Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin.

 2. Za ku iya kada kuri'ar ku

  'Yan takarar dan kwallon BBC na Afirka a 2016 

  • Sadio Mane
  • Riyad Mahrez
  • Andre Ayew
  • Pierre-Emerick Aubameyang
  • Yaya Toure

  An fara yin zabe, za ku iya yin naku ta nan  

  Click here to make your choice.

 3. Yaya Toure

  Mai shekara 33 ya ci kyauta ta biyu ta gwarzon dan kwallon kafa ta Afirka a bara, ko zai iya lashe ta uku? 

  Koda yake ya dan samu sabani da kociyan Manchester City, Pep Guardiola, amma yanzu ana ganin komai ya wuce tun da ya bayar da hakuri. 

  AFOTY
 4. Ku zabe ni - Toure

  Gwarzon dan kwallon kafa na BBC a bana

  Dangarama Yaya Toure

  Sau biyu Yaya Toure yana zama Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC, kuma sau hudu yana lashe makamanciyarta ta Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF).

  Don haka ganin sunansa a jerin wadanda aka ware bana ba abin mamaki ba ne.

  Ko da yake sau 23 kacal ya buga wasa a 2016, saka sunansa a cikin jerin ya nuna irin matsayinsa a fagen kwallon kafa a Afirka.

  Kuma duk da cewa wasannin da ya buga ba su da yawa, tasirinsa ba ya misaltuwa.

  A watan Fabrairu ya daga wa Manchester City Kofin Gasar League ta Ingila - inda ya fasa raga da wani bugun fanariti mai muhimmanci wanda ya ba su damar cin Liverpool a wasan karshe.

  Ku karanta cikakken bayani kan rawar da Toure yake takawa

 5. Pierre-Emerick Aubameyang

  Mai shekara 27, yana taka rawar gani a Borussia Dortmund tun lokacin da ya koma can a shekarar 2013.

  Ya kuma ci wa kungiyar kwallaye 25 a kakar wasan 2015/16.

  AFOTY
 6. Andre Ayew

   Andre Ayew, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da BBC ta karrama a 2011, ya koma murza leda ga West Hama daga Swansea City kan kudi fam miliyan 20.5.

  AFOTY
 7. Ku zabe ni - Aubameyang

  Gwarzon kwalon Afirka na BC a bana

   Dodon Raga Pierre Emerick-Aubameyang

  Tun da ya soma buga kwallo a Borussia Dortmund, dan wasan gaba Pierre Emerick-Aubameyang na ci gaba da burge masoya kwallo.

  Dan takarar na Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2016 na da shekaru 27, kuma ya taso ne a kasar Faransa. 

  Yana cikin wadanda kungiyar kwallon kafar AC Milan ke nema, amma kuma har yanzu bai buga masu kwallo ba, bayan da ya je Dion na Faransa a matsayin aro.

  A wani wasan sada zumunta wanda shi ne wasanshi na farko a shekarar 2008, lokacin yana da shekaru 18, ya burge manyan 'yan wasan da ke cikin tawagarsa.

  Karanta cikakken bayani kan rawar da Aubameyang ke takawa

 8. Ku zabe ni Gwarzon kwallon Afrika - Ayew

  Na BBC a bana

  Gwanin rike kwallo Andre Ayew

  Dan kwallon tawagar Ghana, Andrew Ayew ya nuna cewa shi ba mutum ba ne wanda gwiwarsa za ta yi sanyi a duk lokacin da ya samu kansa a cikin mawuyacin hali.

  A watan Janairu an tilasta wa Ayew, mai shekara 26, buga kwallo ba a wurin da ya saba taka leda ba, lokacin da sabon kociyan Swansea, Francisco Guidolin, ya karbi aiki bayan da aka sallami Garry Monk, Amma ya bai wa marada kunya.

  Kwarewarsa da kwazon da yake nunawa da kwallayen da yake ci, sun nuna karara irin burin da yake son cimmawa, kuma sun taimaka wajen hana Swansea rikitowa daga Gasar Premier.

  Ayew ya ci kwallo biyu daga cikinukun da suka doke Liverpool, wanda daga karshe aka tabbatar da cewar Swansea za ta ci gaba da zama a Gasar Premier bara.

  Saboda haka ba a yi mamaki ba da ya lashe kyautar bakon dan kwallon da ya fi taka rawar-gani a Swansea bara.

 9. Mahrez ya taka rawar-gani

  • Ya lashe gasar Premier ta Ingila
  • Shi aka zaba dan wasan da ya fi kowa a gasar
  • Yana cikin 'yan wasa 30 da ke takarar Ballon d'Or na Fifa

  Ko zai iya lashe gasar BBC ta bana?

 10. Ku zabe ni gwarzon kwallon Afirka - Riyad Mahrez

  Mahrez

  Dan kwallon Algeria da Leicester City Riyad Mahrez ya taka rawar gani a kakar bana.

  "Za ka iya tunanin cewa maganadisu ne a kafarsa idan yana murza leda."

  Wadannan su ne kalaman da Madjid, abokin dan wasan da ke takarar zama Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2016, Riyad Mahrez, ya yi wajen bayyana irin gogewar dan wasan.

  Madjid, wanda abokin Mahrez ne tun suna kanana, ya kara da cewa "A da mukan yi fada da juna domin kawai mu tabbatar Riyad ya buga wa bangarenmu wasa."

  Ya tuna lokacin da suke buga kwallo tare suna yara a garin Beni Snous da ke arewa maso yammacin Algeria.

  Karanta cikakken bayani kan rawar da Mahrez ke takawa

 11. Kamaru da Zambia su tashi wasa 1-1

  Wasan shiga gasar cin kofin duniya

  WCQ
 12. Sadio Mane

  Sadio Mane ya koma Liverpool kan kudi fam miliyan 34 a matsayin dan wasan da ya fi tsada daga Afirka. Mai shekara 24 ya ci kwallaye shida a wasanni 11 da ya buga wa Liverpool a bana.

  Afoy
 13. Ku zabe ni Sadio Mane

  Gwarzon dan kwallon BBC a bana

  Kakar wasanni ta bana ta yi kyau sosai ga dan wasan tawagar Senegal, Sadio Mane.

  Hazikin dan wasan na gaba zai iya taka leda a ko wanne bangare na filin wasa - a gefe, ko a baya, ko a gaba - sannan an wayi gari ya shiga sahun 'yan wasan Gasar Premier da suka fi barazana ga ragar abokan hamayya, kuma daya daga cikin 'yan wasan Afirka da suka fi kwazo.

  Gudun dan wasan, da iya rike kwallo, da saurin tunani, su kan jefa tsoro a zukatan abokan hamayyarsa sun kuma dasa kaunarsa a zukatan 'yan kallo sun kuma jawo masa yabo daga masharhanta.

  Yana da dabaru ba iyaka ga shi kuma kaifi daya a bakin raga, inda yake iya karbar kwallo ya kuma samar da dama ga abokan wasanshi.

  Mady Toure, wanda ya kafa cibiyar koyar da kwallon kafa ta Academie Generation Foot inda Mane ya fara daukar darasin kwallo, ya yi amanna cewa dan wasan komai-da-ruwanka ne.

 14. Za mu fara gabatar da 'yan takara

 15. Gwarzon dan kwallon BBC na bana

  Hasashen da kuke yi a BBC Hausa Facebook

  Tahir Imam Mahmoud: Mane,Iwuobi, Ihenacho,Yaya Toure. da kuma Ahmad Musa.

  falsefalseSani S Rafi: Ba shakka 'yan wasan zasu iya hadawa da irin su RIYAD MAHAREZ, PERRE-EMRIC AUBAMEYANG, AHMED MUSA, YAYA TOURE da kuma MIKEL OBI.  

 16. Nigeria 3 da Algeria 1

 17. Nigeria 2 Algeria 1

  Nigeria ta sauya dan kwallo

  Ahmed Musa ya canji Alex Iwobi

 18. Gwarzon dan kwallon kafa na BBC na bana

  Abedi Pele ne ya fara lashe kyautar dan kwallon kafar da BBC ta karrama a shekarar 1992, yayin da Yaya Toure ya ci kyautar bara. 

  Shin wanene zai lashe kyautar bana? 

  Daf muke da sanar da sunayen fitattun 'yan kwallon Afirka guda biyar da za ku zabi guda daya da ya fi yin fice a bana.  

  Aforty
 19. Nigeria 2 da Algeria 1

  Nabil Bentaleb ne ya ci kwallon 

  WCQ