Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

  1. Nan muka zo karshen shirin sai kuma ranar Asabar

  2. Damben da Dan Sama'ila ya buge Shagon Shamsu

    A ranar Lahadi suka kara a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

    Video content

    Video caption: Damben na su ya zo da takaddama
  3. United za ta karbi bakuncin City a League Cup

    Manchester City za ta zioyarci Old Trafford domin karawa da Manchester United a gasar League Cup wasannin zagaye na hudu a ranar Laraba.

    A cikin watan Satumba kungiyoyin biyu sun kara a gasar Premier a Old Trafford, inda City ta ci United 2-1.

    United wadda ta sha kashi a hannun Chelsea 4-0 a gasar Premier a ranal Lahadi, za ta yi wasa na Hudu a cikin kwanaki tara, bayan da ta tashi babu ci da Liverpool a ranar Litinin.

    League Cup
  4. Sanches ya lashe kyautar matashin dan kwallon Turai

    Dan wasan Bayern Munich, Renato Sanches, ya lashe kyautar matashin dan kwallon kafa da ya fi yin fice a nahiyar Turai.

    Hakan ne ya sa Sanches ya doke abokin takararsa matashin dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford.

    Sanches ya bi sahun Wayne Rooney da Raheem Sterling da Lionel Messi da kuma Sergio Aguero a matsayin wadan da suka lashe kyautar suna da kasa da shekara 21.

    European Player
  5. De Bruyne ba zai buga karawa da United ba

    Dan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne, ba zai buga karawar da kungiyar za ta fafata da Manchester United a gasar League Cup ba, sakamakon rauni da yake jinya.

    Shi ma Pablo Zableta ba zai samu damar buga wasan ba, saboda raunin da ya yi, amma kyaftin din kungiyar Vincent Kompany ya murmure zai kuma yi wasan na hamayya.

    League Cup
  6. Carlos Alberto na Brazil ya mutu

    Fitatcen dan wasan Brazil, Carlos Alberto, ya rasu yana da shekara 72. 

     Dan kwallon ya yi wasanninsa a Santos ta Brazil inda ya buga mata fafatawa 400 daga nan ya koma Amurka da murza leda.

     A lokacin da ya yi kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Brazil da ta ci Italiya 4-1 a gasar cin kofin duniya a shekarar 1970, a kuma lokacin ne kasar ta ci kofin na uku, hakan ya sa aka bar mata kofin mai suna Jules Rimet ya zama na Brazil na din-din-din. 

    Brazil
  7. Gasar League Cup da za a buga

    • Arsenal da Reading Liverpool 
    •  Bristol City da Hull City
    •  Leeds United da Norwich City 
    •  Newcastle United da Preston North End
  8. Audu Mai Kaba ya koma kociyan Akwa Unitedb

    Audu Mai Kaba ya cimma yarjejeniyar horar da kungiyar kwallon kafa ta Akwa United zuwa Shekaru biyu.

    Mai Kaba wanda ya ja ragamar Wikki Tourist zuwa mataki na uku a kan teburin Firimiyar Nigeria da aka kamma, bai saka hannu a kan kwantiragin ba tukunna.

    Kociyan wanda ya yi mataimakin kociya a kungiyoyin da suke buga Firimiya sau da dama, ya horar da Kano Pillars da Enyimba International.

    Akwa United ta garin Uyo ta kare a mataki na 14 a kan teburin Firimiyar kasar da aka kammala da maki 47.

    Audu Mai Kaba
  9. Barkanmu da saduwa a labarin wasanni kai tsaye

    Wannan shafin ne da zai kawo muku bayanai da sharhi kan wasannin da suke wakana a sassan duniya.

    League Cup Liverpool vs Tottenham