Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Mu kwana lafiya

  Nan muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

  Mu haɗu da ku gobe Talata. Umar Mikail ke muku fatan alheri.

 2. Motar jami'an kwastam ta kashe mutum biyar a Jihar Katsina

  Kwastan

  Hukumar hana kula da safarar kaya a Najeriya ta kwastan ta tabbatar da mutuwar mutum biyar a Jihar Katsina da ke arewacin ƙasar bayan motar da wasu jami'anta ke tuƙawa ta bige su.

  Ta ce lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Jibya sanadiyyar shanyewar birkin motar a lokacin da suka shiga yankin domin karya kumallo, inda suka jikkata wasu da ba a san adadinsu ba.

  Hatsarin ya janyo wata ‘yar kwarya-kwaryar zanga-zanga a garin, wadda ta kai har kan iyakar Najeriya da Nijar, inda jami’an ƙasar ke tsayawa.

  Dalha Wada Chedi, shi ne babban kwamandan hukumar a Katsina, ya shaida wa BBC Hausa cewa bayanan da suka tattara na nuna cewa ba wani wanda ake zargi da laifi motar tasu ke bi ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana tun farko.

  Sai dai wani wanda ya shaida faruwar lamarin ya shaida wa BBC Hausa cewa Jami’an tsaron da ke aikin sintiri a kan iyaka ne suka biyo wani mutum ɗauke da shinkafa a kan babur.

  Ya ƙara da cewa yayin gudun tsira da ransa ne kuma ya afka cikin mutane, inda su ma suka bi shi.

  Rahotanni sun ce fusatar da ‘yan gari suka yi ta kai ga kona motar jami’an wadanda suka tsere da kafafuwansu.

  Sun kuma kara da cewa akwai mutane da dama da suka jikkata masu yawa a asibiti wadanda suke rai a hannun Allah.

  A 2019 ne gwamnatin Shugaba Buhari ta haramta safarar shinkafa da wasu sauran kayayyakin masarufi zuwa kasar, kuma yakan zama babban laifi ga duk wanda aka kama da aikata hakan.

 3. Sergio Aguero zai yi jinyar mako 10

  Sergio Aguero

  Kungiyar Barcelona ta sanar da cewa Sergio Aguero ya ji rauni kuma zai yi jinyar mako 10, inda ba za a fara gasar La Liga ta bana da shi ba.

  Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata tana mai tabbatar da raunin na ɗan kwallon tawagar Argentina.

  Aguero mai shekara 33, ya koma Barcelona daga Manchester City kan yarjejeniyar shekara biyu bayan da yarjejeniyarsa ta kare a da Manchester City.

  Dan kwallon wanda ya yi kakar wasanni 10 a City, ya zama kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye da 260 a raga a fafatawa 390 da ya buga.

  Aguero ya lashe Copa America a watan jiya tare da ƙasarsa Argentina tare da Lionel Messi wanda ya tabbatar da barin Barcelona.

 4. Umarnin hana fita na IPOB: An kashe 'mutum biyar' a jihohin kudancin Najeriya

  IPOB

  An harbe aƙalla mutum biyu a birnin Nnewi na jihar Anambra da ke kudancin kasar sannan wasu suka jikkata yayin da jama'a ke cikin zullumin dokar hana fita da ƙungiyar IPOB ta saka.

  Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne a marabar Izuchukwu lokacin da wasu matasa suka tare mutane suna kokarin yi musu ƙwace tare da hana su yin kasuwanci, abin da ya haifar da hatsaniya.

  Kakakin rundunar 'yan sandan Anambra ya tabbatar wa da BBC Hausa faruwar lamarin amma ya ce ba su da labarin rasa rai tukunna. Kazalika ya ce wasu 'yan daba sun kai wa ofishin 'yan sanda hari amma ba su yi nasara ba.

  A Jihar Imo ma rahotanni na cewa mutum uku sun mutu bayan an kunna wa wasu motocin bas wuta.

  Wannan na zuwa ne yayin da akasarin al’ummar jihohin kudu maso gabashin kasar suka zauna a gida sakamakon umarnin da kungiyar ta Indigenous People of Biafra (IPOB) ta bayar.

  Wasu mazauna yankin sun faɗa wa wakilin BBC Hausa Zaharadden Lawan ta waya cewa akasarin mutanen jihohin Ebonyi da Abia da Enugu sun bi umarnin ƙungiyar a ranar Litinin.

  Ƙungiyar wadda ke fafutikar kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabas - inda ƙabilar Igbo ke da rinjaye - ta umarci mazauna yankin da kar su fitto aiki ko kasuwanci saboda nuna ɓacin ransu game da kama shugabanta Nnamdi Kanu.

 5. An tsare minista saboda zargin cin hanci a Malawi

  Newton Kambala

  An kama ministan makamashi na Malawi, Newton Kambala, saboda zargin yunƙurin amfani da muƙaminsa wajen tsarin bayar da kwangilar shiga da man fetur.

  Hukumar yaƙi da rashawa ta Anti-Corruption Bureau (ACB) ta bayyana cewa tana tsare da shugaban jam'iyyar Alliance for Democracy mai suna Enoch Chihana.

  Kazalika ta tsare wani mai bai wa shugaban ƙasa shawara, Chris Chaima Banda.

  ACB ta ce mutum biyun sun taimaka wa ministan "a lokacin da ya yi yunƙurin nuna tasiirinsa a kwangilar shigo da tan 40,000 na fetur".

  Enoch Chihana ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa amsa gayyatar ACB "lamari ne na shari'a da aka saba yi kuma dama ce a gare ni domin wanke kaina daga dukkan zargi".

 6. Najeriya: An saka ranar fara rigakafin korona zagaye na biyu

  Rigakafin korona

  Kwamatin yaƙi da cutar korona a Najeriya ya sanya 16 ga watan Agusta domin fara aiwatar da allurar rigakafin cutar zagaye na biyu.

  Shugaban hukumar lafiya a matakin farko, Dr. Faisal Shuaib, shi ne ya bayyana hakan ranar Litinin.

  Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa a daren Lahadi aka ɗage shirin wanda aka tsara farawa ranar Talata.

  Amurka ce ta bai wa Najeriya rigakafin kamfanin Moderna wadda za a yi amfani da ita a zagaye na biyun, kuma ta isa ƙasar ne ta hannun shirin Covax na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar 2 ga watan Agusta.

  Najeriya ta bayar da rahoton mutum 471 da suka kamu da cutar korona ranar Lahadi, sannan wasu biyu suka rasu.

 7. Sheikh Sudais ya naɗa mata mataimakansa a karon farko

  Sheikh Sudais

  A karon farko, Saudiyya ta naɗa wasu mata biyu a manyan mukamai na hukumar kula da masallatan Harami na Makka da Madina.

  Gidan talabijin na Al Arabiya wanda mallakin Saudiyya ne, ya bayar da rahoto ranar Litinin cewa Sheikh shugaban hukumar Abdulrahman Al-Sudais ya naɗa Dr. Al-Anoud Al-Aboud da Dr. Fatima Al-Rashoud a matsayin mataimakansa.

  Al Arabiya ta ce hukumar na da niyyar horar da ma’aikata mata ’yan saudiyya 320, bayan sanar da fara shirin horon mai taken "Hayyak" a ranar 8 ga watan Agusta domin haɓaka ayyukan matan a masallatan masu tsarki.

  Makamanciyar haka ta faru a shekarar da ta gabata, lokacin da ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta naɗa mata 100 a matsayin ma’aikatan shari’a.

  Dr Hala al-Tuwaijri ce jagorar sabon muƙamin, wadda a shekarar da ta gabata a wani taro ta sanar cewa "gwamnati ta saka taimakon mata a gaba, inda take ɗorawa a kan tsare-tsarenta na baya.

  Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed Bin Salman - wanda ake gani a matsayin shugaban Saudiyya - na jagorantar ƙudirinsa na Muradin 2030, wanda ke zai bai wa mata damar taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasar.

 8. MDD ta yi gargadi kan munin ɗumamar yanayi

  Sauyin yanayi

  Kwararru a Majalisar Dinkin Duniya na gargadin ayyukan bil Adama na kara dumama yanayin duniya.

  Cikin wani rahoto, kwamitin kasa-da-kasa kan sauyin yanayi ya ce ana iya ganin sauye-sauyen a sassan duniya a lokutan matsanancin zafi da ruwan sama mai karfi da kuma fari.

  Wakilin BBC ya ce rahoton karshe da kwamitin ya fitar shi ne a 2013 kuma kwamitin ya ce tun daga lokacin aka kara kaimi kan bincike.

  Za a ci gaba da ganin Sauye-sauyen yanayi sanadin gurbatacciyar iska da aka fitar ko kuma za a fitar a nan gaba abin da zai shafi tafkuna da da kankarar teku da kuma doran kasa tsawon karni ko shekaru.

  Amma har yanzu akwai damar kaucewa fadawa mummunan yanayi ta hanyar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

  Rahoton na hasashen dumamar yanayi a duniya zai kai ko ma ya wuce maki ɗaya da digo biyar a ma'aunin Celcius.

 9. "Ambaliyar ruwa ta tagayyara mutum 90,000 a Sudan ta Kudu"

  s

  Akalla mutum 90,000 ambaliyar ruwa ta daidaita a gabashin garin Jonglei a Sudan ta kudu, a cewar sanarwar hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya.

  Majalisar ta ce hukumomin yankin sun ba da sanarwa cewa wannan shine karo na biyu da sama da mutum 70,000 ke fuskantar irin wannan ambaliya a gundumar Ayod da Canal.

  Sanarwar ta kuma ce mutanen na cikin matsanancin bukatar agajin gaggawa, inda dubbai ke cunkushe wuri guda a wasu tsibirai da ke kewaye da ruwa, da tsugunar da kansu karkashin bishiyoyi da gaggara tsallakewa domin samun kubuta.

  Ruwa mai karfi ya rusa gidaje da gonakin noma,wanda yasa dole iyalai da dabbobinsu tserewa saman tuddai domin samun tsira

  Abinda ya ke faruwa a Ayod misalai ne mara dadi kan yadda canjin yanayi ke kawo sauyi a yanayin da aka saba gani da kuma tsananta tasirin ambaliyar ruwan da daidaita mutane baya ga jefa su cikin matsanancin hali a cewar Arafat Jamal, mukaddashin shugaban hukumar agaji ta majalisar dinkin duniya da ke Sudan ta kudu.

  Ya yi kira da a bada taimakon gaggawa na abinci da,wajen zama da kayan girki da magunguna da samun ruwa mai tsafta.

 10. NCDC: Cutar Kwalara na ƙara ƙamari a Najeriya

  Kwalara

  Hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce cutar kwalara na ci gaba da yaɗuwa a a Najeriya inda aka samu ƙaruwar yaɗuwar cutar da kashi 44.

  Rahoton da hukumar ta fitar ranar Litinin ta ce cutar ta kashe mutum 30 a mako ɗaya a jihohin Bauchi da Katsina da Neja da Jigawa da kuma Abuja.

  Cutar ta fi yin kisa a jihar Bauchi inda mutum 11 suka mutu a mako ɗaya, Katsina mutum 10 sai Neja mutum 6 da kuma Abuja mutum ɗaya.

  Sannan mutum 1,162 suka kamu a johohi bakwai cikin mako ɗaya da suka haɗa da Bauchi da Katsina da Neja da Jigawa da Kano da Borno da Adamawa da kuma Abuja.

  Alƙalumman hukumar sun nuna cewa mutum 816 suka mutu sakamakon kwalara a jihohi 22 da Abuja tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2021.

  Rahoton ya ce cutar ta fi kama yara daga shekara biyar zuwa 14.

 11. Mayaƙan jihadi sun kashe mutum 40 a Mali

  Mali

  Jami’ai a Mali sun ce wasu da ake zargin masu ikirarin Jihadi ne sun halaka sama da mutum 40 a arewacin kasar.

  Mayakan kan Babura sun kai farmaki kan wasu kauyuka uku inda suka kasha mutane da dama.

  A makwabciyar kasar, Burkina Faso, an kasha kimanin sojoji 12 a wani hari da ake zargin masu ikirarin Jihadin ne suka kai kusa da kan iyaka da Mali.

  Majiyoyi daga bangaren tsaro sun ce suna tunanin harin ramuwar gayya ne ga kisan da sojoji suka yi wa biyu daga cikin jagororin masu ikirarin Jihadin biyu ranar Asabar.

 12. Ƙungiyoyi na dauka matakan kare muhalli daga zaizayar kasa a Kano

  A wani mataki na tallafa wa yaƙi da ake yi da sauyi yanayi a duniya, da kuma matsalar zaizayar kasa da kwararowar hamada, wasu kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya sun dukufa wajen dashen bishiyoyi.

  Daya daga cikin kungiyoyin ita ce Gidauniyar Sama wa Al'uma Sai'da - da ake kira Panacea Foundation da ke jihar Kano a arewacin kasar.

  Kungiyar ta kaddamar da wani shiri na dasa bishiyoyi dubu dari daya a sassa daban-daban na jihar.

  A cewar kungiyar, duk da kokarin da gwamnatoci ke yi wajen dashen itatuwan, har yanzu akwai karancin su, kuma hakan na kara barazanar da ake fuskanta wajen samun ingantaciyar iskar shaka mai ni'ima.

  A saurari rahoton wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji.

  Video content

  Video caption: Rahoton Khalifa Shehu Dokaji
 13. An yiwa ɗan jarida yankan rago a gabashin DR Congo

  Mahukunta a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo sun ce an yiwa wani dan jaridar da ke aiki da gidan talabijin na kasa yankan rago a lardin arewacin Kivu.

  Abokan aikin Heritier Magayane sun ce kisan nasa na da alaka da aikinsa, Inda yake gabatar da shirye shiryen da ke kira ga matasa kan samar da zaman lafiya.

  Dan jaridar ya amsa kiran waya ne daga wani wanda ya shirya haduwa dashi a wani kauyen Bunyangula inda aka kashe shi.

  Yankin da abin ya faru na karkashin ikon sojojin Congo ne amma mayaka da daman na gudanar da ayyukansu a yankin.

 14. 'Ambaliya na lalata yankuna 500 a kowacce shekara a Neja'

  Hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja ta shaida cewa ambaliyar ruwa ta tafka barna a yankuna 500 a kowacce shekara.

  Wadanan yankunan ne a kananan hukumomin jihar 13.

  Shugaban hukumar, Alhaji Ibrahim Inga ya shaida cewa suna iya kokarinsu domin tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba a wannan shekarar a mabaliyar.

  Alhaji Inga ya ce a yanzu sun mayar da hankali wajen kare yankunan da gonaki da shawarwari ga mazauna yankuna.

  Hukumar da ke kula da sarrin samaniya a Najeriya, Mr Haruna Zakari ya ce hasashensu ya nuna cewa za a samu ruwan sama da sama da kashi 70 kan wanda aka saba gani daga watan Agusta zuwa Oktoba.

  Ya shawarci mazauna a yankuna masu barazana su sake matsuguni

 15. An kashe mutum 22 a rikicin manoma da makiyaya a Chadi

  Chadi

  Mahukunta a Chadi sun ce mutum 22 ne suka mutu, wasu 18 kuma suka jikkata a rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin kudancin Hadjer-Lamis.

  Mai magana da yawun gwamnati, Abdramane Koulamallah ya ce an tura jami’an tsaro domin su dawo da doka da oda a yankin, sannan su kwantar da hankulan mutanen.

  An shafe tsawon lokaci ana fuskantar tashe-tashen hankula tsakanin manona, asalin mazaunan yankin, da kuma Larabawa makiyaya, abin da a wani lokaci ke sanadin rasa rayuka.

  Gwamnan yankin, Amina Kodjiana, ta shaida wa kamfanin dilancin labarai na Faransa, AFP cewa rikicin ya balle ne a ranar Asabar tsakanin mazaun Boulala da Larabawa makiyaya a kauyen Zohana, mai tazarar kilomita 200 da gabashin birnin N'Djamena.

 16. Labarai cikin Minti Ɗaya da BBC na Rana

  Video content

  Video caption: A saurari labaran duniya cikin minti ɗaya da BBC
 17. Ƴan Najeriya na fargaba kan yadda ake amfani da POS don yin zamba

  POS

  Sannu a hankali sana’ar aikawa da cire kudi ta POS a Najeriya na ci gaba da karbuwa a sassan kasar.

  Babban bankin kasar CBN ne ya samar da irin wannan tsari a wani mataki na kai hada-hadar kudi kusa da jama’a tare da rage cunkoso a bankuna da kuma samar da ayyuka.

  Sai dai wannan kasuwanci na POS na fama da matsaloli ciki har da zamba da kuma zargin miyagu kan yi amfani da kafar wajen karbar kudin fansa.

  A saurari rahoton da Zahraddeen Lawan ya hada mana kan wannan batu.

  Video content

  Video caption: Rahoton Zahraddeen Lawan kan kasuwancin POS
 18. Sojojin Amurka na yiwa mayaƙan Taliban ruwan wuta a Afghanistan

  Taliban

  Jiragen sama na Amurka da na sojin Afghanisatn sun kai hare-hare ta sama a kan mayakan Taliban a Afghanistan bayan gagarumawar dannawa yankuna da masu tayar da ƙayar bayan suka yi.

  Rahotanni na cewa an nufi masu tayar da kayar bayan a lardunan Jawzan da Paktia da kuma Helmand.

  Wakilin BBC ya ce ''Jami'an gwamnatin Afghanistan sun ce an kashe gwamman mayakan Taliban a hare-haren na baya-bayan nan ta sama - musamman a lardin Farah.

  Masu tayar da kayar bayan kuma wadanda a 'yan kwanakin nan suka samu manyan nasarorin yaki, basu maida martani ga kalaman jami'an ba.

  Kafin wannan lokaci Taliban ta ce mayakanta ne ke iko da biranen Kunduz da Sar-e-pul da kuma Taloqan.

  Gwamnatin Afghanisatn ta ce har yanzu sojin kundumbalanta na fafatawa a cikin birnin Kunduz.

  Taliban dai ta yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta duk da matsin lamba na ƙasashen duniya.

 19. An yanke hukuncin kisa ga mutumin da ya kashe matarsa a Jigawa

  J

  Wata babbar kotun jihar Jigawa da ke zamanta a Gumel ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani magidanci mai suna Rabiu Mamman.

  Mutumin mazaunin kauyen Medin Labo a karamar hukumar gagarawa kotu ta yanke masa wannan hukuncin ne bayan samun shi da laifin kashe matarsa.

  Alkalin kotun, Justice Abubakar Mohammed Sambo, ya ce kotu ta tabbatar da wannan hukuncin bayan shaidu da bayanai sun tabbatar, Mamman ya kashe matarsa a daji.

  A cewar sanarwar da kakakin ma'aikatar shari'a ta fitar, Zainab Baba Santali, a shekarar 2016 mutumin ya aikata laifin, lokacin da ya kaɗa matarsa daji sannan ya yi amfani da sanda ya rafka mata a kai, nan take rai ya yi halinsa. Sannan ya haƙa rami ya binne ta.

 20. Nijar za ta kafa rundunar tsaro ta musamman a Diffa

  Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da aniyarta ta samar da wata runduna ta musaman ta mayakan sama a jihar Diffa da ke iyakar kasar da Najeriya.

  Matakin wani ɓangare ne na kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar kasar, abin da shugaba Mohammed Bazoum ya sha alwashin yi.

  Ana fatan kafa rundunar da kuma sansanin zai saukaka aikin sojin ƙasar a yakin da suke da ƙungiyar Boko Haram.

  Yankin Diffa dama dai na fama da matsalar masu tayar da kayar baya tun shekarar 2015.

  A saurari ƙarin bayyani a cikin rahoton Tchima Illa Issoufou.

  Video content

  Video caption: Rahoton Tchima Illa Issoufou daga Nijar