Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

 1. Bankwana

  Masu bibiyarmu a nan ne muka kawo karshen labaran namu na wannan rana.

  Buhari Muhammad Fagge ke cewa safiya ta gari.

 2. Fiye da mutum 200,000 ne suka fita zanga-zangar kin dokar Korona a Faransa

  Reuters

  Hukumomi a kasar Faransa sun ce sama da mutum dubu 200 ne suka fito zanga-zanga a gwamman birane da garuruwan kasar, a makonni 3 a jere don kin amincewa da dokokin cutar korona.

  ‘Yan sandan kwantar da tarzoma a Pari sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar a taho mu gama da suka yi, kuma ‘yan sanda uku sun ji rauni.

  Masu boren sun yi ikirarin dokokin da suka bada damar shiga wasu wurare, za su shiga hakkinsu. Sai da ‘yan jam’iyyar ra’ayin sauyi da na gurguzu sun marawa masu boren baya.

  A watan nan da muke ciki an samu karuwar masu kamuwa da cutar koronar a kasar Faransa.

 3. Likitoci masu neman kwarewa sun shiga yajin aikin sai baba ta gani a Najeriya

  NARD

  Likitoci masu neman kwarewa sun shiga yajin aikin sai baba ta gani a Najeriya.

  Wannan na zuwa ne lokacin da kasar ke cikin tsaka mai wuya na fama da annobar Korna a karo na uku.

  Likitocin sun cimma wannan matsaya ne bayan da kwamitin zartarwar kungiyar ya tattauna da mambobinsu sama da 50 a fadin kasar.

  Sun yi nazari kan cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta gaza mutunta tare da ɗabbaƙa yarjeniyoyin da suka cimma da kwana 100 da suka gabata.

  Shugaban kungiyar Likitocin na kasa Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, yana cewa duk da kokarin da kakakin majalisar kasar Femi Gbajabiamila ya yi na gananin an tabbatar da biyan kuɗaden horo da ake bai wa likitocin amma gwamnati ta gaza yin hakan.

  Kwana 113 kenan da sanya hannu kan wannan yarjejeniya da kungiyar likitocin ta yi da gwamnatin Najeriya.

  Getty Images
 4. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 35 a Nijar ta rusa gidaje 26,000

  Getty Images

  Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a kasar ya janyo mutuwar akalla mutane 35 sannan kuma wasu fiye da dubu 26 sun rasa muhallansu.

  Galibin mutanen sun rasu ne sakamakon ruftawar gidajensu a yayin da kuma wasu suka rasu sakamakon ambaliya.

  Bayanai sun ce tun daga watan Yunin bana, gidaje da makarantu da masallatai sun ruguje sakamakon mamakon ruwan sama.

  A bara an samu karancin ruwan sama a kasar Nijar, lamarin da ya jefa mutum fiye da miliyan biyu bukatar tallafin abinci.

 5. Rasha 'ta yi kutse a imel na manyan masu shigar da kara a Amurka'

  Tambarin ma'aikatar shair'ar Amurka

  Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta yi zargin cewa Rasha ta yi kutse a imel din manyan masu shigar da karar kasar 30 a shekarar da ta wuce.

  Ta yi zargin cewa Rasha ta yi amfani da wata manhaja mai suna SolarWinds don yin kutse mafi muni a shafukan intanet a tarihin kasar.

  Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta ce akalla an yi kutse a kwamfuta daya ta antoni 27 na kasar.

  Hakan ya sanya fargabar cewa watakila masu kutsen sun samu wasu bayanan sirri, ciki har da sunayen masu kwarmata bayanai.

  "Wannan babban lamari ne," a cewar Gil Soffer, wani tsohon mai shigar kara, a hirarsa da BBC.

  Ya kara da cewa imel din masu shigar da karar yana dauke da "bayanai masu muhimmanci da sirri".

 6. Bam ya kashe 'yan kwallon kafa hudu a Somalia

  Akalla 'yan wasan kwallon kafa hudu ne suka mutu bayan wani bam ya fada kan motar bas din tawagarsu a birnin Kismayo da ke kudancin Somalia, a cewar gidan talbijin na kasar.

  Ya kara da cewa mutum 10 sun jikkata sakamakon lamarin.

  Rahoton ya ce motar da ke dauke da 'yan kwallon ta lalace gaba daya.

  Tawagar tana kan hanyar zuwa filin wasan Kismayo domin yin wasa.

  Gidan rediyon Radio Mogadishu ya ce ana sa ran jami'n gwamnati za su halarci filin wasan domin kallon wasan lig da aka yi shirin fafatawa.

  Babu wanda ya dauki nauyin kai harin, sai dai gwamnati ta dora alhakinsa kan kungiyar al-Shabab.

 7. Aston Villa ta kulla yarjejeniya da dan wasan Bayer Leverkusen Leon Bailey

  Leon Bailey

  Aston Villa ta kulla yarjejeniyar daukar dan wasan Bayer Leverkusen Leon Bailey, ko da yake sai an kammala duba lafiyarsa sannan an amince da batun alawus-alawus da sauran abubuwan da suka shafe shi.

  Dan wasan, mai shekara 23 dan kasar Jamaica, ya zura kwallo 28 a wasani 119 na Bundesliga da ya fafata wa Leverkusen.

  Bailey zai kasance dan wasa na uku da Villa ta saya a bazara bayan Emiliano Buendia daga Norwich Cityda Ashley Young daga Inter Milan.

  Manchester City tana son daukar kyaftin din Villa Jack Grealish a kan £100m.

 8. Matawalle ya ziyarci Marafa kan rikicin APC a Zamfara

  Matawalle da Marafa

  Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Mohammed Bello Matawalle ya ziyarci tsohon dan majalisar dattawa Sanata Kabiru Marafa don yin sulhu kan rikicin da ya barke a jam'iyyar APC tun bayan shigar gwamnan cikinta a watan jiya.

  Gwamnan ya ziyarci Sanata Mafara ne a gidansa da ke Kaduna ranar Asabar.

  A wata gajeriyar tattaunawa da BBC Hausa, Sanata Marafa ya ce gwamnan ya ziyarce shi ne domin gano bakin zaren tun bayan sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

  Rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu ne bayan Sanata Marafa da tsohon gwamnan Zamfara Abdul Aziz Yari sun yi fatali da kalaman shugaban riko na jam'iyyar ta APC, Maimala Buni, cewa Gwamna Matawalle shi ne jagoran APC a Zamfara bayan ya sauya sheka zuwa APC.

  Sai dai Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa - wadanda gwamnan ya tarar a cikin jam'iyyar ta APC - sun ce ba za su yarda a yi musu hawan ƙawara ba.

  "Abu guda ne ba mu yarda da shi ba, inda shi Gwamna Maimala ya ce [Matawalle ne jagoran APC] domin babu shi a cikin tattaunawarmu wadda muka yi da gwamnoni guda shida.

  Abin da muka amince shi ne a je a kaddamar da Bello a dawo. Abin da muka amince a matsayin abin da za mu bayar a jam'iyya da abin da za mu dauka a gwamnati. Amma da muka je an yi takaddama mun tarar da an yi tsari in ji wasu cewa idan an je a rusa jam'iyya. Ba a rusa jam'iyya domin babu wanda yake da ikon rusa ta," in ji Abdulaziz Yari.

  Shi ma Sanata Marafa ya ce: "Mu rokonmu aka yi aka ce mu bari a yi abin da aka yi a Gusau. An dai yi biki ne kawai. Mu ne muka ce kafin a ce an zama daya sai an yi zaman [tattaunawa]. Amma wani ya zauna a Abuja ya ce ya rushe jam'iyya ya nada wani shugaba maganar banza da wofi ce."

  Sai dai masu lura da harkokin siyasa na ganin wannan mataki na ziyartar Sanata Marafa da Gwamna Matawalle ya yi zai zama sanadin dinke barakar da ke tsakaninsu.

 9. Taliban ta kai hari kan wasu manyan biranen Afghanistan

  Dan Taliban

  Fada ya kaure a kusa da manyan birane uku da ke kudanci da yammacin Afghanistan a yayin da mayakan Taliban suke neman kwace su daga hannun dakarun gwamnati.

  Mayakan Taliban sun shiga wasu yankunan biranen Herat, Lashkar Gah da kuma Kandahar.

  Sun karbe iko da yankunan karkara tun bayan da aka sanar da fitar dakarun kasashen wajen a watan Satumba.

  Amma makomar wadannan birane na jefa fargaba a zukatan jama'a a yayin da ake ganin za su fada cikin mawuyacin hali da kuma sanin yadda dakarun gwamnati za su wanye da 'yan Taliban.

  Bayanai sun nuna cewa tuni kungiyar ta kwace iko da kusan rabin Afhanistan, ciki har da yankunan da ke kan iyaka da Iran da Pakistan.

 10. Abin da ya sa na yi wa mata waƙar 'kallabi' - Ahmerdy

  Matashin mawakin nan da ya yi fice da wakarsa mai suna 'kallabi', Ahmed Gambo Salman wanda aka fi sani da Ahmerdy, ya ce ya sauke Alku'rani sau biyu.

  A wata tattaunawa da BBC Hausa, Ahmerdy ya ce ya rera wakar 'kallabi' ce domin ya karfafa wa mata gwiwa su rika sanya dankwali.

  Matashin mawakin, dan asalin jihar Kano da ke arewacin Najeriya wanda yanzu haka yake karatun Digiri a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha da ke Wudil, ya ce ya fara waka a 2019.

  Latsa hoton da ke kasa domin kallon bidiyon:

  Video content

  Video caption: Abin da ya sa na yi mata wakar 'kallabi' - Ahmerdy
 11. Zamantakewa: Yadda uwar miji za ta ja girmanta a idon suruka

  Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da zai dinga lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

  A wannan kashi na biyar, shirin ya yi duba ne kan yadda uwar miji za ta ja girmanta a idon suruka.

  Video content

  Video caption: Bidiyon yadda uwar miji za ta ja girmanta a idon suruka
 12. An sake korar ɗan Najeriya daga wasan Olympics

  Divine Oduduru

  An kori ɗan wasan tseren Najeriya, Divine Oduduru, daga gudun mita 100 na gasar Olympics 2020 da ke gudana a birnin Tokyo na Japan.

  Hukumomin tseren sun dakatar da Oduduru ne sakamakon laifin fara gudu ba daidai ba.

  Shi ne ɗan wasan Najeriya na biyu da aka hukunta a yau Asabar bayan an dakatar da Blessing Okagbare daga gasar kwatakwata saboda ta gaza tsallake gwajin ƙwayoyi masu ƙara kuzari.

  Kazalika, a yau ɗin ne kuma aka fitar da tawagar ƙwallon kwando ta maza ta Najeriyar wato D’Tigers daga gasar bayan Italiya ta doke ta da ci 71-80.

  Kwana uku da suka gabata kuma aka hana 'yan wasa 10 na Najeriya shiga gasar saboda ba su shiga an yi musu gwajin ƙwayoyin ƙara kuzari ba kafin fara ta.

 13. Hira ta musamman da Shugaban Nijar Bazoum Mohamed kan ilimi

  Video content

  Video caption: Latsa hoton da ke sama ku saurari Shirin Gane Mani Hanya

  Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya yi hira ta musamman da Shugaba Bazoum Mohamed na Nijar.

  Ahmed Abba ya tattauna da shugaban ne yayin da yake halartar taron shugabannin ƙasa a Birtaniya kan inganta harkokin ilimi a Afirka.

 14. 'Yan fashin daji sun sace ma'aikatan lafiya a asibitin Zamfara

  'Yan fashin daji

  Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kai hari wani asibiti a JIhar Zamfara, inda suka yi garkuwa da ma'aikatan lafiya biyu, a cewar rahotanni.

  Kafafen yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito cewa maharan sun kutsa kai cikin babban asibitin da ke Dansadau a Ƙaramar Hukumar Maru a daren Alhamis zuwa wayewar Juma'a.

  Rahotannin sun ce sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wani mutum ɗaya.

  Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun dinga neman likitoci da kuma ma'aikatan lafiya bayan sun shiga asibitin har sai da suka tsare ɗan uwan wani maras lafiya.

  Suka ƙara da cewa an jikkata wasu mata ma'aikatan jinya biyu yayin harin.

  'Yan fashi na matsa wa garin Dansadau da hare-hare, abin da ya jawo a ranar 1 ga watan Yunin 2021 Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Dansadau Hussaini Umar kan zargin alaƙa da 'yan fashin.

 15. Abin da ya kamata ku sani kan cutar sanyi ta Pneumonia

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari Shirin Lafiya Zinariya

  Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon ya tattauna game da cutar sanyi ta Pneumonia wadda ake ɗauka daga mutum zuwa mutum.

  Habiba Adamu ce ta gabatar da shirin.

 16. 'Yan sandan Katsina sun kama 'matar ɗan fashin daji da kuɗin makamai'

  Kuɗin makamai

  Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wata mata da take zargi ɗauke da maƙudan kuɗin makamai da ta karɓo wa mijinta daga hannun wasu 'yan fashin daji daga Jihar Kaduna.

  Wata sanarwa da Kakakin "yan sanda SP Gambo Isa ya fitar ta ce sun kama Aisha Nura mai shekara 27 a ranar Lahadi, 25 ga Yuli yayin da take ƙoƙarin hawa ɗan acaɓa sakamakon wasu bayanan sirri da suka samu.

  Sanarwar ta ce bayan an bincika Aisha mazauniyar wata rugar Fulani da ke Baranda, sai aka ga tsabar kuɗi naira miliyan biyu da dubu ɗari huɗu da biyar (N2,405,000:00).

  Bayan bincike ya yi nisa ne kuma wadda ake zargin ta amsa laifin cewa kuɗin sayen makamai ne daga 'yan fashi a Jihar Kaduna wanda mijinta mai suna Nura Alhaji Murnai ya aike ta ta karɓo masa daga hannun abokan aikinsa a dajin Kaduna, a cewar sanarwar.

  SP Gambo Isa ya ce Alhaji Murnai ƙasurgumin ɗn fashi ne da ke sansanin wani shugabansu mai suna Abu Radda. Ya ƙra da cewa rundunar na ci gaba da bincike.

 17. An dakatar da 'yar tseren Najeriya Okagbare daga gasar Olympics

  Blessing Okagbare

  Hukumar gasar Olympics da ke gudana a Japan ta dakatar da 'yar tseren Najeriya, Blessing Okagbare, daga gasar saboda ba ta tsallake gwajin shan ƙwayoyi masu ƙara kuzari ba.

  A ranar Juma'a ne Okagbare mai shekara 32 wadda ta ƙware a tsere da kuma tsalle, ta lashe tseren mita 100 sannan ta samu gurbin shiga zagayen kusa da na ƙarshe da za a yi ranar Asabar.

  Sashen kula da halayen 'yan wasa na Athletics Integrity Unit (AIU) ya ce an gano 'yar tseren ta sha ƙwayar da ke ƙara wa wasu ƙwayoyin halittar ɗan Adam ƙarfi biyo bayan wani gwaji da aka yi mata tun ranar 19 ga watan Yuli.

  AIU ya ce an sanar da Okagbare game da dakatarwar a ranar Asabar.

 18. Labarai da dumi-dumiAn fitar da Najeriya daga gasar ƙwallon kwando ta Olympics 2020

  Najeriya

  An fitar da tawagar ƙwallon kwando ta maza ta Najeriya daga gasar Olympics 2020 da ke gudana a birnoin Tokyo na Japan.

  Tawagar D’Tigers ta gamu da gamonta ne a safiyar Asabar, inda 'yan wasan Italiya suka doke na Najeriyar da ci 71-80.

  Wannan shi ne wasa na uku da tawagar ta Najeriya ta yi rashin nasara a rukuninsu na B.

  Tuni tawagar ta gode wa 'yan wasanta da kuma magoya baya, tana mai cewa "za mu sake dawowa", kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

  View more on twitter
 19. Sojojin Afghanistan sun 'fatattaki' mayaƙan Taliban daga Lashkar Gah

  Afghanistan

  Jami'an sojan Afghanistan sun ce sun yi nasarar fatattakar mayaƙan Taliban daga kudancin birnin Lashkar Gah da ke lardin Helmand.

  Wani kwamandan yankin ya ce sun yi wa mayaƙan mummunar ɓarna.

  Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun kutsa kusa da tsakiyar birnin ne ranar Juma'a.

  Lashkar Gah, shi ne babban birnin lardin na biyu da 'yan Taliban suka samu shiga a cikin 'yan kwanakin nan.

  Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fararen hula fiye da 200 sun ji rauni a faɗan da aka yi a cikin mako biyu da suka gabata a kusa da birnin Kandahar.

 20. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum takwas a Najeriya

  Ƙarin mutum 590 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya cikin awa 24 da suka gabata, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar.

  Kazalika, rahoton na NCDC ya nuna cewa cutar ta halaka ƙarin mutum takwas a ranar Juma'ar.

  Rahoton ya ce mutanen da suka kamun sun fito ne daga jiha 18 na faɗin ƙasar. Su ne:

  • Lagos-308
  • Akwa Ibom-54
  • Katsina-40
  • Oyo-39
  • Rivers-26
  • Niger-23
  • Gombe-19
  • Ogun-16
  • Ekiti-15
  • FCT-10
  • Nasarawa-10
  • Delta-9
  • Bayelsa-5
  • Plateau-5
  • Imo-4
  • Ebonyi-3
  • Jigawa-3
  • Kano-1

  Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 173,411 ne uska harbu da cutar, 2,149 daga cikinsu sun rasu yayin da aka sallami 164,978 bayan sun warke.

  View more on facebook