Daga Buhari Muhammad Fagge da Umaymah Sani Abdulmumin
time_stated_uk
Rufewa
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka nake bankwana da ku, sai kuma gobe Asabar da yardar Ubangiji. Umaymah Sani Abdulmumin nake cewa ku huta lafiya.
Umarnin 'ba zuwa aiki ba albashi' zai soma aiki kan likitoci a Najeriya
MINISTRY OF LABOURCopyright: MINISTRY OF LABOUR
Gwamnatin Najeriya ta umarci asibitoci da cibiyoyin lafiya da likitocinsu ke yajin aiki su soma aiwatar da umarnin "ba zuwa aiki ba albashi" kuma lissafin ya soma daga 2 ga watan Agusta, ranar da suka shiga yajin aikin.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar na cewa dole wannan umarni ya soma aiki da ranakun da likitoci suka shiga yajin aiki a kowanne bangare.
Sai dai da alama wannan bai razana likitocin da suka dage akan batunsu ba, suna mai cewa matakin gwamnati ba zai tilasta masu yanje yajin aikin kusan wata daya ba.
Likitocin a jiya Alhamis sun sake jadada matsayinsu a sanarwar da suka fitar bayan taron tattaunawa na kasa.
Labaran yamma cikin minti ɗaya da BBC
Video content
Video caption: A saurari labaran duniya cikin minti ɗaya da BBCA saurari labaran duniya cikin minti ɗaya da BBC
Amurka ta ce mutum 170 ne suka mutu a harin Kabul
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Jami'ai a ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon sun ce mutum dari da saba'in ne su ka mutu a harin bam din da kungiyar IS ta kai jiya a filin jirgin saman Kabul na kasar Afghanistan.
Amma duk da harin bam din, Amurka ta sanar da za ta ci gaba kwashe mutanenta daga filin jirgin saman har zuwa ranar Talata mai zuwa.
Rahotanni na cewa a cikin sa'o'in da su ka gabata, Sweden ta kammala kwashe mutanenta.
Sifaniya da Jamus da Canada da Australia ma duka sun yi sallama da Afghanistan.
An kwashe mutum dubu goma sha biyu da dari biyar cikin kwana guda, kuma akwai sauran mutum fiye da dubu biyar da su ka rage cikin filin jirgin saman.
Jami'an Pentagon sun kuma ce Amurka da taimakon Taliban su na samar da wani sabon tsari domin inganta tsaro a filin jirgin saman na Kabul.
Babban limamin Ghana ya bada gudunmawar gina babban coci a ƙasar
AFPCopyright: AFP
Babban limamin Ghana, Sheikh Osman Sharubutu ya ba da sama da dala dubu takwas a matsayin gudunmawar ginin wani babban coci a ƙasar.
Ginin da ake sa ran za a kammala a 2024, zai kunshi wani wurin adana kayan tarihi na bible da kuma dakin taro mai cin kujeru dubu biyar.
Ghana na da tarihin rashin jituwa tsakanin addinai, ko da yake wannan gudunmawa bai zo da mamaki ba.
Limamin mai shekaru 102 a duniya ya ce ya yanke shawarar yin haka ne domin sake gyara da inganta alaƙa tsakanin Kiristoci da Musulmi.
Ya kuma sha cewa a kullum fatansa shi ne tabbatar da zaman lafiya tsakanin kowanne bangare na addinan ƙasar.
Ko shekaru biyu da suka gabata, sai da ya halarci wani taron kiristoci a coci, batun da ya haifar da ce--ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
Maƙiyan Najeriya ba za su yi nasarar ruguzata ba - Obasanjo
BBCCopyright: BBC
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce makiyan ƙasar da ke fatan ganin kasar ta ruguje ba za su yi nasara ba.
A wata sanarwa da kakakinsa Kehinde Akinyemi ya fitar, tsohon shugaban ya ce kasancewa dunkulalliyar kasa ya fi riba kan raba kawunanta.
Obasanjo ya shaida hakan ne a lokacin kaddamar da wani littafi a Legas.
Tsohon shugaban ya kuma kara da cewa shi masoyin Najeriya ne kuma yana sane da halin da kasar ke ciki.
Sai dai ya ce yana da yaƙinin maƙiyan Najeriya ba za su kai labari ba, domin ƙasar za ta ci gaba da samun wanzuwa.
An kama wani babban jami'in gwamnati da rashawa a China
Wani babban jami'in gwamnatin China da a baya ke jagorantar yaki da cin hanci da rashawa - shi ma an kama shi da laifin karbar cin hanci.
Dong Hong ya gaya wa kotun da ta yi ma sa shari'a cewa ya karbi cin hancin sama da dalar Amurka miliyan saba'in ciin shekara ashirin da su ka gabata.
An kuma tuhume shi da gudanar da rayuwar da ta fi karfin kudaden da yake samu, inda aka same shi yana ziyartar kulob-kulob din da sai hamshakan masu hali ke iya shiga.
A baya Mista Hong ya kasance mataimakin babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta China.
Ya kuma taba zama na hannun daman mataimakin shugaban kasar, Wang Qishan.
Sai dai ba kasafai akan tuhumi jami'ai makusantan shugabannin China da laifukan rashawa ba.
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matan aure a Zaria
@GOVKADUNACopyright: @GOVKADUNA
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu matan aure uku da namiji guda mazaunin Zango a karamar hukumar Sabon Gari ta Kaduna.
Yankin Zango kusa ya ke da jami'ar Ahmadu Bello na Zaria.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan bindigar sun dirar wa garin ne da tsakiyar daren Alhamis, suna harbi kan mai uwa dawabi.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki bayan ƴan bindiga sun kai hari makarantar sojoji ta NDA, tare da kashe sojoji biyu da garkuwa da wani manjo.
Kakakin ƴan sandan Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da harin sannan ya ce suna bincike.
An kama tsohon minista da laifin cin hanci
An kama wani tsohon firaminista kuma ministan tsaron kasar Mali bayan da aka tuhume shi da laifin cin hanci da rashawa kan wata badakalar sayen jirgin saman shugaban kasar, yayin da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ke mulkin kasar.
Ana dai ganin Soumeylou Boubeye Maiga a matsayin wanda zai tsaya takarar mukamin shugaban kasa a zaben da ke tafe shekara mai zuwa.
An sayo jirgin ne a shekarar dubu biyu da goma sha hudu kan dala miliyan 40, wanda yawancin mutanen kasar suka ce akwai ayar tambaya kan sahihancin cinikin.
Wannan badakalar ta zubar da mutuncin tsohon Shugaba Keita, wanda daga baya sojojin kasar suka hambarar da shi daga mulki a watan Agustar bara.
Ronaldo zai koma Manchester United da taka leda
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Manchester United ta ce ta cimma matsaya da Juventus domin sayen dan kwallon Portugal Cristiano Ronaldo.
A wani saƙo da Manchester United ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce "maraba da zuwa gida Ronaldo," wadda wannan alama ce da ke nuna cewa Ronaldo zai koma kulob ɗin
United ta ce kammala cinikin ɗan wasan da ya lashe Ballon d'Or sau biyar ya ta'allaƙa ne da batun abin ɗan wasan yake so da kuma batun samun biza da kuma lafiyarsa.
Ronaldo ya ci ƙwallo 118 a wasanni 292 da ya buga a lokacin da yake Old Trafford kafin daga baya ya koma Real Madrid.
Ana zargin jirgin saman soji da buɗe wa jirgin ruwan farar hula wuta a Ribas
GODSWILL JUMBOCopyright: GODSWILL JUMBO
Ƴan sandan ruwa a garin Bonny na jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Najeriya sun soma bincike kan zargin da ake yi wa wani jirgin soji na buɗe wuta ga wani jirgin ruwan ɗaukar kayayyaki.
Rahotanni sun ce jirgin na ɗauke da kayan abinci da sauran abubuwa inda yake hanyarsa ta zuwa garin Bonny daga tashar ruwa ta Nembe-Bille da ke Fatakwal.
Awwal Rufai, wanda ke cikin jirgin ruwan a lokacin da lamarin ya faru ya shaida cewa lamarin ya faru ne a tsibirin Dutch da ke Okrika kuma har an harbe mutum biyu, cikin waɗanda aka harba har da Awwal ɗin.
"Ni a ɗan yatsa harsashin ya same ni sai dai ɗayan mutumin a ƙwabri harsashin ya same shi.
"Sauran yaran da ke cikin jirgin sun yi tsalle sun faɗa ruwa."
Jami'in ɗan sandan da ke kula da yankin ruwan Bonny, SP Solomon Adeniyi ya shaida wa BBC cewa sun samu rahoto kan wannan lamarin kuma tuni suka fara bincike.
Yadda matafiya suka shafe dare cikin cunkoson ababen hawa a Nairobi
BBCCopyright: BBC
Dubban matafiya ne suka maƙale cikin cunkoson ababen hawa a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya inda suka shafe sama da sa'o'i takwas a cikin cunkoson.
Rahotanni sun ce cunkushewar hanyar ta samo asali ne sakamakon faɗaɗa wata babbar hanya da wani kamfanin China ke yi.
Ma'aikatan da ke aikin ne suka rufe wasu bangarori na hanyar tare da yin rami a gaban hanyoyin da suke gyara domin hana matafiya bin hanyar.
Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun ta wallafa hotuna da bidiyo kan yadda mutane ke ta mita da ƙorafi kan irin halin da suka shiga inda wasu ke cewa sun bar wurin aiki tun shida na yamma amma ba su koma gida ba sai huɗu na asuba.
Wani da ya wallafa saƙo a shafin Twitter ya bayyana cewa akwai wasu da ke dauke da jarirai haka kuma akwai masu yawon buɗe ido da jirgi ya tafi ya bar su.
Cristiano Ronaldo: Man Utd na gab da sayen dan kwallon Juventus
MANCHESTER UNITEDCopyright: MANCHESTER UNITED
Manchester United ta yi nisa a tattaunawa domin sayen dan kwallon Portugal Cristiano Ronaldo daga Juventus.
BBC ta gano cewa dan wasan mai shekaru 36 ba zai koma Manchester City ba.
Kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya tabbatar da cewa Ronaldo ya ce "bai da niyyar ci gaba da murza leda" tare da Juve.
Ronaldo ya kulla yarjejeniya da Manchester United daga Sporting Lisbon a kan fiye da fan miliyan 12 a shekara ta 2003 inda ya zura kwallo 118 cikin wasa 292 a kulob din.
Taliban na son Turkiyya ta ci gaba da kula da filin jirgin Kabul
ReutersCopyright: Reuters
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Taliban ta nemi Turkiyya ta ci gaba da kula da filin jirgin Kabul amma har yanzu babu wani mataki da aka dauka.
Kafin ya bar Bosnia, kafin ya bar filin jirgin sama na Istanbul , "Taliban ta bukaci mu ci gaba da gunar da filin jirgin Kabul. Sai dai ba mu dauki matakin komai ba kan wannan batu har ya zuwa yanzu."
"Za mu bayyana matsayarmu ne kawai bayan an samu daidaituwar gwamnati a kasar," in ji shi.
Erdogan yana nufin wani taro da zai yi na sama da awa uku da za a yi da wakilan Turkiyya da na Taliban a ofishin jakadancin Turkiyya a Kabul.
ReutersCopyright: Reuters
Sai dai bai bayyana takamaimai yaushe ne za a yi wannan tattaunawar ba amma ya ce "za a kara irin wannan tattaunawar a gaba idan da bukatar hakan".
Shugaba Erdogan ya ce za a ci gaba da kwashe dakarun Turkiyya daga Kabul wanda aka soma a ranar Laraba.
Ya kuma yi Allah wadai da harin da aka kai a ranar Alhamis.
An kama wani jami'in China mai yaki da cin hanci da rashawa da zargin karbar na goro
DCCopyright: DC
Wani babban jami'in gwamnatin China da a baya ke jagorantar yaki da cin hanci da rashawa - shi ma an kama shi da laifin karbar cin hanci.
Dong Hong ya gaya wa kotun da ta yi ma sa shari'a cewa ya karbi cin hancin sama da dalar Amurka miliyan saba'in ciin shekara ashirin da su ka gabata.
An kuma tuhume shi da gudanar da rayuwar da ta fi karfin kudaden da yake samu, inda aka same shi yana ziyartar kulob-kulob din da sai hamshakan masu hali ke iya shiga.
A baya Mista Hong ya kasance mataimakin babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta China.
Ya kuma taba zama na hannun daman mataimakin shugaban kasar, Wang Qishan.
Sai dai ba kasafai akan tuhumi jami'ai makusantan shugabannin China da laifukan rashawa ba.
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Rabi'u Rijiyar Lemu
Video content
Video caption: Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Rabi'u Rijiyar LemuBidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Rabi'u Rijiyar Lemu
An kama tsohon Ministan noman rani na Malawi
An kama tsohon ministan ƙasar Malawi bisa zarginsa da biyan kuɗin otel da kuɗin ƙasa.
Ana zargin Charles Mchacha, wanda shi ne ministan noman rani a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Peter Mutharika, da amfani da kuɗin ma'aikatarsa wajen biyan wani katafaren ɗaki a wani otel da ke Blantyre na Scotland bayan bikinsa inda a otel ɗin ne ya je hutu da amaryarsa.
Wata jarida ta Malawi ta wallafa labarin wasu manyan jami'an gwamnatin biyu a shafin Twitter wadanda hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar ACB ta ce za ta gurfanar da duka mutum ukun a gaban kotu bisa zargin sata da ƙin mayar da hankali wurin aiki.
Sai dai duka mutum ukun sun musanta zarge-zargen.
Su wanene suka hana El-Zakzaky tafiya neman magani?
KDNCopyright: KDN
Kimanin makonni hudu da wata
babbar kotun Kaduna ta bayar da belin shugaban kungiyar harka Islamiyya a
Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, da matarsa Malama Zeenah Ibrahim, sai dai
har yanzu sun gaza fita kasashen waje neman magani saboda an jami’an tsaro sun
rike fasfo dinsu.
Cikin wata sanarwa da
kakakin kungiyar Ibrahim Musa ya fitar ta ce ba dai a san fasfo din ko yana
hannun wacce hukuma ba, hukumar leke asiri ta NIA da ta fararen kaya DSS duka
sun ce ba su rike da fasfo din mutanen biyu.
Sanarwar ta kara da cewa abin
da ya bayyana shi ne lokacin da babbar Kotun Kaduna ta yarje wa shugaban da
matarsa fita neman magani Indiya a baya, jami’an tsaro sun karbe takardun
shaidar tafiyarsu.
Wa
aka bai wa takardun? Wannan tambayar da kyar za ta samu amsa ganin cewa an
dauki lokaci da faruwar abin tun 2018.
Sai
dai mabiya na tambayar ko wani babban mai mukami ne ke neman amfani da wannan
damar ya kara yi masu daurin talala a cikin kasar, a cewar sanarwar Ibrahim
Musa mutane da dama na harsashen haka.
Quote Message: Muna amfani da wannan damar domin sanar da mutane kimanin shekara shida, sakamakon rahoton da aka fitar na lafiya a kansu ya nuna cewa suna cikin yanayin rashin lafiya sosai, abin da kotun ta duba kenan ta ba su damar fita neman magani wanda gwamnati ta hana hakan a 2018.. in ji sanarwar
Muna amfani da wannan damar domin sanar da mutane kimanin shekara shida, sakamakon rahoton da aka fitar na lafiya a kansu ya nuna cewa suna cikin yanayin rashin lafiya sosai, abin da kotun ta duba kenan ta ba su damar fita neman magani wanda gwamnati ta hana hakan a 2018.. in ji sanarwar
Moroka za ta rufe ofishin jakadancinta a Aljeriya
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Moroka ta shirya tsaf domin rufe ofishin jakadancinta a Ajeriya a ranar Juma'a, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan da Aljeriya ta sanar da kara tsamin dangantaka tsakaninta da masarautar a wani abu da takita "mataki mai cike da hadari".
Wani da ya nemi a boye sunansa ya ce, Moroko za ta rufe ofishin jakadancinta da ke Aljeris, kuma ma'aikatan da suke aiki a wurin za su tattara su koma gida.
Amma a gefe daya kuma karamin ofishin jakadancinta zai ci gaba d kasancewa a bude, kamar yadda mutumin ya shaida.
Za mu dauki mataki kan Abba Kyari - Rundunar 'yan sandan Najeriya
Abba KyariCopyright: Abba Kyari
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta dauki matakin da ya dace kan dakataccen jami'inta Abba Kyari matukar aka same shi da laifin da ake zarginsa da shi.
Hukumar ta yi wannan bayani ne bayan karbar wani rahoto na musamman kan binciken da ake yi a kansa.
An mika wa Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya rahoton binciken da ake gudanar wa kan Abba Kyari, wanda aka dakatar da shi daga aiki bayan zarginsa da alaka da Hushpuppi, wanda ake kira Ramon Abbas.
Yanzu rundunar 'yan sandan ta kafa wani kwamiti da zai yi na shi binciken kan zargin da Amurka ta yi wa Abba Kyarin wanda ya musanta.
A ranar Alhamis ne Mataimakin shugaban 'yan sanda Joseph Egbunike ya mika rahoton sai dai ba a bayyana me ya kunsa ba.
Shugaban 'yan sanda Usman Baba ya yi alkawarin gudanar da binciken "ba sani ba sabo wanda za a yi a faifai".
Rahoto kai-tsaye
Daga Buhari Muhammad Fagge da Umaymah Sani Abdulmumin
time_stated_uk
Rufewa
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka nake bankwana da ku, sai kuma gobe Asabar da yardar Ubangiji. Umaymah Sani Abdulmumin nake cewa ku huta lafiya.
Umarnin 'ba zuwa aiki ba albashi' zai soma aiki kan likitoci a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta umarci asibitoci da cibiyoyin lafiya da likitocinsu ke yajin aiki su soma aiwatar da umarnin "ba zuwa aiki ba albashi" kuma lissafin ya soma daga 2 ga watan Agusta, ranar da suka shiga yajin aikin.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar na cewa dole wannan umarni ya soma aiki da ranakun da likitoci suka shiga yajin aiki a kowanne bangare.
Sai dai da alama wannan bai razana likitocin da suka dage akan batunsu ba, suna mai cewa matakin gwamnati ba zai tilasta masu yanje yajin aikin kusan wata daya ba.
Likitocin a jiya Alhamis sun sake jadada matsayinsu a sanarwar da suka fitar bayan taron tattaunawa na kasa.
Labaran yamma cikin minti ɗaya da BBC
Video content
Amurka ta ce mutum 170 ne suka mutu a harin Kabul
Jami'ai a ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon sun ce mutum dari da saba'in ne su ka mutu a harin bam din da kungiyar IS ta kai jiya a filin jirgin saman Kabul na kasar Afghanistan.
Amma duk da harin bam din, Amurka ta sanar da za ta ci gaba kwashe mutanenta daga filin jirgin saman har zuwa ranar Talata mai zuwa.
Rahotanni na cewa a cikin sa'o'in da su ka gabata, Sweden ta kammala kwashe mutanenta.
Sifaniya da Jamus da Canada da Australia ma duka sun yi sallama da Afghanistan.
An kwashe mutum dubu goma sha biyu da dari biyar cikin kwana guda, kuma akwai sauran mutum fiye da dubu biyar da su ka rage cikin filin jirgin saman.
Jami'an Pentagon sun kuma ce Amurka da taimakon Taliban su na samar da wani sabon tsari domin inganta tsaro a filin jirgin saman na Kabul.
Babban limamin Ghana ya bada gudunmawar gina babban coci a ƙasar
Babban limamin Ghana, Sheikh Osman Sharubutu ya ba da sama da dala dubu takwas a matsayin gudunmawar ginin wani babban coci a ƙasar.
Ginin da ake sa ran za a kammala a 2024, zai kunshi wani wurin adana kayan tarihi na bible da kuma dakin taro mai cin kujeru dubu biyar.
Ghana na da tarihin rashin jituwa tsakanin addinai, ko da yake wannan gudunmawa bai zo da mamaki ba.
Limamin mai shekaru 102 a duniya ya ce ya yanke shawarar yin haka ne domin sake gyara da inganta alaƙa tsakanin Kiristoci da Musulmi.
Ya kuma sha cewa a kullum fatansa shi ne tabbatar da zaman lafiya tsakanin kowanne bangare na addinan ƙasar.
Ko shekaru biyu da suka gabata, sai da ya halarci wani taron kiristoci a coci, batun da ya haifar da ce--ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
Maƙiyan Najeriya ba za su yi nasarar ruguzata ba - Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce makiyan ƙasar da ke fatan ganin kasar ta ruguje ba za su yi nasara ba.
A wata sanarwa da kakakinsa Kehinde Akinyemi ya fitar, tsohon shugaban ya ce kasancewa dunkulalliyar kasa ya fi riba kan raba kawunanta.
Obasanjo ya shaida hakan ne a lokacin kaddamar da wani littafi a Legas.
Tsohon shugaban ya kuma kara da cewa shi masoyin Najeriya ne kuma yana sane da halin da kasar ke ciki.
Sai dai ya ce yana da yaƙinin maƙiyan Najeriya ba za su kai labari ba, domin ƙasar za ta ci gaba da samun wanzuwa.
An kama wani babban jami'in gwamnati da rashawa a China
Wani babban jami'in gwamnatin China da a baya ke jagorantar yaki da cin hanci da rashawa - shi ma an kama shi da laifin karbar cin hanci.
Dong Hong ya gaya wa kotun da ta yi ma sa shari'a cewa ya karbi cin hancin sama da dalar Amurka miliyan saba'in ciin shekara ashirin da su ka gabata.
An kuma tuhume shi da gudanar da rayuwar da ta fi karfin kudaden da yake samu, inda aka same shi yana ziyartar kulob-kulob din da sai hamshakan masu hali ke iya shiga.
A baya Mista Hong ya kasance mataimakin babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta China. Ya kuma taba zama na hannun daman mataimakin shugaban kasar, Wang Qishan.
Sai dai ba kasafai akan tuhumi jami'ai makusantan shugabannin China da laifukan rashawa ba.
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matan aure a Zaria
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu matan aure uku da namiji guda mazaunin Zango a karamar hukumar Sabon Gari ta Kaduna.
Yankin Zango kusa ya ke da jami'ar Ahmadu Bello na Zaria.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan bindigar sun dirar wa garin ne da tsakiyar daren Alhamis, suna harbi kan mai uwa dawabi.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki bayan ƴan bindiga sun kai hari makarantar sojoji ta NDA, tare da kashe sojoji biyu da garkuwa da wani manjo.
Kakakin ƴan sandan Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da harin sannan ya ce suna bincike.
An kama tsohon minista da laifin cin hanci
An kama wani tsohon firaminista kuma ministan tsaron kasar Mali bayan da aka tuhume shi da laifin cin hanci da rashawa kan wata badakalar sayen jirgin saman shugaban kasar, yayin da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ke mulkin kasar.
Ana dai ganin Soumeylou Boubeye Maiga a matsayin wanda zai tsaya takarar mukamin shugaban kasa a zaben da ke tafe shekara mai zuwa.
An sayo jirgin ne a shekarar dubu biyu da goma sha hudu kan dala miliyan 40, wanda yawancin mutanen kasar suka ce akwai ayar tambaya kan sahihancin cinikin.
Wannan badakalar ta zubar da mutuncin tsohon Shugaba Keita, wanda daga baya sojojin kasar suka hambarar da shi daga mulki a watan Agustar bara.
Ronaldo zai koma Manchester United da taka leda
Manchester United ta ce ta cimma matsaya da Juventus domin sayen dan kwallon Portugal Cristiano Ronaldo.
A wani saƙo da Manchester United ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce "maraba da zuwa gida Ronaldo," wadda wannan alama ce da ke nuna cewa Ronaldo zai koma kulob ɗin
United ta ce kammala cinikin ɗan wasan da ya lashe Ballon d'Or sau biyar ya ta'allaƙa ne da batun abin ɗan wasan yake so da kuma batun samun biza da kuma lafiyarsa.
Ronaldo ya ci ƙwallo 118 a wasanni 292 da ya buga a lokacin da yake Old Trafford kafin daga baya ya koma Real Madrid.
Ana zargin jirgin saman soji da buɗe wa jirgin ruwan farar hula wuta a Ribas
Ƴan sandan ruwa a garin Bonny na jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Najeriya sun soma bincike kan zargin da ake yi wa wani jirgin soji na buɗe wuta ga wani jirgin ruwan ɗaukar kayayyaki.
Rahotanni sun ce jirgin na ɗauke da kayan abinci da sauran abubuwa inda yake hanyarsa ta zuwa garin Bonny daga tashar ruwa ta Nembe-Bille da ke Fatakwal.
Awwal Rufai, wanda ke cikin jirgin ruwan a lokacin da lamarin ya faru ya shaida cewa lamarin ya faru ne a tsibirin Dutch da ke Okrika kuma har an harbe mutum biyu, cikin waɗanda aka harba har da Awwal ɗin.
"Ni a ɗan yatsa harsashin ya same ni sai dai ɗayan mutumin a ƙwabri harsashin ya same shi.
"Sauran yaran da ke cikin jirgin sun yi tsalle sun faɗa ruwa."
Jami'in ɗan sandan da ke kula da yankin ruwan Bonny, SP Solomon Adeniyi ya shaida wa BBC cewa sun samu rahoto kan wannan lamarin kuma tuni suka fara bincike.
Yadda matafiya suka shafe dare cikin cunkoson ababen hawa a Nairobi
Dubban matafiya ne suka maƙale cikin cunkoson ababen hawa a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya inda suka shafe sama da sa'o'i takwas a cikin cunkoson.
Rahotanni sun ce cunkushewar hanyar ta samo asali ne sakamakon faɗaɗa wata babbar hanya da wani kamfanin China ke yi.
Ma'aikatan da ke aikin ne suka rufe wasu bangarori na hanyar tare da yin rami a gaban hanyoyin da suke gyara domin hana matafiya bin hanyar.
Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun ta wallafa hotuna da bidiyo kan yadda mutane ke ta mita da ƙorafi kan irin halin da suka shiga inda wasu ke cewa sun bar wurin aiki tun shida na yamma amma ba su koma gida ba sai huɗu na asuba.
Wani da ya wallafa saƙo a shafin Twitter ya bayyana cewa akwai wasu da ke dauke da jarirai haka kuma akwai masu yawon buɗe ido da jirgi ya tafi ya bar su.
Cristiano Ronaldo: Man Utd na gab da sayen dan kwallon Juventus
Manchester United ta yi nisa a tattaunawa domin sayen dan kwallon Portugal Cristiano Ronaldo daga Juventus.
BBC ta gano cewa dan wasan mai shekaru 36 ba zai koma Manchester City ba.
Kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya tabbatar da cewa Ronaldo ya ce "bai da niyyar ci gaba da murza leda" tare da Juve.
Ronaldo ya kulla yarjejeniya da Manchester United daga Sporting Lisbon a kan fiye da fan miliyan 12 a shekara ta 2003 inda ya zura kwallo 118 cikin wasa 292 a kulob din.
Taliban na son Turkiyya ta ci gaba da kula da filin jirgin Kabul
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Taliban ta nemi Turkiyya ta ci gaba da kula da filin jirgin Kabul amma har yanzu babu wani mataki da aka dauka.
Kafin ya bar Bosnia, kafin ya bar filin jirgin sama na Istanbul , "Taliban ta bukaci mu ci gaba da gunar da filin jirgin Kabul. Sai dai ba mu dauki matakin komai ba kan wannan batu har ya zuwa yanzu."
"Za mu bayyana matsayarmu ne kawai bayan an samu daidaituwar gwamnati a kasar," in ji shi.
Erdogan yana nufin wani taro da zai yi na sama da awa uku da za a yi da wakilan Turkiyya da na Taliban a ofishin jakadancin Turkiyya a Kabul.
Sai dai bai bayyana takamaimai yaushe ne za a yi wannan tattaunawar ba amma ya ce "za a kara irin wannan tattaunawar a gaba idan da bukatar hakan".
Shugaba Erdogan ya ce za a ci gaba da kwashe dakarun Turkiyya daga Kabul wanda aka soma a ranar Laraba.
Ya kuma yi Allah wadai da harin da aka kai a ranar Alhamis.
An kama wani jami'in China mai yaki da cin hanci da rashawa da zargin karbar na goro
Wani babban jami'in gwamnatin China da a baya ke jagorantar yaki da cin hanci da rashawa - shi ma an kama shi da laifin karbar cin hanci.
Dong Hong ya gaya wa kotun da ta yi ma sa shari'a cewa ya karbi cin hancin sama da dalar Amurka miliyan saba'in ciin shekara ashirin da su ka gabata.
An kuma tuhume shi da gudanar da rayuwar da ta fi karfin kudaden da yake samu, inda aka same shi yana ziyartar kulob-kulob din da sai hamshakan masu hali ke iya shiga.
A baya Mista Hong ya kasance mataimakin babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta China.
Ya kuma taba zama na hannun daman mataimakin shugaban kasar, Wang Qishan.
Sai dai ba kasafai akan tuhumi jami'ai makusantan shugabannin China da laifukan rashawa ba.
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Rabi'u Rijiyar Lemu
Video content
An kama tsohon Ministan noman rani na Malawi
An kama tsohon ministan ƙasar Malawi bisa zarginsa da biyan kuɗin otel da kuɗin ƙasa.
Ana zargin Charles Mchacha, wanda shi ne ministan noman rani a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Peter Mutharika, da amfani da kuɗin ma'aikatarsa wajen biyan wani katafaren ɗaki a wani otel da ke Blantyre na Scotland bayan bikinsa inda a otel ɗin ne ya je hutu da amaryarsa.
Wata jarida ta Malawi ta wallafa labarin wasu manyan jami'an gwamnatin biyu a shafin Twitter wadanda hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar ACB ta ce za ta gurfanar da duka mutum ukun a gaban kotu bisa zargin sata da ƙin mayar da hankali wurin aiki.
Sai dai duka mutum ukun sun musanta zarge-zargen.
Su wanene suka hana El-Zakzaky tafiya neman magani?
Kimanin makonni hudu da wata babbar kotun Kaduna ta bayar da belin shugaban kungiyar harka Islamiyya a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, da matarsa Malama Zeenah Ibrahim, sai dai har yanzu sun gaza fita kasashen waje neman magani saboda an jami’an tsaro sun rike fasfo dinsu.
Cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar Ibrahim Musa ya fitar ta ce ba dai a san fasfo din ko yana hannun wacce hukuma ba, hukumar leke asiri ta NIA da ta fararen kaya DSS duka sun ce ba su rike da fasfo din mutanen biyu.
Sanarwar ta kara da cewa abin da ya bayyana shi ne lokacin da babbar Kotun Kaduna ta yarje wa shugaban da matarsa fita neman magani Indiya a baya, jami’an tsaro sun karbe takardun shaidar tafiyarsu.
Wa aka bai wa takardun? Wannan tambayar da kyar za ta samu amsa ganin cewa an dauki lokaci da faruwar abin tun 2018.
Sai dai mabiya na tambayar ko wani babban mai mukami ne ke neman amfani da wannan damar ya kara yi masu daurin talala a cikin kasar, a cewar sanarwar Ibrahim Musa mutane da dama na harsashen haka.