Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Ana fargabar barkewar yaki tsakanin kungiyoyin Shi'a a Iraqi

  Muqtada al-Sadr
  Image caption: Muqtada al-Sadr ya ce muddin ba a yi hankali ba yaki zai barke a tsakaninsu

  Kungiyoyin Shi’a guda biyu wadanda ba sa ga-maciji a Iraqi sun yi Allah-wadai da kisan gillar da suke yi wa juna a yankin kudancin kasar.

  Babban malamin nan mai ikon fadi a ji na Shi’a, Muqtada al-Sadr ya yi gargadin cewa idan ba a yi hankali ba yaki zai barke a tsakanin bangarensa da kuma bangaren kungiyar nan mai gwagwarmaya da makamai ta ‘yan Shi'ar wadda Iran ke mara wa baya, Asaib Ahl al-Haq.

  Rahotanni sun ce wakilan bangarorin biyu sun yi ganawarsu ta farko yau Juma’a 11 ga watan Fabrairu, 2022 a lardin Maysan wanda ya yi kaurin suna da aikata miyagun laifuka.

  A farkon makon nan majalisar dokokin Iraqi ta dage zaman da za ta zabi sabon shugaban kasa saboda rikicin da ake fama da shi a tsakanin bangarori.

 2. Wata mota ta haure gada ta fada ruwa a Abuja

  Motar a ruwa

  Wata mota ta tsunduma tafki, bayan da ta kwace wa direbanta ta haure gadar Shehu Musa ‘Yar Adu’a da ke kusa da katafaren kantin nan na Jabi Lake Mall da ke unguwar Jabi a cikin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

  Aikin tsamo motar

  Wasu rahotanni na cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar Juma'ar nan 11 ga watan Fabrairu 2022, sakamakon tsananin gudu da direban motar yake yi ne, wanda hakan ya sa ta kwace masa ta afka tafkin, a lokacin da wata mota ta shiga gabansa, ya yi kokarin kauce mata.

  Aikin tsamo motar

  Sai dai rahotanni sun ce direban ya yi sa’a, domin ya tsira da ransa, kuma kadan ya rage motar fara kirar KIA, ba ta nitse cikin ruwan ba.

 3. 'Yar Tanzania da ke cike da burin zama Sarauniyar Kyau ta Nakasassu ta Duniya

  Witness Raphael za ta wakilci Tanzania a gasar duniya ta sarauniyar kyau ta guragu ko masu nakasar da ke keken guragu ta wannan shekarar a Mexico.

  Ms Raphael, wadda aka haife ta da nakasar laka, ta ce tana sa ran ta zama sarauniyar gasar saboda ta shirya mata tsawon shekaru.

  A hirar ta da BBC ta ce, "Na saba shiga gasa a makaranta har a wani lokaci ma na zo ta biyu.’’

  A kwanan nan ta gamu da cin zarafi a shafukan intanet, bayan wani daga cikin shahararru a shafukan sada zumunta da muhawara na Tanzania ya rubuta labarinta a shafinsa.

  "Wasu kalaman na cin mutunci ne – inda suke tambaya, me ya sa nake bata lokacina shiga gasar sarauniyar kyau. Wasu na cewa na yi shafe-shafe na sauya fatata, yayin da wasu ke cewa na yi lukuta,’’ in ji Ms Raphael.

  View more on instagram

  To amma ta ce kawaye da ‘yan-uwa har da iyayenta su ne ke karfafa mata guiwa, saboda haka ba ta wata nadama dangane da aniyar tata.

  Raphael na fatan zama sarauniyar gasar ta duniya domin ta karfafa wa sauran mata masu nakasa a Afirka guiwa.

  Sauran kasashen Afirka da za su shiga gasar sarauniyar kyauwun ta nakasassu ta duniya a shekarar nan sun hada da Najeriya da Afirka ta Kudu da Kamaru da kuma Kenya.

 4. An sanya masu yi wa kasa hidima (corpers) cikin inshorar lafiya ta Najeriya

  Ministan matasa da shugaban NYSC da sauran jami'ai
  Image caption: An bukaci duk mai yi wa kasa hidima ya je ya yi rijista da asibiti domin fara cin moriyar shirin

  Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima ta Najeriya (NYSC), ta kaddamar da shirinta na shigar da masu hidimar cikin tsarin inshorar kula da lafiya na kasar.

  A shirin wanda aka kaddamar yau Juma’a 11 ga watan Fabrairu 2022, a hedikwatar hukumar da ke, Abuja babban birnin Najeriya, masu hidimar za su rika cin moriyar kula da lafiyarsu daga lokacin da matashi ya karbi takardarsa ta zuwa sansanin horo zuwa sati uku bayan kammala aikin na kasa.

  Domin tabbatar da shirin na tafiya yadda ya kamata, hukumar ta NYSC ta ce ta zabi asibitoci shida daga shiyyoyi shida na kasar domin gudanar da shi.

  Hukumar ta bukaci matasan da ke cikin aikin bautar kasar da su je su yi rijista da asibitocin da ke yankunan da suke aikin.

  Shugaban hukumar ta NYSC Manjo Janar Shuaibu Ibrahim ya ce kaddamar da shirin kula da lafiyar cika umarnin da shugaban kasar ya bayar ne a shekara ta 2016, wanda ya biyo bayan kisan da aka yi wa wasu masu yi wa kasa hidima uku da aka tura sansanonin horon aikin a jihohin Kano da Zamfara da kuma Bayelsa.

 5. 'Yan majalisar Tanzania sun damu kan yawan sayar da kayan hana daukar ciki

  Kororon robo
  Image caption: mata da 'yan mata sun fi sayen abubuwan hana daukar ciki maimakon na kariya daga cutuka

  'Yan majalisar dokokin Tanzanian sun ce ana samun karuwar amfani da ababan hana daukar ciki a tsakanin 'yan mata da kuma mata da ke tsakanin shekara 14 da 24 a kasar.

  Wani rahoto kan yawaitar masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki da kwamitin kula da harkokin lafiya na majalisar dokokin kasar ya fitar a kwanan nan ya nuna cewa mata da 'yan mata na mayar da hankali ne a kan matakan kariya daga daukar ciki fiye da neman kariyar daga kamuwa da HIV.

  Kororon roba na maza na bayar da kariya daga kamuwa da cutuka a lokacin jima'i da hana daukar ciki da kashi 98 cikin dari.

  'Yan kwamitin sun bayar da shawarar cewa, ya kamata masu sayar da kwayoyin hana daukar ciki su rika hada wa kwastominsu da kyautar kororon maza, sannan su rika shawartarsu kan su rika amfani da kororon domin samun kariya daga kwayar cuta mai karya garkuwar jiki.

  Kusan mutum miliyan daya da dubu 700 ne ke dauke da cuta mai karya garkuwar jiki daga cikin al'ummar Tanzania miliyan 60.

 6. Akwai yiwuwar yaƙin basasa ya sake ɓarkewa a Sudan

  ..

  Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Sudan ta Kudu za ta iya komawa yakin basasa saboda jinkirin da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 da ta kawo karshen yakin da ake tayi na tsawon shekaru shida.

  Wakilan Majalisar Dinkin Duniya da su ka ziyarci kasar sun ce wasu muhimman abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar ba a aiwatar da su ba, waɗanda suka kunshi gabatar da sabon kundin tsarin mulki da shirya zabe da shigar da yan tawaye cikin rundunar sojin ƙasar da kuma kafa kotun da za ta hukunta wadanda suka aikata laifuka.

  Tawagar Majalisar Dinkin Duniyar ta hadu da ma'aikatan gwamnati da yan gudun hijira da kuma mutanen da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata - inda har wasu ma suka ce sojojin kasar sun kai musu hari.

  Dubban mutane ne aka kashe haka kuma miliyoyi suka zama ƴan gudun hijira sakamakon yaƙin basasa

 7. Kotun Ƙoli ta yi watsi da umarnin Buhari na bai wa majalisun jiha 'yancin kai

  Buhari

  Kotun Ƙoli a Najeriya ta ayyana umarnin gwamnati da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar na bai wa kotuna da majalisun jiha 'yancin cin gashin kansu a matsayin wadda ta saɓa wa kundin tsarin mulki.

  Buhari ya saka wa dokar mai laƙabin Executive Order 10 hannu ranar 22 ga watan Mayun 2020 da zimmar bai wa ɓangaren shari'a na jihohi 36 da kuma majalisun dokoki 'yancin cin gashin kansu ba tare da sa hannun gwamnatin jiha ba.

  Hakan na nufin babban akanta na ƙasa zai iya tura wa kotunan da majalisun kasonsu na kuɗi kai-tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

  Sai dai shida cikin bakwai na alƙalan kotun sun amince cewa shugaban ƙasar ya wuce ƙarfin ikonsa da kundin tsarin mulkin ya ba shi wajen bayar da umarnin, saboda haka suka ce ta saɓa wa doka.

  A wata shari'ar ta daban a yau Juma'a, kotun mafi girma a ƙasar ta kori ƙarar da gwamnoni suka shigar da gwamnatin tarayya suna neman ta biya su naira biliyan 66 da suka kashe wajen tafiyar da kotunan da kuma manyan ayyuka.

 8. 'Yan Majalisar Dokokin Zamfara 18 sun amince da tsige mataimakin gwamnan jihar

  Zamfara

  Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta jefa uria’r amincewa da tsige Mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau daga kan muƙaminsa da gagarumin rinjaye.

  Yayin wani zama a jiya Alhamis, ‘yan majalisa 18 cikin 22 ne suka amince da ɗaukar matakin yayin da ɗaya tak ya ki amincewa.

  Haka nan, 'yan majalisar sun nemi Alƙalin Alƙalai na Zamfara Mai Shari'a Kulu Aliyu ya kafa kwamatin da zai binciki Mahdi bisa zargin saɓa sashe na 190 da 193 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

  Dangantaka tsakanin mataimakin gwamnan da uban gidansa Gwamna Bello Muhammad Matawalle ta yi tsami tun lokacin ya gwamnan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a bara amma Mahdi ya ci gaba da zama a PDP.

  Honorabul Shamsudden Hassan Bosko, shi ne Shugaban Kwamitin Watsa Labarai na majalisar kuma ya shaida wa Haruna Shehu Tangaza yadda aka yi wannan zaman:

  Latsa hoton ƙasa ku saurari hirar:

  Video content

  Video caption: 'Yan Majalisar Dokokin Zamfara sun amince da tsige mataimakin gwamnan jihar
 9. Ƙyanda ta kashe yara 160 a Afghanistan

  Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutum 160 a Afghanistan sun mutu sanadin cutar kyanda yayin da wasu dubbai na daban suka kamu da cutar a watan jiya.

  Kusan duka wadanda suka kamu yara ne da suke kasa da shekara biyar.

  Kakakin hukumar Christian Lindmaya, ya ce adadin wadanda suka mutun zai iya karuwa cikin sauri a makonni masu zuwa.

  Ya ce matsalar abinci da ake fama da ita a Afghanistan ta kara sanya cutar kama mutane cikin gaggawa.

  Yanzu haka WHO da abokan aikinta na gudanar da aikin rigakafi a yankunan da cutar ta fi kamari.

 10. Sojojin Najeriya sun 'kashe 'yan Boko Haram 120' cikin mako uku

  Sojojin Najeriya

  Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ce sojojinta sun kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da Islamic State West Africa Province (ISWAP) 120 cikin mako uku a arewa maso gabashin ƙasar.

  Manjo Janar Bernard Onyeuko, shugaban sashen hulɗa da jama'a na rundunar, shi ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis.

  Ya ce daga 20 ga watan Janairu zuwa Alhamis ɗin, dakarunsu sun yi nasarar kashe wasu kwamandojin ƙungiyar masu iƙirarin jihadin da kuma wasu mayaƙa 'yan ƙasashen waje da ke haɗa musu ababen fashewa.

  Ya ƙara da cewa mayaƙa 965 da iyalansu sun miƙa wuya ga sojoji a wurare daban-daban na Najeriya.

  Adadin 104 na mutanen da ta kira 'yan ta'adda na ƙungiyar ISWAP ne, yayin da aka ceto mutum 25 daga hannun 'yan bindigar, in ji Mista Onyeuko.

 11. Shugaban Faransa Macron ya ƙi yarda a yi masa gwajin korona a Rasha

  Rasha

  Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ƙi yarda a yi masa gwajin cutar korona a Rasha gabanin ganawarsa da Shugaba Vladimir Putin, kamar yadda Fadar Kremlin ta tabbatar.

  Gwajin ya buƙaci wasu hanyoyi da za a bi waɗanda Faransa ba ta amince da su ba, kamar yadda wata majiya a Faransa ta faɗa wa BBC.

  Lamarin na fitowa ne bayan wasu rahotanni da ke cewa Macron ya ƙi yarda da gwajin ne saboda kar mutanen Rasha su riƙe samfurin ƙwayar halittarsa na DNA.

  A ƙarshe dai shugannin sun gana cikin bai wa juna tazara.

  Ba su musabaha ba kuma sun zauna da tazarar mita huɗu tsakanin juna, yayin da masu sharhi ke cewa ƙila Mista Putin ya yi hakan ne don ya aika wani saƙo na difilomasiyya.

 12. Kwastam ta kama katan 383 na maganin ƙarfin maza a Legas

  Kwastam

  Hukumar kwastam mai hana fasaƙwaurin kayayyaki a Najeriya ta ce ta kama maganin tari na codeine mai darajar naira miliyan 212 da kuma maganin ƙarfin maza.

  Kwantirola na yankin Apapa da ke Jihar Legas, Hammi Swomen, ya ce sun kama kwantena ɗauke da katan 2,875 na maganin tarin da kuma katan 383 na ƙwayar da ke ƙara ƙarfin jima'i, waɗanda aka bayyana da wani suna na daban.

  Haka nan, akwai katan 99 na na'urar niƙa abubuwa a cikin kwantenar.

  "Abin da aka ce an ɗauko shi ne flas na abinci, amma kamar yadda kuke gani a bayana abubuwa ne daban kwatakwata," a cewarsa.

  Ya ƙara da cewa "wannan ba ƙarya ba ce kawai, an shigo da haramtattun abubuwa".

  View more on twitter
 13. CBN zai daina sayar wa bankunan Najeriya kuɗaɗen ƙasar waje

  Kuɗi

  Babban Bankin Najeriya CBN ya ce zai daina sayar wa bankunan kasuwanci na ƙasar kuɗaɗen ƙasar waje nan da ƙarshen shekarar 2022.

  Gwamnan CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya yi jiya Alhamis, yana mai cewa wajibi ne bankunan su fara nemo kuɗaɗen ƙasar wajen da kansu ta hanyar kasuwancin abin da suka fitar zuwa ƙasashen wajen.

  "Lokacin yana zuwa ƙarshe, idan kwastomominka na buƙatar dala miliyan 100 ko miliyan 200, sai ka zo CBN ya ɗebi duk dalolin ya ba ka. (Wannan) na zuwa ƙarshe kafin ko kuma zuwa ƙarshen shekarar nan.," in ji shi.

  "Za mu faɗa musu cewa kar ku sake zuwa wajen CBN (neman dala), ku je ku nemo kuɗaɗenku. Idan kuɗin suka zo mu kuma sai mu sayar muku su a kan ribar kashi 5 cikin 100, ku kuma sai ku sayar wa kwastomomin da ke son dala miliyan 100.

  "Amma dai ku ce za ku ci gaba da zuwa CBN don ya ba ku dala, za mu dakatar da wannan."

  A shekarar 2021 ne babban bankin ya dakatar da sayar wa kamfanonin 'yan kasuwa masu harkar canji kuɗaɗen ƙasar waje, inda ya koma sayar wa bankuna kaɗai.

 14. Moroko za ta bincika dukkan rijiyoyin ƙasar da ba a amfani da su

  Moroko

  Hukumomi a kasar Moroko sun yanke shawarar bibiyar dukkan tsofaffin rijiyoyin da ba a amfani da su a daukacin kasar bayan mutuwar wani yaro da ya faɗa rijiya a lokacin da mahaifinsa ke aikin rijiyar.

  An kwashe kwanaki ana kokarin kubutar da Rayan wanda ya fada rijiya mai zurfin mita 32, amma sai gawarsa aka ceto, abin da ya janyo tashin hankali a ciki da wajen ƙasar.

  Wani jami'i a ma'aikatar ruwan kasar, Abdelaziz Zerouali, ya ce matakin duba tsofaffin rijiyoyin an dauke shi ne domin kauce wa faruwar hakan nan gaba.

  Ya kara da cewa a kowacce shekara ana hukunta dubban 'yan Moroko da ke hakar rijiya ba bisa ka'ida ba, amma duk da haka lamarin ba ya sauki.

 15. Rikicin Ukraine: Najeriya ta jaddada gargaɗi ga 'yan ƙasar mazauna Ukraine

  Najeriya a Ukraine

  Hukumar kula da lamurran 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta sake jaddada kira ga 'yan ƙasar mazauna Ukraine da su "ankare" kuma su "rage tafiye-tafiye" musamman zuwa gabashin ƙasar.

  Kiran na zuwa ne yayin da ake ta nuna fargaba kan yunƙurin Rasha na afka wa maƙociyarta Ukraine, inda ta jibge dakaru 100,000 a kan iyaka.

  Tun a ƙarshen watan Janairu ne Nigerians in Diaspora Commission ta gargaɗi 'yan Najeriya da su kula da tsaron lafiyarsu sannan ta ba su shawara kan yadda za su tuntuɓi ofishin jakadancin ƙasar a Ukraine.

  Rasha ta sha musanta batun cewa tana shirin mamaye maƙociyar tata.

  Tuni Amurka ta umarci 'yan ƙasarta da su fice daga Ukraine ɗin.

  View more on twitter
 16. Ƙarin mutum 48 sun kamu da korona a Najeriya

  Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce ƙarin mutum 48 sun kamu da cutar korona ranar Alhamis.

  Rahoton da hukumar ta wallafa ya ce a jiha tara aka samu sabbin waɗanda suka kamun, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

  Jihohin su ne:

  • Legas-15
  • Cross River-12
  • Abuja-8
  • Plateau-7
  • Ogun-2
  • Abia-1
  • Delta-1
  • Oyo-1
  • Rivers-1

  Zuwa yanzu, jumillar mutum 253,923 ne suka kamu da cutar a Najeriya, sannan ta yi ajalin mutum 3,139.

  View more on twitter
 17. Joe Biden ya umarci Amurkawa su fice daga Ukraine

  Ukraine

  Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga 'yan kasar mazauna Ukraine su gaggauta tattara ya-na-su-ya-na-su kuma su fice daga kasar ba tare da ɓata lokaci ba.

  A wata hira da gidan talbijin na NBC, Mista Biden ya ce: "Amurkawa su fice daga Ukraine nan take, lamurra za su iya dagulewa cikin sauri, domin sojojin Amurkar ba za su samu damar zuwa kwashe su ba."

  Rasha ta sha musanta cewa tana shirin afka wa Ukraine duk da cewa ta jibge dakaru 100,000 a kusa da iyakarta.

  Sai dai ta fara wani atisayen soja tare da maƙociyarta Belarus, sannan Ukraine ta zargi Rashar da rufe mata hanyar kaiwa ga teku.

  Fadar Kremlin ta Rasha ta ce tana so ta "shata layi" don tabbatar da cewa tsohuwar mambanta a tsohuwar Tarayyar Soviet ba ta shiga ƙungiyar tsaro ta Nato.

 18. Assalamu alaikum

  Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-taye, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

  Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi.

  Ku biyo mu!