Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibiyar mu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

  A madadin sauran Abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafaiya.

 2. Mutum 17 ne suka mutu a gobarar Indonesia

  Gobara

  Jami'ai a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 17 a wata mummunar gobara da ta tashi a wani rumbun adana man fetur.

  Wasu mutane da dama ne kuma suka samu raunuka, kamar yadda jami'an suka bayyana.

  Da yammacin jiya Jumma'a ne gobarar ta tashi a rumbunan adana man fetur da ke arewacin birnin, inda har ta kai ga cinye wasu gidaje da ke kusa da wajen kafin a kasheta.

  Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce akwai yara biyu daga cikin waɗanda suka rasa ran nasu a gobarar, sannan kuma har yanzu jami'an ceto na neman ƙarin wasu mutanen da gobarar ta rutsa da su.

 3. Ana ci gaba da gwabza faɗa a kan titunan birnin Bakmut

  yaƙi

  Dakarun sojin Rasha da na Ukraine na ci gaba da gwambza faɗa a kan titunan birnin Bakhmut, to sai dai mataimakin magajin garin ya ce a halin yanzu birnin ya fice daga hannun Rasha.

  Oleksandr Marchenko ya shaida wa BBC cewa fararen hula da ke zaune a garin su kusan 4,000, ba sa samun gas da lantarki da kuma ruwan sha.

  Mista Marchenko ya ce ''Babu ginin da ke garin da yaƙin bai shafa ba, an lalata kusan ilahirin birnin''.

  An kwashe watanni ana fafatawa na Bakhmut, a yayin da dakarun Rasha ke ƙoƙarin ƙwace iko da birnin.

  ''Ana faɗa a garin da ke makwabtaka da birnin, in da a can ma ake fafatawa a kan tinunan garin,'' kamar yadda Mista Marchenko ya bayyana.

  Ƙwace iko da birnin zai zama nasara ta baya-bayan nan da Rasha za ta samu cikin 'yan watannin baya-bayan nan.

  Dubban sojojin Rasha ne suka mutu a ƙoƙarinsu na ƙwace iko da birnin Bakhmut, wanda kafin yaƙin ke da yawan al'umma kusan 75,000.

  Kwamandojin sojin Ukraine sun ce Rasha ta yi asarar sojoji masu yawan gaske a ƙoƙarinsu na ƙwace iko da birnin.

 4. INEC ta sha alwashin magance matsalolin da aka samu da BVAS a zaɓen gwamnoni

  Zaɓe

  Shugaban hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa da 'yan ƙasar cewa za a yi amfani da na'urar BVAS a zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da ke tafe a makon gobe.

  Farfesa Yakubu ya tabbatar da haka ranar Asabar a lokacin ganawa da kwamishinonin hukumar zaɓe na jihohi a shalkwatar hukumar da ke Abuja babban birnin ƙasar.

  Ya ce za a yi amfani da na'urar BVAS a zaɓen, domin kuwa a cewarsa ana sake duba na'urorin domin kauce wa matsalolin da suka bayar a wasu wuraren a zaɓen makon da ya gabata.

  “A ranar zaɓe za a yi amfani da na'urar BVAS domin tantance masu kaɗa ƙuri'a da tattara sakamakon zaɓe,'' in ji Yakubu

  “Aiki da na'urar ta BVAS ya taimaka wajen tsabtace aikin tantance masu zaɓe kamar yadda muka gani a zaɓukan da suka gabata''.

  ''Tun makon da ya gabata, hukumar zaɓe ta ƙara ƙaimi wajen sake duba na'u'rorin domin kauce wa matsalolin da aka samu a wasu wuraren a zaɓen da ya gabata, musamman kan ɗora sakamakon zaɓe a rumbun adana sakamakon da muka tanadar a shafin intanet. Kuma muna da tabbacin cewa na'urorin za su yi aiki kamar yadda ya kamata.''

 5. Gane Mini Hanya tare da gwamnan jihar Jigawa

  Hira da Gwaman jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya, kan nasarar da ɗan takarar jam'iyyarsu ta APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen shugaban Najeriya da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

  Video content

  Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron hirar
 6. Arsenal ta doke Bournemouth 3-2

  Arsenal

  Arsenal ta ci gaba da jan zarenta a gasar Premier bayan da ta doke Bournemouth da ci 3-2 a wasan mako na 26.

  Bournemouth ce ta fara shiga gaban Arsenal a wasan bayan da ɗan wasanta Philip Billing ya zura ƙwallo cikin daƙiƙa 10 da fara wasa.

  Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma Marco Senesi ya ƙara wa Bournemouth ƙwallo ta biyu bayan wata kwana da suka samu.

  To sai dai Arsenal sun yi ta kai hare-hare babu ƙaƙautawa har sai da suka farke ƙwallayen biyu ta hannun Thomas Partey da Ben White.

  A cikin ƙarin lokaci ne kuma Reiss Nelson ya ci wa Arsenal ƙwallo ta uku daga tazarar yadi na 25, wadda ta bai wa ƙungiyar maki uku a wasan.

  Tun da farko Manchester City wadda ke mataki na biyu ta doke Newcastle wadda ke ta biyar da ci biyu ne nema.

  Sauran sakamakon wasannin da aka buga yau.

  • Manchester City 2-0 Newcastle
  • Aston Villa 1-0 Crystal Palace
  • Brigton 4-0 Westham
  • Chelsea 1-0 Leeds
  • Wolves 1-0 Tottenham
 7. Ƙungiyar haɗin kan Afirka ta taya Tinubu murnar cin zaɓe

  generationunlimited

  Shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya taya Bola Tinubu murnar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a makon da ya wuce a Najeriya.

  Tsohon firaministan na Chadi, ya ce duk wani ƙorafi da za a yi a kan zaɓen, to za a iya kallonsa ne ta fuskar dokar zaɓen ƙasar.

  Daga nan ya buƙaci dukkanin sauran jam'iyyun da su rungumi zaman lafiya.

  An ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi ne bayan ya samu kaso kusan 37 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

 8. MDD za ta gana da jami'an Iran kan nukiliyar ƙasar

  Tashar Nukiliyar Iran
  Image caption: Tashar nukiliyar Iran

  Shugaban hukumar da ke sa idon kan makamin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya na shirin ganawa da manyan jami'an Iran, bayan wasu jami'an hukumar sun gano wani makamin a ƙasar.

  Nan gaba a yau ne ake kyautata tsammanin Rafeal Grossi, zai gana da shugaba Iran Ebrahim Ra'isi.

  Jami'an diplomasiyya sun ce Mr Grossi zai ƙara wani yunƙuri na ƙara samar wa ƙasarsa haɗin kai daga masu sanya ido na Majalisar Dinkin Duniya a kan makamin Nukiliya.

  Rahotannin sun ce an gano ɓurɓushin ma'adinin Uranium a ƙarƙashin wata tashar samar da makamin Nukiliya da ke ƙarƙashin ƙasa a Iran.

  Iran ɗin dai ta daɗe tana cewa shirinta na makamin nukiliyar na zaman lafiya ne.

 9. Lafiya Zinariya: Abin da ke janyo warin balaga

  Video content

  Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin

  Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa akwai wasu kwayoyin cuta wadanda sukan sa mutum ya yi warin jiki tamkar wani rubabben kifi.

  Haka kuma wasu cututtuka kamar ciwon hanta da ciwon suga idan suka yi tsanani su ma sukan janyo mutum ya dinga wari kamar warin kifi.

  Yawancin warin da aka fi sani shi ne warin da matasa ke yi idan suka kawo shekarun balaga, wanda aka fi sani da warin balaga.

  Mata masu jiki su ma su kan samu warin jiki.

  Sai dai a jikin mutane akwai wasu wurare da kan yi wari wadanda suka hada da baki da hammata da kuma al'aura.

  Ko da yake likitoci sun bayyana cewa tsaftace wadannan wurare ta hanyar wanke su da kuma cire gashin da ke nan na taimakawa wajen kawar da warin da ake samu.

  Wasu masu wannan matsala dai musamman a tsakanin matasa su kan fuskanci tsangwama a tsakanin tsararrakinsu ko a cikin al'umma.

 10. Ɗan tsohon shugaban ƙasar Najeriya Sani Abacha ya rasu

  Mahmud Sani Abacha

  Ɗaya daga cikin 'yan'yan tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Sani Abacha ya rasu.

  Abdullahi Sani Abacha ya rasu ne lokacin da yake bacci a daren ranar Asabar, kamar yadda 'yar uwarsa Gumsu Sani Abacha ta wallafa a shafinta na Twitter.

  View more on twitter

  Rahotanni sun ce Abdullahi Abacha wanda shi ne na biyun ƙarshe cikin 'ya'yan marigayin, ya mutu ne yana da shekara 36 a duniya.

  Marigayin ya rasu ne a gidansu da ke Abuja babban birnin Najeriya.

 11. INEC za ta dakatar da ma'aikatan da aka kama da sakaci a zaɓen shugaban ƙasa

  INEC

  Hukumar Zaɓen ta Najeriya ta dakatar da dukkan ma'aikatan da aka samu da sakaci lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar asabar da ta gabata 25 ga watan Fabirairu.

  INEC ta ce dukkansu ba za su yi aikin zaɓen da za a yi ba na 'yan majalisar jiha da na gwamnonin a ƙasar da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.

  Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da kwamishinonin zaɓe a ranar Asabar a Abuja.

  "Yayin da muke tunkarar zaɓen gwamna da na 'yan majalisar jiha, dole mu ƙara ƙoƙari domin shawo kan matsalolin da muka fuskanta a zaɓen da ya gabata. 'Yan Najeriya ba za su yarda da wani abu ba bayan wannan.

  "Dukkan ma'aikacin da aka samu da sakaci, ma'aikacin INEC ne ko kuma na wucin gadi ne, cikin harda masu tattara sakamako da turawan zaɓe to ba za mu kyale su yi aikin zaɓen mai zuwa ba.

  "Dole kwamishinonin zaɓe su ɗauki matakan da suka dace a wuraren da aka samu hujjojin cewa an yi abubuwa ba daidai ba," in ji Farfesa Mahmood.

 12. Tarayyar Turai ta ce 'dole a bi wa Falasɗinawa haƙƙinsu'

  BBC

  Shugaban tawagar ƙungiyar Tarayyar Turai da suka kai ziyara yankunan Falasdinawa, ya yi kira da a gurfanar da waɗanda ke da alhakin mummunan harin da aka kai ƙauyen Hawara da ke gabar yamma da kogin Jordan gaban kotu.

  Isra’ilawa ‘yan kama wuri zauna sun ƙona kayayyakin Falasdinawa a kauyen bayan da aka kashe wasu Isra’ilawa biyu ‘yan uwan juna a ƙauyen.

  A ziyarar da ya kai ƙauyen, Sivenkun von Burgsdoff, ya ce dole a tabbatar da an yi wa Falasdinawa adalci.

  Rikici takanin ɓangarorin biyu na ƙara ƙamari a 'yan kwanakin nan.

 13. Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmi ta taya sabon shugaban Najeriya murnar cin zaɓe

  OIC

  Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmi ta taya sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya murnar samun nasara a zaɓen da aka gudanar a ƙasar ranar Asabar da ta gabata.

  Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Malam Hissein Brahim Taha, ya fitar mai ɗauke da sa hannun daranktan yaɗa labaranta Wajdi Sindi, wanda ya ce a madadin shi da mambobin baki ɗaya suna aika saƙon taya murna ga Asuwaju Bola Ahmed Tinubu kan zaɓen da ya lashe.

  Shugaban ya ce zaɓen da 'yan Najeriya suka yi wa shugaban yardarsu ce suka ba shi game da burinsa kan Najeriya na ta zama maɗaukakiya, saboda kwarewar da yake da ita a rayuwa, zai lura da lamurn Najeriya domin tabbatar da ci gabanta da kuma bunƙasarta.

  Ya kuma jaddada muhimmancin da ƙungiyarsu ke da shi a alaƙarta da Najeriya tare da ba da tabbacin ƙarfafa alaƙa ta hanyar haɗin kai ga Najeriya ta ko wanne bangare, musamman ta fanni ci gaban al'umma da kuma yaƙi da 'yan ta'add da masu tsattauran ra'ayi.

  A ƙarshe ya yi wa ƙasar fatan alheri da kuma samun nasara mai ɗorewa.

 14. Dakarun Najeriya sun kashe 'yan bindiga sun ceto mutum 14 da aka sace

  BBC

  Dakarun Najeriya na rukuni na huɗu da wasu dakaru na musamman na bataliya ta 167 sun kashe 'yan bindiga tare da ceto mutu 14 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

  Dakarun waɗanda suka shafe dogon lokaci suna bata kashi da 'yan bindigar a yankin Ƙaramar Hukumar Chikun sun tashi wata maɓoyar 'yan bindigar a lokacin rikicin.

  Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya fitar, yace "yayin wannan samame an ceto mutum 14, da suka haɗa da maza tara da mata biyar. An kai waɗanda aka ceto ɗin wani wuri mai aminci za a yi musu gwaje-gwaje kan a haɗa su da iyalansu."

  A cewarsa a yayin wannan simamen, dakarun sun lalata sansanin 'yan bindiyar da dama an kuma kwato wasu motoci biyu.

 15. Burundi za ta tura sojoji domin yaƙar ƴan tawayen Congo

  BBC

  Burundi ta ce za ta tura kimanin sojoji 100 zuwa Lardin North Kivu a gabashin Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo inda ƙungiyoyin masu riƙe da makamai ke gwabza faɗa.

  Za su haɗu da dakarun gabashin Afirka da suka haɗa da sojoji daga Kenya.

  An tura sojojin a watan Nuwamba sakamakon sake ɓullar ƴan tawayen M23 da ake zargin Rwanda da mara wa baya amma gwamnatin ta musanta.

  Ƴan tawayen na dab da janyewa a ƙarshen watan nan daga yankunan da suka ƙwace.

  A baya dai an gaza cika wa'adin da aka ɗiba, kuma a baya-bayan nan mutanen da ke son sojojin gabashin Afirka su ɗauki wani mataki na murƙushe ƴan tawaye suka gudanar da zanga-zanga a gabashin Congo.

 16. 'Mun tanadi lauyoyinmu tsaf domin tunkarar PDP da LP a kotu'

  j

  Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC ya ce jam'iyyar ta shirya lauyoyinta tsaf waɗanda za su tunkari lauyoyin 'yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP da LP a kotu.

  A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar da Peter Obi suka ƙalubalanci sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Asabar ɗin da ta gabata suna cewa za su kai kotu, wanda ɗan takarar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a cikinsa , kuma INEC ta bayyan shi a matsayin wanda ya lashe shi.

  Da yake tattunawa da manema labari daraktan hulɗa da jama'a kuma kakakin kwamitin Festus Keyamo, ya ce jam'iyyar ta tanadi tawagar manyan lauyoyi na Najeriya wanda suke a shirye domin kare nasarar da Tinubu ya samu lokacin da za su kotu da Atiku da Obi.

  Ya ce "tuni mun haɗa tawagarmu ta lauyoyi. muna da waɗanda su kuma suka zo a raɗin kansu wanda dukkansu za su yi aikin kariyar."

 17. Shugaba Buhari zai tafi Qatar

  presidency

  Shugaban Najeriya muhammadu Buhari zai tafi Qatar a yau Asabar, domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na biyar game da abin da ya shafi kasashe masu ƙarancin ci gaba wanda za a yi a Doha babban birnin Qatar.

  Cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban na musamman kan harkokin yaɗa labarai Garba Shehu ya fitar, ya ce wannan ya biyo bayan saƙon gayyatar da Sarkin Qatar Sheik Tamim bin Hamad al Thani ya turo wa shugaban.

  Taron wanda za a yi tsakanin 5 zuwa 9 gawatan nan an yi masa take ne da: "daga ƙasa mai yiwuwar ci gaba zuwa mai haɓɓaka" ana yi shi ne sau ɗaya cikin shekara 10.

  Wata dama ce ga ƙasashe masu tasowa su samu taimako daga ƙasashen duniya domin samun cimma muraden ƙarni cikin gaggawa kuma su taimaka musu wajen samun ci gaba.

 18. 'Yan Najeriya na ɗarɗar da umarnin kotun ƙoli kan ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗi

  BBC

  A jiya ne kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

  Bisa dalilan da ta ce sun ci karo da kundin tsarin mulki da kuma dokar da ta kafa CBN sashe na 20 na dokar 2007.

  Kotun ta kuma soke matakin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.

  BBC

  A hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a mai shari’a Emmanuel Agim, ya ce sahalewar da Shugaba Buhari ya yi wa CBN na janyo takardun tsofaffin kuɗi ba daidai ba ne.

  Sai dai wasu al'umar ƙasar da BBC ta tattauna da su, sun ce har yanzu ba su gamsu da wannan umarnin ba, ganin cewa kotun ta sha bayar da umarni a baya kuma ba a bi.

  Malam Abba wani mai sayar da kayan marmari a Abuja ya ce "ai sai na ji sanarwa daga CBN ko kuma shugaban ƙasa amma ba yadda za a yi na karɓi waɗan nan kuɗi".

  Wata matashiy cewa ta yi " ina kuɗin suke bayan sun janye duka tsofaffin kuma babu sabbin a ƙasa ai wannan ba ta sauya zani ba ne," in ji matashiyar.

  Duk da kotun ta bayar da wannan umarni amma yan ƙasar suna cikin zullumi na rashin tabbas.

 19. Barka da hatsi

  Buhari Muhammad Fagge ke fatn an tashi lafiya.

  Ku kasance da mu domin kawo muku labarai da rahotanni a wannan yini na yau.

  Labarai masu ban haushi, tausayi, nishaɗi, da dai sauransu.