Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Jabir Mustapha Sambo da Imam Saleh

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Imam Saleh

  Multimedia Broadcast Journalist

  BBC Hausa
  Image caption: Imam Saleh

  Masu bibiyarmu a wannan shafi a nan za mu dakata da kawo muku labaran halin da duniya ke ciki kai tsaye, amma za mu sake dawowa gobe da safe domin ɗorawa daga inda muka tsaya.

  Za ku iya sake karanta labarai masu jan hankali da muka wallafa tun daga safiyar wannan rana har zuwa yanzu idan kuka duba ƙasa.

  Sunana Imam Saleh. Allah ya bamu alheri.

 2. Babban kuskure ne Buhari ya bamu ikon juya jami'an tsaro - Gwamna Wike

  Gwamnan Rivers
  Image caption: Nyesom Wike

  Jaridar Vanguard News a Najeriya ta rawaito gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, na cewa ya saba wa tsarin mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari ya karkatar da ikon tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya ga gwamnonin jihohin.

  Wike ya ce Shugaba Muhammadu Buhari shi ne Babban Kwamandan Sojoji kuma ba zai iya bayyana cewa gwamnoni ne ke kula da tsaro a jihohin su ba.

  Gwamnan, wanda ya yi magana a yayin kaddamar da titin Odufor-Akpoku-Umuoye mai nisan kilomita 21 a karamar hukumar Etche na jihar, a ranar Talata, a cewar wata sanarwa daga Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai Kelvin Ebiri, ya ce irin wannan matsayin ya nuna cewa APC ta jagoranci gwamnati ta rasa makamar dabarun yadda za a magance rashin tsaro.

  Ya ce: “Ya Shugaba, kai ne Babban Kwamandan askarawan Sojojin Tarayyar Najeriya. Kun nada Sufeto Janar na 'yan sanda (IG), kun nada shugaban hafsoshin soja, shugaban hafsan sojin ruwa, Daraktan hukumar tsaron farin kaya (DSS), da sauran shugabannin tsaro. Wanne zamu sanya? Ta yaya mutanen da Shugaban Kasa ya nada za su kasance a karkashina?

 3. ''Shugaban Twitter da kamfaninsa ne ke da alhakin rayukan da suka salwanta a zanga zangar EndSARS''

  Jack Dorsey da Buhari
  Image caption: Jack Dorsey da Buhari

  Gwamnatin Najeriya ta daura alhakin mutanen da aka kashe yayin zanga zangar End SARS kan shugaban kamfanin twitter Jack Doresey.

  Ministan watsa labarai na Najeriya Lai Muhammad ya ce Mista Dorsey da kamfanin sada zumuntarsa ne ke da hannu a kisan. Har yanzu ba su mayar da martani kan zargin ba.

  Dubban ‘yan Najeriya sun fita kan tituna a watan Oktoban da ya gabata a zanga-zangar adawa da cin zarafin‘ yan sanda.

  Ministan yada labarai Lai Mohammed ya yi zargin cewa Mista Dorsey ya kaddamar da gidauniyar hada kudi don gudanar da zanga-zangar, yana neman mutane su ba da gudummawa ta hanyar bada kudin Internet wato Bitcoin.

  ''Twitter ya kara ruruta wutar rikicin ta hanyar samar da hoton alama dake dauke da tambarin EndSars'', in ji shi.

  Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito Ministan yana cewa "Idan ka nemi mutane su ba da gudummawar kudi ta hanyar Bitcoin don masu zanga-zangar EndSars to lallai za ka dauki alhakin duk abin da sakamakon zanga-zangar ya haifar."

  "Mun manta cewa EndSars ta haifar da asarar rayuka, ciki har da 'yan sanda 37, sojoji shida, fararen hula 57 yayin da aka lalata dukiya ta biliyoyin nairori." Inji shi.

 4. Korona ta kashe mutane dubu 600 a Amurka

  Biden
  Image caption: Biden

  Mutum fiye da dubu dari shida ne suka rasa rayukansu Amurka sanadin cutar Korona.

  Cibiyar Johns Hopkins da ke bibiyar annobar ne ya tattara alkaluman wanda shi ne mafi girma a duniya.

  Haka kuma wannan shi ne matsayin da kasar ta dauka bayan bazuwar cutar a kasashen duniya.

  Alkaluman na zuwa ne a ranar da gwmnan jihar Newyork Andrew Cuomo ya sasauta dokar kule a daukacin jihar.

  Ya dauki wannan mataki ne bayan da aka yi wa sama da kashi sabain cikin dari na manyan da ke jihar alluran rigakafin cutar korona karo na farko

 5. Muna son karfafa kawancenmu da Najeriya - Koriya Ta Arewa

  Kim Jong Un
  Image caption: Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un

  Jakadan Koriya ta Arewa a Najeriya Chi Tun Chon Hu, ya ce gwamnatinsu ta ba da fifiko wajen bunkasa alakar kasashen biyu.

  Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja lokacin da ya ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

  Ya ce ya lura cewa Najeriya da Koriya ta Arewa sun yi tarayya a abu daya, inda ya ce rajistar jam’iyya da jam’iyya mai mulki a kasar ta APC ta yi a kwanan nan babbar nasara ce.

  Jakadan ya ce: “Kasashenmu biyu suna da dadaddiyar dangantaka da hadin kai.musamman ta fuskar kirkire-kirkire da ke amfanar kasashen biyu.

 6. Najeriya za ta buga wa ƙasar Gambia kuɗi

  Buhari da shugaban Gambia
  Image caption: Buhari da shugaban Gambia

  Babban Bankin Najeriya CBN ya amince ya buga wa ƙasar Gambia nau'in kuɗinta na Dalasi.

  Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin takwaransa na Gambia Buah Saidi yayin da ya ziyarce shi da tawagarsa a ranar Talata.

  Mista Emefiele ya ce Najeriya na da damar da za ta iya bugawa Gambia kudin, da yake ta jima tana buga kudi tun shekarun 1960.

  Tun da farko gwamnan babban bankin Gambian ya ce kasarsa na fama da karancin kuɗi, sannan suna fatan samun ƙwarewa wajen buga kuɗin daga Najeriya.

 7. Yahudawa na cincirindo a gabashin ƙudus

  Yahudawa
  Image caption: Yahudawan da suka taru a gabashin ƙudus

  Kungiyoyin masu kishin Yahudawa a Isra'ila na taruwa a gabashin Kudus da aka mamaye don gudanar da taron shekara -shekara da ake yi don tunawa da ranar da Isra'ila ta kwace gundumar a shekara 1967.

  Macin na tutocin zakaran gwajin dafi ga sabuwar gomnatin Israila wadda kawance ne na lalura da ya kunshi masu ra’ayin mazan jiya da masu sassaucin ra'ayi da kuma jamiyyun Larabawa.

  Louis Fishman mai sharhi ne akan alanurab yau da kullum a Israilar, ya ce a yanzu mun samu gomnati da ke da sassaucin ra’ayi da kuma jammiyun larabawa, akan haka muna ganin wannan zai isar da sako mai karfi, sai dai ana ganin macin zai sake janyo tashin hankali tsakanin kungiyar Hamas da sauran kungiiyoyin Falasdinu wadanda suka ayyana shi a matsayin ranar fushi

 8. Ana barazanar halaka ni - AbdulRasheed Bawa

  Shugaban hukumar EFCC
  Image caption: Abdulrashin Bawa

  Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya ta'annati wato EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce ana ta aika masa da sakonnin barazana ga rayuwarsa tun bayan da ya hau shugabancin hukumar.

  Ya bayyana hakan ne yayin wani shirin barka da safiya na gidan talabin ɗin Channels dake Najeriya.

  ''A makon da ya wuce ina New York aka kira wani babban mutum a kasar nan aka gaya masa cewa za mu halaka wannan yaron da yake shugabancin hukumar EFCC'', in ji Bawa.

  Ya ƙara da cewa ''Toh ka ga wannan yana nuna maka irin yadda cin hanci ke yaƙarka a lokacin da kai kake yaƙi da shi, gaskiya ne duk inda ka waiwaya za ka ga cewa akwai matsalar nan, amma ina da kwarin guiwar cewa za mu karo karshenta a Najeriya", a cewarsa.

 9. Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 15/06/2021

  Ku saurari labarai cikin Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 15/06/2021. Jabir Mustafa Sambo da Imam Saleh ne suka karanto.

  Video content

  Video caption: Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 15/06/2021
 10. Gwamnonin PDP sun bukaci Buhari ya janye dakatarwar da ya yi wa Tuwita

  Peoples Democratic Party

  Gwamnoni daga jam'iyyar PDP a Najeriya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya duba yiwuwar janye dakatarwar da ya yi wa kamfanin sada zumunta na Tuwita.

  A sanarwar da gwamnonin suka fitar bayan wani taro da suka yi a garin Uyo na jahar Akwa Ibom, sun zargi gwamnatin Najeriya da nuna son rai wurin ɗaukar matakin.

  Sanarwar ta ƙara da cewa matakin ya ƙuntata wa matasan Najeriya da dama, wadanda sun dogara ne da kafar Tuwita wurin neman abinci.

  A makonnin da suka wuce ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da Tuwita, bayan zargin kamfanin da saɓa dokokin sadarwa da ta shimfiɗa.

  Tun a lokacin ne a ke ci gaba da cece-kuce kan dakatarwar.

 11. Ƙungiyar ƙabilar Igbo ta zargi gwamnati da kashe ƴaƴanta fiye da 500 cikin kwana 160

  Ndigbo

  Kungiyar kare al'adu da muradun ƙabilar Igbo, wato Ohanaeze Ndigbo, ta zargi gwamnatin Najeriya da halaka 'yan kabilarta fiye da 500 a cikin kwana 160 din da suka wuce.

  Kazalika kungiyar ta soki lamirin dattawan arewacin Najeriya, tana cewa sun yi ko-oho da abin da ake yi wa al`ummarta.

  Babban sakataren Ohanaeze Ndigbo, Okechukwu Isiguzoro, a cikin wata sanarwar, ya ce ƴan kabilarsu mutum 513 ne aka kashe, sannan mutum fiye da 2,400 sun ɓace a cikin kwana 160 din da suka wuce.

  Har zuwa lokacin bayar da wannan rahoton dai gwamnatin Najeriya ba ta ce komai game da wannan zargi da Ohanaeze ke yi ba.

  Amma kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta sha fadar matsayinta a kan ta-da-kayar bayan da masu fafutukar ballewa daga kasar, wato IPOB ke yi.

  Kungiyar dattawan arewacin Najeriyar ta ce ya kamata gwamnati ta gaggauta bai wa ƴan kabilar Igbo damar ɓallewa ko kafa tasu kasar cikin ruwan-sanyi, maimakon hare-haren da suke kaiwa suna kashe jama'a, musmaman 'yan arewa, tare da lalata musu dukiya.

  ACF na cewa dattawan kabilar Igbo sun ki cewa uffan a kan kisan da ake yi wa ƴan arewa da ke zuwa yankin kudu maso gabashin Najeriyar, kama daga zanga-zangar End Sars zuwa hare-haren da ke kaiwa na baya-bayan nan.

 12. Amurka da Tarayyar Turai sun warware rikicinsu na tsawon shekara 17

  EU

  Amurka da Tarayyar Turai EU sun warware rikicinsu na tsawon shekara 17 a kan tallafin jiragen sama kuma sun amince sun janye tallafin biliyoyin dala da ake bai wa wasu kayayyaki.

  Mai magana da yawun EU ta ce "matsayar da muka cimma ta ba mu damar bude sabon babi a dangantakar da ke tsakaninmu saboda yanzu za mu mai da hankali a kan yadda za mu riƙa haɗa kai kan batutuwan da suka shafi jiragen sama."

  Tun shekarar 2004 ne Amurka da Tarayyar Turai suke takaddama a kungiyar cinikayya ta duniya, a kan tallafin da Amurka ta ba kamfanin jirgin sama na kasar wato Boeing da kuma wanda EU take bai wa kamfanin Airbus na Turai.

  A yanzu matsayar da suka cimma za ta ba su damar mayar da hankali a kan kalubalen da suke fuskanta daga fannin masana'antun jiragen sama na China.

 13. Kundin Tsarin Mulkin Abacha na 1995 ne ya fi dacewa da Najeriya - Ngige

  Ngige

  Ministan Ƙwadago da Ayyukan Yi na Najeriya Dr Chris Ngige, ya ce Kundin Tsarin Mulkin kasar na shekarar 1995 ƙarƙashin mulkin Janar Sani Abacha, wanda ya yi mulki tsakanin shekarun 1993 zuwa 1998, shi zai fi dacewa da ƙasar.

  Da yake magana a gidan talbijin na Channels a ranar Litinin, ministan ya ce wa'adin mulki na shekara biyar karo guda kawai da kuma tsarin karɓa-karɓa shi ne kawai zai warware matsalar nuna bambanci.

  "Na yi amanna a yau, da gobe, Kundin Tsarin Mulkin Abacha na 1995 da ya tsara karɓa-karɓar mulkin shugabancin ƙasa zuwa yankunan Najeriya shida, da wa'adin shekara biyar a karo ɗaya kawai, zai magance dukkan matsaloli; da magance jin zafin yaƙin basasa, da kuma jin zafin June 12," kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

  "A yanzu, wannan kundin tsarin mulki shi ne zai fi dacewa ga ƴan Najeriya su yi amfani da shi nan da shekara 30 inda dukkan yankunan ƙasar shida za su ɗanɗani zaƙin shugabancin ƙasar," in ji shi.

  Ngge ya kuma ce da hakan zai magance batun bambanci idan yankin Kudu Maso Gabashin ƙasar ya samar da shugaban ƙasa na gaba.

  "Mutanen yankin suna ganin kamar an ware su, ba a yaba musu, ko dai don farfaganda ko kuma don an zuga su, wanda a yanzu hakan ba shi da amfani," in ji Ngige.

 14. China ta gargadi NATO kan yi mata katsalandan

  China

  China ta zargi kungiyar NATO da yi wa shirinta na samar da zaman lafiya kafar ungulu.

  Tun da farko Nato ta zargi gwamnati a Beijing da cewa take-takenta na fadada makamashin Nukiliya ya saba wa dokar tsaro ta kasa da kasa.

  Wannan ne karon farko da Nato ta mayar da hankali kan Chana a irin wadannan taruka.

  Sa dai a martanin da ta mayar China ta ce tsarin tsaron da take dashi na kariyar kai ne, inda ta bukaci kungiyar da ta maida hankali kan tattaunawa ba takalar magana ba.

  Sanarwar ofishin jekadancin China a kasashen Turai ta ce ''tsarin da muke da shi kan sha'anin tsaro mun gina shi ne bisa ka'ida da hujja da kuma sanin yakamata''.

  Sanarwar ta kara da cewa ''akwai bukatar Nato ta kalli ci gaban da China ke samarwa ba ta maida hankali kan batutuwan siyasa da ba su da tushe ba.

 15. UNICEF ta nemi a gaggauta ceto 'yan Islamiyya da aka sace a jihar Neja

  Tegina

  Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef, ya bayyana matukar damuwa kan makomar yaran da aka sace a wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina a karamar hukumar Rafi a jihar Nejan Najeriya.

  A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, Unicef ta yi kira da a yi gaggawar ceto yaran, wadanda a cikinsu har da 'yan kasa da shekara biyar.

  "Iyaye na kewar 'yan uwansu, 'yan uwa na kewar 'yan uwansu - dole a saki yaran nan cikin koshin lafiya a mayar da su wajen iyalansu.

  "Abin tsoro ne a ce yanzu kai hare-hare ya kan makarantu da 'yan makaranta - kuma a wannan lamarin a ce har da 'yan shekara uku a cikin yaran da aka sace.

  "Kawai muna tunanin irin halin kaɗuwar da suke ciki, da illar da hakan zai yi a kan lafiyar jikinsu da ƙwaƙwalwarsu.

  Unicef ta jaddada cewa hare-hare a kan makarantu take haƙƙin yara da na ilimi ne.

  Sannan ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi duk abin da ya dace don kare makarantun ƙasar, ta yadda babu yaran da zai dinga jin tsoron tafiya karatu.

 16. Ƴan sanda sun gaza hana mutane rububin kwasar daiman

  rububin daiman

  Ƴan sanda a ƙauyen Kwazulu-Natal da ke Afirka Ta Kudu suna ta fafutukar dakatar d mutane daga neman abin da suka yi amannar cewa daiman ne, a yayin da ɗumbin jama'a ke ci gaba da rububin zuwa wajen.

  Mutane na ta rububin zuwa ne bayan da wani makiyayi ya gano abin da ya yi amannar cewa daiman ne fiye da mako ɗaya da ya wuce.

  Ganowar ta sa mutane daga sauran yankuna na ta zuwa wajen da ƙafa don rububin nema.

  A lokacin da wakiliyar BBC ta isa wajen, ta ga ɗaruruwan mutane da yawancinsu mata ne marasa aikin yi, sun taru suna jin ɗumin wuta, bayan da suka shafe dare suna haƙo abin da suke fatan ya zama daiman.

  rububin daiman

  Ana iya jiyo wasu matan suna waƙe-waƙe daga nesa yayin da ake amfani da shebur da fartanya don haƙo ƙasar.

  Gwamnati ta tura tawagar masu ilimin haƙar ƙasa da masu haƙar ma'adinai don tabbatar da cewa idan har daiman ne aka gani a yankin.

  Tuni gwamnatin yankin ta bayyana abin da mutanen ke yi a matsayin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

  rububin daiman
 17. Dole a gudanar da sahihin zaɓe a Mali - MDD

  Col Assimi Goita

  Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira da a gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a Mali.

  A ƴan makonnin da suka wuce ne sojoji suka yi juyin mulki a ƙarƙashin jagorancin Kanar Assimi Goita.

  Kwamitin ya kuma ce bai amince sojojin su shiga zaben na watan Fabrairun baɗi ba.

  A cewar jakadan Faransa a MDD Nicolas de Riviere ''babban abin da ya kamata a bai wa fifiko shi ne shirya zaben shugaban kasa a Mali a watan Fabrairun 2022''.

  Shi ma wakilin MDD na musamman a Mali El-Ghassami Wane, ya yi kira ga kasashen duniya da su zo a haɗa ƙarfi don ceto Mali daga halin rashin tsaro da kuma matsin rayuwa.

  Ya kara da cewa sabon shugaban kasa da Firaminista sun ba da tabbacin cewa za su boi matsayar da aka cimma kan batun miƙa mulki.

  An yi juyin mulki biyu cikin watanni tara a Mali, inda Kanar Assimi Goita ya bayyana kansa a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.

  Ya kuma naɗa jagoran adawa Choguel Maiga a matsayin Firaminista.

 18. 'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a tsakiyar Najeriya

  Bandits

  Rahotanni daga tsakiyar Najeriya na cewa aana fargabaran kashe gwammai a jihohin Filato da Benue.

  A Tagwayen hare-haren da aka kai jahar Benue an kashe mutun 11 a ranar 13 ga watan Yuni bayan wani kazamin hari kwana guda kafin nan.

  Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa an kona mutun shida da ransu a jahar Anambra, yayin da aka kashe karin wasu mutun 20 a jahar Plateau.

  Rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara a Najeriya.

  Amma a hira da gidajen talabijin, Shugaban Muhammadu Buhari ya ce nakasun da gwamnatinsa ke samu wurin tunkarar matsalar tsaro na da alaka da rashin damar shigowa da isassun makamai.

 19. ISWAP ta saki ma'aikatan agaji a Najeriya

  ISWAP

  Kungiyar ISWAP reshen Afrika Ta Yamma ta saki wasu ma'aikatan agaji da ta ke rike da su watanni biyar da suka wuce.

  Mai magana da yawun hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNHCR ya tabbatar wa da BBC cewa kungiyar ISWAP ta saki ma'aikacinsu da ke hannunta a ranar Litinin.

  Ya kara da cewa UNHCR na godewa hukumomin Najeriya kan rawar da suka taka.

  Kafafen yada labarai na cikin gida na cewa yanzu haka wadanda aka sakon da yawansu ya kai 10, na asibiti ana bincikar lafiyarsu kafin a miƙa su ga iyalansu.

  Sai dai babu wata sanarwa game da yadda yarjejeniyar sako su ta gudana.

  A baya ISWAP ta sha kashe wadanda take garkuwa da su a duk lokacin da suka gaza cimma matsaya tsakaninsu da hukumomin Najeriya.

 20. Ƴan Najeriya na fama da yunwa da rashin tsaro - CAN

  Nigeria hunger

  Kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN reshen arewacin kasar ta ce tabarbarewar tsaro da kuma matsin tattalin arziki ya jefa miliyoyin yan Najeriya cikin yunwa da talauci.

  CAN ta ce ba ta ga alfanun bikin ranar demokradiyya ba da aka yi a ranar 12 ga watan Yuni, la'akari da yadda ake ci gaba da satar dalibai da kuma hana manoma shiga gonakinsu, wanda kungiyar tace zai haifar da yunwa a nan gaba.

  Jaridar The Nation ta ambato kakakin kungiyar reshen arewa, Rabaran Jechonia Albert na cewa ''CAN ta damu da yadda hare-hare ke karuwa a makarantu, da kuma satar dalibai musamman a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da kuma Neja.

  A makonnin da suka gabata ne wasu mahara suka sace daruruwan daliban makarantar Islamiyya a garin Tegina na jahar Neja.

  Shugaba Buhari a jawabinsa na ranar demokradiyya ya sha alwashin tabbatar da gwamnatinsa ta kawo karshen hare-haren 'yan bindiga.