Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

  1. A nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a mako mai zuwa

  2. An yi wa Shamsu Kanin Emi Ajo a Kano

    Damben gargajiya

    A ranar Asabar a gidan damben Danliti da ke Ado Bayero Square a jihar Kano, Nigeria aka yi wa dan damben Arewa Shamsu Kanin Emi Ajo.

    Damben gargajiya
  3. Swansea 5 - 4 Crystal Palace

  4. Swansea 3 - 4 Crystal Palace

  5. Wasu sakamakon wasannin Premier

    •  Hull 1-1 West Brom 
    •  Leicester 1-2 Middlesbrough 
    •  Swansea 3-3 Crystal Palace  
  6. Kamaru ta kai wasan daf da karshe

    Gasar cin kofin Afirka ta kwallon kafar mata

    Tawagar kwallon kafa ta Kamaru ta kai wasan daf da karshe a gasar kwallon kafa ta mata ta cin kofin nahiyar Afirka, bayan da ta ci ta Zimbabwe 2-0 a karawar da suka yi a ranar Juma'a.

    Da wannan sakamakon Kamaru ta hada maki tara ta kuma jagoranci rukunin farko, bayan da ta ci Masar 2-0 ta kuma doke Afirka ta Kudu daya mai ban haushi.

    A wasa na biyu na rukunin farko, ita ma Afirka ta Kudu ta kai wasan daf da karshe, bayan da ta casa Masar da ci 5-0.

    Afirka ta Kudu ta hada maki hudu, bayan da ta yi canjaras babu ci da Zimbabwe, ta kuma sha kashi a hannun Kamaru da ci daya mai ban haushi.

    CAF
  7. Liverpool 1 - 0 Sunderland

    Origi ne ya ci kwallon

  8. Yadda ake gara wasa Liverpool 0 - 0 Sunderland

    EPL
  9. Shin ko raunin da Coutinho ya yi zai yi muni?

    Liverpool 0 - 0 Sunderland

    EPL
  10. Gasar kwallon kafa ta mata ta cin kofin nahiyar Afirka

    Wasan karshe na cikin rukuni na biyu

    • Mali vs Ghana 
    • Kenya vs Nigeria
  11. Real Madrid 2 - 1 Sporting Gijon

    Gasar La Liga mako na 13

    La Liga
  12. Labarai da dumi-dumiHamilton ya lashe tseren Abu Dhabi

    Gasar tseren motoci ta Abu Dhabi

     1 ) Hamilton 2) Rosberg 3) Ricciardo 4) Raikkonen 5) Vettel 6) Verstappen 7) Hulkenberg 8) Perez 9) Alonso 10) Massa  

    Gasar tseren motoci
  13. Chelsea vs Tottenham

    Chelsea za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan gasar Premier na hamayya, inda Chelsea ke fatan cin wasa na bakwai a jere.

     A bara Chelsea ce ta hana Tottenham damar daukar kofin Premier da Leicester City ta lashe, inda suka kara a daya daga cikin wasa mai zafi da hatsaniya. 

    Rabon da Tottenham ta ci Chelsea a Stamford Bridge tun 1990, kuma Antonio Conte ya umarci 'yan wasansa da su saka kaimi domin su ci gaba da zama a matsayi na daya a kan teburin Premier.       

    EPL
  14. Kwallo na biyu da Aguero ya ci Burnley

    EPL
  15. Burnley 1 vs Manchester City 2

    Sergio Aguero ne ya ci kwallon kuma ta biyu a wasan

  16. Kompany zai yi jinyar sati shida

    Mai horar da Manchester City, Pep Guardiola, ya ce kyaftin din kungiyar Vincent Kompany zai yi jinya sati shida, sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa.

    Komapany dan kwallon tawagar Belgium ya yi rauni ne a karawar da City ta ci Crystal Palace 2-1 a wasan Premier da suka yi a ranar Asabar.

    Dan kwallon na fama da yin jinya tun fara kakar wasan bana, kuma wasanni biyu kacal ya buga wa City a fafatawar da ta yi.

    Wannan kuma shi ne karo na 35 da Komapany ke yin rauni a wurare dabam-dabam tun komawarsa City daga Hamburg a shekarar 2008.

    EPL
  17. FA ba za ta hukunta Rooney kan buguwa da giya ba

    Hukumar kwallon kafar Ingila ba za ta hukunta kyaftin din kasar Wayne Rooney ba bayan da aka wallafa wasu hotunasa ya bugu da giya lokacin da suka tafi kasashen waje domin yin wasa.

    Dan wasan na Manchester United ya nemi gafara saboda daukar hotunan "da ba su dace ba" kwana daya bayan wasan cancantar neman shiga gasar cin kofin duniya da suka doke Scotland.

    Wasu jiga-jigan hukumar FA sun tabbatar wa Rooney, mai shekara 31, cewa ba za a hukunta shi ba.

    EPL
  18. Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Liverpool vs Sunderland

    Shu'aibu Idris Kofar-fada Bulangu: Toh ga dukkan alamu dai a wannan wasa Liverpool za ta ci Sunderland, to amma dai mu magoya bayan Arsenal fatan mu dai shi ne wasa ya juya liverpool baya Sunderland ta samu nasara a kansu. Up Arsenal.

     Abubakar Sa'ad Ganye: A Gaskiya indai Liverpool din dana sani ne na yanzu to kuwa Sunderland su shirya karban ruwan kwallaye a ragar su kawai, Fadan da ba ruwanka dadin kallo. 

    Bashar Kansila Maitukunya Dirin: Ni mai goyon bayan Sundaland ne, gaskiya ina da ja Liverpool ba za ta iya komai dani ba, domin yanzu na dawo kan ganiya ta wasa biyu a jere ina nasara, ina sa rai zan ci Liverpool.

    Jamilu Musa Sabonlayi: Hahaha, Yau sundaland za ku gane shayi ruwa ne, domin kuwa ba za mu raga maku ba up liverpool 4-1.

  19. Yadda kididdigar wasan take

    Burnley 1 vs Manchester City 1

    EPL
  20. An je hutun rabin lokaci

    Burnley 1-1 Man City