Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

  1. Sai da safe

    Mustapha Musa Kaita

    Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Alassane Ouattara ya isa Abuja domin halartar taron ECOWAS

    FACEBOOB/ ALASSANE OUATTARA

    Shugaban ƙasar Ivory Coast Alassane Ouattara, ya isa Abuja babban birnin Najeriya domin taron Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS.

    Shugaban zai halarci taron wanda za a yi a gobe Lahadi 12 ga watan Disamba.

    Taron da za a yi na shugabannin ƙasashen shi ne na 60 kuma ana yin irin wannan taron a duk shekara.

    Ana sa ran tattaunawa kan batun siyasa da tsaro da tattalin arziƙin ƙasashen.

    Haka kuma ana sa ran tattaunawa kan halin da ƙasashen Mali da Guinea suke ciki.

    C
    FACEBOOB/ ALASSANE OUATTARA
    FACEBOOB/ ALASSANE OUATTARA
  3. Ko ana yin ingantaccen gwajin korona ga jami'an Sudan Ta Kudu?

    ,

    Wani bincike da gwamnatin Sudan Ta Kudu ta gano cewa akwai yiwuwar ba a yi wa jami'anta gwajin korona da kyau ba kafin su yi tafiya zuwa Qatar.

    An tilasta wa Shugaba Silva Kiir soke tafiyarsa zuwa Qatar a watan Nuwamba bayan jami'ansa da dama waɗanda suka riga shi tafiya aka tabbatar da suna ɗauke da cutar korona a lokacin da suka isa.

    Wani bincike da gwamnatin Sudan Ta Kudun ta yi ya gano cewa da dama daga cikin manyan jami'an suna ba ma'aikatan ɗakin gwajin umarnin su yi musu gwajin baki kawai ban da hanci wanda hakan ba lallai ya bayar da sakamako ingantacce ba.

  4. Guguwa ta kashe aƙalla mutum 70 cikin dare ɗaya a Amurka

    .

    Gwamnan jihar Kentucky ta Amurka ya ce aƙalla mutum 70 ne suka mutu sakamakon guguwar da aka yi ranar Juma'a da dare.

    Andy Beshear ya ce akwai yiwuwar cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai 100 a abin da ya kira guguwa mafi muni a tarihin jihar.

    Gwamman mutane ne ake kyautata zaton sun mutu a wani kamfanin haɗa kendir.

    Aƙalla mutum biyar ne suka mutu a lokacin da guguwar ta shafi wasu jihohi ciki har da wani da ya mutu a wajen ajiye kayayyaki na kamfanin Amazon a Illinois.

    A halin yanzu dai Mista Beshear ya ayyana dokar ta-ɓa-ci a Kentucky.

  5. Bayern Munich ta sha da kyar a hannun Mainz

    .

    Wadda take ta daya a Bundesliga, Bayern Munich ta sha da kyar a hannun Mainz a wasan da suka kara a Allianz Arena ranar Asabar.

    Mainz ce ta fara cin kwallo ta hannun Karim Onisiwo a minti na 22 da fara tamaula a gasar ta Bundesliga.

    Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Kingsley Coman ya farke, sannan Jamal Musiala ya kara na biyu da ya bai wa Bayern maki ukun da take bukata.

    Mainz ta kusan farkewa ta hannun Moussa Niakhat, wanda ya buga kwallo ta nufi wajen mai tsaron raga Manuel Neuer kai tsaye shi kuma ya rike gam.

  6. Sarki Salman ya buƙaci a gudanar da addu'o'in roƙon ruwa a ƙasar ranar Litinin

    ...

    Sarki Salman na Saudiyya ya buƙaci a gudanar da addu'o'in roƙon ruwa a ranar Litinin.

    A sanarwar da ya fitar, ya buƙaci kowa ya tuba ya koma ga Allah da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi kamar su taimakon jama'a da bayar da sadaka da addu'o'i inda ya ce duka waɗannan sunnoni ne masu ƙarfi.

    Ma'aikatar harkokin addini ta ƙasar ta sanar da daidai lokacin da za a yi addu'o'in inda ta ce minti 15 bayan fitowar rana a duka yankunan ƙasar.

  7. Ƴan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a Guinea

    ..

    Ƴan sanda a Guinea sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan gwamman masu zanga-zanga inda suke kira ga sojojin ƙasar su saki tsohon shugaban ƙasar, Alpha Conde daga ɗaurin talalar da ake yi masa.

    Laftanar Kanal Mamady Doumbouya ne ya kifar da gwamnatin Mista Conde mai shekara 83 a watan Satumba.

    A shekarar da ta gabata ne aka soma zanga-zanga bayan tsohon shugaban ƙasar ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar da zai ba shi damar tsayawa takara a karo na uku.

    Bayan juyin mulkin, Laftanar Kanal Doumbouya ya yi alƙwarin mayar da mulkin hannun farar hula bayan zaɓe - duk da babu wani tabbaci kan ko yaushe ne za a yi zaɓen.

  8. An sace yara huɗu da mahaifiyarsu a Kaduna

    ...

    Ƴan bindiga sun sace wata mata da ƴayanta huɗu a wani ƙauye da ke kusa da Sabon Tasha da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

    Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru ne a lokaci guda da wani yunƙurin yin garkuwa da mutane duk a Unguwar Sabon Tasha.

    Ya ce maharan waɗanda sun kai 30, wasunsu na sanye da kayan sojoji ɗauke da muggan makamai inda suka yi ƙoƙarin shiga wani gida a GRA Sabon Tasha amma jami'an tsaro sun daƙile hakan sai dai sun shiga wani ƙauye sun sace wata mata da ƴaƴanta huɗu.

    Ya ce waɗanda aka sace an yi awon gaba da su zuwa wani wurin da ba a sani inda ya ce an ƙoƙarin ceto su.

  9. An sako ma'aikatan ƙungiyar Red Cross da aka sace a Kongo

    ..

    Ma'aikatan agajin da aka yi garkuwa da su a gabashin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo sun samu yancinsu.

    Ƙungiyar Red Cross ta ce ta ji daɗi bayan ta ga an sako ma'aikatanta sun koma ga iyalansu.

    An yi garkuwa da ma'aikatan ne wanda ɗaya daga cikinsu asalin ɗan Kongo ne ɗaya kuma baƙo ne inda aka sace su a arewacin lardin Kivu - yankin da gwamman masu iƙirarin jihadi suke kai hare-hare.

    Babu wani ƙarin bayani kan yadda aka yi aka sako su.

    Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙungiyoyin bayar da agaji da dama sun yi gargaɗi kan ƙaruwar hare-hare kan ma'aikatan bayar da agaji a gabashin Kongo.

    Ko a ranar Laraba sai da aka raunata ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya a arewacin Kivu bayan an buɗe wa motarsu wuta.

  10. Samuel Eto'o ya zama shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru

    Samuel Eto'o

    An zaɓi Samuel Eto'o a matsayin sabon shugban hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru wato Cameroon Football Federation.

    Tsohon tauraron ɗan wasan na Kamaru da ƙungiyoyin Inter Milan da Barcelona ya doke muƙaddashin shugaba Seidou Mbombo Njoya a zaɓen da aka gudanar yau Asabar.

    An kaɗa ƙuri'un ne bayan Kotun Sasanta Harkokin Wasanni ta soke nasarar Mista Njoya a zaɓen 2018.

  11. Shugaba Bazoum na Nijar ya isa Abuja domin taron ECOWAS

    ..

    Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum ya isa Abuja babban birnin Najeriya domin taron Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS.

    Shugaban zai halarci taron wanda za a yi a gobe Lahadi 12 ga watan Disamba.

    Taron da za a yi na shugabannin ƙasashen shi ne na 60 kuma ana yin irin wannan taron a duk shekara.

    Ana sa ran tattaunawa kan batun siyasa da tsaro da tattalin arziƙin ƙasashen.

    Haka kuma ana sa ran tattaunawa kan halin da ƙasashen Mali da Guinea suke ciki.

    ..
    ..
  12. Abin fashewa ya jikkata mutane da yawa a Lebanon

    Lebanon

    Wasu abubuwa masu ara sun fashe a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Tyre na kudancin Lebanon.

    Kafar yaa labarai ta kasar ta ce wata tankar mai ce ta kama da wuta, inda ta bazu zuwa wani ma'adanin makaman sojojin asar wanda hakan ya sa suka fashe.

    An yi nasarar kashe wutar amma ta jikkata gwammai.

    Ko a ranar 4 ga watan Agustan 2020 sinadarin amonium nitrate ya fashe a Beirut, ya kuma kashe mutum 218 tare da janyo asara ta biliyoyin dala.

  13. Rikicin Najeriya da Dubai: Daular Larabawa ta nemi taimakon Minista Hadi Sirika

    Jirgin Emirates

    Ƙasar Daular Larabawa wato United Arab Emirates (UAE) ta nemi taimakon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya Hadi Sirika game da taƙaita wa jirgin Emirates zirga-zirga a Najeriyar da hukumomi suka yi.

    Ranar Juma'a ne dai hukumar kula da zirga-zirgar jirgin sama Nigeria Civil Aviation Authority (NCAA) ta aike wa kamfanin wasiƙa tana mai haramta masa sauka a filin jirgin sama na Legas da kuma rage saukarsa a Abuja zuwa sau ɗaya a sati.

    A cewar NCAA, an ɗauki matakin ne saboda hukumomin UAE sun ƙi bai wa Air Peace, kamfanin Najeriya ɗaya tilo da ke zuwa UAE, damar shiga birnin Dubai ta Sharjah.

    Cikin wata wasiƙa da Daily Trust ta ruwaito, Ministan Tattalin Arziki kuma Shugban Hukumar GCAA Abdulla Bin Touq Al Marri ya faɗa wa Hadi Sirika cewa lamarin da ya jawo aka dakatar da Air Peace shiga Sharjah tsakaninsa ne da filin jirgi na Sharjah.

    Ya ƙara da cewa lamarin bai shafi kamfanin Emirates ba.

    Tirka-tirkar ta jawo Emirates ya dakatar da shiga Najeriya baki ɗaya.

  14. Guguwa ta kashe kusan mutum 50 a Amurka

    Amurka
    Image caption: An kira ma'aikatan agaji zuwa wajen ajiyar kaya na Amazon a

    Gwamnan jihar Kentucky a Amurka ya yi gargaɗin cewa mutum fiye da 50 ake zaton sun rasu sakamakon guguwa mai ƙarfin gaske da aka yi da tsakar dare.

    Andy Beshear ya ce akwai yiwuwar adadin ya zarta haka zuwa 100 a guguwar da ya kira mafi muni a tarihin jihar.

    Guguwar na ci gaba da ɗaiɗaita jihohi a Amurka, yayin da ta ritsa da wasu ma'aikatan Amazon a wani wajen ajiyar kaya a Illinois.

    Mutum ɗaya ya rasu sannan wasu 20 suka maƙale a gidan kula da marasa lafiya a Arkansas bayan ya rushe.

  15. Ƙungiyar ASUU ta sake yin barazanar shiga yajin aiki

    ASUU

    Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta sake yin barazanar shiga yajin aiki biyo bayan ƙarewar wa'adin gargaɗi da ta bai wa gwamnatin tarayya na sati uku.

    Sai dai mambobin ƙungiyar sun yi kira ga 'yan Najeriya da ke son ci gaban ƙasar da su shiga tsakani a tattaunawarta da gwamnatin.

    Malaman sun yi kiran ne ranar Juma'a yayin taron da suka yi a arewaci da kudancin Najeriya, suna masu cewa take-taken gwamnatin ya sa ba su da wani zaɓi illa su dakatar da aiki.

    Bayan kammala taron reshenta na Kudu da aka yi a Ibadan, shugaban ƙungiyar a yankin Farfesa Oyebamiji Oyegoke ya ce "an ƙure ƙungiyar ne saboda ƙin cika alƙawurran da gwamnati ta yi".

    Ya ce: "Take-taken gwamnati wajen zaɓar alƙawurran 2020 da za ta cika maimakon cika su baki ɗaya, babu gaskiya a ciki.

    "Zaɓar wani ɓangare game da lamura a madadin cika su lokaci guda ba abin amincewa ba ne a wajenmu saboda ba za mu sake ɗaukar walwalar abokan aikinmu da wasa ba."

    Karo na ƙarshe da ASUU ta tafi yajin aiki sai da ɗaliban jami'a suka shafe wata tara a gida ba cas ba as.

  16. Lafiya Zinariya: Wayewa ce ta sa mata suka fi maza zuwa ganin likitar kwakwalwa?

    Likitoci a fannin lafiyar kwakwalwa sun ce matsananciyar damuwa na janyo kisan kai da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin al'umma.

    Sai dai wasu mata masu dubban mabiya a shafin sada zumunta na da ra'ayin dandalin na kawo mafita ga matan da ke fuskantar rashin lafiyar kwakwalwa.

    Masana a fannin kiwon lafiya sun ce mata sun fi maza fuskantar matsalar matsananciyar damuwa.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake nuna bukatar karin fadakarwa ga al'umma cewa, rashin lafiyar kwakwalwa matsalar kiwon lafiya ce da ke bukatar ganin likita.

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce rashin lafiyar da ke samun kwakwalwar bil'adama ta kasu kashi-kashi.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari Shirin Lafiya Zinariya:

    Video content

    Video caption: Lafiya Zinariya: Wayewa ce ta sa mata suka fi maza zuwa ganin likitar kwakwalwa?
  17. Jirgin Emirates ya sake dakatar da zirga-zirga zuwa Najeriya

    Jirgin Emirates

    Kamfanin sufurin jirgin sama na Emirates mallakar Daular Larabawa wato United Arab Emirate (UAE) ya ce zai sake dakatar da zirga-zirga zuwa Najeriya daga ranar 13 ga Disamba.

    Matakin kamfanin na zuwa ne bayan hukumar kula da sufurin jirgi ta Najeriya NCAA ta taƙaita wa kamfanin shiga Najeriya ta Abuja da Legas.

    NCAA ta zargi hukumomin Daular Larabawa (UAE) da ƙin bai wa Air Peace, kamfanin Najeriya ɗaya tilo da ke shiga UAE, damar shiga birnin Dubai ta Sharjah.

    "Sakamakon haramcin da aka saka wa Emirates na shiga Najeriya ta Abuja sau ɗaya a mako, kamfanin zai dakatar da zirga-zirga tsakanin Dubai da Najeriya daga 13 ga Disamban 2021 har sai Najeriya da UAE sun sasanta matsalolin da ke tsakaninsu," in ji sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Juma'a.

    Najeriya da UAE dai sun shafe kusan tsawon shekarar 2021 suna rikici kan gwajin annobar korona, abin da ya jawo hana zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu a lokuta da dama.

    A farkon makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya halarci taron kasuwanci a Dubai, sai dai babu tabbas ko ya tattauna matsalar da hukumomin ƙasar.

  18. Ya kamata Buhari ya ji tsoron gamuwarsa da Allah - Attahiru Bafarawa

    Attahiru Bafarawa

    Tsohon gwamnan Sokoto a arewacin Najeriya Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya bayyana takaicinsa kan kashe-kashen al'umma da 'yan bindiga ke yi a yankin, yana mai kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da "ya ji tsoron haɗuwarsa da Allah".

    Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da BBC Hausa kwanaki kaɗan bayan 'yan fashin daji sun ƙona wata motar bas ɗauke da mutum kusan mutum 30 a cikinta a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Sokoto.

    Bafarawa ya ce: "Wajibi ne Buhari ya bi al'umma a zauna a tattauna kamar yadda ya bi su gida-gida lokacin da yake neman ƙuri'a, saboda mu taimaka masa wajen haɗuwarsa da Allah."

    Hare-haren na masu garkuwa da mutane na ci gaba da haddasa salwantar rayukan al'umma a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

    Lamarin ya fi ƙamari a 'yan kwanakin nan a yankin Isa da Sabon Birni na jihar Sokoto da kuma yankin Shinkafi na jihar Zamfara duk da kokarin da gwamnatin tarraya da na jihohin ke cewa suna yi.

    Latsa hoton da ke ƙasa ku saurari cikakkiyar hirar:

    Video content

    Video caption: Ya kamata Buhari ya ji tsoron gamuwarsa da Allah - Attahiru Bafarawa
  19. Ra'ayi Riga: Halin da nau'in korona na Omicron ya jefa matafiya

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari Shirin Ra'ayi Riga

    Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya tafka muhawara ne kan irin halin da nau'in korona na Omicron ya jefa matafiya a ƙasashen duniya, musamman Najeriya.

    Ƙasashen Saudiyya da Birtaniya da Kanada sun hana matafiya daga Najeriya shiga ƙasashensu saboda Omicron, matakin da aka bayyana da cewa "na wariya" ne.

  20. Falasɗinawa na jefa ƙuri'a a zaɓukan lardi

    Al'umma a kauyukan Falasdinu da ke zaune a gabar yamma da kogin Jordan na shirin jefa kuri'a a yau Asabar a kananan zabuka.

    Wannan ne zaɓe karon farko cikin shekara hudu a Falasɗinu.

    Sai dai kungiyar Hamas ta ki amincewa ta shiga zaben a matsayin matakin nuna rashin amincewa da ɗage manyan zabuka zuwa badi.

    Hakan ta sa kananan zabukan ba za su gudana ba a zirin Gaza, inda Hamas din ke da iko.