Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin

  Sai ku sake tarawa a ranar Asabar

 2. Man City 1-0 Middlesbrough

  Sergio Aguero

 3. Hertha ta koma matsayi na uku a teburin Bundesliga

  Hertha 3 da Borussia Monchengladbach 0

  Tsohon dan wasan Chelsea, Salomon Kalou, ya ci kwallaye uku a karawar da Hertha Berling ta doke Borussia Monchengladbach da ci 3-0 a gasar Bundesliga da suka yi a ranar Asabar. 

  Da wannan sakamakon Hertha ta koma mataki na uku a kan teburin gasar ta Jamus, bayan da ta yi wasanni 10.  

  Bundesliga
 4. An fitar da Konta daga gasar China

  Elina Svitolina ta kai wasan karshe a gasar kwararru da ake yi Zhuhai ta China.

  Svitolina ta samu nasarar doke Johanna Konta ne a ranar Asabar da ci 2-6 6-1 6-4.   

  Tennis
 5. Burnley 2-0 Crystal Palace

  Johann Berg Gudmundsson

 6. Bournemouth 1-0 Sunderland

  Dan Gosling (a minti na11)

 7. Labarai da dumi-dumiMurray ya dare mataki na daya a Tennis

  Andy Murray ya hau mataki na daya a jerin wadanda suke kan gaba a iya kwallon tennis a duniya, bayan da Milos Raonic ya janye daga wasan da ya kamata su fafata a ranar Asabar sakamakon raunin da ya yi.

  Murray ya karbi matakin ne a wajen Novak Djokovic.

 8. Manchester City da Middlesbrough

  'Yan wasan da za a fara buga tamaula da su

  City 11: Bravo, Zabaleta, Stones, Kolarov, Clichy, Fernandinho, Gundogan, Silva, De Bruyne, Navas, Aguero

  Masu jiran kar-ta-kwana: Caballero, Kompany, Maffeo, Garcia, Nolito, Iheanacho. Sane

  EPL

  Boro 11: Valdes, Barragan, Chambers, Gibson, Friend, Traore, De Roon, Clayton, Forshaw, Downing, Negredo 

  Masu jiran kar-ta-kwana: Da Silva, Bernardo, Leadbitter, Fischer, Guzan, Stuani, Nugent

  EPL
 9. Sunan kofin League Cup na Ingila zai koma Carabao

  Manchester City ce ta lashe kofin bara

  Kofin League Cup na kawllon kafa na Ingila (EFL), zai samu sabon suna daga kaka mai zuwa ta 2017-18, inda za a rika kiransa kofin Carabao, a karkashin wata yarjejeniya da aka kulla ta daukar nauyin gasar.

  Hukumar gasar cin kofin ta kulla yarjejeniyar tsawon shekara uku a kan fam miliyan 18 da kamfanin lemon gwangwani na kara kuzari na kasar Thailand.

  League Cup
 10. West Ham United da Stoke City

  An kai jami'an tsaro da dama filin wasa na West Ham United. West Ham za ta kara da Stoke City a gasar Premier wasan mako na 11. Ana ta samun yamutsi a filin wasan West Ham, na baya-bayan ne shi ne wanda kungiyar ta ci Chelsea 2-1 a League. Bayan da aka tashi daga wasan aka yi yamutsi. 

  EPL
  EPL
 11. Ibrahimovich na kanfar kwallaye

  Bayan da Zlatan Ibrahimovich ya dunga cin kwallo a wasanni hudu da ya fara buga wa Manchester United a jere, yanzu yana fama da kanfar cin su a raga. 

  Dan wasan ya ci kwallo daya tilo a wasanni 11 da ya yi wa United a yanzu. 

  Ga wasannin da ya ci wa United kwallaye

  • Leicester 1 - 2 Man Utd ya ci daya 
  • Bournemouth 1 - 3 Man Utd ya ci daya 
  • Man Utd 2 - 0 Southampton ya ci biyu 
  • Man Utd 1 - 2 Man City ya ci daya 
  • Man Utd 1 - 0 Zorya ya ci daya  
  Premier
 12. Za a buga wasan karshe a Federation Cup na Nigeria

  Ranar Lahadi a Legas, Nigeria

  Za a buga wasan karshe na Federation Cup a wasan maza tsakanin IfeanyiUbah da Nasarawa United. 

  A wasan mata kuwa Bayelsa Queens da Rivers Angel ne za su kece raini. 

  Za a yi dukkan wasannin ne a ranar Lahadi da yammaci a jihar Legas a Nigeria.

 13. Gudunmawarku a BBC Hausa Facebook

  Musa Usman Dutsinma: Middelesbroug kada ku bamu kunya, mu 'yan adawa so muke Man City ta kwashi kashinta a hannu, up Arsenal

  Mubarak Sani Kankia: A karawar da za a yi tsakanin Manchester City da Middlesbrough Allah ya sa a tashi babu ci. 

  Sa'idu Gagiyo Katamma: Wasa tsakanin Manchester City da Midlesbrough dai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

 14. Konta ta kai wasan daf da karshe a China

  Johanna Konta ta kai wasan daf da karshe a gasar kwararru da ake yi a Zhuhai, China, bayan da ta doke Caroline Garcia da ci 6-2 da 6-2. 

  Konta mai shekara 25 za ta fafata ne da Elina Svitolina. Daya wasa na biyu shi ne tsakanin Petra Kvitova da Zhang Shuai.         

  Tennis
 15. Sakamakon wasannin damben jihar Kano

  Manyan wasanni hudu aka yi a ranar Juma'a

  Ali Kanin Bello daga Arewa ya yi nasarar doke Garkuwan Mai Caji daga Kudu a turmin farko. 

  Bahagon Bahagon Sanin Kurna daga Arewa ya buge Dan Ali Shagon Bata Isarka daga Kudu. 

  Audu Bahago Guramada da Shagon Mai Caji daga Kudu aka yi canjaras.

  Dogon Kyallu Guramada da Bahagon Isya Na Wukari suka tashi wasa babu kisa. 

  Damben Gargajiya
 16. Murray na daf da hawa mataki na daya a Tennis

   Da zarar Andy Murray ya ci wasa daya a gasar kwallon tennis ta kwararru da ake yi a Paris zai dare matsayi na daya a jerin wadanda suke kan gaba a iya wasan a duniya. 

  Wanda yake mataki na daya Novak Djokovic ya sha kashi a hannun Marin Cilic da ci 6-4 7-6 (7-2) a wasan daf da na kusa da na karshe da suka yi a ranar Jumma'a. 

  A kuma ranar ce Murray ya doke Tomas Berdych 7-6 (11-9) 7-5, zai kuma fafata da Milos Raonic a ranar Asabar a wasan daf da karshe da karfe 4:30 na yamma agogon Nigeria. 15:30  

  Tennis
 17. Wasu damben da aka yi a farkon watan Oktoba a Abuja

  Damben gargajiya da aka yi a Dei-Dei da ke Abuja, Nigeria

  Video content

  Video caption: Wasu damben gargajiya da aka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria
 18. Bundesliga wasannin mako na 10

  • Freiburg da VfL Wolfsburg          
  • Hamburger da Borussia Dortmund          
  • Bayer 04 Leverkusen da SV Darmstadt  
  • Bayern Munich da Hoffenheim
  • FC Ingolstadt 04 da FC Augsburg
  • Eintracht Frankfurt da FC Koln 
 19. Sakamakon gasar damben mota ta Minna

  Shagon Sama'ila daga Kudu ya kai wasan zagayen gaba, bayan da Dogon Gobiraje Guramada bai halarci filin wasa ba. 

  Shagon Dirago daga Arewa ya samu nasara ne a kan Shagon Audu Gurumada, bayan da suka yi turmi uku babu kisa, aka yi kuri'a Shagon Audu ya yi nasara. 

  Da yammacin Asabar za a raba jadawalin wasannin zagaye na biyu. Ana yin wasannin gasar damben da za a ci mota ta matasa a filin wasa na U.K Bello Art and Theater da ke Minna jihar Niger, Nigeria.    

  Damben gargajiya
 20. Gasar Serie A wasannin mako na 12

  • Torino da Cagliari Calcio
  • Napoli da Lazio