Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu binmu a nan muka kawo ƙarshen labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labari.

  Abdullahi Bello Diginza ke cewa sai gobe

 2. Real Madrid ta doke Espanyol 3-1 gabanin wasan El Clasico

  Madrid

  Real Madrid ta doke Espanyol da ci 3-1 karon farko da ƙungiyar ta samu nasara cikin wasan La Liga uku da ta buga a baya-bayan nan.

  Espanyol ce ta fara zura ƙwallo a ragar Madrid minti takwas da take wasa.

  To sai dai Vinicius Jr ya farke ƙwallon a minti na 22, sannan kuma Eder Militao ya ƙara ƙwallo ta biyu kafin a je hutun rabin lokaci.

  Sai kuma Marco Asensio da ya ƙara ƙwallo ta uku a cikin karin lokaci kafin tashi daga wasan.

  Real - wadda ke ta biyu a kan teburin La Liga da tazarar maki shida tsakaninta da Barcelona ta ɗaya - za ta kara da Barcelona a wasan hamayyar El Clasico mako mai zuwa.

 3. Angola za ta aike da dakaru zuwa gabashin Kongo

  Dakaru

  Angola na shirin aikawa da sojojinta zuwa gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, kwanaki bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da ta jagoranta ta kasa magance rikicin da ake yi tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati.

  Haka kuma an kai dakarun wanzar da zaman lafiya na yankin gabashin Afirka zuwa gabashin Kongon.

  Ana ci gaba da nuna damuwa kan halin da mazauna yankin za su shiga sakamakon faɗan.

  Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 300,000 ne yaƙin ya raba da muhallansu a lardin arewacin Kivu a watan da ya gabata.

  Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban ƙasar Angola, ta ce za a kai sojojin gabashin Kongo domin taimakawa wajen ƙwato yankunan da 'yan tawayen M23 suka ƙwace.

  Ƙungiyar - wadda rahotonni da yawa ke cewa tana samun goyon bayan ƙasar Rwanda - ta ce za ta fice daga yankuna da ƙauyukan da ke hannunta.

  Gwamnatin Kongo za ta yi maraba da zuwan dakarun na Angola domin taimaka mata wajen yaƙar 'yan tawayen. To sai dai akwai hatsarin hakan ka iya zama yaƙin ƙasa-da-ƙasa.

  Shekaru 20 da suka gabata sojojin ƙasashen Afirka aƙalla takwas sun yaƙi juna a gabashin Kongo mai arzikin ma'adinai, yaƙin da ya yi mummunar illa ga fararen hula mazauna yankin

 4. Zulum ya ziyarci iyalan masuntan da Boko haram ta hallaka

  Babagana Umara Zulum

  Gwaman jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ga iyalan masunta sama da 30 da 'yan Boko Haram suka kashe a ƙauyen Mukdolo.

  A wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa Tuwita, ya ce ya je garin Dikwa inda daga nan ne masintan ke zuwa sana'ar tasu inda mayaƙan Boko Haram suka yi musu kwantan ɓauna, domin jajantawa iyalan mamatan.

  Ƙaramar hukumar Dikwa na daga cikin ƙananan hukumomin da Boko Haram ta mamaye a shekarar 2014 kafin sojoji su kore su tare da ƙwace garin.

  Gwamnan ya gana da iyalan mamatan a fadar Shehun Dikwa Alhaji Ibrahim Ibn Ibrahim El-Kanemi.

  Zulum ya kuma jajanta wa iyalan tare da yin addu'ar neman rahama ga mamatan.

  “A madadin gwamnati da mutane, ina miƙa saƙon ta'aziya ga iyalai da 'yan uwan mamatan waɗanda aka kashe a ƙoƙarinsu na neman na kansu domin ciyar da iyalansu''.

  Sanarwar ta ƙara da cewa gwaman ya bayar da tallafi ga iyalan mamatan a lokacin ziyarar.

  View more on twitter
 5. Abin da ke janyo ƙurajen fuska

  Ƙungiyar ƙwararrun likitocin fata ta Amurka da Canada wato AAD ta ce ana samun wasu mutanen da ke ƙurajen fuska masu girma.

  Inda ta ce cutar na kama wasu a lokacin da suke da shekara 30 da ɗoriya ko 40 da doriya ko ma shekara 50 da wani abun.

  Ƙungiyar ta ƙara da cewa ga masu shekaru hamsin da ke ƙurajen, an fi samun hakan a tsakanin matan da ke cikin shekarun daina jinin al'ada.

  Haka kuma masu binkice sun gano cewa wasu mutane na gadon ƙurajen fuska, musamman waɗanda ke samun ƙurajen a lokacin da suka girma.

  Sai dai mata sun fi maza samun ƙurajen fuska a shekaru 30 zuwa hamsin, a cewar ta.

  Ƙungiyar ta bayyana wasu dalilai da ta ce su ne suke janyo kurajen fuska a wadannan shekaru.

  Waɗanda suka haɗa da rashin daidaito a ƙwayoyin halitta na hormones da shan wasu magungunan asibiti.

  Video content

  Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
 6. Bournemouth ta doke Liverpool da ci 1-0

  Liverpool

  Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bournemouth ta samu nasarar fita daga ukun ƙarshe a kan Teburin Premier bayan da ta doke Liverpool da ci 1-0, nasarar kuma da ta hana Liverpool ɗin shiga sahun huɗun farko a kan teburin.

  Liverpool ta yi rashin nasararsa ne bayan da ta doke Manchester United da ci 7-0 a makon da ya gabata, yayin da ita kuma Bournemouth ta fara wasan a cikin ukun ƙarshe a teburin Premier.

  Rashin tsare gida da kyau ne ya sa Philip Billing ya zura ƙwallo a ragar Liverpool daga tazarar yadi takwas.

  Liverpool ta samu bugun Fenareti a wasan bayan da ƙwallon da Diogo Jota ya sanya wa kai ta taɓa hannun Adam Smith.

  To sai dai Mo Salah - wanda ya zama ɗan wasan da ya fi ci wa Liverpool ƙwallo a gasar Premier inda ya ci ƙwallo ta 129 a makon da ya gabata - ya ɓarar da bugun fenaretin bayan da ya buga ta waje.

 7. Hukumar Civil Defence ta kama ganga 150 ta man fetur da aka yi shirin fitarwa zuwa Kamaru

  Audi

  Hukumar tsaro ta Civil Defence a Najeriya ta ce ta kama ganga 150 na man fetur da aka yi safarsa da niyyar fitarwa daga ƙasar tare da kama mutum biyu da ake zargi

  Babban kwamandan hukumar mai lura da jihar Akwa Ibom Yusuf Imam ne ya bayyana haka ga manema labarai a Uyo babban birnin jihar ranar Asabar.

  Imam ya ce shashen rundunar mai kula da gaɓar teku ne ya yi aiki da bayanan sirrin da ya samu na cewa wasu mutane ɗauke da man fetur a cikin kwale-kwalen katako na kan hanyar zuwa Kamaru.

  Ya ƙara da cewa jami'an hukumar sun kuma ƙwace injina biyar tare da wani inji da ake amfani da shi wajen satar mai.

  “Jami'an hukumarmu da ke kula da bakin teku sun kama mutum biyu tare da ƙwace gangar man fetur 150 a cikin wani kwale-kwalen katako a cikin teku a daidai yankin ƙaramar hukumar Ibeno ta jihar Akwea Ibom'', kamar yadda babban kwamandan jihar ya bayyana.

  Imam ya kuma ƙara jan kunnen masu aikata irin waɗananna laifuka a gabar ruwa - waɗanda ke kawo tarnaki ko yin ƙafar-ungulu ga tattalin arzikin ƙasar - da cewa za su fuskanci mummunan hukunci

 8. Yadda ƴan Bako Haram suka kashe masunta 30 a jihar Borno

  Buhari

  Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan fararen hula akalla 30 da mayakan Boko Haram masu kiran kansu ƴan ƙungiyar IS a yankin Afirka ta yamma wato ISWAP a jihar Borno.

  Lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba 8 ga watan Maris, a yankin ƙaramar hukumar Gamborun Ngala lokacin mutanen da galibi manoma ne da masunta suka fita neman abin da za su ci.

  An kai harin ne kusa da garin Mukdolo wanda ke kusa da wata matattarar ƴan Boko Haram inda mutanen suka shiga don kamun kifi da kuma neman itacen wuta.

  Bayan mutanen kusan talatin da maharan suka harbe akwai waɗanda suka tsira amma da raunukan bindiga da kuma wasu da rahotanni suka ce ba a san inda suke ba har yanzu.

  Latsa nan domin karanta cikakken labarin

 9. Gane Mini Hanya

  Tattaunawa tare da shugaban hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Abdurrasheen Bawa

  Video content

  Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron hirar
 10. Barcelona na fuskantar tuhumar bayar da cin hanci ga alƙalan wasa

  Laporta

  Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona na fuskantar tuhume-tuhume kan biyan wasu kuɗi da ƙungiyar ta yi wa Jose Maria Enriquez Negreira tsohon mataimakin shugaban kwamitin alƙalan wasa.

  A watan da ya gabata aka gano cewa ƙungiyar ta biya euro miliyan 8.m ga Negreira tare da wani kamfani da ya mallaka tsakanin shekarar 2001 zuwa 2018.

  An faɗa wa wata kotu a birnin Barcelona ranar Juma'a cewa ana tuhumar tsoffin jami'an ƙungiyar tare da Negreira da aikata laifin ''cin hanci'' da ''cin amana'' da ƙarya a nasarorin ƙungiyar''

  Ofishin babban mai shigar da ƙara na birnin Barcelona na zargin ƙungiyar tare da tsoffin shugabanninta Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell da hannu a aikata laifukan.

  "Ƙungiyar Barcelona ta ƙulla yarjejeniyar baka da Jose Maria Enriquez Negreira a matsayinsa na mataimakin shugaban kwamitin alƙalan wasa, inda ta riƙa ba shi kuɗi domin ɗaukar matakan da za su riƙa taimaka wa ƙungiyar a hukuncin da alƙalan wasa za su riƙa yankewa a lokacin da ƙungiyar ke wasa'' kamar yadda ofishin babban mai shigar da ƙarar ya bayyana.

  A watan da ya gabata shugaban gasar La Liga Javier Tebas ya ce dole shugaban ƙungiyar Barcelona na yanzu Joan Laporta ya sauka daga muƙaminsa matuƙar ya kasa yin bayani game da biyan kuɗaɗen da ake zargin ƙungiyar da aikatawa.

  Laporta ya mayar da martani da cewa ''ko da ya sauka daga muƙaminsa mista Tebas ba zai samu abinda yake so ba''.

  Tuhumar na zuwa ne kwana uku bayan da Laporta ya kafe cewa ƙungiyarsa ba ta taɓa sayen alƙalin wasa ba.

  "Bari na gaya muku gaskiyar magana Barca ba ta taɓa sayen alƙalan wasa ba, kuma ba ta da niyyar sayen alƙalan wasa, ba za ta taɓa ba'', kamar yadda shugaban ƙungiyar ya bayyana ranara Talata.

 11. An zaɓi Li Qiang a matsayin sabon firaministan China

  LI and XI

  Majalisar dokokin China ta zaɓi mutumin da shugaban ƙasar Xi Jinping ya tsayar a matsayin firaministan ƙasar.

  Li Qiang - wanda tsohon shugaban jam'iyyar kwamunisanci ne na birnin Shanghai - a yanzu zai jagoranci gwamnatin ƙasar bayan maye gurbin Li Keqiang wanda ya sauka kwanan nan.

  Mista Li mai shekara 63 ya samu ƙuri'un duka 'yan majalisar jam'iyyar su fiye da 2,900

  Ana yi wa mista Li - wanda babban aminin shugaban ƙasar ne - kallon jajirtacce, kuma za a ɗora masa aikin inganta tattalin arzikin ƙasar da ke fama da tarin ƙalubale.

  Ana sa ran bayyana sunayen sabbin ministocin ƙasar ranar Lahadi

  Mista Li - wanda a yanzu shi ne na biyu mafi girman muƙami a ƙasar - ya samu ƙuri'a 2,936, 'yan majalisa uku ne kawai ba su zaɓe shi ba, yayin da 'yan majalisa takwas ba su halarci zaman ba.

  Ya kuma sha alwashin yin aiki da kundin tsarin mulkin ƙasar, da kuma yin aiki tuƙuru domin inganta ci gaban ƙasar, da dimokraɗiyyarta.

 12. PDP ta karyata janye takarar Yakubu Lado Danmarke a Katsina

  Jam'iyya PDP

  Yayin da zaɓen da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisa dpokokin jihohi ke ƙara ƙaratowa a baya-bayan nan ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Katsina sun zargi wasu da ke neman yi musu bi-ta-da ƙulli ta hanyar yaɗa labaran ƙarya da ke cewa wai ɗan takararsu na gwamna Yakubu Lado Danmarke ya janye daga takarar.

  Wata takarda da aka yi ta yaɗa wa a shafukan sada zumunta, ta yi iƙirarin cewa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar ya janye daga takarar tasa

  Ahmad Inuwa Fagam ya tattauna da kwared Imrana Nass dakartan yaɗa labaran ɗan takarar gwaman na jam’iyyar PDP wanda ya musanta batun wata takarda da ke kara-kaina a shafukan sada zumunta

  Video content

  Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron hirar
 13. Ɗage zaɓen gwamnoni ka iya shafar aikin ƙidayar 2023 – NPC

  shugaban kidaya

  Shugaban hukumar Kidayar jama'a ta Najeriya Nasir Isa Kwarra ya ce ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi da ka yi a ƙasar ka iya shafar aikin ƙidayar jama'ar da aka shirya gudanarwa cikin watan Maris

  Mista Nasir ya yi wannan iƙiƙari ne a lokacin da yake ganawa da wakilan asusun ƙidayar jama'a na Majalisar Dinkin Duniya a Abuja babban birnin ƙasar.

  Hukumar zaɓen Najeriya dai ta ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi da aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris zuwa ranar 18 ga watan Maris.

  shugaban hukumar ƙidayar ya shaida wa manema labarai cewa duk da kawo yanzu ba a saka tartibiyar ranar fara aikin ba, zai tuntuɓi shugaban ƙasar Muhammadu Buhari domin saka ranar da za a fara gudanar da wannan aiki.

  A nata ɓangaren wakiliyar asusun Majalisar Dinkin Duniya kan ƙidayar jama'a Ms Ulla Mueller, ta alƙawarta bayar da tallafin asusun domin tabbatar da gudanar da aikin kamar yadda aka tsara.

 14. Fiye da 'yan ci-rani 1,000 aka kuɓutar cikin dare guda a tekun Tunisiya

  "yan ci-rani

  Fiye da 'yan ci-rani 1,000 ne aka kuɓutar cikin dare guda a ƙoƙarinsu na shiga Turai a gaɓar tekun Tunisiya kamar yadda jami'an kula da tuekun suka bayyana.

  A watan da ya gabata ne shugaban Tunisiya Kais Saied ya bayar da umarni ga jami'an ƙasar da su ɗauki matakin gaggawa domin magance turarar 'yan ci-ranin da ba su da cikakkun takardun izini bi ta Tunisiya, yana mai cewa hakan ka iya kawo matsala ga al'ummar ƙasar.

  A wata sanarwa da masu tsaron tekun duka fitar, sun ce suna kama 'yan ci-rani kimanin 1008 a cikin dare guda a kan iyakar tekun ƙasar da Italiya.

  Mafiya yawan 'yan ci-ranin sun fito ne daga ƙasashen Afirka baƙar fata, sai dai masu gadin tekun sun ce cikin har da 'yan Tunisiya 54.

  Mai magana da yawun hukumar ya ce aƙalla ƙananan jiragen ruwa 25 suka hana tsallakawa cikin daren.

  'Yan Afirka 14 ne suka mutu a makon da ya gabata lokacin da jirage biyu da suke ciki suka nutse a tekun Bahar Rum.

 15. An faɗaɗa zanga-zangar adawa da ƙarin shekarun ritaya a Faransa

  zanga-zanga

  Faransa ta ƙara faɗaɗa gagarumar zanga-zanga, kan matakin gwamnatin na ƙara wa’adin yin ritaya ga ma’aikata da shekara biyu.

  Ƙungiyar ma’aikata da jam’iyyun adawa na fatan jami’an tsaro za su sako mutanen da suka kama ranar Alhamis lokacin da sama da mutum miliyan ɗaya suka yi zanga-zanga.

  Gangamin - na ƙin amincewa da shekaru 64 ne maimakon 62 da aka saba yin ritaya daga aiki a ƙasar – ya janyo toshewar birin Paris wanda ya cika da cinkoson manyan motocin dakon mai da na ɗaukar kaya.

  Shugaba Macron da gwamnatinsa sun kafe cewa dole sai ‘yan majalisa sun amince da dokar, kuma a cewarsu sai nan gaba ne ‘yan ƙasar za su gane alfanun dokar.

 16. Assalamu alaikum

  Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wana rana ta Asabar, ku kasance tare da mu domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a sassan duniya.

  Za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da sauran maƙwabtan ƙasashe. Haka kuma kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa.

  Abdullahi Bello Diginza ne zai kasance da ku a daidai wannan lokaci.