Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Imam Saleh da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Da haka muke bankwana da ku, sai kuma gobe Laraba da yardar Allah. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.

 2. Ana tuhumar firaministan Haiti kan mutuwar tsohon shugaba Jovenel Moise

  Haiti

  Wani mai shigar da kara a Haiti ya gabatar da wata kara wadda a ciki ya ke tuhumar firaministan ƙasar Ariel Henry da hannu cikin kisan gillar da aka yi wa shugaban ƙasar Jovenel Moise a watan Yuli.

  Wannan matakin ya biyo bayan matakin da babban mai shigar da kara na ƙasar Bedford Claude ya dauka na neman Mista Henry ya bayyana alakarsa da mutumin da ake tuhuma da bayar da umarnin kashe shugaban ƙasar.

  Ya ce bayanan da wani bincike ya bankaɗo sun tabbatar cewa mutanen biyu sun tattauna da juna har sau biyu jim kadan bayan an kashe Mista Moise.

  Mutuwarsa a gidansa da ke wajen birnin Port-au-Prince ya haifar da wata matsalar siyasa wadda gagarumar girgizar ƙasar da aka yi a watan jiya ya kara dagula lamurra a Haiti.

  A dalilan wannan karar an hana Mista Henry barin kasar.

 3. Labarai da dumi-dumiAn yi garkuwa da Sarkin Bungudu

  Rahotanni da ke shigo mana na tabbatar da cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Bungudu na Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da yammacin yau Talata.

 4. WHO ta ce nahiyar Afirka ta fuskanci koma baya a karɓan rigakafin korona

  WHO

  Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta gargadi cewa an bar Afirka a baya wajen karbar rigakafin annobar korona.

  A lokacin wani jawabi ga manema labarai, Dr Tedros Adganom Ghebreyesus ya ce ƙasashen Afirka biyu kaɗai ne suka cimma kashi 40 cikin 100 na al'ummar da WHO ke fatan ganin an yi wa rigakafi zuwa karshen 2021.

  Ya ce wannan adadi shi ne mafi kankanta ga kowanne yanki.

  Dr Tedros ya ce sama da allura biliyan 5.7 aka fitar a duniya, sai dai kashi 2 cikin 100 na wannan adadin nahiyar Afirka ta samu.

  Ya yi gargadi cewa idan ba a kasafta rigakafin yada ya dace ba annobar za ta sake dawo wa.

 5. Taliban ta ce Amurka na siyasantar da batun samar da agaji

  m

  Ministan harkokin waje na Afghanistan wanda kungiyar Taliban ta nada, Amir Khan Mottaqi, ya yi kira ga Amurka da sauran kasashe da su daina mayar da batun samar da agaji ya koma na siyasa.

  Ya ce Amurka babar kasa ce, kuma ya dace ta zama mai tausayawa.

  A wani jawabi da ya gabatar a talabijin, ministan ya gode wa kasashen duniya da su ka yi alkawarin tara fiye da dala biliyan guda domin tallafa wa kasarsa.

  Mista Mottaqi ya kuma ce sabuwar gwamnatin Afghanistan za ta yi duka mai yiwuwa domin taimaka wa 'yan kasar da ke cikin mawuyacin hali ba tare da nuna bambanci ba.

  A halin da ake ciki an kiyasta cewa akwai kimanin 'yan Afghanistan miliyan uku da rabi da aka raba da muhallansu a cikin kasar.

 6. 'Yan bindiga sun hallaka jami'in soja da garkuwa da matar aure da ƴaƴanta a Zaria

  Zaria

  'Yan bindiga sun hallaka soja da garkuwa da matar aure da ƴaƴanta biyu a kusa da asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke shika a Zaria.

  Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami'in soja ya mutu a wani asibiti da ba a ambato suna ba sakamakon raunin da ya samu a lokacin musayar wuta da 'yan bindiga.

  Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na yammacin Litinin.

  A cewar wata majiya maharan su kusan 30, sun yi ta harbe-harbe lokacin harin a yankin.

  Babu dai wani bayanai da aka samu kan ko an yi nasarar kashe daga cikin 'yan bindigar kawo yanzu.

 7. Gwamnatin Legas ta kaddamar da ayyukan kakkabe mabarata da gajiyayyu mazauna gindin gada

  Gwamnatin jihar Legas ta ce ta fara ayyukan ceto "don duba kasuwanni, gine -ginen da ba a kammala ba da karkashin gadoji domin kakkabe mabarata da sauran gajiyayyu da ke zaune a wuraren da basu dace ba.

  To sai dai mabarata a wani taron manema labarai a karkashin sarkin makafin jihar Legas sun bayyana cewa wannan ceto na gwamnatin jihar Legas, a matsayin wani mataki na cin mutuncinsu da kuma jefa rayuwarsu da ta iyalansu cikin wani yanayi na tsaka mai wuya.

  A saurari rahoton wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman kan dambarwar.

  Video content

  Video caption: Rahoto kan kaddamar da ayyukan kakkabe mabarata da gajiyayyu mazauna gindin gada a Legas
 8. Iran ta aika wa Lebanon tallafin man fetur saboda fama da rashinsa

  Matsalar mai a Lebanon

  Ana sauke dubban ton-ton na man fetur a Syria daga cikin wata tankar dakon man da aka yo dakonsa daga Iran, gabanin a kai shi Lebanon.

  Wannan ne kashi na farko na jerin tankokin man fetur da kungiyar Hezbollah ta shirya shigar da shi Lebanon - wadda ke fuskantar karancin man fetur irin wanda ba ta taba fuskanta ba a tarihinta.

  Ana shigar da man ne ta Syria domin kauce wa jefa Lebanon cikin rikicin takunkumin karya tattalin arziki da Amurka ta kakaba wa Iran.

  Kungiyar Hezbollah ta ce da zarar man ya isa kasar, za a fifita asibitoci da gidajen marayu wajen raba shi ga al'umomin kasar.

 9. Masu neman ɓallewa daga Najeriya na zanga-zanga a hedikwatar MDD a New York

  Nigeria

  Masu fafutikar neman ɓallewa daga Najeriya da wasu ƙungiyoyin adawa na zanga-zanga a gaban hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York.

  Shugaban ƙungiyar 'yan Najeriya masu neman ballewar mazauna Turai, Farfesa Banji Akintoye ya shaida cewa za a gudanar da wannan tattaki tsakanin 14 zuwa 24 ga watan Satumban, 2021 a hedikwatar MDD da ke birnin New York na Amurka.

  Akintoye ya ce masu zanga-zangar na son nunawa duniya irin kisan da makiyaya ke aikatawa da suna kiwo a kudanci da tsakiyar Najeriya.

  Ya kuma shaida cewa mutane a kudanci da tsakiyar Najeriya na son ankarar da duniya irin ketta hakkin da ake aikatawa, tauye 'yanci fadin albarkacin baki, da sauran ayyukan da ake zargin gwamnatin Buhari da nuna sakaci.

 10. Sojojin da suka kifar da gwamnatin Guinea sun fara tattaunawa da farar hula

  Sojojin da suka hambarar da gwamnatin Guinea

  Sojojin da su ka hambarar da gwamnatin kasar Guinea sun fara tattauna wa da wakilan jam'iyyun siyasar kasar.

  Jagororin masu juyin mulin sun ce tattaunawar ta kwana hudu za ta mayarda hankali kan makomar kasar ne wanda zai samar da jadawalin mayar da kasar bisa tafarkin mulkin farar hula.

  Cikin 'yan siyasar da ake tattaunawar da su akwai Cellou Dalein Diallo - jagoran babbar jam'iyyar adawa ta kasar - da kuma jami'ai na jam'iyyar hambararren shugaban kasar Alpha Conde.

  Sojojin sun ce za su tattauna da malaman addinai da wakilan 'yan kasuwa da 'yan kwadago da kuma kungiyoyin fararen hula.

 11. Buhari ya ce ƴan Najeriya miliyan 8 ke amfana da tallafinsa

  Shugaba Buhari

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gidaje miliyan 1.6 da ƴan Najeriya miliyan takwas ne ke amfana da tallafin kudi da gwamnatinsa ke bayarwa domin rage raɗaɗin talauci.

  Cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar a ranar Talata, Buhari ya ce ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na rage talauci a Najeriya na ci gaba da bunƙasa.

  Sanarwar ta ce Buhari ya faɗi haka ne a bikin buɗe taron shekara-shekara na harakokin banki da kuɗi na cibiyar horar da ma’aikatan banki ta Najeriya.

  A cikin jawabinsa a cewar sanarwar, shugaban ya ce rajistar talakawa da aka yi da marasa galihu ta ƙunshi mutum miliyan 32.6 daga gidaje miliyan 7 na masu ƙaramin ƙarfi.

  Ya kuma roƙi bankuna su taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwarsu.

 12. Taliban na son ƴan kasar da suka gudu saboda tsoron mulkinta su koma gida

  Taliban

  Ministan harkokin waje na Afghanistan Amir Khan Mottaki - wanda kungiyar Taliban ta nada a makon jiya - ya shaida wa shugaban hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi cewa ya kamata a karfafa wa wadanda suka tsere daga Afghanistan gwiwa su koma gida.

  Wakiliyar BBC ta ce jawabin na ministan ya tabo batun mayar da 'yan kasar miliyan daya da rabi wadanda rikicin kasar ya raba da muhallansu zuwa gidajensu gabanin shigowar hunturu.

  Wadannan kalaman na zuwa ne yayin da jami'an Majalisar Dinkin Duniya ke gargadin cewa har yanzu masu son ficewa daga kasar sai karuwa su ke yi.

  A jiya Litinin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa kasashe sun yi alkawurran tara fiye da dala biliyan daya domin tallafa wa kasar ta Afghanisan.

 13. Daular Larabawa na neman wasu ƴan Najeriya ruwa a jallo

  Sarkin UAE

  Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ayyana neman wasu 'yan Najeriya shida ruwa a jallo, saboda zargin aikata ta'addanci.

  Kafar yada labaran kasar ta Al Arabiya ta ce "Wannan shawarar, ta zo cikin wani sabon tsarin Hadaddiyar Daular Larabawa na yaki da harkokin ta'addanci a kasar.

  Baya ga 'yan Najeriyar akwai kuma wasu 'yan Daular Larabawar hudu da ake nema, da yan Lebanon biyu, da Yamalawa 8, da 'yan Siriya biyar.

  Akwai kuma wasu Iraniyawa biyar, da 'yan Iraki biyu, da mutum dai-dai daga ƙasashen Afghanistan da Indiya.

 14. Shugaba Buhari na son majalisa ta bashi dama ya ranto bashin kusan Triliyan 2

  Muhammadu Buhari

  Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya buƙaci majalisar dokokin ƙasar ta bashi dama ya ranto Naira 1,668, 417, 229, 124.5, wato Naira Triliyan daya da biliyan dari shida da sittin da takwas da miliyan dari hudu da goma sha bakwai da motsi.

  Jaridar Premium Times ta rawaito cewa shugaban ya ce za a yi amfani da kudin ne domin aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2021.

  Cikin wata wasika da shugaban ya aika wa majalisar dokokin kasar, ya ce bashin wani bangare ne na shirin yin rance, da aka tsara tun shekarar 2018 zuwa 2020.

  Ya ƙara da cewa ciyo bashin ya zama dole, domin cimma burin aiwatar da wasu ayyuka da za su amfani jama'ar kasar.

 15. Ambaliya ta kashe mutane 80 a Sudan

  Ambaliya
  Image caption: Ambaliya

  Fiye da mutane 80 sun rasa rayukansu, tun bayan fara damuna a watan Yuli a Sudan.

  Mai magana da yawun hukumar kare fararen hula ta kasar ya ce fiye da mutane 67 sun samu raunuka.

  Ambaliyar dai ta shafi larduna 14 cikin 18 na kasar, yayin da ta rusa gidaje dubu 30.

  Gonaki da dama da gine-ginen gwamnati sun lalace.

  Majalisar Dinkin Duniya ta ce ambaliyar ta shafi aƙalla mutane dubu dari da biyu a dukkan sassan ƙasar.

  A bara ne hukumomi a Sudan suka ayyana dokar ta ɓaci ta tsawon wata uku saboda ambaliyar da ta hallaka mutane 100 a shekarar.

 16. Hotunan yadda ambaliya ta lalata gidaje a Abuja

  Wasu gidaje da suka rushe kenan
  Image caption: Wasu gidaje da suka rushe kenan

  Ambaliya ta lalata gidaje da dama a rukunin gidaje na Trademoore da ke unguwar Lugbe, a babban birin Najeriya Abuja.

  Lamarin ya auku ne shekaranjiya litinin, kana mutum uku sun rasa rayukansu.

  Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar reshen birnin Abuja NEMA, ta ce motoci da dama sun lalace, yayin da gwamman gidaje suka rushe.

  Mutane sun yi cirko-cirko suna ƙirga asara
  Image caption: Mutane sun yi cirko-cirko suna ƙirga asara
  Wata mota da ake kokarin cirowa
  Image caption: Wata mota da ake kokarin cirowa
 17. Tantabarun da ake kashe wa sama da Naira miliyan biyu wajen kwalliya a shekara

  An ware musu dakinsu musamman inda suke sakata su wala
  Image caption: An ware musu dakinsu musamman inda suke sakata su wala

  Watakila nasan kun saba jin labarin mutanen da ke kashewa karnukansu makudan kudi don kula da su ko ?.

  To sai dai a wannan karon wata mata mai suna Meggy Johnson ce ke kashe wa wasu tantabarunta biyu £4,000, kwatankwacin Naira Miliyan biyu da dubu dari biyu da motsi wajen kula da su, da kuma ɗanɗasa musu kwalliya ta kece raini, abun gwanin ban sha’awa.

  Da farko ta tsinci tantabarun ne a wani waje da aka yasar da su cikin wahala, ta kai su gida ta rika kula da su har tsawon makwanni shida, lokacin ne ta saba da su ta ƙaunace su, suka shiga ranta kamar me.

  Budurwar mai shekara 23 da ke zaune a Lincolnshire, ta ce ta keɓe musu ɗakinsu musamman, ta dinka musu kaya kala kala, sannan takan je kanti don yi musu siyayya, kuma kowaccensu na da kayan da yawansu bai gaza kala 17 ba aƙalla.

  Ana shirya musu ƙayataccen bikin murnar ranar haihuwarsu har ma a yanka musu Kyak.

  Dama dai Hausawa kan ce wanda ya san darajar goro shi yake yafa masa algarara.

  Meggy ta shaku kwarai da tantabarunta
  Image caption: Meggy ta shaku kwarai da tantabarunta
  Tana zuwa yi musu siyayya a kai a kai
  Image caption: Tana zuwa yi musu siyayya a kai a kai
 18. An kashe mutum 13 a wani sabon hari da aka kai kudancin Kaduna

  'Yan bindiga

  Bayanai na cewa an kashe mutum 12, yayin wani sabon hari da aka kai karamar hukumar Zangon Kata a kudancin Kaduna.

  Jaridar The Nations NIgeria ta rawaito ƙungiyar jama'ar kudancin Kaduna ta SOKAPU na cewa an kai harin ne wani gari mai suna Ajiye Jim.

  Mai magana da yawun kungiyar Luka Binniyat, ya ce an kai harin ne yayin da ake tsaka da ruwan sama.

  A cewarsa maharan sun kuma kashe karin wani mutum guda a Atakshusho, mai nisan kilomita 3 daga inda aka kai harin na farko, abun da ke nufin mutum 13 kenan aka kashe.

 19. Ana luguden laɓɓa kan zaɓen ƙananan hukumomin Kaduna

  Ana ci gaba da ta da jijiyoyin wuya kan zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a farkon wannan wata a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

  Lamarin na faruwa ne bayan matakin da hukumar zaɓen jihar ta ɗauka na ayyana cewa zaɓen ƙananan hukumomi guda huɗu a cikin 19 bai kammala ba.

  Yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke iƙirarin cewa ita ce ta lashe akasarin kujerun ƙananan hukumomin da ta ce ana ƙoƙarin hana ta, jam’iyyar APC mai mulki a nata ɓangare na cewa lamarin ba haka ba ne.

  Latsa lasifikar da ke ƙasa, don samun karin bayani a rahoton Yusuf Tijjani.

  Video content

  Video caption: Yadda zaben kananan hukumomin Kaduna ya bar baya da ƙura
 20. Birtaniya ta bukaci kada Rwanda ta aika mata sabon jakada

  Dominic Raab

  Sakataren harkokin wajen Birtaniya Dominic Raab, ya bukaci kada a nada sabon jakadan Rwanda a kasarsa.

  Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Amurka mai suna Lantos Foundation ta ce Johnson Busingye ya na da hannu a tsare fitaccen mai sukar gwamnatin Rwanda nan Paul Rusesa-bagina, wanda ka yi fim din nan Hotek Rwanda saboda gudummawar da ya bada lokacin da akai kisan kare dangin kasar.

  An dai yaudare shi tare da tilasta ma sa komawa gida daga gudun hijirar da ya ke yi, inda ake tuhumarsa da laifukan ta'addanci.

  Wakilin BBC ya ce kafin Jonson Busingye ya zama wakilin Rwanda a Birtaniya, dole sai ofishin harkokin waje ya yi nazari akan takardunsa, wannan ta sanya kungiyar Lantos Foundation ta ce kar a tabbatar da shi, saboda rawar da ya taka ta tsare Rosasebagina.