Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Manchester United 1 - 1 Arsenal
 2. Atletico Madrid da Real Madrid
 3. Tennis: Murray ya kai wasan daf da karshe a ATP Tour
 4. Gasar kofin Afirka ta Mata da za a fara a Kamaru
 5. Dambe: Ali Kanin Bello da Mai Takwasara

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Gasar kwallon Tennis

Andy Murray da Raonic, Djoko da Nishikori

Andy Murray ne ya yin a daya a rukunin da yake ciki a gasar kwallon tennis ta kwararru da ake yi a Landan, ya kuma kai was an daf da karshe bayan da ya doke Stan Wawrinka

Murray zai fafata da Milos Raonic – wanda ya doke a gasar Wimbledon domin samun wanda zai kai was an karshe.

Djoko zai kara da Kei Nishikori a daya wasan na daf da karshe.

Tennis
Getty Images

FULL-TIME Man United 1- 1 Arsenal

GOAL Man United 1-1 Arsenal

Olivier Giroud

Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Umar B Modibbo WuroBiriji Gabadai gabadai Manchester United! Muna fatan  United za ta yi wuju wuju da Arsenal! Ko mu yi wa Mourinho ihuuuuuu! Up Manchester United!

Mubarak Sani Kankia Wasa tsakanin Manchester united da Arsenal Allah kaba mai rabo sa'a. Up Mourinho

Umar Alassan Kamaru agaskiya wannan wasa zai matukar dauke hankalin yan kallon domin ganin yadda Wenger yake da takaicin Mourinho tun lokacin da yake Chelsea

Deportivo La Coruna 2 - 3 Sevilla FC

La Liga wasan mako na 12

La Liga
Getty Images

Man United 1-0 Arsenal

Olivier Giroud ya shiga filin wasa inda ya canji Mohamed Elneny. Ko zai iya farke kwallon da United ta ci Arsenal?

GOAL Man United 1 da Arsenal 0

Juan Mata

Man United 0 da Arsenal 0

United ta yi canji

Wayne Rooney ya shida fili Anthony Martial ya fita daga wasan

Man United 0 vs Arsenal 0

EPL
AP

HALF-TIME

Manchester United 0 da Arsenal 0

Damben gargajiya a jihar Legas

Mai Takwasara da Ali Kanin Bello

A ranar Asabar da yamma ake sa ran dambatawa tsakanin Dogo Mai Takwasara Guramada da Ali Kanin Bello daga Arewa a gidan damben Aminu Goje da ke Alaba Rago a jihar Legas, Nigeria.

'Yan damben biyu za su kara ne a ranar Asabar da kuma Lahadi, duk wanda ya samu nasara ya karbi babur na hawa.

DAmben gargajiya
BBC

Man United 0 da Arsenal 0

KICK-OFF

An take wasa Man United da Arsenal

Jamus Bundesliga mako na 11

 • VfL Wolfsburg da Schalke 04      
 • Borussia Monchengladbach da FC Koln 
 • FSV Mainz 05 da SC Freiburg      
 • FC Augsburg da Hertha Berlin    
 • SV Darmstadt 98 da FC Ingolstadt 04       
 • BV Borussia Dortmund da Bayern Munich

Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Man United da Arsenal

Rukaiyya Usman Fari Jebuwa Tabbas juma’ar da za ta yi kyau tun daga laraba ake gane ta dan haka kungiyar kwallon kafa ta Man United za ta doke Arsenal da ci 2 da 1 up Paul Pogba..

Muh'd Tasi'u Abdullahi Wan nan wasa zai matukar dau hankalin yan kallo duba da yadda za a fafatane tsakanin manyan masu horas wa da kuma manyan club a Ingila, amma a nawa hassashe Arsenal ce zata mamaye wasa sannan kuma za ta iya samun nasara.

Ibrahim Sabo Kofa Wasa tsakanin Arsenal da Man United tarihi ne zai maimaita kansa tun da Arsene Wenger  bai taba samun nasaraba akan murinho ba kuma za a ci Arsenal daci 3 da banza upp Pogba Mata Rooney

Shu'aibu Idris Kofar-fada Bulangu Hahahaha! Lallai yau akwai karan batta, amma bi sa dukkan alamu za muyi wuju wuju da Manchester United kamar da ci 2-0. Up Gunners

Prince Yau Adamu Bulkachuwa Gabadai gabadai 'yan dugwi dugwi samarin Wenger yau ina so ku nanawa Mourinho cewa dabara ce ke daure kaya ba igiyaba up Gunners

Man United Arsenal

'Yan wasan da za su buga wa Arsenal

Arsenal: Cech, Jenkinson, Mustafi, Koscielny, Monreal, Coquelin, Elneny, Walcott, Ozil, Ramsey, Sanchez. Subs: Gibbs, Gabriel, Giroud, Ospina, Oxlade-Chamberlain, Iwobi, Xhaka.  

EPL
BBC Sport

Man United da Arsenal

'Yan wasan da za su taka-leda a United

Man Utd: de Gea, Valencia, Jones, Rojo, Darmian, Carrick, Ander Herrera, Mata, Pogba, Martial, Rashford. Subs: Depay, Rooney, Lingard, Blind, Young, Romero, Schneiderlin.

Alkalin wasa: Andre Marriner (West Midlands)

EPL
BBC Sport

Italiya Serie A mako na 13

 • Chievo Verona da Cagliari Calcio               
 • Udinese Calcio da Napoli             
 • Juventus da Pescara

Manchester United da Arsenal

Watakila magoya bayan United su dan dara

Arsene Wenger kan yi rashin nasara a duk wasan farko da zai yi da sabon kociyan Manchester United a gasar Premier, ya yi rashin nasara a hannun Ferguson a Nuwambar 1996 da Moyes Nowambar 2013 da Van Gaal a Nuwambar 2014 ga shi zai kara da Mourinho a Nuwambar 2016.

EPL
Reuters

Yadda teburin Premier yake bayan wasanni 11

EPL
BBC

Gasar cin kofin Afirka ta mata

Kamaru ke karbar bauncin gasar bana

 • Kamaru da Masar            
 • Afirka ta Kudu da Zimbabwe

&

Spanish La Liga mako na 12

 • Deportivo La Coruna da Sevilla FC            
 • FC Barcelona da Malaga CF         
 • SD Eibar da Celta de Vigo             
 • Atletico de Madrid da Real Madrid

La Liga
Getty Images

Gasar cin kofin Premier mako na 12

 • Manchester United da Arsenal
 • Everton da Swansea City     
 • Southampton da Liverpool  
 • Sunderland da Hull City       
 • Crystal Palace da Manchester City         
 • Watford da Leicester City    
 • Stoke City da Bournemouth      
 • Tottenham da West Ham United

Wasan da za mu kawo muku kai tsaye a BBC Hausa

A shirinmu na sharhi da bayanai kan gasar cin kofin Premier a ranar Asabar 19 ga watan Nuwamba, za mu kawo muku daya daga cikin wasannin mako na 12 a karawar da za a yi tsakanin Manchester United da Arsenal. Za mu fara gabatar da shirin da karfe 1:15 na rana agogon Nigeria da Nijar. Za ku iya bayar da gudunmawarku a lokacin da ake gabatar da shirin kai tsaye a BBC Hausa Facebook ko ta BBC Hausa Google+.  

EPL
Getty Images

Barkanmu da saduwa a cikin shirin labaran wasanni kai tsaye