Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Umar Mikail ke cewa mu haɗu gobe Alhamis don ci gaba da samun sabbin rahotanni.
Mu kwana lafiya.
Najeriya ta yi asarar dala biliyan 50 saboda rashin dokar PIB - Buhari
State HouseCopyright: State House
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya faɗa ranar Laraba cewa ƙasar ta yi asarar dala biliyan 50 na zuba jari cikin shekara 10 da suka wuce.
A cewarsa, hakan ya faru ne sakamakon jan ƙafa da aka dinga yi wajen fara aiki da dokar man fetur ta Petroleum Industry Bill (PIB), wadda ya sanya wa hannu ranar Litinin.
Da yake magana gabanin fara zaman Majalisar Zartarwa da ake yi duk Laraba, Buhari ya soki gwamnatocin baya da gazawa wajen ƙaddamar da dokar.
Shugaban ya ce hannun da ya saka wa dokar PIB ya kawo ƙarshen rashin tabbas da aka shafe shekaru ana ciki game da zuba jari a harkar man fetur ta Najeriya.
"Muna sane da cewa gwamnatocin baya sun fahimci akwai buƙatar su gyara ma'aikatar [mai] domin ta dace da kasuwanci, amma ba su mayar da hankali ba wajen tabbatar da samun sauyin," in ji Buhari.
"Wannan jan ƙafar ya daƙile ci gaban ma'aikatar da kuma haɓakar tattalin arzikinmu. Cikin shekara 10 da suka wuce, Najeriya ta yi asarar abin da aka yi ƙiyasin ya kai dala biliyan 50 na kuɗaɗen zuba jari saboda rashin tabbas da aka shiga sakamakon ƙin amincewa da dokar PIB."
Taliban: Ƙasashen Turai na rububin kwashe mutanensu daga Afghanistan
Getty ImagesCopyright: Getty Images
An samu rahotannin yamutsi a wajen filin jirgi na birnin Kabul yayin da ƙasashen Turai ke hanƙoron kwashe 'yan ƙasarsu da kuma abokan aikinsu na Afghanistan daga ƙasar.
Faransa da Netherlands da Sifaniya da Czech da Poland duk sun kwashi mutanensu a 'yan awannin da suka wuce.
An jiyo ƙarar harbe-harbe a kusa da filin jirgin a yau Laraba yayin da mutane suke ƙara tururuwa zuwa cikinsa.
Tafiyar ta zo wa ma'aikatan ofishin jakadancin Netherlands da ba-zata soai har ma suka manta ba su faɗa wa abokan aikinsu na Afghanistan ba cewa za su tafi a ranar Lahadi.
Wani jami'in sojan Netherlands ya ce yana fargabar babu isasshen lokacin kwashe masu tafinta da sauran ma'aikata 'yan Afghanistan.
"Idan ba mu iya gamawa ba cikin kwana biyu ko uku masu zuwa to mun makara," kamar yadda Anne-Marie ya faɗa wa BBC.
'Yan fashin daji: Mazauna Batsari na guduwa daga gidajensu saboda hare-hare
Video content
Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Zahradden LawanLatsa hoton sama ku saurari rahoton Zahradden Lawan
A Najeriya,
al’ummomi a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari na jihar Katsina na ci gaba da
tserewa matsugunansu sakamakon
farmakin da ‘yan bindiga suka kai musu a yammacin Talata.
Shaidu sun ce maharan
sun yi artabu da mutanen garin Batsari da kuma na kauyen Dankar abin da ya yi
sanadin mutuwar mutum uku.
Sai dai jami’an tsaro sun ce mutum biyu ne suka
rasu sannan aka sace mutum tara.
Masu iƙirarin jihadi sun kashe mutum 47 a Burkina Faso
AFPCopyright: AFP
'Yan bindiga masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso sun kashe mutum 47, ciki har da fararen hula 30 yayin wani hari a yau Laraba.
Kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ce harin wanda aka kai kusa da garin Arbinda da ke arewacin ƙasar ya yi sanadiyyar kashe wasu mayaƙan sa-kai da gwamnati ke mara wa baya guda uku.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin labarai na Reuters cewa an kashe 'yan bindigar 58 sakamakon fafatawar.
'Yan bindigar da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Islamic State na yawan kai hare-hare a arewacin Burkina Faso da kuma maƙotan ƙasashe kamar Nijar da Mali.
An zargi Rasha da yin dirar mikiya ga magoya bayan ƴan adawa
Masu kare hakkin dan Adam a Rasha na cewa jami'an 'yan sandan kasar sun kai
samame a gidajen magoya bayan 'yan adawa
a cikin dare, bayan da aka yi musu kutse cikin na'urorinsu kuma aka wallafa
bayanan a intanet.
Wata kungiya mai suna OVD-Info ta ce fiye da mutane talatin sun kira wata lambar
wayarta ta musamman - suna cewa 'yan
sanda sun far musu a cikin gidajensu yayin da suke barci.
Sunayensu sun bayyana a wani shafin intanet mallakin mai fafutukar ƙasar Alexei
Navalny, babban mai adawa da shugaba Putin, wanda ke tsare a kurkuku, wanda kuma Rasha ke kallon kungiyarsa a
matsayin ta masu tsattsauran ra'ayi.
Wani cikin wadanda aka yi wa samamen ya ce 'yan sandan sun yi kokarin
tursasa masa ya kai karar MistaNavalny.
Taliban: Daular Larabawa ta bai wa Shugaba Ashraf Ghani mafaka
ReutersCopyright: Reuters
Shugaban Ƙasar Afghanistan Ashraf Ghani ya nemi mafaka a ƙasar Daular Larabawa wato UAE, kamar yadda ƙasar ta tabbatar.
Mista Ghani ya tsere daga Afghanistan ne bayan ƙungiyar Taliban ta ƙwace iko da babban birnin ƙasar Kabul a ƙarshen makon da ya gabata.
Ma'aikatar Harkokin Wajen UAE ta ce ta yi wa Ghani da iyalinsa maraba bisa dalilai na jin ƙai.
An yi ta yaɗa jita-jitar cewa Tajikistan ya gudu tun farko. Kazalika, akwai ƙilawaƙala cewa yana ɗauke da tsabar kuɗi masu yawa tare da shi.
Cikin wani saƙon Facebook da ya wallafa ranar Lahadi, Ghani ya ce ya ɗauki matakin ne domin guje wa zubar da jini a Kabul.
Sai dai duk da haka ya sha suka daga wasu 'yan siyasar ƙasar saboda tserewar da ya yi.
Afirka ta Kudu: 'Yan kasa da shekara 15 sun haifi yara 934 cikin shekara ɗaya
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Wasu alƙaluma na baya-bayan nan sun bayyana yadda 'yan mata suka haifi yara masu yawa a yankin Gauteng na Afirka ta Kudu.
Jumillar jarirai 934 ne 'yan mata masu shekaru 10 zuwa 14 suka haifa a cikin shekara ɗaya, a cewar ministan lafiya na yankin yayin wani zaman majalisa.
Shekarun da doka ta yarda mace ta fara jima'i a Afirka ta Kudu su ne 16.
Duk da cewa wasu daga iyayen yaran maza su ma ba su kai shekarun doka ba, da yawa daga cikin 'yan matan suna samun ciki ne daga samarinsu masu shekaru da yawa, waɗanda ke ba su kuɗi da kuma kayayyakin ƙawa.
A baya an zargi malamai da hannu a lalata da yaran amma hukumomin ilimi sun ce an kori duk wanda aka samu da laifin aikata kawalci - wato haɗa masu neman mata da ɗalibansu.
Masu fafutika na cewa akwai buƙatar a zage damtse wajen wayar da kan 'yan mata game da ilimin jinsi ko jima'a domin kare rayuwarsu.
Mutum 1,000 aka kashe a Myanmar bayan juyin mulki
Wata kungiyar mai fafutukar ganin an saki fursunonin siyasa a Myanmar ta ce
yawan 'yan kasar da aka kashe tunbayan
juyin mulkin watan Fabrairu ya kai mutum 1,000.
Wadannan alkaluman sun fito ne daga kungiyar Assistance Association of
Political Prisoners, mai shalkwatarta aThailand - wadda kuma ke sa ido kan kashe-kashen da jami'an tsaron
gwamnatin ta Myanmar ke yi.
Sakataren kungiyar Tate Naing ya ce alkaluman ainihin wadanda jami'an
tsaron suka jikkata sun fi haka yawa matuka.
Gwamnatin mulkin soja ta kasar ba ta mayar da martani ba kan wannan
rahoton, amma a baya ta rika cewakungiyar ta AAPP tana zuzuta alkaluman wadanda rikicin siyasar kasar ya
shafa.
Sojoji sun hambare
gwamnatin zababbiyar shugaba Aung San Suu Kyi, suna cewa akwai kura-kurai a
zaben da yakawo ta mulki na watan
Nuwambar 2020.
An zargi Ghani da kwashe $169m daga baitul malun Afghanistan
An tabbatar da cewa Shugaba Ashraf Ghani ya tsere zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa bayan ya fice daga Kabul.
A gefe guda, jakadan Afghanistan a Tajikstan ya yi zargin cewa Mr Ghani ya tafi da kimanin $169m lokacin da ya fice daga kasar ranar Lahadi.
Ya bayyana tserewar da Ghani ya yi a matsayin "cin amanar kasarsa".
Jakada Mohammad Zahir Aghbar ya bayyana haka ne a wajen taron manema labarai a ofishin jakadancin Afghanistan da ke Dushanbe, babban birnin Tajikstan.
Ya kara da cewa ofishin jakadancin Afghanistan ya so ayyana mataimakin Ghani Amrullah Saleh a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar.
A wani sakon murya da ya aike wa BBC News jiya da daddare, Mr Saleh ya yi ikirarin cewa shi ne "halastaccen shugaban riko na Afghanistan" sannan ya yi alkwarin cewa "yaki ya zo karshe".
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Afghanistan na iya zama matattarar ƴan ta’adda - Theresa May
PACopyright: PA
Tsohuwar Firaiministar
Birtaniya, Theresa May, ta yi gargadin cewa duk da irin tabbacin da Taliban ke
bayarwa, akwai yiwuwar Afghanistan ta sake zama wata matattara ta 'yan ta'adda da shan alwashin kai hare-hare a
kan kasashen Yamma.
Ta ce ya zama wajibi
a sa ido kan take-taken Taliban ba furucinsu.
Amurka dai ta ce tana fatan Taliban za ta cika
alkawuran da ta dauka na mutunta hakkin dan Adam, bayan da ta karbe iko da
kasar ta Afghanistan.
Shugabannin kungiyar
kasashe bakwai mafiya karfin tattalin arziki za su gana a makon gobe domin
tattaunawa kan manufar bai-daya da za su ɗauka kan sabbin shugabannin na
Afghanistan.
Taliban ta tattauna da tsohon shugaban Afghanistan Hamid Karzai
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Jami'an Taliban sun ce Anas Haqqani, babban jagoran kungiyar Haqqani mai
alaka da kungiyar ta Taliban, ya tattauna da tsohon shugaban Afghanistan Hamid Karzai yayin da kungiyar
masu tayar da kayar baya ke kokarin kafa
gwamnati.
Jakada na musamman mai shiga tsakani na tsohuwar gwamnati Abdullah Abdullah
ma ya halarci tattaunawar.
Wasu 'yan Afghanistan sun bayyana mamakinsu da suka ga hotunan Mista
Haqqani - wanda aka yanke wa hukuncin
kisa a 2016, yana ganawa da wasu manyan jami'ian Taliban biyu.
Mista Haqqani - wanda kanin jagoran kungiyar Haqqani wato Sirajudine
Haqqani ne, kuma an sako shi daga kurkuku a 2019 tare da wasu 'yan bindiga biyu domin kungiyarsu ta saki
wasu malaman jami'a biyu 'yan yammacin
Turai da ke aiki a Kabul.
Labarai da dumi-dumiBuhari zai rusa NNPC
Video content
Video caption: Latsa hoton da ke sama don sauraren hira da Malam Garba Shehu kan rusa NNPCLatsa hoton da ke sama don sauraren hira da Malam Garba Shehu kan rusa NNPC
Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da cewa za a rusa babban kamfanin na kasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da BBC.
Sai dai ya ce za a maye gurbinsa da wani kamfanin mai zaman kansa.
Wannan na daga cikin ayukkan da aka dorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa a dazu yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.
Ministan albarkatun man fetur Timipreye Silver ne zai jagoranci wannan kwamitin.
Mutum 7 sun mutu bayan shaƙar iska mai guba a Osun
@ngpoliceCopyright: @ngpolice
Ƴan sanda a jihar
Osun sun tabbatar da mutuwar mutum bakwai ƴan gida ɗaya sakamakon shaƙar iska mai
guba.
Rundunar ƴan
sandan Osun ta ce mutum takwas aka samu kwance a ɗakunansu a gidan da suke amma
mutum ɗaya aka samu yana numfashi.
Kakakin ƴan
sandan jihar Yemisi Opalola ta shaida wa BBC cewa makwabta ne suka fara
fahimtar al’amarin waɗanda suka yi tunanin dukkaninsu sun mutu.
Ta ce ƴan sanda
na gudanar da bincike kan musabbabin al’amarin.
Jami’ar ƴan
sandan ta ce hayaƙin janareto na iya kasancewa musabbabin kisan.
Ana zaman makoki a Nijar
@Mohamed.BazoumCopyright: @Mohamed.Bazoum
Ana zaman makoki Jamhuriyar Nijar na kwana biyu domin nuna alhinin mutanen
da ƴan bindiga suka kashe a yankin Tillaberi.
Hukumomin Nijar sun tabbatar da cewa mutum 37 aka kashe a harin da ake
tunanin ƴan bindiga daga Mali ne suka kai.
Daga cikin waɗanda aka kashe har da mata da yara ƙanana.
Masu fafutukar farar hula sun soki gwamnati inda suka ce ana jan kafa kafin
ta fitar da sanarwa a duk lokacin da wani mummunan abu ya faru.
Ma’aikatan otal mata sun gudu saboda tsoron Taliban
Ma’aikata a
Afghanistan sun fara komawa bakin aiki yayin da aka fara ganin motoci kan titi, amma ɗabi’un mutane sun fara sauyawa a Kabul kwana biyu bayan Taliban ta ƙwace
mulkin ƙasar.
Manajan otal
din Kabul ya ce dukkanin ma’aikatansa mata sun gudu saboda tsoron Taliban.
Ya kuma ce ya
lura ma’aikatansa maza ba su aske gemu ba tsawon kwana uku.
Manajan ya ce
ma’aikatan sun tsorata bayan da wani gungun Taliban mutum 28 suka shigo otal ɗauke
da bindigogi suna tambayar abinci.
“Nan take na ji
an kashe kiɗa. Na tambayi ɗaya daga cikin ma’aikatan wanda ya ba ni amsa cewa, mutanen
fa na nan, don haka ba kiɗa,” in ji shi.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
An samu gawa a tayar jirgin Amurka da ya fito daga Afghanistan
Rundunar sojin sama ta Amurka ta ƙaddamar da bincike bayan samun gawar mutum a tayar jirgin sama wanda ya fito daga Kabul a ranar Litinin
Wani bidiyo da aka nuna ya ja hankalin duniya inda mutane suka maƙale a jirgi a lokacin da yake ƙoƙarin tashi sama a ƙoƙarin da suke na tserewa daga Afghanistan.
Rundunar ta ce za ta yi nazari kan bidiyon tare da fitar da rahoto kan mutanen da suka faɗo daga jirgin.
BBCCopyright: BBC
Ana fargabar ɓacewar awaki a Najeriya
Masana harkokin dabbobi
a Najeriya sun ce nan da shekaru biyu masu zuwa akwai yiwuwar bacewar awakan da
ake da su a ƙasar sakamakon
matsalar tsaro da kumaƙaruwar shigo da na kasashen waje.
Masanan na bayyana
hakan ne a dai dai lokacin da wasu masu cinikin awaki a kasar ke kokawa
da yadda rashin tsaro da ake fama da shi
a Najeriya ya shafi kiwon awakin gida.
Wakilinmu na Kano
Khalifa Shehu Dokaji ya ziyarci kasuwar ƴan
awaki da ke Unguwa Uku, a birnin Kano.
Ku saurari rahotonsa:
Video content
Video caption: Ana fargabar bacewar awaki a NajeriyaAna fargabar bacewar awaki a Najeriya
Zanga-zanga ta ɓarke a Afghanistan kan adawa da sauya tuta
Hutunan bidiyo a shafukan sada zumunta na intanet sun nuna yadda mutane suka fito saman titi suna zanga-zanga a birnin Jalalabad da ke gabashin Afghanistan.
Masu zanga-zangar na yin kira ne ga sabuwar gwamnatin Taliban kada ta sauya tutar ƙasar.
An gudanar da irin wannan zanga-zangar a wasu yankunan Afghanistan a jiya Talata.
A cikin hotunan bidiyon da ake yaɗawa an ji ƙarar harbin bindiga a wasu yankunan da mutane suka haɗa gangami. Babu tabbaci kan abin da ya biyo baya.
Taliban wacce ta sauya sunan Afghanistan zuwa ƙasar Daular Musulunci ta Afghanistan a yanzu tana amfani ne da farar tuta mai ɗauke da kalmar Shahada.
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid suna ci gaba da tattaunawa kan sabuwar tutar ƙasar.
An ɗage shari'ar Malam Abduljabbar a Kano
Kotun Kano ta ɗage sauraren ƙarar Malam Abduljabbar a zaman da ta yi a ranar Laraba.
Kotun ta tsayar 2 ga watan Satumban 2021 a matsayin ranar ci gaba da shari'ar.
Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ce abubuwan da aka gabatar bai kai ga tsayar da hukunci ba a zaman da kotun ta yi ranar Laraba inda ya ce akwai buƙatar ya yi nazari, kafin yanke hukunci.
Rahoto kai-tsaye
Daga Awwal Ahmad Janyau da Umar Mikail
time_stated_uk
Sai da safenku
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Umar Mikail ke cewa mu haɗu gobe Alhamis don ci gaba da samun sabbin rahotanni.
Mu kwana lafiya.
Najeriya ta yi asarar dala biliyan 50 saboda rashin dokar PIB - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya faɗa ranar Laraba cewa ƙasar ta yi asarar dala biliyan 50 na zuba jari cikin shekara 10 da suka wuce.
A cewarsa, hakan ya faru ne sakamakon jan ƙafa da aka dinga yi wajen fara aiki da dokar man fetur ta Petroleum Industry Bill (PIB), wadda ya sanya wa hannu ranar Litinin.
Da yake magana gabanin fara zaman Majalisar Zartarwa da ake yi duk Laraba, Buhari ya soki gwamnatocin baya da gazawa wajen ƙaddamar da dokar.
Shugaban ya ce hannun da ya saka wa dokar PIB ya kawo ƙarshen rashin tabbas da aka shafe shekaru ana ciki game da zuba jari a harkar man fetur ta Najeriya.
"Muna sane da cewa gwamnatocin baya sun fahimci akwai buƙatar su gyara ma'aikatar [mai] domin ta dace da kasuwanci, amma ba su mayar da hankali ba wajen tabbatar da samun sauyin," in ji Buhari.
"Wannan jan ƙafar ya daƙile ci gaban ma'aikatar da kuma haɓakar tattalin arzikinmu. Cikin shekara 10 da suka wuce, Najeriya ta yi asarar abin da aka yi ƙiyasin ya kai dala biliyan 50 na kuɗaɗen zuba jari saboda rashin tabbas da aka shiga sakamakon ƙin amincewa da dokar PIB."
Taliban: Ƙasashen Turai na rububin kwashe mutanensu daga Afghanistan
An samu rahotannin yamutsi a wajen filin jirgi na birnin Kabul yayin da ƙasashen Turai ke hanƙoron kwashe 'yan ƙasarsu da kuma abokan aikinsu na Afghanistan daga ƙasar.
Faransa da Netherlands da Sifaniya da Czech da Poland duk sun kwashi mutanensu a 'yan awannin da suka wuce.
An jiyo ƙarar harbe-harbe a kusa da filin jirgin a yau Laraba yayin da mutane suke ƙara tururuwa zuwa cikinsa.
Tafiyar ta zo wa ma'aikatan ofishin jakadancin Netherlands da ba-zata soai har ma suka manta ba su faɗa wa abokan aikinsu na Afghanistan ba cewa za su tafi a ranar Lahadi.
Wani jami'in sojan Netherlands ya ce yana fargabar babu isasshen lokacin kwashe masu tafinta da sauran ma'aikata 'yan Afghanistan.
"Idan ba mu iya gamawa ba cikin kwana biyu ko uku masu zuwa to mun makara," kamar yadda Anne-Marie ya faɗa wa BBC.
'Yan fashin daji: Mazauna Batsari na guduwa daga gidajensu saboda hare-hare
Video content
A Najeriya, al’ummomi a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari na jihar Katsina na ci gaba da tserewa matsugunansu sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai musu a yammacin Talata.
Shaidu sun ce maharan sun yi artabu da mutanen garin Batsari da kuma na kauyen Dankar abin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku.
Sai dai jami’an tsaro sun ce mutum biyu ne suka rasu sannan aka sace mutum tara.
Masu iƙirarin jihadi sun kashe mutum 47 a Burkina Faso
'Yan bindiga masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso sun kashe mutum 47, ciki har da fararen hula 30 yayin wani hari a yau Laraba.
Kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ce harin wanda aka kai kusa da garin Arbinda da ke arewacin ƙasar ya yi sanadiyyar kashe wasu mayaƙan sa-kai da gwamnati ke mara wa baya guda uku.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin labarai na Reuters cewa an kashe 'yan bindigar 58 sakamakon fafatawar.
'Yan bindigar da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Islamic State na yawan kai hare-hare a arewacin Burkina Faso da kuma maƙotan ƙasashe kamar Nijar da Mali.
An zargi Rasha da yin dirar mikiya ga magoya bayan ƴan adawa
Masu kare hakkin dan Adam a Rasha na cewa jami'an 'yan sandan kasar sun kai samame a gidajen magoya bayan 'yan adawa a cikin dare, bayan da aka yi musu kutse cikin na'urorinsu kuma aka wallafa bayanan a intanet.
Wata kungiya mai suna OVD-Info ta ce fiye da mutane talatin sun kira wata lambar wayarta ta musamman - suna cewa 'yan sanda sun far musu a cikin gidajensu yayin da suke barci.
Sunayensu sun bayyana a wani shafin intanet mallakin mai fafutukar ƙasar Alexei Navalny, babban mai adawa da shugaba Putin, wanda ke tsare a kurkuku, wanda kuma Rasha ke kallon kungiyarsa a matsayin ta masu tsattsauran ra'ayi.
Wani cikin wadanda aka yi wa samamen ya ce 'yan sandan sun yi kokarin tursasa masa ya kai karar MistaNavalny.
Taliban: Daular Larabawa ta bai wa Shugaba Ashraf Ghani mafaka
Shugaban Ƙasar Afghanistan Ashraf Ghani ya nemi mafaka a ƙasar Daular Larabawa wato UAE, kamar yadda ƙasar ta tabbatar.
Mista Ghani ya tsere daga Afghanistan ne bayan ƙungiyar Taliban ta ƙwace iko da babban birnin ƙasar Kabul a ƙarshen makon da ya gabata.
Ma'aikatar Harkokin Wajen UAE ta ce ta yi wa Ghani da iyalinsa maraba bisa dalilai na jin ƙai.
An yi ta yaɗa jita-jitar cewa Tajikistan ya gudu tun farko. Kazalika, akwai ƙilawaƙala cewa yana ɗauke da tsabar kuɗi masu yawa tare da shi.
Cikin wani saƙon Facebook da ya wallafa ranar Lahadi, Ghani ya ce ya ɗauki matakin ne domin guje wa zubar da jini a Kabul.
Sai dai duk da haka ya sha suka daga wasu 'yan siyasar ƙasar saboda tserewar da ya yi.
Afirka ta Kudu: 'Yan kasa da shekara 15 sun haifi yara 934 cikin shekara ɗaya
Wasu alƙaluma na baya-bayan nan sun bayyana yadda 'yan mata suka haifi yara masu yawa a yankin Gauteng na Afirka ta Kudu.
Jumillar jarirai 934 ne 'yan mata masu shekaru 10 zuwa 14 suka haifa a cikin shekara ɗaya, a cewar ministan lafiya na yankin yayin wani zaman majalisa.
Shekarun da doka ta yarda mace ta fara jima'i a Afirka ta Kudu su ne 16.
Duk da cewa wasu daga iyayen yaran maza su ma ba su kai shekarun doka ba, da yawa daga cikin 'yan matan suna samun ciki ne daga samarinsu masu shekaru da yawa, waɗanda ke ba su kuɗi da kuma kayayyakin ƙawa.
A baya an zargi malamai da hannu a lalata da yaran amma hukumomin ilimi sun ce an kori duk wanda aka samu da laifin aikata kawalci - wato haɗa masu neman mata da ɗalibansu.
Masu fafutika na cewa akwai buƙatar a zage damtse wajen wayar da kan 'yan mata game da ilimin jinsi ko jima'a domin kare rayuwarsu.
Mutum 1,000 aka kashe a Myanmar bayan juyin mulki
Wata kungiyar mai fafutukar ganin an saki fursunonin siyasa a Myanmar ta ce yawan 'yan kasar da aka kashe tunbayan juyin mulkin watan Fabrairu ya kai mutum 1,000.
Wadannan alkaluman sun fito ne daga kungiyar Assistance Association of Political Prisoners, mai shalkwatarta aThailand - wadda kuma ke sa ido kan kashe-kashen da jami'an tsaron gwamnatin ta Myanmar ke yi.
Sakataren kungiyar Tate Naing ya ce alkaluman ainihin wadanda jami'an tsaron suka jikkata sun fi haka yawa matuka.
Gwamnatin mulkin soja ta kasar ba ta mayar da martani ba kan wannan rahoton, amma a baya ta rika cewakungiyar ta AAPP tana zuzuta alkaluman wadanda rikicin siyasar kasar ya shafa.
Sojoji sun hambare gwamnatin zababbiyar shugaba Aung San Suu Kyi, suna cewa akwai kura-kurai a zaben da yakawo ta mulki na watan Nuwambar 2020.
An zargi Ghani da kwashe $169m daga baitul malun Afghanistan
An tabbatar da cewa Shugaba Ashraf Ghani ya tsere zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa bayan ya fice daga Kabul.
A gefe guda, jakadan Afghanistan a Tajikstan ya yi zargin cewa Mr Ghani ya tafi da kimanin $169m lokacin da ya fice daga kasar ranar Lahadi.
Ya bayyana tserewar da Ghani ya yi a matsayin "cin amanar kasarsa".
Jakada Mohammad Zahir Aghbar ya bayyana haka ne a wajen taron manema labarai a ofishin jakadancin Afghanistan da ke Dushanbe, babban birnin Tajikstan.
Ya kara da cewa ofishin jakadancin Afghanistan ya so ayyana mataimakin Ghani Amrullah Saleh a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar.
A wani sakon murya da ya aike wa BBC News jiya da daddare, Mr Saleh ya yi ikirarin cewa shi ne "halastaccen shugaban riko na Afghanistan" sannan ya yi alkwarin cewa "yaki ya zo karshe".
Afghanistan na iya zama matattarar ƴan ta’adda - Theresa May
Tsohuwar Firaiministar Birtaniya, Theresa May, ta yi gargadin cewa duk da irin tabbacin da Taliban ke bayarwa, akwai yiwuwar Afghanistan ta sake zama wata matattara ta 'yan ta'adda da shan alwashin kai hare-hare a kan kasashen Yamma.
Ta ce ya zama wajibi a sa ido kan take-taken Taliban ba furucinsu.
Amurka dai ta ce tana fatan Taliban za ta cika alkawuran da ta dauka na mutunta hakkin dan Adam, bayan da ta karbe iko da kasar ta Afghanistan.
Shugabannin kungiyar kasashe bakwai mafiya karfin tattalin arziki za su gana a makon gobe domin tattaunawa kan manufar bai-daya da za su ɗauka kan sabbin shugabannin na Afghanistan.
Taliban ta tattauna da tsohon shugaban Afghanistan Hamid Karzai
Jami'an Taliban sun ce Anas Haqqani, babban jagoran kungiyar Haqqani mai alaka da kungiyar ta Taliban, ya tattauna da tsohon shugaban Afghanistan Hamid Karzai yayin da kungiyar masu tayar da kayar baya ke kokarin kafa gwamnati.
Jakada na musamman mai shiga tsakani na tsohuwar gwamnati Abdullah Abdullah ma ya halarci tattaunawar.
Wasu 'yan Afghanistan sun bayyana mamakinsu da suka ga hotunan Mista Haqqani - wanda aka yanke wa hukuncin kisa a 2016, yana ganawa da wasu manyan jami'ian Taliban biyu.
Mista Haqqani - wanda kanin jagoran kungiyar Haqqani wato Sirajudine Haqqani ne, kuma an sako shi daga kurkuku a 2019 tare da wasu 'yan bindiga biyu domin kungiyarsu ta saki wasu malaman jami'a biyu 'yan yammacin Turai da ke aiki a Kabul.
Labarai da dumi-dumiBuhari zai rusa NNPC
Video content
Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da cewa za a rusa babban kamfanin na kasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da BBC.
Sai dai ya ce za a maye gurbinsa da wani kamfanin mai zaman kansa.
Wannan na daga cikin ayukkan da aka dorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa a dazu yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.
Ministan albarkatun man fetur Timipreye Silver ne zai jagoranci wannan kwamitin.
Mutum 7 sun mutu bayan shaƙar iska mai guba a Osun
Ƴan sanda a jihar Osun sun tabbatar da mutuwar mutum bakwai ƴan gida ɗaya sakamakon shaƙar iska mai guba.
Rundunar ƴan sandan Osun ta ce mutum takwas aka samu kwance a ɗakunansu a gidan da suke amma mutum ɗaya aka samu yana numfashi.
Kakakin ƴan sandan jihar Yemisi Opalola ta shaida wa BBC cewa makwabta ne suka fara fahimtar al’amarin waɗanda suka yi tunanin dukkaninsu sun mutu.
Ta ce ƴan sanda na gudanar da bincike kan musabbabin al’amarin.
Jami’ar ƴan sandan ta ce hayaƙin janareto na iya kasancewa musabbabin kisan.
Ana zaman makoki a Nijar
Ana zaman makoki Jamhuriyar Nijar na kwana biyu domin nuna alhinin mutanen da ƴan bindiga suka kashe a yankin Tillaberi.
Hukumomin Nijar sun tabbatar da cewa mutum 37 aka kashe a harin da ake tunanin ƴan bindiga daga Mali ne suka kai.
Daga cikin waɗanda aka kashe har da mata da yara ƙanana.
Masu fafutukar farar hula sun soki gwamnati inda suka ce ana jan kafa kafin ta fitar da sanarwa a duk lokacin da wani mummunan abu ya faru.
Ma’aikatan otal mata sun gudu saboda tsoron Taliban
Ma’aikata a Afghanistan sun fara komawa bakin aiki yayin da aka fara ganin motoci kan titi, amma ɗabi’un mutane sun fara sauyawa a Kabul kwana biyu bayan Taliban ta ƙwace mulkin ƙasar.
Manajan otal din Kabul ya ce dukkanin ma’aikatansa mata sun gudu saboda tsoron Taliban.
Ya kuma ce ya lura ma’aikatansa maza ba su aske gemu ba tsawon kwana uku.
Manajan ya ce ma’aikatan sun tsorata bayan da wani gungun Taliban mutum 28 suka shigo otal ɗauke da bindigogi suna tambayar abinci.
“Nan take na ji an kashe kiɗa. Na tambayi ɗaya daga cikin ma’aikatan wanda ya ba ni amsa cewa, mutanen fa na nan, don haka ba kiɗa,” in ji shi.
An samu gawa a tayar jirgin Amurka da ya fito daga Afghanistan
Rundunar sojin sama ta Amurka ta ƙaddamar da bincike bayan samun gawar mutum a tayar jirgin sama wanda ya fito daga Kabul a ranar Litinin
Wani bidiyo da aka nuna ya ja hankalin duniya inda mutane suka maƙale a jirgi a lokacin da yake ƙoƙarin tashi sama a ƙoƙarin da suke na tserewa daga Afghanistan.
Rundunar ta ce za ta yi nazari kan bidiyon tare da fitar da rahoto kan mutanen da suka faɗo daga jirgin.
Ana fargabar ɓacewar awaki a Najeriya
Masana harkokin dabbobi a Najeriya sun ce nan da shekaru biyu masu zuwa akwai yiwuwar bacewar awakan da ake da su a ƙasar sakamakon matsalar tsaro da kumaƙaruwar shigo da na kasashen waje.
Masanan na bayyana hakan ne a dai dai lokacin da wasu masu cinikin awaki a kasar ke kokawa da yadda rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya ya shafi kiwon awakin gida.
Wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ziyarci kasuwar ƴan awaki da ke Unguwa Uku, a birnin Kano.