An kwashe gwamman mazauna kauyukan da ke kudancin Turkiyya, a daidai lokacin da wutar daji ke ci gaba da yaduwa a yankin, har zuwa yankin Turai.
Dumammar yanayi da kakkarfar iskar da ake yi na kara rura wutar a garuruwan kasar da ke gabar teku, lamarin da ya tilastawa mutane amfani da kwale-kwale domin tserewa.
Kawo yanzu mutum 8 ne suka mutu, a gobarar daji mafi muni da Turkiyya ta fuskanta cikin gwamman shekaru.
Hotunan tauraron dan adam sun nuna yadda gobarar ta kone kusan Eka dubu 100, har wa yau wutar ta yadu zuwa yankin gabashin kasar Girka, dakudancin birnin Catania na Italiya, da Palermo da Syracuse.
A bangare guda 'yan kwana-kwana a Sifaniya na kokarin kashe gobarar da ta tashi a birnin Madrid.
An yi taho mu gama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a Jamus
ReutersCopyright: Reuters
‘Yan sanda a birnin Berlin na kasar Jamus sun yi taho mu gama da masu zanga-zangar kin amincewa da dokokin kulle, bayan sun yi watsi da haramcin da kotu ta yi musu na fitowa zanga-zanga ba bisa ka’ida ba.
‘Yan sandan sun yi amfani da harsasan roba da hayaki mai sa hawaye, inda suka kare matakin da cewa an ci zarafin wasu daga cikin jami’ansu da kai musu hari a yammacin gundumar Shalottin-barg, an kuma kama yawancin masu zanga-zangar.
Kungiyar Lateral Thinkers ce ta kira zanga-zangar, wadda ta kasance kakkarfar muryar da ke yaki da dokokin yaki da cutar korona a kasar Jamus.
Kotu dai ta haramtawa masu boren fitowa, kan fargabar ba za su sanya takunkumin rufe fuska ba, wanda zai kara yada cutar ta korona.
Mayaƙan ISWAP sun yi wa sojojin Najeriya kwantan ɓauna
BBCCopyright: BBC
Gwamman mayaƙan ISWAP sun yi wa jerin gwanon motocin sojin Najeriya kwantan ɓauna a kan hanyar Gubio zuwa Damasak a yankin arewacin jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta ruwato cewa sojoji da dama sun jikkata a yayin hari na aka kai musu na ranar Asabar, aka kuma dauki mota guda daga cikin motocinsu da suke ta fiya da ita ana tsaka da harbe-harben.
Sojojin sun fada tarkon ISWAP din ne a Kareto lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Gubio a Jihar Borno domin dauko wasu mambobin jam'iyyar APC daga mazabunsu zuwa Damasak.
An bar yankin Kareto a baya na shekaru saboda ayyukan Boko Haram da ISWAP.
Sojoji ne ya kamata su raka yan siyasar daga Abadam zuwa Damasa inda aka tsara yin taron yankin nasu.
Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai ba kan wannan hari.
Babban kwamanda a yankin Tigray ya sha alwashin ci gaba da yaki har sai an amince sharudɗan da suka gindaya
BBCCopyright: BBC
Babban kwamanda a yankin Tigray da ke arewacin Habasha, ya sha alwashin ci gaba da yaki har sai an bude toshewar da dakarun gwamnati suka yi wa yankin, tare da amincewa sharuddan da suka gindaya na dakatar da bude wuta.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Janaral Tsad-kan Gebre-tense, ya shaida wa BBC cewa mayakan Tigray ba za su bar makoftan yankinsu Afar da kuma Amhara ba, har sai sun cimma nasara.
Ya ce, a karshe dole mu ne za mu yi n asarar karbe iko da yankinmu.
Amma baya ga haka babban burinmu shi ne mu bude hanyar da aka toshe mu, sannan mu matsawa gwamnatin Habasha lambar amincewa da sharuddanmu kafin sasantawa ta amfani da siyasa.
Barcelona za ta nuna sabon dan wasan da ta saya Emerson Royal
GETTY IMAGESCopyright: GETTY IMAGES
A gobe Litinin ne Barcelona za ta gabatar da Emerson Royal a matsayin sabon dan wasanta a Camp Nou.
Tun a makon jiya dan kwallon tawagar Brazil ya je Barcelona domin shirin gabatar da shi ga mahukuntan kungiyar da kuma ganawa da 'yan jarida.
Ranar 2 ga watan Yunin 2021, Barcelona ta kammala cinikin dan wasan na Atletico Mineiro da Real Betis.
Mai tsaron bayan Brazil ya yi hutu ne, bayanm kammala gasar Copa America, wanda ya wakilci kasarsa a gasar da ta karbi bakunci.
Ranar 31 ga watan Janairun 2019, Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar dan wasan tsakanin Atletico Mineiro da Real Betis, wadda ya yi wa wasannin aro, sannan ta saye shi.
Mai shekara 22, wanda aka haifa a Sao Paulo ya fara taka leda a matakin kwararren dan wasa a Ponte Preta daga 2016 zuwa 2018.
Daga yanzu babu wanda zai shiga jama'a sai wanda aka yi wa rigakafi - Saudiyya
HaramainCopyright: Haramain
Gwamnatin Saudiyya ta ce daga ranar Lahadi ta 1 ga watan Agusta babu wanda zai shiga kantinan zamani ko kuma wuraren sana'o'i ko motar haya ko ofisoshin gwamnati sai wanda aka yi wa rigakafin korona.
Ma'aikatar cikin gidan kasar ce ta bayyana hakan, tana cewa dole kowa ya fito a yi masa rigakafin ko a wanne yanki yake na masarautar.
Saboda fargabar sabuwar dokar, an karo yawan rigakafin kuma ana samun dogayen layuka a Riyadh da sauran wurare.
Adadin wadanda aka yi wa rigakafin cikakkiya a Saudiyya ba shi da yawa idan aka kwatanta da makonta na yankin Golf.
Tun daga farkon bullar annobar, masarautar na ɗaukar tsauraran matakan da suka kamata - wadanda suka shafi dakatar da aikin Hajj har saubiyu.
Ko a makon jiya, sai da aka yi wa mutane gargadi kan cewa za su iya fuskantar haramcin tafiya idan suka shiga Saudiyya daga kasashen da Saudiyyar ta hana zuwa.
Firaiministan Isra'ila ya ce 'ya san yadda zai aika sakon ramuwar gayya kan Iran'
EPACopyright: EPA
Firaiministan Isra'ila ya ce ya na "da tabbacin" iran na da hannu kan harin da aka aika jirginta a Oman, zargin da Tehran ta ce "bashi da tushe bare mamaka".
A ranar Alhamis ne aka kai harin wanda ya yi sanadin mutuwar ma'aikatan jirgin biyu.
Firaiminisran Isra'ila Naftali Bennett ya yi gargadin cewa "mun san yadda za mu aika sakon ramuwar gayya kan Iran'.
Yayin da ita ma Iran ta ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin duk abin da za ta iya domin ta kare kanta.
A baya-bayan nan ana yawan samun hare-hare kan jiragen ruwan kasashen biyu.
Ana kallon harin da aka kai tun watan Maris a matsayin na ramuwar gayya.
NDLEA ta kama wata mata da ɗauri 35 na hodar iblis da kwayoyi
NDLEACopyright: NDLEA
Hukumar yaki hana sha da fataucin kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kwace wasu dauri 35 na hodar iblis daga wajen wata mata a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke ikeja a Legas.
NDLEA ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labaranta Femi Babafemi, ya bai wa kamfanin dillancin labarai na kasar NAN a Abuja.
An kama matar mai suna Okafor Ebere Edith, ranar 31 ga watan Yulin jiya yayin da ake aikin duba kayan matafiya.
Yace matar ta boye hodar iblis din ne cikin wandonta na ciki domin ta dauke hankalin jami'an tsaro yayin binciken, amma daga karshe an bankado abin da ta boye.
"Yayin tambayoyin da aka fara mata matar ta nuna cewa son ta tasa kudi ne ya jefata wannan mummunar harkar ta safarar kwayoyi," a cewarsa.
An kashe mutum hudu a wani rikicin ƙabilanci da ya barke a Jihar Filato
GoogleCopyright: Google
Wani rikcin ƙabilanci tsakanin Fulani da Irigwe da ya ɓarke a Jihar Filato da ke arewacin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu a karamar hukumar Bassa da ke Jihar.
Kakakin 'yan sanda na jihar ASP Ubah Gabriel ya tabbatar wa da Jahidar Daily Trust ce wa an kona gidaje kimanin 50 yayin rikicin.
Quote Message: A ranar 31 ga watan Yulin jiya ne, muka samu rahoton barkewar rikici tsakanin wasu da ake zargin 'yan bindiga ne da matasan Irigwe a Jebbo Miango da ke Bassa, kuma abin takaici an kona gidaje 50 an kuma harbe mutum hudu ... in ji ASP Ubah Gabriel
A ranar 31 ga watan Yulin jiya ne, muka samu rahoton barkewar rikici tsakanin wasu da ake zargin 'yan bindiga ne da matasan Irigwe a Jebbo Miango da ke Bassa, kuma abin takaici an kona gidaje 50 an kuma harbe mutum hudu ... in ji ASP Ubah Gabriel
"Bayan karbar rahoton, aka aike da dakaru na musamman domin tabbatar da tsaro a yankin da kuma tabbatar da doka da oda.
"Kwamishinan yan sanda Edward Egbuka, da wasu manyan jami'ai sun ziyarci inda lamarin ya faru tare da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan gano musabbabin wannan rikici.
"Amma yanzu komai ya koma daidai a yankin," in ji shi.
Rahotanni sun ce sama da mutum 10 ne suka jikkata a rikicin.
Ghana za ta lashe kyautar farko a Olympics cikin shekara 29
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Ɗan damben Ghana Samuel Takyi na kan hanyar lashe kyautar aƙalla tagulla a gasar Olympics da ke gudana a Japan bayan ya yi nasarar zuwa zagayen ƙarshe.
Rabon da Ghana ta ci wata kyauta a Olympics tun wadda aka yi a birnin Barcelona na Spain a 1992, kuma akwai yiwuwar Takyi ya lashe zinare.
Shi ma ɗan tseren Najeriya Enoch Adegoke da na Afirka ta Kudu Akani Simbine za su fafata domin lashe zinare a zagayen ƙarshe na gudun mita 100 na maza.
Wata 'yar Najeriyar, Tobi Asuman, ta samu kai wa zagayen ƙarshe a tseren mita 100 na mata.
'Yan Afirka biyar ne za su fafata a zagayen ƙarshe a tseren steeplechase na mita 3,000 na mata, yayin da ita kuma 'yar Najeriya Ese Brume ta kai zagayen ƙarshe a wasan dogon tsalle.
Mayaƙan Taliban da dakarun gwamnati na fafatawa a gari uku
AFPCopyright: AFP
Ana tafka ƙazamin faɗa a gari uku da ke kudanci da yammacin Afghanistan, yayin da ƙungiyar Taliban ke yunƙurin ƙwace su daga hannun gwamnatin ƙasar.
An ci gaba da fafatawa a garuruwan Herat da Lashkar Gah da Kandahar a yau Lahadi.
Taliban ta kama garuruwa da dama tun bayan da aka sanar da cewa kusan dukkan sojojin ƙasar waje za su fice daga ƙasar a ƙarshen Satumba.
Sai dai makomar waɗan nan garuruwa na da muhimmanci sakamakon taɓarɓarrwar rayuwa da mazaunansu ke fuskanta da kuma tsawon lokacin da dakarun gwamnati za su ɗauka wajen kare shi daga harin Taliban.
An yi imanin cewa ƙungiyar ta kama kusan rabin ƙasar, ciki har da garuruwan kan iyakarta da Pakistan da kuma Iran. Sai dai har yanzu ba ta iya ƙwatar babbar birnin yankin ba.
An ceto ƙarin ɗaliban sakandaren Birnin Yawuri daga hannun 'yan fashi
Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara a Najeriya ta ce ita ce ta ceto ɗalibai biyu na sakandaren Birnin Yawuri ta JIhar Kebbi da 'yan bindiga suka sace a watan Yuni.
Tun farko dai rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin Dandalla ne suka tsinci ɗaliban na Federal Governent College, Birnin Yauri suna watangaririya a dajin Dansadau na Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara ranar Asabar.
Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Lahadi, Kwamishinan 'Yan Sandan Zamfara Hussaini Abubakar ya ce jami'ansu ne suka yi nasarar ceto Maryam Abdulkarim mai shekara 15 da Faruk Buhari mai shekara 17.
"Ina mai shaida muku cewa a ranar 31 ga watan Yuli [Asabar], dakarun rundunar 'yan sanda ta musamman mai suna Operation Restore Peace suka yi nasarar ceto yaran," a in ji CP Hussaini.
Ya ce Maryam 'yar garin Wushishi ce da ke Jihar Neja, shi kuma Faruk ya fito ne daga Wara na Jihar Kebbi. An ceto su ne daga wani daji da ke ƙauyen Babbar Doka a garin Dansadau.
A ranar 17 ga watan Yuni ne 'yan bindiga suka kutsa makarantar sakandaren ta garin Yawuri suka sace ɗalibai fiye da 30 da wasu malamansu.
Rundunar sojan Najeriya ta ce ta ceto wasu daga cikin ɗaliban sannan ta kashe 'yan fashin kusan 80.
'Yan tawaye sun kashe mutum shida a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Rahotanni na cewa 'yan tawaye a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika sun kashe mutum shida a wani hari da suka kai kan wani kauye a arewa maso gabashin kasar.
Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya shaida wa kamfanin labarai na AFP cewa sojojin gwamnati da ke zaune a Mann sun fuskanci hari daga wata kungiya da ake kira 3-R.
Ƙungiyar na daya daga cikin dimbin kungiyoyin mayakan sa-kai da suka kafu cikin shekara 10 da suka gabata.
Tashin hankalin 'yan tawaye a karshen shekarar da ta gabata ya kai har Bangui, babban birnin kasar, amma sojojin gwamnatin da ke samun goyon bayan sojojin Ruwanda da sojojin sa-kai na Rasha sun fatattake su.
'Yan sandan Jihar Imo sun 'kashe 'yan fashi biyu'
NG PoliceCopyright: NG Police
Rundunar 'yan sandan JIhar Imo a kudancin Najeriya ta ce jami'anta sun kashe 'yan fashi biyu yayin wata musayar wuta a Ƙaramar Hukumar Njaba ranar Asabar.
Kwamishinan "Yan Sandan Imo, Mr Abutu Yaro, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.
Ya ce sun ƙwace bindigar AK-47 ɗaya da kuma wata mota yayin fafatawar.
"Yayin musayar wutar, an lalata ɗaya daga cikin abin hawansu ['yan fashi] sannan aka kashe biyu daga cikinsu yayin da sauran suka shiga daji a guje," a cewar sanarwar.
Baya ga AK-47, kazalika an samu wata ƙaramar bindiga ƙirar gida a motar tasu. Sanarwar ta ƙara da cewa 'yan sanda na ci gaba da bin sawun su.
Sojoji sun yi alƙawarin gudanar da zaɓe a Myanmar
ReutersCopyright: Reuters
Shugaban gwamnatin soja a Myanmar ya yi alƙawarin gudanar da sabon zaɓe da zai kunshi jam'iyyu da dama tare da yin aiki da sauran ƙasashe wata shida bayan sun kwace mulki.
Sai dai yayin wani jawabi da ya gabatar ta talabijin, Janar Min Aung Hlaing ya bayyana jam'iyyar da ya kifar ta Aung San Suu Kyi a matsayin ta 'yan ta'adda.
Myanmar na fama da tashe-tashen hankali tun bayan da sojoji suka karbe iko a watan Fabrairu.
An hana zanga -zangar kan tituna a duk fadin kasar da ake yi don nuna goyon baya ga Aung San Suu Kyi.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da ayyukan hukumomin sojin, amma China ta hana kwamitin sulhu daukar wani tartibin mataki.
Labarai da dumi-dumiSufeto janar na 'yan sandan Najeriya ya nemi a dakatar da Abba Kyari daga aiki
Facebook/Abba KyariCopyright: Facebook/Abba Kyari
Sufeton Janar na 'Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya nemi a dakatar da Abba Kyari daga aikin ɗan sanda bisa zargin karɓar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa.
Kazalika, IGP ɗin ya kafa wani kwamati na mutum huɗu ƙarƙashin jagorancin DIG Joseph Egbunike wanda zai binciki zargin da ake yi wa Abba Kyari mai muƙamin mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).
Usman Alkali ya bayar da shawarar dakatarwar ce cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa Hukumar Kula da Harkokin 'Yan Sanda ranar Asabar, yana mai cewa matakin "ɗaya ne daga cikin matakan ladaftarwa na rundunar 'yan sanda".
Ana zargin Abba Kyari da karɓar rashawa a hannun matashi ɗan Najeriya kuma mazaunin Amurka mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppy, domin kamawa da kuma muzguna wa wani abokin harkarsa. Sai dai Kyari ya musanta zargin.
Hushpuppy ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar ce yayin da hukumar tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane.
Sai dai rundunar ta ce har yanzu tana ɗaukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa.
Ƙarin mutum 497 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Alkaluman da hukumar daƙile cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta fitar ranar Juma'a sun nuna cewa wasu ƙarin mutum 497 sun kamu da cutar korona jiya Asabar.
Ya zuwa yanzu adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 173,908, kodayake an sallami 164,994 da aka tabbatar sun warke garau. Sai kuma mutum 2,149 da suka rasa rayukansu.
A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau'in cutar korona da ake kira Delta a kasar wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.
Ga jerin jihohin da aka samu masu ɗauke da cutar ranarJuma'a.
Legas-211
Akwa Ibom-80
Kwara-73
Osun-29
Oyo-17
Rivers-17
Cross River-15
Edo-14
Anambra-9
Ogun-8
Ekiti-6
Bayelsa-4
Abuja-4
Plateau-4
Bauchi-2
Nasarawa-2
Kaduna-1
Jigawa-1
Maraba
Barkanmu da hantsin Lahadi, tare da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya sumul ƙalau.
Umar Mikail ke muku maraba da shigowa shafin rahotanni kai-tsaye wanda zai kawo labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Daga Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge
time_stated_uk
Ban kwana
Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu kwana lafiya.
Wutar daji na kara kutsa kai nahiyar Turai

Kuna iya karanta cikakken labarin a nan:
Ƙarin mutum 497 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Alkaluman da hukumar daƙile cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta fitar ranar Juma'a sun nuna cewa wasu ƙarin mutum 497 sun kamu da cutar korona jiya Asabar.
Ya zuwa yanzu adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 173,908, kodayake an sallami 164,994 da aka tabbatar sun warke garau. Sai kuma mutum 2,149 da suka rasa rayukansu.
A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau'in cutar korona da ake kira Delta a kasar wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.
Ga jerin jihohin da aka samu masu ɗauke da cutar ranarJuma'a.
Maraba
Barkanmu da hantsin Lahadi, tare da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya sumul ƙalau.
Umar Mikail ke muku maraba da shigowa shafin rahotanni kai-tsaye wanda zai kawo labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Ku biyo ni zuwa yammaci.