Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. A nan za mu dakatar da kawo labarai, sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

 2. Darajar Naira ta ƙara faɗuwa

  Naira

  Darajar kuɗin Najeriya naira ta ƙara faɗuwa a kasuwar bayan fage a Najeriya a ranar Litinin.

  Ƴan kasuwar bayan fage sun ce ana canza kowacce dala ɗaya ta Amurka kan N532.

  Sun bayyana cewa darajar naira ta ƙara faɗuwa ne saboda ƙarancin dala a kasuwa.

  Tun a watan Yuli darajar naira ke faɗuwa a kasuwar bayan fage a Najeriya, sakamakon sabbin matakan da baban bankin ya ɗauka kan kasuwar canji.

 3. Yadda Taliban ta kafa tuta a yanki na ƙarshe da ta ƙwace a Afghanistan

  Mayakan Taliban

  Kungiyar Taliban ta ce a yanzu ita ke iko da dukkan lardunan kasar Afghanistan bayan da ta kwace lardin Panjshir.

  An wallafa wasu hotunan bidiyo a intanet da ke nuna mayakan Taliban na kafa tutarsu a wajen ofishin gwamnan lardin.

  Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya shaida wa manema labarai a Kabul cewa babu wanda za a muzguna wa a Panjshir.

  Wani mazaunin Kabul dan asalin Kwarin Panjshir wanda ya ce 'yan uwansu na fargabar abin da zai biyo bayan kwace yankin ya ce ƴan Taliban na magana magana ne kawai kan nasarar da suka samu da daga tutarsu, amma ba su cewa komi kan ɓarnar da suka yi wa Panjshir da al'ummarta.

  Har zuwa wannan lokaci babu wanda ya san inda Ahmad Massoud, wanda shi ne jagoran masu yi wa Taliban turjiya ya shiga, sai dai dazu ya aika da wani sako na sauti yana musanta nasarar da Taliban ke ikirarin samu.

 4. Fursunoni Falasdinawa sun tsere daga gidan yarin Isra’ila ta hanyar haƙa rami

  Gidan yarin Gilboa cikin gidajen yari mafi tsaro a Isra'ila
  Image caption: Gidan yarin Gilboa cikin gidajen yari mafi tsaro a Isra'ila

  Hukumomin Isra'ila sun shiga farautar wasu fursunoni Falasdinawa su shida wadanda suka tsere daga ɗaya daga cikin gidajen yari mafi tsaro na kasar.

  Hotunan bidiyo da aka samo daga cikin gidan yarin Gilboa ya nuna ƙofar wani rami da fursunonin suka haƙa a cikin wani makewayi, wanda ɗaya kofarsa ta ke wajen gidan yarin, a karkashin wani ginin da masu gadi ke zama.

  Jami’ai sun ce manoma ne suka ankarar da su lokacin da fursunonin ke gudu a gona.

  Cikin fursunonin da suka tsere akwai Zakariya Zubeidi - wani tsohon kwamandan kungiyar Al-Aqsa Brigade da kuma mambobin ƙungiyar masu da’awar jihadi ta Islamic Jihad guda biyar.

  Firaministan Isra'ila Naftali Bennett ya ce ya ɗauki lamarin da matukar muhimmanci, inda mayaƙan Falasdinawa kuwa ke cewa abin da fursunonin suka yi abin yabo ne.

  Tserewar fursunonin wani al’amari ne da ke nuna rauni a tsaron gidajen yarin Isra’ila.

  Ramin da fursunonin suka haƙa suka tsere
  Image caption: Ramin da fursunonin suka haƙa suka tsere
 5. Iyalan mamatan jirgin Malaysia sun ba da bahasi a kotu

  'Yan uwan fasinjoji dari biyu da casa'in da suka halaka a wani harin roka mai linzami da aka kai kan wani jirgin saman Malaysia sun sanar da wata kotu a kasar Holland irin mawuyacin halin da su ke ciki.

  Yawancin fasinjojin da ke cikin jirgin mai lamba MH-Seventen da ya tashi daga Amsterdam za shi Kuala Lumpur sun kasance 'yan kasar Holland ne.

  An gurfanar da wasu Rashawa uku da wani ɗan tawaye ɗan kasar Ukraine amma a bayan idonsu.

  Ana tuhumarsu da harbo jirgin yayin da yake bi ta sararin samaniyar kasar Ukraine wanda a lokacin yankin na karkashin ikon 'yan tawaye ne cikin shekarar dubu biyu da goma sha hudu.

  Rasha ta musanta cewa ita ce ta samar da makamin da aka harbo jirgin da shi.

 6. Hasashe ya nuna za a tafka ruwan sama da iska da ambaliya a ƙasashen yammacin Afirka

  Hasashen yanayi ya nuna matsalar da ba a saba gani ba ta ruwan sama da iska na iya faɗaɗa yayin da yanayin ke tunkarar yammacin Afirka da zai haifar da wasu munanan sakamako.

  Hasashen ya nuna za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a wasu ƙasashen na yammacin Afirka.

  Hasashen ya nuna za a maka ruwan saman ne a yankin Chadi da arewacin Najeriya da Burkina Faso da kuma wasu yankuna na Mali.

  Za a maka ruwan sama mai tafe da iska da tsawa a arewacin Najeriya a ranar Talata, kamar yadda hasashen yanayin ya nuna.

  Matsalar za ta kuma zafi yankunan Senegal da Mauritania zuwa ƙarshen mako.

  Hasashen ya ce ruwan saman zai haifar da mummunan yanayi na ambaliya a yankunan na yammacin Afirka.

  Hasashen yanayi
 7. Za a yi wa maza miliyan ɗaya da rabi kaciya a Sudan ta Kudu

  Kaciya a Sudan

  An kaddamar da wani aikin yi wa mazajen Sudan ta Kudu miliyan ɗaya da rabi kaciya.

  Shirin kaciyar ya shafi ƴan shekaru daga 15 zuwa 49 a ƙasar a wani mataki na rage yaɗuwar cutar HIV da ta yi bazu a ƙasar.

  Bincike ya nuna mazan da aka yi wa kaciya ba su kai waɗanda ba su da kaciya haɗarin kamuwa da HIV ba, idan har suka sadu da wanda ke ɗauke da cutar.

  Wata ƙungiyar sa-kai ta Human Appeal Associates tare da haɗin gwiwar ma'aikatar lafiya, na neman waɗanda za su gabatar da kansu nan da shekara biyar.

  A yankuna uku kawai ake yi wa maza kaciya cikin yankuna 10 na Sudan ta Kudu, inda wasu yankunan haramun ne yin kaciya.

  Gwamnati ta bayyana rashin yin kaciya a matsayin wata babbar damuwa idan ana maganar yaɗuwar cutar HIV.

  "Buƙatar kaciyar a babban birnin ƙasar Juba, kaɗai na da matuƙar gima," kamar yadda Robert Matthew Uku na Human Appeal Associates ya shaida wa BBC.

  "Kusan maza 100 - da suka hada da manya 25 aka yi wa kaciya a ƙarshen mako"

  Kusan kashi 2.3 na ƴan shekara daga 15 zuwa 49 a Sudan ta Kudu ana tunanin suna ɗauke da HIV, in ji UNAids

 8. Sojojin da suka yi juyin mulki sun ce za su kafa sabuwar gwamnati a Guinea

  A kasar Guinea, jagoran sojojin da suka hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde, ya sanar da cewa za su kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya cikin makonni masu zuwa.

  Laftanal kanar Mamady Doumbouya ya shaida wa mambobin tsohuwar gwamnatin cewa ba za a muzgunawa kowa ba.

  Sai dai ya shaida wa ministocin gwamnatin cewa ba za a barsu su fita daga kasar ba, kuma ya bukaci su mika motocin gwamnati da ke hannayensu ga sojojin kasar.

  Shugaba Alpha Conde mai shekara 83, wanda sojojin ke tsare da shi a yanzu - a bara ya tsawaita mulkinsa inda ya so ya jagoranci kasar a karo na uku.

  Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

  Guinea
  Image caption: Kanal Mamady Doumbouya an bayyana cewa shi ya jagoranci hambarar da Alpha Conde
 9. Hotunan yadda INEC ta gana da jam'iyyun siyasa

  Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gana da jam'iyyun siyasa hedikwatar hukumar da ke Abuja.

  INEC
  INEC
  INEC
  INEC
  INEC
  INEC
 10. NCC ta karyata katse layukan wayoyin sadarwa a Katsina

  k

  Hukumar sadarwa ta NCC a Najeriya ta karyata rahotanni da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa ta katse layukan wayoyin sadarwa a jihar Katsina.

  Shugaban hukumar a wata sanarwa da ya fitar, Farfesa Umar D. Danbatta wanda ya zanta da gwamnatin jihar ya ce labaran boge ake yaɗawa.

  NCC ya ce sanarwar da aka fitar kan Zamfara shi ne mutane suka jirkita ta da alakanta sanarwar da Katsina.

  Tun a sanyin safiyar yau sanarwar ke ta yawo a shafukan sada zumunta cewa an toshe layukan sadarwa a Katsina da jihohi makwabta.

 11. Zaɓen kananan hukumomi ya bar baya da kura a Kaduna

  EL RUFAI

  Bisa ga dukkan alamu zabubbukan kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Kaduna a karshen mako sun bar baya da kura.

  Yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke nuna ta-ba-ba kan sahihancin zabubbukan, a nata ɓangaren jam’iyyar APC mai mulki jinjina ta yi ga gwamnati da hukumar zaɓe kan yadda zabubbukan suka guduna.

  A saurari rahoton Yusuf Tijjani kan halin da ake ciki

  Video content

  Video caption: Rahoto kan halin da ake ciki bayan zaɓen kananan hukumomi a Kaduna
 12. An kama 'yan wasan Argentina kan karya dokokin korona

  Argentina

  Yan sanda da hukumomin lafiya a Brazil sun dakatar da wasan share fage na cin kofin duniya da kasar ke bugawa da Argentina, da nufin kama wasu yan wasan Argentina hudu da suka saba dokar kullen Korona.

  Yan wasan sun hada da Lo Celso da Romero da Martinez da Buendia da dukansu ke wasa a Ingila.

  An zarge su da kin killace kansu duk da cewa sun fito daga yankin kasashen da Brazil ta ayyana mafiya hadarin kamuwa da cutar Korona nau'in Delta.

  Hukumomin sun kutsa kai filin jim kadan bayan fara wasa, suka kuma bukaci a basu yan wasan su wuce dasu.

  Sai dai hakan ya haifar da sa-in-sa, wadda tasa duka yan wasan Argentina suka yanke shawarar ficewa daga filin.

  Rahotanni na cewa sun nuna cewa 'yan wasan ba su fadi cewa suna Ingila ba kasa da mako biyu da suka wuce, wanda kuma hakan ya saba wa dokokin killace kai na Brazil.

 13. Bayani kan Guinea Conakry

  Guinea Conakry
 14. MDD ta ce dole Taliban ta kare hakkin mata a Afghanista

  Shugaban Hukumar samar da kayan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffith ya ce dole ne Taliban ta kare hakkin mata da tsiraru a Afghanistan.

  Yayin ziyara a Kabul, Mr Griffiths ya gana da Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda daya ne daga jagororin kungiyar.

  Rahotanni na cewa Martin Griffiths ya bai wa Taliban tabbacin cewa za su aike da kayan agaji ba tare da nuna bambanci ba, inda su kuma suka yi masa alkawarin kare ma'aikatan agajin.

  Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutun miliyan goma sha takwas ne ke fuskantar matsin rayuwa a Afghanistan.

 15. An rufe makarantun kwana a Adamawa saboda tsaro

  Fintiri

  Gwamnatin Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta rufe makarantun kwana 30 cikin 34 da ke fadin jihar saboda matsaloli na tsaro.

  Sanarwar da kwamishiniyar Lafiya, Mrs Wilbina Jackson ta fitar na cewa an rufe makarantun daga yau Litinin har sai baba ta gani.

  A cewar sanarwar an ɗauki wannan mataki ne la'akari da taɓarɓarewa lamuran tsaro musamman na ɗalibai a makarantu.

  Adamawa na daga cikin jihohohin da ke fuskantar barazana daga hare-haren 'yan bindiga.

 16. Zulum ya kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Borno da Bankin kasashen Larabawa

  Borno

  Gwamnan Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya kulla hulɗar kasuwanci tsakanin Bankin ƙasashen Larabawa kan raya tattalin arzikin Afirka, (BADEA) da ke Khartoum, babban kasar Sudan.

  Yarjejeniyar ta ƙunshi fitar da alkama da ƙaro da manomar Borno ke samarwa.

  Jihar Borno ce kan gaba wajen noman alkama da ƙaro a Najeriya.

  Gwamna Zulum ya bayyana irin kalubalen da Borno ke fuskanta saboda hare-hare mayaƙan Boko Haram da suka durkusar da tattalin arziki da fannin noma don haka wannan hanya ce da za ta sake farfaɗo da ƙasar.

  Zulum ya ziyarci birnin Sudan tare da rakiyar tsohon karamin minista a ma'aikatar noma, Bukar Tijjani da wasu masu ruwa da tsaki da gwanacewa a fanin cinikayya da noma.

  Bankin ya ce zai bayar da cikakken hadin-kai ga gwamnatin Borno wajen ganin alakarta su ta samar da ci gaba.

  Borno
  BORNO
  BORNO
  BORNO
 17. An yi garkuwa da amaryar da ake shirin soma bikinta a Katsina

  Yan bindiga

  Rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.

  An sace Asama'u Dalhatu ana tsaka da shirye-shiryen soma bikinta, a cewar ɗan majalisar.

  Ƴan bindigar sun kai hari ne kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskarin Katsina tare da sace Amaryar.

  A lokacin tabbatar da faruwar lamarin, ɗan majalisar ya shaida wa jaridar Daily Trust cew an sace kanwar tasa da sanyin safiyar Lahadin.

  Ya kara da cewa har yanzu 'yan bindigar ba su tuntube su ba domin neman kudin fansa.

 18. Rikicin jam'iyyar APC na sake tsanani kan zaɓen kananan hukumomi

  MAI MALA BUNI

  Rikici na ci gaba da ruruwa a tsakanin ƴaƴan jam’iyyar APC a wasu daga cikin jihohin Najeriya, biyo bayan yadda ake samun ɓullar shugabanci biyu a zaɓen shugabancin jam’iyyar da aka gudanar a Asabar din karshen makon nan.

  Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar na cewa ba a yi zaɓen ba, yayin da shugabancin riƙo da ke jihohin ke cewa masalaha aka yi, kamar yadda uwar jam’iyyar ta bukaci a yi.

  A Kano Khalifa Shehu Dokaji ya duba yadda zaɓen ya gudana a jihar da ma wasu jihohin Najeriya, ana iya sauraron rahotonsa.

  Video content

  Video caption: Rahoto kan rikicin Jam'iyyar APC
 19. Amurka ta yi alla-wadai da kifar da gwamnatin Guinea

  Amurka ta yi alla-wadai da juyin-mulkin sojoji a Guniea, tana mai kira ga sojoji kar su haddasa rikici a ƙasar.

  Ma'aikatar tsaron Amurka tana mai cewa rikici da wuce iyaka wajen aiwatar da dokokin kuɗin tsarin mulki za su sake dilmiyar da ƙasar da haifar da barazana ga zaman lafiyarta da 'yanci dimokuraɗiya.

  Wannan na zuwa ne yayinda ƙasashen duniya da makwabtan ƙasar ke alla-wadai da kifar da shugaba Alpha Conde.

  Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS, sun yi tir da juyin-mulkin da jaddada rashin amincewarsu da duk wani yunkurin sauyi a kuɗin tsarin mulki.

  Ta kuma bukaci a mutunta shugaba Conde da gaggauta sakinsa da sauran mukarabansa da yanzu haka ke hannun sojoji.

  Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres da Tarayyar Afirka sun nuna rashin dadinsu da umartar gaggauta sakin shugaba Conde.

  Har yanzu dai babu wani karin haske kan makomar shugaban yayinda wani faifai bidiyon da ake yaɗawa ke nuna sojoji zagaye da shugaban.

 20. Wane ne sojan da ya jagoranci ƙwace mulki a Guinea?

  Guinea

  Wani juyin mulkin soji a kasar Guinea ya kawo karshen mulkin Shugaba Alpha Conde mai cike da ce-ce -ku-ce, kasa da shekara guda bayan da ya lashe zabe a wa'adi na uku wanda ya yi sanadiyyar haifar da mummunanr zanga -zanga da zubar da jini a kasar ta Yammacin Afirka.

  Dakarun runduna ta musamman a kasar da ake kira (GFS) ne suka tsare Conde, mai shekaru 83, a ranar 5 ga Satumba, sa'o'i bayan da aka samu rahoton harbe -harbe a kusa da fadar shugaban kasa a Conakry.

  Kwamandan GFS Kanar Mahamady Doumbouya ya tabbatar da karbe mulkin a gidan Talabijin na kasar kuma ya yi alkawarin sa ido kan sauyi cikin lumana.

  Kanal Doumbouya, wanda rahotanni suka ce ya samu horon soji mai yawa a Faransa, ga dukkan alamu shi ne jagoran tawagar juyin mulkin da aka yi wa lakabi da National Rally and Development Committee (CNRD).

  Kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta Yammacin Afirka Ecowas, da Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin kuma ana sa ran za su matsa lamba ga gwamnatin mai ci ta mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya ta farar hula.

  Da alama jagororin juyin mulkin sun samu kwarin guiwa ne daga ganin irin yadda hakan ta faru a makwabtan Guinea, wato Mali da kuma Chadi, kuma ana danganta hakan da raunin martani ga irin wannan lamari a wadannan kasashe.

  Shiga nan domin karanta cikakken Tarihin