Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mustapha Musa Kaita da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Sai da safenku

  Mun kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.

  Umar Mikail ke cewa mu haɗu da ku a wani shafin gobe idan Allah ya kai mu.

 2. 'Yan bindiga sun sace mutum 11 a Sokoto

  'Yan fashi

  Rahotanni daga Jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun sace mutum 11 a yankin Sabon Birni.

  Daga cikin mutanen har da wani malami a harin da 'yan bindigar suka kai ranar Juma'a da kuma Asabar.

  Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro Manjo Janar Ali Monguno (mai ritaya) na ziyara a yankin yayin da aka kai harin, biyo bayan ƙona mutum 23 da 'yan fashin daji suka yi a motar bas ranar Litinin da ta gabata.

  A ranar Juma'a ne wasu 'yan ƙasar suka yi zanga-zangar nuna ɓacin ransu ga gwamnatin Shugaba Buhari game da taɓarɓarewar tsaro a wasu jihohin Arewa. .

 3. Barcelona ta sake yin tuntuɓe a La Liga

  Barca

  Barcelona ta tashi 2-2 a gidan Osasuna a wasan mako na 17 da suka kara a gasar La Liga ranar Lahadi.

  Barcelona ce ta fara cin kwallo ta hannun Nico Gonzalez minti 12 da fara tamaula, daga baya Osasuna ta farke ta hannun David Garcia minti biyu tsakani.

  Barcelona ta kara na biyu bayan minti hudu da komawa hutun rabin lokaci ta hannun Abde Ezzalzouli, yayin da saura minti uku a tashi daga fafatawar Osasuna ta farke ta hannun Ezequiel Avila.

  Xavi wanda ya karbi aikin horar da Barcelona a watan Nuwamba bayan maye gurbin Ronald Koeman, ya ja ragamar wasa shida, inda ya yi nasara biyu da canjaras biyu da shan kashi a fafatawa biyu.

  Tun kafin wasan na Lahadi Barcelona ta yi rashin nasara a hannun Real Betis da ci 1-0 a Camp Nou a gasar La Liga, kwana hudu bayan haka Bayern Munich ta yi waje da ita daga gasar Champions League, bayan ta doke ta 3-0 a Jamus.

 4. Najeriya za ta dakatar da jiragen ƙasashen da suka hana 'yan ƙasar shiga ƙasashensu

  Jirgin British Airways

  Daga ranar Talata, 14 ga watan Disamba gwamnatin Najeriya za ta dakatar da jirage daga ƙasashen Birtaniya da Kanada da Saudiyya da Argentina sauka a ƙasar a matsayin ramuwar gayya.

  Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ne ya sanar da matakin ranar Lahadi a Jihar Legas, yana mai cewa an ɗauke shi ne da zimmar ramuwar gayya kan hana matafiya daga Najeriya shiga ƙasashen saboda nau'in korona na Omicron, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

  Ministan ya ƙara da cewa gwamnati za ta saka Birtaniya da Kanada da Saudiyya da Argentina cikin jerin ƙasashen da za ta haramta wa shiga ƙasar saboda annobar ta korona da kuma yaɗuwar Omicron.

  "Kamar yadda suka yi mana, idan har ba za su ƙyale mutanenmu su shiga ƙasashensu ba, to su wa jiragensu za su ɗauka idan suka shigo ƙasarmu?," in ji shi.

  "Mun gama tattaunawa cewa ba za mu yarda ba kuma mun ba da shawara a saka Birtaniya da Saudiyya da Kanada da Argentina cikin jerin dakatattu."

 5. An rufe layukan waya miliyan 63 a Najeriya cikin shekara ɗaya

  Layukan waya

  Jumillar layin waya miliyan 63.97 aka toshe cikin shekara ɗaya a Najeriya yayin da hukumar sadarwa ta Nigerian Communications Commission (NCC) ke ci gaba da haɗa lambar ɗan ƙasa NIN da layukan salula.

  Wasu bayanai da NCC ta wallafa sun nuna cewa jumillar adadin layukan salula da ke aiki a Najeriya sun ragu da kashi 21.79 cikin 100 zuwa 229,582,206 a watan Oktoban 2021 daga 293,554,598 a Oktoban 2020, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

  A tsakanin lokacin da ake magana, adadin layukan da ke aiki ya fi yawa a Agustan 2021 (328,114,538) sannan ya fi raguwa a Satumban 2021 (229,467,077).

  Kazalika, jumillar adadin layukan da ke aiki ya ragu daga 207,578,237 zuwa 191,618,839, wato raguwar kashi 7.69 kenan cikin 100 (15,959,398).

  A cewar hukumar, layuka 37,963,367 da ke aiki a baya sun daina aiki ya zuwa Oktoban 2021, inda aka samu raguwa daga 85,976,361 a watan na Oktoba na shekarar 2020.

  Kamfunnan sadarwa a Najeriya na ci gaba da ganin raguwar yawan layukan da ke amfani tun bayan da NCC ta fara haɗa layukan salula da lambar ɗan ƙasa ta National Identity Number (NIN) bisa dalilai na tsaro.

 6. Ƙasashen G7 sun gargaɗi Iran kan tattaunawar nukiliya

  Iran

  Ministocin kasashen G7 - ƙasa bakwai mafiya girman tattalin arziki - na shirin yi wa Iran gargadin cewa lokaci na kure mata kan ci gaba da tattauna shirinta na Nukiliya.

  Masu shiga tsakani daga Amurka za su sake komawa birnin Vienna na Austria don ci gaba da zama kan batun.

  Wakilin BBC ya ce a halin da ake ciki babu tabbas ko gwamnati a Tehran na da zimmar kawo karshen wannan tirka-tirka.

  Amma Shugaba Raisi na Iran ya kafe cewa kasarsa da gaske take, kuma suna fatan a cimma abin da ake so bayan tattaunawar a wannan karon.

 7. Hazard da Bale na cikin 'yan Real da za su kara da Atletico

  Real Madrid

  Real Madrid za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasan mako na 17 a gasar La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

  Wasan na hamayya na birnin Madrid, za a yi shi ne a lokacin da Real ke jan ragama da maki 39 wato tazarar maki 10 tsakaninta da Atletico, ta hudu a teburi.

  Tuni kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da za su karbi bakuncin Atletico a wasan na hamayya ciki har da Eden Hazard da Gareth Bale.

  Haka kuma Karim Benzema wanda bai buga wasan da Real ta doke Sociedad 2-0 a karawar mako na 16 ba sakamakon jinya, yana cikin wadanda za su fuskanci kungiyar da Diego Simeone ke jan ragama.

  Bale da Hazard manyan 'yan wasa ne a Real Madrid da suke karbar albashi mai tsoka, wadanda ke fama da jinya a kodayaushe.

  Hazard ya buga minti 424 a kakar bana, sai dai minti tara kacal ya yi a wasa uku a baya. Rashin lafiyar da dan wasan ya kamu da ita lokacin da ya je buga wa tawagar Belgium wasa ta sa bai yi wa Real Madrid wasanni da yawa ba.

 8. Sarkin Musulmi ya buƙaci a fara alƙunutu kan kashe-kashe a Arewa

  Sultan Abubakar III

  Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al'ummar Musulmi su fara gudanar da addu'o'i na alƙunutu game da kashe-kashen da yankin arewacin ƙasar ke fama da shi na 'yan bindiga.

  Kazalika sarkin ya nemi dukkan masallatai da majalisun tattaunawa a faɗin Najeriya da su dage da addu'o'i "a irin wannan lokaci na bala'o'i don neman tausayin Allah".

  Wata sanarwa daga ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) wadda sarkin Musulmi ke jagoranta ta ce an yi kiran ne saboda ya zama dole.

  "Wannan kiran ya zama dole idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaƙanta su gabagaɗi kamar yadda muka gani a Sokoto da Gidan Bawa da Beni-sheikh da Kaga (Jihar Borno)," a cewar sanarwar da sakataren JNI Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu.

  Tun daga farkon makon da ya gabata; 'yan fashin daji sun ƙona mutum 23 da ransu a cikin motar fasinja a Jihar Sokoto sannan suka sake kashe uku tare da sace wasu da dama; 'yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 15 a masallaci a Jihar Neja; an kashe kwamashina a Jihar Katsina a cikin gidansa.

 9. Buhari ya yi ta'aziyya ga al'ummar jihar Oyo kan rasuwar Sarkin Ogbomosho

  ..

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa jama'ar jihar Oyo da kuma da kuma an Ogbomosho kan rasuwar Sarki Jimoh Oladunni Oyewumi, Ajagungbade III.

  A wata sanarwa da babban mai ba shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, shugaban ya ce mulkin Sarki Oyewumi na shekara 48 ya kawo sauyi matuƙa da kuma zaman lafiya.

  Shugaban ya jaddada cewa za a ci gaba da tunawa da shugaban kan irin gudunmawar da ya bayar wajen haɗin kan ƙasa musamman a tsakanin sarakunan gargajiya

 10. Buhari ya nemi ƴan Najeriya su yi wa Amurkawan da guguwa ta halaka addu'a

  ..

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Amurka da mutanen ƙasar kan mahaukaciyar guguwar da ta kashe sama da mutum 100 a jihohi shida.

  A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce ya damu ƙwarai kan yadda gidaje da makarantu da wuraren sana'o'i da asibitoci suka lalace.

  Shugaban ya yi kira ga mutanen Najeriya su taya sauran mutanen duniya addu'a ga waɗanda suka rasa ransu da kuma samun sauƙin wadanda suka jikkata.

  Sama da mutum 100 ne suka rasu a guguwar wadda ta fi ɓarna a jihar Kentucky ta Amurka.

 11. Rasha da Amurka za su sake tattaunawa kan batun Ukraine

  ..

  Rasha ta ce Shugaba Putin da kuma Joe Biden sun amince su ƙara tattaunawa a daidai lokacin da Rasha ke fuskantar matsin lamba kan ƙoƙarin mamaye Ukraine da da ake zargin take so ta yi.

  Mai magana da yawun Mista Putin, Dmitry Peskov ya ce tattaunawar da aka yi ta intanet ba ta yi wani armashi ba.

  Sai dai ya ce duka ɓangarorin biyu na so a ci gaba da tattaunawa. Mista Peskov ya yi iƙirarin cewa da gangan ake yi wa Rasha matsin lamba domin a kai ta bango.

  Ya bayyana cewa Mista Putin ya shaida wa shugaban Amurka cewa dakarun Rasha suna cikin ƙasarsu ba tare da yi wa kowa barazana ba.

  Wannan batu ya zama abin faɗa a taron G7 inda ministocin harkokin wajen ƙasashen ke ta gargaɗi kan abin da zai biyo baya idan Rasha ta yi mamaya.

 12. Zamantakewa: Hana aure saboda bambancin yare 'rashin wayewar addini ce'

  Video content

  Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
 13. Firaiministan Isra'ila zai kai ziyara Daular Larabawa

  ..

  Firaiministan Isra'ila Naftali Bennett zai kai ziyara Abu Dhabi a yau Lahadi, wadda ita ce ziyara mafi girma tun bayan da Isra'ilar ta sasanta da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

  Ana sa ran zai haɗu da yarima mai jiran gado na ƙasar Sheikh Mohammed bin Zayed a ranar Litinin.

  Wannan ce tafiya ta farko da wani shugaban Isra'ila ya taɓa kai wa Daular Larabawan.

  Tuni Daular Larabawan da Bahrain da Sudan da Morocco duk suka yunƙura domin sasantawa da Isra'ila inda Amurka ce ta shiga gaba ta tabbatar da sasancin.

  Kamfanoni da dama a Isra'ila da Daular Larabawa sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar kasuwanci a ƴan makonnin nan kuma ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan batun yauƙaƙa dangantakarsu ta fuskar tattalin arziƙi.

  Ziyarar Mista Bennet ɗin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin fargaba kan batun tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliya da Iran a Vienna.

 14. Yadda fasto ya hada baki da matarsa don yi wa wata yarinya 'fyade'

  .

  Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Ogun ta ce ta kama wani fasto kan zargin haɗa baki da matarsa domin ya yi wa wata yarinya ƴar shekara 16 fyaɗe.

  Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana cewa an kama faston mai suna Peter Taiwo tun a ranar Juma'a wanda yake a Cocin Christ Apostolic Bible wadda ke a Alaja Oke a jihar Abeokuta.

  Rundunar ta ce an kuma kama matarsa mai suna Elizabeth wadda ake zargin da haɗin bakinta har aka yi wa yarinyar fyaɗe.

  Yarinyar ta bayyana cewa a lokacin da ta je coci domin gudanar da waƙe-waƙen da suka saba, sai matar faston ta kirata sa'annan ta ce mata ta je wani ɗaki wajen fasto yana nemanta saboda zai aike ta.

 15. Kocin Crystal Palace na nuna damuwa kan yiwuwar dawo da buga wasa ba ƴan kallo

  gg

  Kocin Crystal Palace, Patrick Vieira ya bayyana cewa za a fuskanci bala'i idan tsoron korona ya sa aka koma buga ƙwallo ba tare da ƴan kallo ba.

  Ana sa ran daga ranar Laraba dole ƴan kallo sai sun nuna gwajin korona kafin a bari su shiga kallon wasa a Ingila.

  Ana dai ganin cewa idan aka ɗauki wannan mataki, ƴan kallo ƙalilan ne kawai za su rinƙa zuwa.

  Tuni ƙungiyar Crystal Palace ta soke dabdalar Kirisimetin da ta yi niyyar yi sakamakon yadda sabon nau'in Omicron ke ƙara bazuwa a Birtaniya.

  An rinƙa buga wasa ba ƴan kallo bayan hutun da aka je a Yunin 2020, inda ba a bari an dawo baki ɗaya ba sai a farkon kakar bana.

  Bayan ƴan kallo sun soma halartar fili a Disambar bara, an soma gwaji ne da ƴan kallo 2,000 inda daga baya kuma aka kai har dubu goma.

 16. Lafiya Zinariya: Wayewa ce ta sa mata suka fi maza zuwa ganin likitar kwakwalwa?

  Video content

  Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraren shirin
 17. An yi wa shafin Twitter na firaiministan India kutse

  /

  An yi kutse a shafin Twitter na Firaiministan Indiya, Narendra Modi.

  An wallafa wani saƙo a shafin nasa tare da cewa Indiya ta amince da bitcoin a matsayin hanyar saye da siyarwa haka kuma gwamnati za ta ba kowane ɗan ƙasar bitcoin 500.

  An yi sauri an goge saƙon; inda ofishin Mista Modi ɗin yake cewa an ɗan yi kutse a shafin na shugaban na ɗan wani lokaci.

  Wannan ne karo na biyu da ake yi wa shafin firaiministan kutse ganin cewa hakan ta faru a bara.

  Shugaban na yawan wallafa saƙonni a Twitter kuma yana da mabiya sama da miliyan 70.

 18. Labarai da dumi-dumiSarkin Ogbomosho Jimoh Oyewumi ya rasu

  ..

  Sarkin Ogbomosho Jimoh Oyewumi ya rasu yana da shekara 95.

  Wani babban jami'i a masarautar da ke jihar Oyo a kudancin Najeriya ya tabbatar wa BBC da rasuwar sarkin.

  An haifi marigayin a ranar 26 ga watan Mayun 1926, kuma ya hau kan karagar mulki a ranar 24 ga watan Oktoban 1973.

  Sarkin dai yana daga cikin sarakunan da suka fi daɗewa kan karagar mulki a masarautun Najeriya.

 19. Sama da mutum 100 sun mutu a Amurka sakamakon guguwa

  ..

  Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya wurin taimaka wa jihohin ƙasar shida da bala'in mahaukaciyar guguwa ta daidaita.

  Mr Biden ya ayyana dokar ta ɓaci a Kentucky, inda rahotanni ke cewa sama da mutun 100 sun mutu sakamakon guguwa.

  Garin Mayfield ne ya fi jin jiki a wannan bala'in, inda gine-gine suka rushe, haka gidaje da kuma coci-coci.

  Ko a Illinois aƙalla mutun shida guguwar ta kashe, a lokacin da iska ya ruguza ginin ma'aikatar da suke ciki.

  Shugaba Biden ya ce sun shirya bada agajin gaggawa ga ɗimbin mabuƙata, lura da cewa da dama sun rasa ruwan sha da wutar lantarki.

  Rahotanni sun ce ko a jihohin Arkansas da Missouri da Tennessee an samu mace-mace, kuma yanzu haka guguwar ta afka wa Mississipi.

 20. Mutum 483 sun kamu da korona a Legas a ranar Asabar

  ..

  Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 612 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Asabar 11 ga watan Disamba 2021.

  Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Lagos tana kan gaba da mutane 483 sai babban birnin tarayyar Najeriyar, Abuja mai mutane 49 sai jihar Rivers 38 sai Oyo mai mutane 31.

  Sauran su ne Delta mai mutane 5 sai Ekiti 4, yayin da Bauchi take da mutum 1 kamar yadda ita ma jihar Jigawa take da mutum 1.

  Yanzu dai adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta ya kai 217,063 amma kuma an sallami 207,703 daga asibiti.

  Yawan waɗanda suka rasa rayukansu sanadin cutar kuwa ya kai 2,981.