Darajar Firaiministan Birtaniya Boris Johnson na lilo a idon jama'a, a daidai lokacin da ake shirin wallafa wani rahoto kan zargin dabdalar da aka shirya a gidan firaministan da ke lamba 10, titin downing a daidai lokacin da ake tsakiyar annobar korona.
Rahoto kai-tsaye
Daga Umar Mikail
time_stated_uk
Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu
Cutar korona nau'in Omicron ta bazu sosai a duniya – WHO
Shugaban Hukumar Lafiya ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya gargadi cewa sabon nau’in annobar korona na Omicron ya yadu fiye da tunani.
Ya kara da cewa da alama tuni dama akwai cutar tana yaduwa a cikin kasashen duniya.
Dr Tedros ya ce ba daidai ba ne kasashe, su yi tunanin cutar bata wani tasiri ga jikin dan adam.
Kafin wannan lokaci WHO ta ce Omicron za ta kwantar da mutane da dama nan da makonni masu zuwa a asibitoci.
Fashewar tankar mai ta kashe mutum 60 a Haiti
Akalla mutum 50 ne suka mutu sanadiyyar fashewar wata tankar dakon mai a kasar Haiti.
Wani jami'in yankin da ke arewacin kasar ya ce ya ga gawarwaki a kasa bayan fashewar. Kuma yanzu haka asibitocin yankin sun cika makil.
Firaministan Haiti, Ariel Henry ya ayyana zaman makokin kwanaki uku a kasar bayan mutuwar sama da mutum 60 a gobarar tankar man fetur.
Rahotanni na cewa galibin mutanen da suka mutu masu koƙarin kwasar mai ne lokacin da tankar man ta yi karo da wata motar dako.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gobarar ta tsananta.
Wani ganau ya shaida wa wata kafar yaɗa labaran kasar yanayi na muni da aka tsinci kai a ciki.
Asibitoci da ke birnin Cap Haitien sun cike makil da mutanen da suka samu rauni sakamakon gobarar.
Iraƙi ta rataye mutum uku kan alaƙa da ta’addanci
Rahotanni daga Iraƙi na cewa an rataye wasu maza uku bayan an tuhumesu da alaƙa da ta’addanci.
Jami’an tsaro sun ce ɗaya daga cikin wanda aka rataye an same shi da hannu a harin bam da aka kai da mota a Nasiriyah cikin shekara ta 2013, an kuma samu guda da kai makamancin wannan hari a birnin Karbala.
Mahukunta a Iraqi sun yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan dubban mutane da ake samu da hannu a ayyukan ta’addanci a 2017.
Buhari ya yi iya yinsa kan tsaro a Najeriya ba zai yi sama da haka ba - Obasanjo
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ya yi duk abin da zai iya kan matsalolin da Najeriya ke fama da su, ba kuma zai yi sama da hakan ba.
Karanta labarin a nan
Matawalle ya nemi taimakon shugaba Bazoum kan matsalar ƴan bindiga a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya nemi taimakon shugaban Nijar Mohamed Bazoum kan kawo ƙarshen matsalar ɓarayin daji da suka addabi jiharsa da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Sanarwar da gwamnatin Zamfara ta fitar ta ce gwamnan ya kai wa Bazoum ziyara ne fadarsa a Yamai babban birnin Nijar inda suka tattauna kan goyon baya da haɗin kai tsakanin gwamnatin Zamfara da gwamnatin Nijar musamman yankunan ƙasar da ke kan iyaka da Zamfara.
Gwamna Matawalle ya yi alƙawalin samar da mota ƙirar Toyota Hilux guda biyar ga jami’an tsaro da za su yi sintiri a yankin Maradi da sauran sassan Nijar da ke kan iyaka da Zamfara da Katsina da Sokoto.
A nasa ɓangaren Bazoum ya ce Nijar a shirye take ta taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro inda ya nemi gwamnonin Najeriya su haramta shigo da babura a ƙasar
Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar ɓarayin daji da ke kai hare-hare da satar mutane da ƙona gari, kuma matsalar ta shafi jihohin Katsina da Sokoto da Kaduna da ke makwabtaka da jihar.
Birtaniya ta ɗage haramcin hana ƴan Najeriya shiga ƙasarta
Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta ɗage haramcin shiga ƙasarta ga dukkanin ƙasashe 11 da ta hana daga ranar Laraba.
Ƙasashen sun ƙunshi Angola da Botswana da Eswatini da Lesotho da Malawi da Mozambique da Namibia da Najeriya da Afrika ta Kudu da Zambia da kuma Zimbabwe.
A ƙarshen watan Nuwamba ne Birtaniya ta sake ɗaukar matakin na hana ƙasashen shiga ƙasarta saboda tsoron nau’in korona na Omicron.
Sakataren lafiya na ƙasar Sajid Javid ya ce cutar ta bazu sosai don hana matakin ba ya da wani amfani.
Sai dai ya ce za a ɗauki matakai na yin gwaji ga baƙi da suka shiga ƙasar, kuma duk wanda ya fito daga ƙasashen sai ya biya kuɗin otal na kwanaki 10 da zai killace kansa.
Najeriya za ta lalata allurar rigakafi miliyan ɗaya
Hukumomin Najeriya sun tabbatar da cewa suna shirin lalata alluran rigakafin korona kimanin miliyan ɗaya sakamakon rashin amfani da su.
Hukumomin sun ce wa’adin aikinsu ne ya ƙare, don haka ba su dace a yi amfani da su ba.
Wannan ne karon farko da hukumomin lafiya a Najeriya suka sanar da yawan rigakafin da za a lalata.
Shugaban hukumar lafiya matakin farko Dr Faisal Shuaib ya ce hukumarsa za ta yi aiki da hukumar NAFDAC domin tsayar da ranar da za a lalata rigakafin.
Hukumomin sun ce ba yi amfani da rigakafin ba da ta lalace.
Zuwa yanzu kashi biyu ne kawai suka yi rigakafi a Najeriya mai yawan al’umma miliyan 200.
Buhari ya gana da dattawan Katsina
Shugaba Buhari ya gana da dattawan Katsina da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello ya jagoranta zuwa fadar shugaban a Abuja a ranar Talata.
Ana sa ran tawagar dattawan na Katsina, jihar da Buhari ya fito sun tattauna ne kan matsalar tsaro da ta addabi Katsina da wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
A makon da ya gabata shugaba Buhari ya tura wata tawagar gwamnati zuwa yankunan Sokoto da Zamfara da Katsina musamman bayan harin da ƴan bindiga suka kai wa wasu matafiya a yankin Sabon Birni inda suka ƙona mutum kusan 40.
Arsenal ta tuɓe Aubameyang a matsayin kyaftin ɗinta
Arsenal ta karɓe muƙamin kyaftin daga hannun Pierre-Emerick Aubameyang sakamakon nuna halin rashin ɗa'a.
Ɗan ƙwallon tawagar Gabon wanda bai buga wasan da Arsenal ta doke Southampton 3-0 ranar Asabar a gasar Premier League ba, ba zai yi wa Gunners fafatawar da za ta kara da West Ham ba ranar Laraba a Premier League.
"Muna sa ran 'yan wasanmu, musamman kyaftinmu, su yi aiki da dokoki da tsare-tsaren da muka shimfiɗa kuma muka amince baki ɗayanmu," a cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar.
An taɓa ajiye Aubameyang mai shekara 32 a benci saboda dalilan rashin ɗa'a a watan Maris da ya gabata.
Buhari ya naɗa sabon minista Muazu Sambo
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rubuta wa Majalisar Dattawa wasiƙa yana neman amincewarta kan naɗa Muazu Sambo a matsayin minista.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasiƙar a zaman majalisar na yau Talata.
Ana kyautata zaton Muazu wanda ɗan asalin Jihar Taraba ne, zai maye gurbin tsohon Ministan Lantarki Sale Mamman da aka kora a watan Satumba.
Haka nan, Buhari ya nemi majalisar ta amince da naɗin wasu kwamashinonin hukumar zaɓe ta ƙasa domin su maye gurbin waɗanda za su ajiye aiki.
Bugu da ƙari, shugaban ya buƙaci majalisa ta amince da naɗa kwamashinoni a Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa wato National Population Commisssion.
Dalilin da ya sa muka tarwatsa masu zanga-zanga - 'Yan sandan Katsina
Masu zanga-zanga kan matsalar tsaro a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya sun fuskanci fatattaka daga 'yan sandan jihar.
'Yan zanga-zangar sun faɗa wa BBC Hausa cewa jami'an tsaro sun kore su daga wurin da suka taru a safiyar yau Talata.
Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan Katsina ya ce sun fatattaki masu zanga-zangar ce saboda ba su faɗa musu ba kafin gudanar da ita, amma mutanen sun ce sun faɗa wa hedikwatar 'yan sandan ta ƙasa saboda ana yin irinta a wasu yankunan ƙasar.
Jihar Katsina ce mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari kuma tana cikin waɗanda suka fi fuskantar hare-haren 'yan fashin daji masu garkuwa da mutane. A makon da ya wuce aka kashe kwamashina har gidansa a jihar.
An gudanar da irin wannan zanga-zanga a Abuja babban birnin ƙasar.
Kashe-kashe a Arewa: A Abuja ma an yi zanga-zanga
'Yan ƙungiyar asiri sun ƙona ɗalibin jami'a saboda ya ƙi shiga gungunsu
Jami'ar Jihar Osun da ke kudancin Najeriya ta tabbatar da ƙona wani ɗalibin shekarar ƙarshe da wasu suka yi saboda ya ƙi shiga ƙungiyarsu ta asiiri.
An ceto ɗalibin kuma yanzu haka yana samun kulawa a asibiti sakamakon raunukan ƙuna da suka ji masa.
A ranar Litinin ne hukumar makarantar ta bayyana cewa tana aiki tare da 'yan sanda domin tabbatar da cewa an kama 'yan ƙungiyar asirin da ake zargi.
An gano lamarin ne bayan da aka nemi ɗalibin aka rasa a ɗakin jarrabawa. Daga nan ne aka nemi iyayensa, inda su kuma suka faɗa musu cewa an ji masa ciwo kuma yana asibiti.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa an jiyo matashin yana cewa ba zai shiga ƙungiyar tasu ba kafin daga baya ya fara ihun neman taimako.
Ana yawan samun tashin hankali mai alaƙa da ƙungiyoyin asiri a jami'o'in Najeriya musamman a ɓangaren kudancin ƙasar.
Tunisia za ta yi zaɓe nan da shekara ɗaya
Shugaban kasar Tunisiya, Kais Saied, ya sanar da cewa majalisar dokokin kasar za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai bayan gudanar da zaben shekara mai zuwa.
A wani jawabi da ya yi na kasa da aka nuna ta kafar talibijin, Mista Saied ya ce za a fara shirin tuntubar jama'a a wata mai zuwa tare da gudanar da zaben raba-gardama kan sauye-sauyen da za a yi wa kundin tsarin mulkin kasar a watan Yuli.
Shugaban Tunisiya ya sallami firaiministan na wancan lokacin kuma ya dakatar da majalisar dokokin kasar tare da ba wa kansa ikon gudanar da mulki na musamman a wata biyar da suka gabata.
Sai dai 'yan hammaya sun yi Allah wadai da hakan a matsayin juyin mulki.
'Yan sandan Kaduna sun kashe 'yan fashi biyu
'Yan sandan Jihar Kaduna sun yi nasarar kashe 'yan bindiga biyu da suka addabi yankin Ƙaramar Hukumar Giwa yayin wata arangama.
Dakarun rundunar 47 Zariya ne suka gamu da 'yan fashin yayin da suke kan aikin sintiri a kusa da ƙauyen Riheyi na garin Fatika ranar Litinin da dare, in ji kakakin rundunar a Kaduna Mohammed Jalige
Da yake magana da Channels TV, Mista Jalige ya ce nan take suka fara fafatawa, inda jami'ansu suka yi nasarar kashe biyu daga cikinsu.
Ya ƙara da cewa 'yan sanda sun ƙwace bindiagar AK-47 da kuma harsasai daga hannun 'yan fashin.
A ranar Litinin ɗin da dare wasu 'yan fashi suka tare babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya, inda rahotanni suka ce an kashe mutum ɗaya tare da sace wasu da dama.
Sojojin Nijar da Burkina Faso sun kashe masu iƙirarin jihadi 100
Rundunar sojan Burkina Faso ta ce aikin haɗin gwiwa da suka yi da sojojin Nijar ya ba su nasarar kashe 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi aƙalla 100.
Sai dai ta ce an kashe soja aƙalla 14 yayin fafatawar tare da kama 'yan bindigar 20 da makamansu masu yawa cikin sati biyu da suka gabata.
Samamen na sojoji na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Burkina Faso game da zargin gazawarta wajen daƙile hare-haren 'yan bindigar da ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda da Islamic State a ƙasar da ke Afirka ta Yamma.
Shugaban Ƙasa Roch Marc Christian Kabore ya ɗauki matakin korar firaministansa Christophe Joseph Dabiré don faranta wa masu zanga-zangar sannan ya naɗa Lassina Zerbo, abin da ake ganin yunƙuri ne na tunkarar matsalar tsaron.
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Katsina
Labaran duniya cikin minti ɗaya
Video content
Gwamnatin Najeriya za ta ƙara wa 'yan ƙasa haraji
Ministar Kuɗi da Tsare-Tsare ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta ce 'yan Najeriya za su fara biyan sabon kuɗin haraji nan gaba.
Da take magana ranar Litinin yayin taron jin ra'ayin jama'a kan Ƙudirin Dokar Kuɗi ta 2021 (Finance Bill 2021), Zainab ta faɗa wa kwamatin kuɗi na Majalisar Wakilai cewa matakin na ƙunshe ne cikin dokar.
"Yayin da waɗan nan lamurra ke buƙatar ƙarin haraji a kan wasu harkokin kasuwanci da wasu ɗaiɗaikun mutane da ma'aikatu, wannan gwamnatin za ta ci gaba da jajircewa wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma ƙungiyoyin al'umma," a cewarta.
Sai dai ta faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa ya yi wuri a fayyace sashen da za a ƙara wa harajin - ko dai a kan harajin sayen kayayyakin yau da kullum na VAT ko kuma harajin shigo da kaya na Stamp Duty.
Ta ƙara da cewa wajibi ne Najeriya ta faɗaɗa hanyoyin samunta daga man fetur domin gudanar da manyan ayyuka.
A cewarta, ya zuwa Satumban 2021 harajin da gwamnati ta karɓa ya kai naira tiriliyan 4.56, inda aka samu kashi 75 cikin 100 na abin da ake nema. Haka nan, an samu tiriliyan 1.31 na harajin da ba na man fetur ba - kashi 117 cikin 100 kenan na abin da ake nema.
Sai dai ta ce gwamnati za ta ƙara azama wajen ƙara haraji kan lemukan gwangwani kamar barasa da lemon kwalaba da taba sigari domin gudanar da ayyuka a fannin ilimi da lafiya da sauransu.