Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Halima Umar Saleh da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

 1. Mu kwana lafiya

  A nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke ba ku a wannan shafi na kai-tsaye. Sai ku tare mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni.

  Kada ku manta za ku iya karanta karin labarai a babban shafinmu na bbchausa.com, sannan kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta.

 2. Majalisar dokoki ta amince a daina yanke hukuncin kisa a Sierra Leone

  'Yan majalisar dokokin Sierra Leone sun amince da gagarumin rinjaye da kudin dokar daina yanke hukuncin kisa a kasar, kamar yadda wakilin BBC a kasar Umaru Fofana ya rawaito.

  Za a maye gurbin hukuncin kisa da daurin rai da rai a gidan yari, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

  A watan Mayu, mataimakin ministan shari'ar kasar ya sanar cewa za a daina yanke hukuncin kisa a kaar.

  Kungiyar kare hakkn dan adam ta Amnesty International ta ce an yanke hukuncin kisa 39 a Sierra Leone a shekarar da ta wuce.

  Sai dai ba a zartar da hukuncin kisa ba tun 1998.

 3. Wasu 'yan fashin teku za su sha daurin shekaru 12 a Najeriya

  Mai gadin teku

  Wata kotu a Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara 12 kan wasu 'yan fashin teku da suka sace wani jirgin ruwan kamun kifi na kasar China da kuma matukansa a watan Mayun shekarar da ta wuce.

  Wannan shi ne hukunci irinsa na farko da aka yanke wa barayin tekun a karkashin sabuwar dokar haramta sata a kan teku da aka zartar a 2019.

  Kazalika alkalin babbar kotun ya umarci mutanen da aka samu da laifi su biya tarar $600 (£435) sannan ya ce su "abin kunya ne ga kasar nan" kuma fashin da suka yi ya yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito.

  A watan Agustan da ya wuce, wata kotu a kudancin Najeriya ta yanke hukunci na farko kan masu fashin teku guda uku, karkashin sabuwar dokar, inda ta ci su tara kan kwace wata tanka a gabar tekun Equatorial Guinea sannan suka nemi kudin fansar da ya kai $200,000 kan mutanen da suka sace.

 4. An bude Gasar Olympics ta 2020 a Tokyo

  Naomi rike da fitilar gasar Olympic

  A hukumance an soma gasar Olympic ta 2020 a birnin Tokyo na kasar Japan bayan da 'yar wasan tennis Naomi Osaka ta kunna fitilar kaddamar da gasar a wurin bikin bude ta ranar Juma'a.

  An soma gasar ce, wadda aka so gudanarwa a bara amma aka ɗaga sakamakon annobar korona, ba tare da irin bukukuwan da aka saba aiwatarwa ba.

  Da yake jawabi yayin bude gasar, shugaban kwamitin duniya kan gasar ta Olympic Thomas Bach, ya ce "Eh, yanayi ne na daban idan aka kwatanta da abin da muka yi tsammani. Amma bari mu yi godiya kan yadda daga karshe muka zo nan."

  Wannan gasa za ta kasance daban da wadda aka sha gudanarwa saboda dole mahalartanta su rika sanya takunkumi, sannan an yi ta samun masu dauke da cutar korona kana babu 'yan kallo.

  Amma duk da haka gasar Olympics ce; wacce ta kasance wasa mafi girma a doron kasa.

 5. 'Yan bindiga sun sace matan aure da kananan yara a Dansadau

  Mazauna garin Dansadau na jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kwana cikin fargaba bayan da wasu mahara dauke da

  manyan bindigogi da makamai su ka afka wa garin cikin daren jiya.

  Mazauna garin sun shaida wa BBC cewa tun karfe 2:30 'yan bindigan suke bi layi-layi, gida-gida suna balle gidajen

  mutane, kuma bayan nan sai su ka rika daukar matan aure da kananan yara suna tafiya da su cikin daji.

  Latsa hoton da ke kasa domin sauraren rahoton da Sani Aliyu ya hada mana:

  Video content

  Video caption: 'Yan bindiga sun sace matan aure da yara kanana a Dansadau
 6. Kotu ta bayar da umarni a saki matar Sunday Igboho

  Kotun daukaka kara da ke Cotonou, Jamhuriyar Benin ta ba da umarnin a saki Misis Ropo, mai dakin dan fafutuka kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo da ake kira Sunday Igboho.

  Ana zargin Sunday Igboho da shiga kasar jamhuriyar Benin ba bisa ka’ida ba.

  Za a ci gaba da shari’arsa zuwa ranar Litinin, 26 ga Yuli, 2021 domin bin bahasin ko za a tasa keyarsa zuwa Najeriya ko kuma a’a.

  Latsa hoton da ke kasa don sauraren rahoton Umar Shehu Elleman:

  Video content

  Video caption: Kotu ta bayar da umarni a saki matar Sunday Igboho
 7. Kenya na amfani jirgi marar tuƙi wajen kashe sauro

  Kenya Mosquito

  Kenya ta fara amfani da jirgi marar matuƙi wajen gano wuraren da sauro ke hayayyafa a ƙasar tare da kashe su tun suna ƙwayaye.

  Ministan Lafiya Mutahi Kagwe ya ce jirage marasa matuƙan za su taimaka wajen gano wuraren da ke da wuyar kai wa musamman a ƙasashen da cutar maleriya ta fi ƙamari.

  Jiragen za su dinga fesa wani magana mara cutarwa ga ɗan adam da zai kashe ƙwayayen sauraye.

  Wannan zai tabbatar da cewa sauro ba su hayayyafa a yayin da ake ci gaba da yaƙi da cutar maleriya.

  Hukumar Maleriya ce ta gabatar da fasahar ga gwamnatin Kenya - wata hukuma ta hadin gwiwa da gwamnati da ke yaƙi da maleriya a ƙasar - a cewar ministan lafiyan.

 8. Son ya tsawaita zamansa a Tottenham

  Son

  Dan wasan gaba na Tottenham Son Heung-min ya sanya hannu a sabuwar kwangilar shekara hudu a kungiyar inda zai ci gaba da murza leda zuwa 2025.

  Son, mai shekara 29, ya zura kwallaye 107 a wasanni 280 da ya buga wa kungiyar tun da ta saye shi daga Bayer Leverkusen a 2015.

  Ya buga wa kasarsa Koriya Ta Kudu wasanni 93, kuma ya ci mata kwallaye 27 sannan sau biyu yana buga Gasar cin Kofin Duniya.

  "Ban yanke wata shawara ba. Komai ya zo cikin sauki. Ina cike da farin ciki a nan kuma zan yi matukar murnar sake ganin masu goyon bayana," in ji shi.

  "Babbar martaba ce a gare ni na buga wasa a nan na shekaru shida. Kungiyar nan ta yi matukar martaba ni kuma a bayyane yake cewa ina farin cikin kasancewa ta a nan."

  Karanta cikakken labarin a nan:

 9. Wani mutum ya 'kashe' matarsa kan N1,000 a Adamawa

  Babban sufeton 'yan sandan Najeriya

  Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa da ke area maso gabashin Najeriya ta ce ta kama wani magidanci da take zargi da kisan matarsa sakamakon rikici kan N1,000.

  Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Sulaiman Nguroje, ya fitar ranar Alhamis ta ce mutumin mai suna Hammawa Usman, mai shekara 41, da ke karamar hukumar Ganye yana hannunta bisa zargin kisan matarsa mai suna Rabiyatu Usman.

  Mr Nguroje ya ce mutumin ya soma fada da Rabiyatu bayan ta nemi ya biya ta N1,000 da take binsa.

  “Mutumin da ake zargin ya mayar da martani cikin fushi inda ya buga kanta a jikin bango... hakan ya sa ta fadi a sume inda aka garzaya da ita asibiti kuma a nan rai ya yi halinsa.

  “Daga bisani 'yan sanda sun kamo mutumin bayan wani dan uwan matar ya kai musu rahoton faruwar lamarin,” in ji Mr Nguroje.

  Ya kara da cewa bincike ya gano cewa mutumin da ake zargi da kisan, wanda ma'aikacin gwamnati ne, yana da 'ya'ya biyar d suka haifa tare da matar a shekaru 16 da suka yi a matsayin mata da miji.

 10. An ci tarar kamfani £2.6m kan ikirarin da yi cewa tufafinsa yana maganin korona

  Wata mace sanye da tufafin Lorna Jane

  An ci tarar wani kamfanin tufafin masu motsa jiki na Australia £2.6m sakamakon ikirarin da ya yi cewa tufafin da ya samar suna "kawar da" cutar korona.

  Kamfanin Lorna Jane ya dade yana talla cewa tufafin da ya samar suna amfani da "wata fasaha ta musamman" da ake kira LJ Shield domin hana "yada dukkan kwayoyin cuta".

  Sai dai a wani zama da kotu ta yi, alkali ya yanke hukuncin cewa ikirarin da kamfanin yake yi yana yi ne da zummar "yaudara kuma yana da matukar hatsari".

  Lorna Jane ya ce ya amince da hukuncin kotun.

  Kamfanin ya dage cewa masu kawo masa kayan sarrafa tufafin ne suka yaudare shi.

  "Wani mai kawo mana kayan sarrafa tufafin da muka amince da shi ne ya sayar mana da kayan da ba su yi aikin da suka yi alkawarin yi ba," a cewar Bill Clarkson, shugaban kamfanin na Lorna Jane.

 11. Ana zanga-zanga a Haiti gabanin jana'izar shugaban da aka kashe

  Jovenel Moise
  Image caption: Za a yi jana'izar ne a cikin tsauraran matakan tsaro

  Magoya bayan tsohon shugaban Haiti da aka kashe, Jovenel Moise sun yi zanga-zanga a mahaifarsa da ke Kapaisiya, gabanin jana'izarsa da za a yi nan gaba a yau.

  An toshe tituna da yawa tare da ƙona tayoyi, yayin da masu zanga-zangar ke neman a yi wa Mista Moise adalci.

  Ya zuwa yanzu an kama sama da mutum 20, galibi sojojin haya daga Colombia dangane da kisan.

  Za a yi jana'izar ne a cikin tsauraran matakan tsaro a gidan ahalinsa da ke wajen garin.

  An kuma gudanar da bukukuwan tunawa da tsohon shugaban a wannan makon a babban birnin Haiti, Port-au-Prince.

 12. Gwamnatin Zamfara ta bai wa iyalan 'yan sandan da aka kashe N15m

  Wani dan sandan Najeriya

  Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bayar da N15m ga iyalan 'yan sandan nan 13 da aka kashe a jihar a makon jiya.

  Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Juma'a ta ce ta bayar da N1m ga iyalin ko wanne dan sanda da aka kashe, sannan ta bayar da N2m ga iyalan 'yan sandan da suka samu raunuka.

  Gwamnatin ta ce kudin da ta bayar cika alkawari ne da Gwamna Bello Muhammed Matawalle ya yi na tallafa wa iyalan jami'an tsaron da suka mutu a bakin aiki.

  A farkon makon nan ne rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar jami'anta 13 a ƙauyen Kurar Mota na Karamar Hukumar Bungudu.

  Rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin ne a wata sanarwa da ta fitar wa manema labarar a ranar Lahadi, inda take cewa kisan jami'an ƴan sandan ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 12.30 na dare.

  Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jami'an suka amsa kiran kai daukin gaggawa kan yunƙurin kai farmaki a ƙauyukan da ke kusa a yankin karamar hukumar.

 13. Masu sayar da kaya a bakin hanya na iya rasa ciniki nan da shekaru - Dr Gwarzo

  Masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci a Najeriya sun yi gargaɗin cewar nan da wasu shekaru masu zuwa, ƴan kasuwar kasar da ke kasa kaya a kasuwa ka iya rasa abokan cinikinsu, matsawar ba su rungumi harkar cinikin zamani ta internet ba.

  Masanan dai na tsokacin ne yayin wani taron da masu kanana da matsakaitan masana’antu suka gudanar a Kano tare da babban sakataren ma’aikatar ciniki ta Najeriya Dr Nasiru Sani Gwarzo.

  A cewar babban sakataren lokaci ya yi, da cibiyar bunkasa kasuwanci da noma ta jihar Kano wato KASSIIMA za ta mayar da hankali wajen wayar da kan yan kasuwar jihar game da runfumar kasuwancin zamani.

  Ga yadda tattaunawarsu ta kasance da wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji:

  Video content

  Video caption: Hira da Dr Nasiru Sani Gwarzo kan kasuwanci a Kano
 14. Macron ya sauya waya da lamba saboda "tsoron kutsen Isra'ila"

  Macron

  Shugaban Faransa Emmanuel Macon, ya canza wayarsa da lambar da yake amfani da ita bayan an bayar da rahoton cewa tana cikin jerin lambobin mutanen da wata manhajar Isra'ila ke yi wa leƙen asiri.

  Ya kuma ba da umarnin sake yin garambawul a tawagar jami'an da ke ba shi kariya.

  A halin da ake ciki dai ana ta tafka muhawara a duniya kan wannan manhaja da ake kira Pegasus, bayan da wata gamayyar kungiyoyin ƴan jarida ta fallasa cewa ana amfani da ita wajen yi wa ƴan jarida da masu rajin kare hakkin dan Adam da kuma ƴan siyasa leƙen asiri.

  Sauran shugabannin da sunayensu suka bayyana cikin wadanda manhajar ke satar bayanansu, sun hadar da Sarkin Moroko da Firaiministan Pakistan Imran Khan.

 15. Sunday Igboho zai bayyana a gaban kotu a Cotonou

  Sunday Igboho Facebook

  Mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawan nan a Najeriya Sunday Adeyemo, dan aka fi sani da Sunday Igboho, zai bayyana a gaban kotu a yau a Cotonou, babban birnin Jamhuriyyar Benin.

  A jiya ya amsa tambayoyi a gaban ƴan sanda.

  Mai shigar da ƙara zai duba yiwuwar ko za a mayar da mai fafutukar Najeriya ko za a ci gaba da tsare shi kafin a yi masa shari'a ko kuma za a sake shi ya jira a ƙasar a yi bincike.

  Tun ranar Litinin yake tsare a Cotonou bayan kama shi da aka yi shi da matarsa.

  Sai dai an saki matar tasa a jiya Alhamis.

  Ana zargin cewa gwamnatin Najeriya na son a mayar mata da shi ƙasar.

  Rahotanni sun ce gwamnatin Benin a baya ta y=ƙi amincewa da buƙatar mayar da shi Najeriya.

  Gwamnatin Najeriya na nemansa ruwa a jalli kan zargin tara makamai da kuma kiraye-kirayen a yi zanga0zangar adawa da gwamnati.

 16. Yankunan Afirka da dama na cikin matsaloli da yamutsi

  Yankuna da dama na Afrika na fuskantar matsaloli na yamutsi da hare -hare da tashe-tashen hankulla.

  Duk da matakan da gwamnatocin kashen Afrika ke cewa suna dauka domin shawo kan wannan lamari, har yanzu lamarin tsaro na kara sukurkuce musu.

  Wannan matsala dai ta yi sanadin raba dubban mutane da matsugunansu, yayin da wasu suka rasa dukiya mai tarin yawa.

  A kan wannan lamari Abdou Halilou ya tattauna da Nicolas Dominique, shugaban wani kamfani da ke ba da shawara kan harkokin tsaro wato SECURITA GOM a Jamhuriyyar Nijar.

  Ya fara da tsokaci kan halin da ake ciki a Mali.

  Ga dai yadda hirar ta kasance:

  Video content

  Video caption: Hira da Nicolas Dominique na kamfanin SECURITA GOM a Nijar
 17. Amurka ta soki China da ƙin barin WHO ta yi binciken asalin cutar korona

  Coronavirus testing china

  Amurka ta soki China game da rashin barin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta binciki waɗansu ɗakunan gwaje-gwaje, a matsayin wani ɗangare na binciken asalin cutar korona.

  Mai magana da yawun fadar mulki ta White House, Jen Psaki, ta bayyana matsayin na Beijing a matsayin 'rashin sanin ya kamata, da ke cike da haɗari''.

  A makon da ya gabata ne WHO ta ce akwai buƙatar zagaye na biyu na binciken da ake gudanarwa ya hada da bincike kan dakunan gwaje-gwaje da ke Wuhan, garin da aka fara samun ɓullar cutar.

  Wakiliyar BBC ta ce tawagar ta WHO a Wuhan ta ziyarci kasuwanni da cibiyoyin bincike da kuma asibitoci, inda ta ce an samu wasu muhimman bayanai, sai dai har yanzu akwai jan aiki a gaba.

 18. An fara Gasar Wasannin Olympic a Japan

  Olympic

  An jima kadan ne ake sa ran bude Gasar Wasannin Olympic ta wannan shekara da ake ta ce-ce-ku-ce a kanta.

  An ɗage gasar daga shekarar da ta gabata saboda cutar korona, amma yanzu za a fara ta a Tokyo, babban birnin Japan, a wani yanayi da masu kamuwa da cutar ke ci gaba da ƙaruwa a duniya.

  An gano ƴan wasa da dama da jami'ai dauke da wannan cuta, abin da ya sa aka tursasa musu killace kansu.

  Sai dai duk da haka, kimanin jami'ai da manyan mutane 1,000 ne za su halarci bikin bude gasar a filin wasa na Olympics.

 19. Ba aikin mu ne dakatar da masu fafutuka ba, amma ba za mu laminci rikici ba - Rundunar Soji

  State House

  Rundunar sojin Najeriya ta ce ba aikinta ko na jami'anta ba ne ta dakatar da masu fafutukar ɓallewa daga ƙasar.

  Babban hafsan tsaro na Najeriya Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a birnin Owerri na jihar Imo, a lokacin wata tattaunawa da manyan jami'an soji da suka yi riitaya ƴan kudu maso gabashin ƙasar, kamar yafdda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

  Irabor, ya ce akwai tanade-tanaden da kundin tsarin mulki ya yi na yadda za a magance ƙungiyoyin fafutuka, yana mai jaddada cewa sai dai duk da haka rundunar soji ba za ta ɗauki duk wani cin kashi da ya shafi ta da rikici ba.

  "Ba aikin sojoji ba ne su dakatar da duk wani mai son yin fafutuka. Abu ne na siyasa, amma ba mu yarda da duk wani abu da zai jawo rikici ba kan irin wannan fafutukar.

 20. Buɗewa

  Jama'a assalamu alaikum, barkanmu da wayar garin Juma'a lafiya, kuma barkanku da shigowa shafin bbchausa.com

  Ku biyo mu don karanta labaran wasu abubuwan da suke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya a yau.