da talatin a hannun ‘yan bindigar ko da yake hukumomi na cewa suna kokarin kubutar da su.

  A saurare ƙarin bayani a cikin rahoton Zahraddeen Lawan

  Video content

  Video caption: Saurari yadda aka damka ɗaliban kwalejin Kaduna da aka gano a hannun iyayensu
 3. Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 87 a Sudan

  Likitoci a yankin Dafur na yammacin Sudan sun ce kwanaki biyar da aka shafe ana rikicin kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutun tamanin da bakwai.

  Hakama alkaluman da likitocin suka fitar sun nuna cewa rikicin ya jikkata kusan mutun dari biyu.

  Wani likita a birnin El Geneina ya ce hatta su kansu likitoci basu tsira daha hare-hare ba, a daidai lokacin da suke kokarin ceto rayukan al'umma.

  Rikicin kabilanci a yankin na Dafur na ci gaba a tsakanin al'ummar Masalit da wasu kungiyoyin Larabawa.

  To sai dai mazauna yankin sun ce hukumomi sun fara girke jami'an tsaro tun bayan ayyana dokar ta baci a ranar Litinin.

  Sama da mutun dubu dari ne suka rasa matsugunai a yankin Dafur daga farkon shekara zuwa yanzu.

 4. Kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan saka hoton masallaci a rigar mawaƙi Jay-Z

  MOSQUE
  Image caption: Wannan shi ne masallacin da aka sanya hotonsa a jikin rigar mawakin Amurka Jay-Z

  Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan sanya hoton masallaci mai dimbin tarihi a yankin Lamu na Kenya, a rigar mawaƙin Amurka Jay-Z.

  Shugaban masallacin ya nuna adawarsa da rigar wanda ya ke cewa ana iya sanyata a wuraren da ake munanan ayyuka kamar mashaya.

  "Mun karɓi wasikar afuwan saboda anyi shi ne da zuciya guda," a cewar malaman masallacin.

  Mai kamfanin Zeddie Loky ya ce sun sanya tambarin masallacin ne a jikin rigar domin tallata yankin Lamu.

  Lamu yankin ne mai dimbin tarihi kuma masallacin da aka gina tun a ƙarni na 19 na jan hankali masu zuwa yawon buɗe ido.

  JAYZ
 5. Gwamna Zulum ya rabawa ƴan gudun hijira miliyan 200 a Borno

  BORNO

  Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya rabawa ƴan gudun hijira sama da dubu 70 naira miliyan 200 da kayayyakin abinci a garin Bama.

  Ƴan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, sannan suka rasa damar noma da kasuwanci na tsawon shekaru na rayuwa a sansanoni da dama da ke garin Bama.

  Gwamnan ya raba wannan tallafin ne a sansanoni biyar da ke garin Bama inda kowanne mutum ya samu kuɗi da kayan abinci, sannan mata sun samu atamfa.

  Tun a jiya Talata gwamnan ya je garin na Bama inda ya yi kwana guda da umarta a gaggauta gina gidaje 500 a yankin Nguro Soye, na Baman.

  Sannan ya kuma umarci a gina wasu ƙarin gidajen 1,000 a garin, wanda Boko Haram suka ruguza, domin ganin mutanen da suka rasa muhallansu sun koma gida.

  ZULUM
  BORNO
  BORNO
  BORNO
 6. Gwamnatin Ivory Coast ta bai wa Laurent Gbagbo damar komawa ƙasar

  Shugaban Ivory coast Alassane Outarra ya ce tsohon shugaba Laurent Gbagbo da na hannun damarsa charles na iya dawowa ƙasar duk lokacin suke so.

  Mr Outarra na magana ne mako ɗaya bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta wanke Gbagbo daga aikata laifukan cin zarafin al'umma shekaru goma da suka wuce.

  Sama da mutum dubu uku aka kashe a yaƙin basasa da ya biyo bayan zaben shekarar 2010 a Ivory coast, a lokacin da Gbagbo yaƙi ya sauka daga mulki duk da kayen da ya sha.

  Yanzu dai kotu ta halasta masa karbar duk wani alawus da ake bai wa tsofaffin shugabanni a ƙasar.

 7. Abdulsalami Abubakar ya jagoranci taron Kwamitin zaman lafiya na ƙasa a Abuja

  @raufaregbesola

  Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya tattauna da mambobin kwamitin zaman lafiya na ƙasa wanda tsohon shugaba Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ke jagoranta, a Abuja.

  Sauran mahalarta taron sun haɗa da shugaban cocin katolika na Sokoto, Matthew Kukah da Sultana Sa'ad Abubakar III; da sauran mambobin kwamitin.

  A cewar minista, an gudanar da taron ne a otel din Transcorp da ke Abuja.

  Sai dai ministan bai shaida manufar taron ko abubuwan da suka tattauna ba a taron.

  @raufaregbesola
  @raufaregbesola
  @raufaregbesola
 8. FIFA ta dakatar da Chadi daga shiga harkokin wasan ƙwallon ƙafa

  FIFA

  Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar Chad daga shiga harkokin ƙwallon ƙafa bisa abinda ta kira katsalandan a bangaren gwamnati.

  FIFA ta dakatar da Chadi ne bayan matakin ministan matasa da wasannin ƙasar na kwace ikon da hukumar ƙwallon ƙafar Chadi take dashi.

  Hakama a lokaci guda ministan ya kwace ofishin hukumar watan da ya gabata.

  Dama FIFA ta haramta katsalandan daga bangaren gwamnati kan harkokin kwallon kafa.

  Tuni hukumar kwallon kafa ta Afrika wato CAF ta soke Chadi daga kasashen da za su samu damar halartar gasar cin kofin nahiyar da za a yi a Kamaru.

 9. 'Surutai ba za su hana shugaba Buhari fita waje domin neman magani ba'

  buhari

  Mataimakiya ga shugaba Buhari, Lauretta Onochie, ta ce ba za a iya ɗauke damar da shugaba ke da ita na fita waje domin ganin likita ko neman magani ba.

  Kalamanta sun biyo bayan cacakar shugaban da ake kan fita ƙetare domin duba lafiyar a birnin Landan.

  Wannan batu har ya kai ga wasu rukunin mutane sun gudanar da zanga-zangar a gaban gidan gwamnatin Najeriya da ke birnin Landan.

  Sannan ko a wannan rana ta Larabar, sai da wata ƙungiya ƙarkashin jagoranci Omoyele Sowere ta shirya zanga-zanga a Landan domin tilastawa shugaba Buhari ya koma Najeriya domin duba lafiyarsa, yayinda likitocin ƙasar ke yajin aiki.

  A martanin da ta mayar a shafin tuwita, Onochie ta ce babu abin da zai hana shugaba Buhari fita waje neman magani ko duba lafiyarsa, ko da za a ci gaba da irin waɗanan surutai.

  Ta kuma jadada cewa yanzu shugaban ya soma tafiya domin ko baɗi zai sake zuwa duba lafiyarsa kamar yada aka saba tun 2016 don haka masu surutu su rungumi wannan tsarin domin babu abin da zai sauya.

  View more on twitter
 10. NDLEA ta gano gonakin da ake noman tabar wiwi a Kano

  Hukumar hana sha da fatacin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta gano gonaki uku ake noman tabar wiwi a jihar Kano.

  Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Kano Isa Liktia Muhamamd ya ce sun kuma gano wasu gidaje biyu da ake ɓoye tabar.

  Ya ce an gano gonakin ne a Gwarzo da Dambatta da Ungogo inda tabar wiwin nauyinta ya kai kusan tan ɗaya.

  A rahotanin da hukumar NDLEA ta fitar a baya ta nuna cewa jahar Kano na daga cikin jahohin da ake fama da matsalar shaye-shaye a kasar.

  Isa Likita yashaida wa BBC cewa sun kama mutum biyar da ake zargin su da noma tabar wiwin.

  Ku saurari ƙarin bayanin da shugaban hukumar ya yi wa wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji.

  Video content

  Video caption: Hirar Khalifa Shehu Dokaji da shugaban hukumar NDLEA
 11. An yi wa ɗaruruwan maniyata aikin hajji rigakafin korona a Gombe

  Hukumomi a jihar Gombe ta Najeriya sun ce sun yi wa ɗaruruwan maniyata aikin Hajjin bana rigakafin cutar korona duk da rashin tabbas da ake da na samun tafiya aikin Hajjin daga kasar.

  Wannan na zuwa ne yayin da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta ce sai mutanen da aka yi wa rigakafin ne kawai za a ba izinin gudanar da aikin Umrah da kuma salloli a masallacin harami da ke Makkah a bana.

  Ga karin bayanin da Alhaji Sa'adu Hassan, Shugaban Hukumar Alhazzai ta jihar Gombe ya yi wa Haruna Shehu Tangaza kan dalilansu na yi wa maniyyatan rigakafin.

  Video content

  Video caption: Hirar Haruna Tangaza da Shugaban Hukumar Alhazzai na jihar Gombe
 12. An rantsar da sabon Firaministan Nijar

  Sabon Firaministan Nijar Ouhoumoudou Mahamadou

  An rantsar da sabon Firaministan Nijar Ouhoumoudou Mahamadou wanda zai jagorancin gwamnatin farko ta shugaba Mohamed Bazoum.

  Firaministan ya sha rantsuwar kama aikin ne gaban ƴan majalisa bangaren masu rinjaye, bayan ƴan adawa sun ƙaurace.

  Kafin zaɓensa Mahamadou shi ne shugaban ma’aikata a fadar tsohon shugaban ƙasa Mahamadou Issoufou.

  Mahamadou, mai shekara 69, ya taɓa riƙe muƙamin ministan ma’adinai da makamashi 1999 da kuma ministan kuɗi tsakanin 2011 zuwa 2012. A 2015 aka naɗa shi shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasa.

 13. An ƙaddamar da rigakafin korona a jihar Kogi

  Karon farko an soma rigakafin korona a jihar Kogi da ke yankin tsakiyar Najeriya kusan tsawon wata ɗaya da aka kaddamar da rigakafin a sauran jihohin ƙasar.

  Hukumar kula da lafiya matakin farko ta wallafa a shafinta na Twitter yadda aka soma gudanar da rigakafin a Kogi.

  Gwamnan Kogi Alhaji Yahaya Bello ya taɓa iƙirarin cewa bai yarda da allurar rigakafin korona ba.

  Kwamishinan lafiyar jihar aka fara yi wa allurar da kuma sauran ma'aikatan lafiya. Sai dai ba a ga gwamna Yahaya Bello ba wurin kaddamar da rigakafin.

  View more on twitter
 14. Najeriya ta buƙaci jihohi su dakatar da bayar da rigakafin korona

  Najeriya ta umarci jihohi 36 da babban birnin tarayya da su dakatar da bayar da allurar korona ta farko taAstraZeneca da zarar sun yi amfani da rabi daga cikin kasonsu da aka raba masu domin samun damar bayar da rigakafin ta biyu ga waɗanda aka yi wa ta farko.

  Ministan lafiya Osagie Ehanire wanda ya bayar da umurnin ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da tabbas kan lokacin da za ta samu karin rigakafin bayan Indiya ta dakatar da fitar da dukkanin rigakafin da cibiyar Serum a ƙasar ke samarwa.

  "Mun yi tunanin cewa ya fi dacewa a kammala yi wa waɗanda aka fara yi wa rigakafin gaba ɗaya,” in ji ministan.

  A ranar 2 ga watan Maris ne Najeriya ta karɓi rigakafin korona kusan miliyan 4 na AstraZeneca.

 15. Indiya ta ba Najeriya tallafin rigakafin korona

  Najeriya ta karɓi tallafin korona 100,000 daga gwamnatin Indiya a ranar Laraba.

  Hukumar kula da kiwon lafiya matakin farko ta wallafa hoto a Twitter na sakataren gwamnati Boss Mustapha lokacin da yake karɓar rigakafin daga jakadan Indiya a Najeriya.

  Sai dai gwamnatin Najeriya ba ta bayyana sunan kamfanin da ya samar da rigakafin da ta karɓa daga gwamnatin Indiya ba.

  View more on twitter
 16. Fifa ta dakatar da ƙasar Chadi

  FIfa

  Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya Fifa, ta dakatar da Chadi saboda katsalandan da gwamnati ke yi a harakokin ƙwallon ƙafa.

  Matakin na zuwa bayan ministan wasanni na Chadi ya kori shugabannin hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar a watan Maris.

  Tun da farko hukumar ƙwallon Afrika Caf ta dakatar da tawagar Chadi daga buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika.

  Fifa ta ce za ta iya ɗage dakatarwar a ko wane lokaci kafin babban taronta da za a gudanar ta intanet a ranar 21 ga Mayu

 17. Ƴan bindiga sun kashe mutum 8 a Kaduna

  Najeriya na fama da hare-haren ƴan bindiga a sassan ƙasar

  Hukumomi a jihar Kaduna sun ce ƴan bindiga sun harbe akalla mutum takwas tare da raunata wasu a jerin hare-haren da suka kai ƙauyen Kadanye.

  Kwamishinan tsaro na jihar Samuel Aruwan ya ce ƴan bindigar sun tare hanya ne inda suka buɗe wa motar fasinja wuta da kuma wata buɗaɗɗiyar mota mai ɗauke da katako, kuma nan take suka kashe mutum biyar.

  Wasu rahotanni sun ce mutane da dama ƴan bindigar suka yi daji da su a hari.

  A wata sanarwa da ya fitar, kwamishinan ya ce an kuma kashe mutum uku a wani hari da aka kai ƙauyukan Akibu da Inwola a ƙaramar hukumar Kachia inda aka sace shanu sama da 180.

 18. Mummunan hatsarin mota ya kashe mutum 15 a Kenya

  Akalla mutum 15 suka mutu a wani mummunan hatsarin mota akan hanyar Mombasa-Malindi a Kenya.

  Wani jami’in gwamnati da ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin ya ce wasu da dama ne suka jikkata bayan motar ɗaukar fasinja biyu sun yi taho mu gama. Dukkanin direbobin motar sun mutu

  Wani ganau ya ce hatsarin ya faru ne a hanyar daidai inda da ake gyara

 19. Forbes: Arzikin Dangote da Abdulsamad Isiyaka Rabiu ya ƙaru

  Aliko Dangote

  Arzikin mutane uku da suka fi kuɗi a Najeriya ya ƙaru cikin shekara ɗaya, kamar yadda mujallarForbes ta bayyana bayan fitar da jerin attajiran duniya na 2021.

  Attajiran na Najeriya sun haɗa da shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote da shugaban Glo da Conoil, Dr Mike Adenuga da kuma shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Isiyaka Rabiu.

  Mujallar ta ce arzikinsu ya ƙaru zuwa dala biliyan 22.5 a cikin shekara ɗaya.

  Jerin sunayen attajiran duniya da Forbes ta wallafa a ranar Talata ya ƙunshi attajiran Afrika 14 da suka fi kowa kuɗi a nahiyar.

  Kuma har yanzu a cewar Forbes, shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ne attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.

  Forbes ta ce arzikin Dangote, ya ƙaru inda ya haura $11.5bn daga $ 8.3bn a shekarar 2020, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 191 da ya fi kowa kuɗi a duniya.

  Shugaban kamfanin Glo da Conoil, Dr Mike Adenuga, wanda shi ne na biyu mafi arziki a Najeriya kuma na biyar a Afirka, shi ne na 440 a duniya inda arzikinsa ya ƙaru zuwa dala biliyan $6.1 daga dala biliyan $5.6 a bara.

  Arzikin shugaban kamfanin BUA kuma Abdulsamad Rabiu, arzikinsa ya ƙaru zuwa dala biliyan $4.9 daga dala biliyan $2.9 a bara, kuma shi ne na 574 a jerin attajiran duniya kuma na shida a Afirka.

 20. Tsawon mako ɗaya korona ba ta yi kisa ba Najeriya

  Alƙalumman da hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ke fitarwa game da cutar korona a ƙasar ya nuna cewa tsawon mako ɗaya cutar ba ta yi kisa ba a ƙasar.

  Alƙalumman waɗanda cutar ta kashe ba su sauya ba tun daga 31 ga watan Maris zuwa 7 ga watan Afrilu inda cutar ta kashe jimillar mutum 2,058.

  Alƙalumman da hukumar ta fitar ranar Talata sun nuna cewa ƙarin mutum 58 da sun kamu da cutar korona a Najeriya.

  Jihar Legas da cutar ta fi kamari ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar da mutum 32.

  View more on twitter