Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Ƙarshen rahotannin kenan

  Masu bibiyarmu nan muke rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.

  Mu haɗu da ku gobe domin kawo muku wasu ƙayatattun rahotannin.

 2. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 a Yemen

  Aƙalla mutum huɗu sun mutu a Yemen sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa a birnin Tarim mai ɗumbin Tarihi.

  Gidaje da dama sun ruguje sannan ɓaraguzan gine-gine da suka rushe sun rufe motoci a kan titunan da ke shafe da ruwa.

  Birnin ya shahara da dogayen gine-gine na ƙasa, wadda siffa ce ta musamman da yankin Hadramawt ke da ita.

  A kowace shekara ambaliyar ruwa kan jawo asarar rayuka a Yemen, wanda hakan ke yin barazana ga rayuwar ababen tarihin birnin.

 3. WHO na neman dala biliyan 40 don tallafa wa ƙasashe da rigakafin korona

  Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus

  Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta ce tana buƙatar kimanin dala biliyan 35 zuwa 40 domin tallafa wa shirinta na Covax mai samar da rigakafi ga ƙasashe masu rangwamen arziki.

  Shugaban hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira da a cire dokokin da aka saka kan haɗa rigakafi tare da bayar da dama a haɗa rigakafin a ƙasashen da ake da ƙarancinsa.

  "Idan muna so mu yi wa akasarin al'umma wannan riga-kafin, lallai adadin da muke buƙata a yanzu ya ɗara wanda muke da shi a ƙasa," i ji shi.

  A yau Litinin ne kamfanin Moderna ya yi alƙawarin bai wa shirin Covax rigakafi miliyan 500 cikin wanda zai samar a bana da kuma shekara mai zuwa.

 4. Labarai da dumi-dumiBa mu tabbatar ko 'yan Boko Haram ne suka shigo ba - Gwamnatin Bauchi

  Bala Mohammed

  Gwamnatin Jihar Bauchi ta musanta rahotannin da ke cewa mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun shiga wasu yankuna na jihar.

  Sakataren Gwamnati Sabiu Baba ya shaida wa BBC Hausa cewa ya zuwa yanzu ba su tabbatar ba ko 'yan ƙungiyar ne amma suna taka-tsantsan wajen karɓar mutanen da ƙetarawa cikin jihar daga Yobe sakamakon hare-haren Boko Haram.

  "A halin yanzu ba za a ce 'yan Boko Haram ba ne, abin da muka sani shi ne mutane ne da aka samu matsala a yankunansu suka ga ya kamata su koma wani wuri saboda ba su da inda za su zauna," in ji shi.

  "Mun ɗauki waɗannan matakai ne saboda mun lura tun bayan hare-haren da aka kai a Geidam mutane da yawa ke shigowa Gamawa a lokaci guda.

  "Saboda haka za mu karɓe su amma za mu tantance su saboda kar wajen taimako kuma 'yan Boko Haram ɗin su samu yadda za su shigo."

  Sakataren gwamnatin ya tabbatar da cewa sojoji sun kama mutum biyar da ake zargi da lalata turakun samar da layin sadarwa a yankunan kuma sun miƙa wa 'yan sanda domin gudanar da bincike.

  Kazalika ya nanata cewa mutanen sun kwarara ne cikin ƙananan hukumomin Zaki da Gamawa da Darazo da Dambam.

  Jihar Bauchi na maƙotaka da Yobe ta gabas, inda Boko Haram ta kai zafafan hare-hare a watan da ya gabata, abin da ya jawo fafatwa ta kwana uku a jere tsakaninsu da dakarun Najeriya a garin Geidam.

 5. Microsoft zai samar wa 'yan Najeriya 27,000 aikin yi

  Microsoft

  Katafaren kamfanin fasaha na Amurka, Microsoft, zai haɗa gwiwa da Najeriya domin samar wa mutum aƙalla 27,000 aikin yi, a cewar gwamnatin ƙasar.

  Kazalika, aikin zai samar da layin intanet "mai ƙarfin gaske" a yankuna guda shida na ƙasar sannan kuma za a fara shi nan da 'yan watanni masu zuwa, a cewar Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo.

  Shugaban Microsoft Brad Smith ya ce kamfanin zai horar da 'yan Najeriya miliyan biyar a cikin shekara uku masu zuwa.

  Kamfanin ya ce ƙwararru 1,700 ne za su horar da matasan Najeriya da kuma ma'aikatan gwamnati a ƙasar.

  Haka nan, ya ce yana fatan yaƙar cin hanci da rashawa ta hanyar haɗa kai da gwamnati domin ƙirƙirar fasahohi da ke aiki da intanet zalla wato internet cloud.

  Bugu da ƙari, Microsoft zai haɗa kai da hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC wajen ƙaddamar ƙirƙirarriyar fasaha a yaƙi da cin hanci.

  View more on twitter
 6. An sauke minista a Burundi saboda sayar da jirgin sama

  An sauke ministar Ciniki Da Tafiye-Tfiye da Yawon Bude Ido ta Burundi, Immaculée Ndabaneze daga kan mukaminta saboda "sanya tattalin arziki cikin hatsari da kuma zubar da mutuncin kasa".

  An tsare ta na dan karamin lokaci, sannan aka yi mata tambayoyi kana aka sake ta ranar Lahadi.

  Mrs Ndabaneze tana fuskantar tuhume-tuhume kan cin hanci game da sayar da jirgin sama na kamfanin jiragen saman Air Burundi da aka rusa.

  An sayar da jirgin tsakanin watan Disambar 2020 zuwa watan Janairun 2021 “ga wani dan kasuwar Afirka ta kudu bisa farashi mai matukar rahusa”, a cewar Olucome-Burundi, wata kungiyar da ke yaki da cin hanci ta kasar.

 7. Biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane haramun ne - Sheikh Maqari

  Farfesa Ibrahim Maqari

  Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Najeriya, Farfesa Ibrahim Maqari, ya bayyana cewa biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane haramun ne a Musulunci.

  Jaridar Dateline da ake wallafawa a shafin intanet ta ambato malamin, wanda shi ne mataimakin babban limamin Masallacin Juma'a na Abuja, yana cewa Musulunci ya hana mabiyansa bayar da kudin fansa ga makiya da ake yaki da su.

  Malamin, wanda ya bayyana haka lokacin Tafsirin da yake gabatarwa a watana azumin Ramadana, ya kara da cewa biyan kudin fansa zai karfafa gwiwar masu garkuwa da mutane da kuma ba su karin kudi da za su sayi makamai don ci gaba da kai hare-hare.

  “Tun da Allah (SWT) ya haramta biyan kudi ga makiyi wanda yake yaki da kai, domin kada ka kara masa karfi, don haka biyan kudin fansa domin a saki wanda aka yi garkuwa da shi haramun,” in ji shi.

  Malamin ya ambato Hadisin da wani mutum ya je wurin Manzon Allah yana tambayarsa kan abin da zai yi idan wani ya yi yunkurin ya yi masa fashi da makami, inda Annabi (SAW) ya umarce shi da ya yake shi.

  Batun biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane dai yana jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya inda wasu ke ganin ya dace a biya domin ceton rai, yayin da wasu ke ganin hakan raguwar dabara ce.

 8. Kotu ta yanke hukunci kisan kan kwamandojin kungiyar al-Shabab

  Wata kotu a arewa mao gabashin yankin Puntland mai cin gashin kasa da ke Somalia ta yanke hukunci kisa kan kwamandojin kungiyar al-Shabab guda biyar.

  Kwamandojin su ne Mohamed Hashi Mumin (Abu-dayib), Abdulkadir Ahmed Ummal (Abu-Abdalla), Mohamed Ali Awke (Jeri), Mohamed Abdullahi Ayanle (Abbeyle) da kuma Qasim Jaylani Al-Turabi, a cewar shafin intanet na Radio Dalsan.

  Alkalin kotun sojin Puntland, Kanar Ali Shire, ya ce an samu mutanen biyar da laifin kai hare-hare kan jami'an gwanati.

  An ba su kwanaki 30 domin su daukaka kara.

  Ranar 23 ga watan Afriliu, kotun ta yanke hukuncin kisa kan mayakan al-Shabab takwas bayan ta same su da laifin kashe-kashe da kuma hai hare-hare a lardin Mudug.

 9. Buhari ya amince a kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai a kasar.

  A sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin, ya ambato mai magana da yawun ofishin mai ba Buhari shawara kan sha'anin tsaro yana cewa hukumar za ta kasance a ofishin nasu.

  Hukumar za ta maye gurbin kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar kananan makamai, in ji sanarwar.

  View more on twitter

  Kafa hukumar "na cikin matakan inganta tsaron Najeriya domin magance barazanar tsaro da kuma karfafa shirin da kasashen yankin ke yi wajen takaitawa da magance matsalar yaduwar kananan makamai," a cewar sanarwar.

  A baya dai Shugaba Buhari ya sha kokawa kan karakainar kananan makamai da ma manya cikin kasar, lamarin da ya ta'allaka da yakin da aka yi a kasar Libya.

  Hukumomi sun bayyana cewa akwai dubban kananan makamai a hannun 'yan kasar, abin da ke ta'azzara hare-hare da kuma yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya.

 10. ‘Ana damfarar jama’a da sunan shugaban NNPC Mele Kyari’

  Shugaban babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, Mele Kyari, ya ja hankalin jama'a da su guji yin mu'amala da wasu 'yan damfara da suka bude shafukan Facebook da sunansa.

  Mr Kyari ya ce 'yan damfarar suna amfani da sunansa inda suke kwadaita wa mutane cewa yana bayar da bashi na gudanar da aikin gona.

  View more on twitter

  "Ba ni da wani shafi a Facebook. Akai shafuka da dama a Facebook da aka bude da sunana, amma ba ni da ko daya. Ku kiyaye da 'yan damfara," in j Mele Kyari.

  'Yan damfarar intanet dai suna amfani da sunayen manyan jami'an gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin damfarar jama'a.

 11. Jam'iyyar Narendra Modi ta sha kaye a zaben muhimmiyar jiha

  Masu zabe

  Jam'iyyar Firaiministan India Narendra Modi ta sha kashi a zaben wata muhimmiyar jiha wanda aka gudanar yayin da cutar korona ke ci gaba da kashe dimbin mutane a kasar.

  Jam'iyyar BJP ta yi kokarin cin zaben jihar Bengal inda ta gudanar da gagarumin yakin neman zabe sai dai Mamata Banerjee, gwamnar da ke kan mulki kuma babbar mai adawa da Mordi, ta sake yin nasara.

  Nasarar tata ta bai wa masu fashin-baki kan siyasa mamaki musamman ganin irin makudan kudi da lokacin da BJP ta kashe a jihar.

  Hasalima sai da aka zargi Mr Modi mayar da hankali kan zaben jihar fiye da cutar korona da ke addabar kasar.

  Kazalika an gudanar da zabuka a jihohin Assam, Tamil Nadu da kuma Kerala da kuma lardin Pondicherry (Puducherry).

  Jam'iyyar ta lashe zaben jihar Assam sai dai ba ta kai bantenta ba a sauran jihohin.

 12. DSS ta gargaɗi malaman addini da 'yan siyasa

  DSS

  Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) ta bayyana cewa daga yanzu ba za ta kawar da kai daga wasu mutane da ke neman tayar da zaune tsaye a kasar ba.

  DSS ta soki abin da ta kira wasu kalamai na marasa son zaman lafiya da ke barazana ga gwamnati da dorewar kasar.

  Ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi.

  "Abin da ya ja hankalinmu shi ne kalaman da ba su dace da kuma wasu ayyukan malaman addini da shugabannin siyasa da suka gabata wadanda ko dai suka yi kira a cire gwamnati da karfi ko mkuma suke so a yi tarzoma. Mu gano cewa sun yi hakan ne domin kawo rashin zaman lafiya," a cewar DSS.

  Hukumar ta kara da cewa abin takaici ne mutanen da ake gani da kima suna yin irin wadannan kalamai domin biyan bukatun kashin kansu.

  "Muna masu tuna musu cewa kodayake mulkin dimokradiyya ya bayar da 'yancin fadar albarkacin baki, amma ba ta bayar da damar yin kalamai na ganganci da ka iya shafar tsaron kasa ba," in ji hukumar ta DSS.

 13. An kashe sojojin Jamhuriyar Nijar 16

  Akalla sojoji 16 ne suka mutu a Jamhuriyar Nijar a karshen mako sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai musu a lardin Tahoua.

  An kai harin ne a yankin da aka kashe fiye da fararen hula 200 a wani hari da babu wanda ya dauki alhakin kai shi a watan Maris.

  Wasu masu dauke da makamai ne suka yi wa sojojin kwanton-bauna kusa da garin Agando da ke yankin na Tahoua.

  Sojoji shida sun jikkata a harin kuma ba a san inda soja daya yake ba.

  Shafin intanet na ActuNiger ya rawaito cewa an kai sojojin da suka jikkata wani asibiti da ke yankin na Tahoua yayin da aka binne wadanda suka mutu a gaban jami'an gwamnati da na tsaro.

  'Yan bindigar sun yi gaba da motocin soji uku sannan suka lalata daya, a cewar ActuNiger.

  Yankunan Tillia da Tassara da ke lardin nan Tahoua sun kasance cikin dokar ta-baci tsawon watanni sakamakon hare-haren 'yan ta'adda a yankin da ke kan iyaka da kasar Mali.

 14. Za a ci tarar N100,000 kan duk wanda ya sare bishiya a Abuja

  Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta ce daga yanzu duk wanda aka samu da laifin sare bishiya zai biya tarar N100,000.

  Hukumar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin.

  Sanarwar ta ambato Daraktar kula da wuraren shakatawa, Mrs Riskatu Abdulazeez, tana kara da cewa "haramun ne sare bishiyoyin da aka dasa a cikin gidajen jama'a ba tare da neman izinin gwamnati ba."

  View more on twitter

  A cewarta sare bishiyoyin na ta'azzara matsalolin da ke da dangantaka da sauyin yanayi don haka ba za su bari mazauna birnin su ci gaba da sare bishiyoyi ba tare da la'akari da illar yin hakan ba.

  “Duk wanda ya sare bishiya ba bisa ka'ida ba zai biya tarar N100,000 kuma za a tilasta masa dasa sabbin bishiyoyi biyu domin maye gurbin wacce ya sare." in ji Mrs Riskatu.

 15. Ana taƙaddama kan wanda zai gaji Sarkin Zulu

  Shiyiwe Mantfombi Dlamini Zulu

  Kafofin watsa labaran Afirka ta Kudu sun rawaito cewa takaddama ta kaure kan wanda zai gaji kujerar Sarkin Zulu, Goodwill Zwelithini, lamarin da ya sa aka garzaya kotu.

  Matarsa ta fari, Sarauniya Sibongile Dlamini, ta tafi kotu inda take kalubalantar wasiyyar da ya yi kan wanda zai gaje shi - a yayin da ake zargin cewa an sauya wasiyyar tasa da ta boge.

  Wannan lamari na faruwa kwanaki kadan bayan mutuwar Sarauniya Shiyiwe Mantfombi Dlamini Zulu.

  Ranar 24 ga watan Maris aka nada ta a matsayin Sarauniyar rikon kwarya bayan mutuwar Sarki Zwethilini a wani asibiti sakamakon cutar suga yana da shekara 72.

  Sai dai a takardar karar wadda aka kalubalanci nadin Sarauniya Mantfombi a matsayin mai rikon mukamin Sarkin, Sarauniya Sibongile tana so kotu ta amince cewa aurenta da marigayi sarkin shi ne kawai halastacce.

  Kazalika ta nemi a ba ta damar yin iko da kashi 50 na masarautar.

  Ranar Lahadi, Firaiministan Zulu Yarima Mangosuthu Buthelezi ya bayyana matakin zuwa kotun a matsayin "abin kunya", a yayin da yake magana da gidan rediyon gwamnatin Afirka ta Kudu.

  "Galibin al'ummar Masarautar sun kadu da jin matakin da ta dauka saboda har yanzu tana idda," in ji shi.

 16. Najeriya za ta iya shiga yaki idan ta wargaje - Tinubu

  Tinubu

  Jagoran jam'iyyar APC a Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Tinubu, ya yi gargadin cewa kasar za ta iya fuskantar wani sabon yaki idan ta wargaje.

  Da yake jawabi a wurin lacca da gwamnatin jihar Lagos ta hada a kan azumin Ramadan ranar Lahadi, Tinubu ya ce Najeriya za ta fi dorewa idan tana dunkule wuri daya.

  Yana yin wannan jan hankali ne a yayin da wasu 'yan kasar musamman 'yan IPOB ke fafutukat ballewa daga Najeriya, inda suke matsa kaimi wajen kai hare-hare kan 'yan sanda da wasu hukumomin gwamnati a yankin kudu maso gabashin kasar.

  Sai dai Tinubu ya ce "ba za mu amince" Najeriya ta balle ba yana mai cewa ba shi da kasar da zai je idan kasar ta wargaje.

  Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya kara da cewa kasar ba za ta yi ganganci sake fadawa yaki ba saboda har yanzu tana ci gaba da shan wahala sakamakon illar da yakin basasa ya yi mata.

  "Allah ba zai bar Najeriya ta sake shiga yaki ba. Idan muka ce Najeriya ta rabu, ya kamata mutane su tuna abin da yaki ya haifar a Sudan da Iraki," in ji shi.

 17. Barkanku da warhaka

  Barkanku da hantsi. Da fatan an wayi gari lafiya.

  Ku biyo ni Nasidi Adamu Yahaya a wannan shafi domin karanta labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya a Nijar da maƙwabtansu.