Nan muka kawo karshen shirin da fatan za a tara a mako mai zuwa
El Clasico: Barcelona vs Real Madrid
Kyaftin din Barcelona Iniesta yana kan benci, bayan da ya dawo dga jinyar makonni shida da ya yi.
APCopyright: AP
Blatter zai ji sakamakon karar da ya daukaka
A ranar Litinin kotun daukaka kara ta wasanni ta duniya za ta yanke hukunci a kan karar da tsohon shugaban FIFA, Sepp Blatter, ya daukaka a gabanta.
Sepp Blatter ya daukaka karar ne yana neman a yi watsi da hukuncin da kwamitin da'a na hukumar FIFA ya zartar, wanda ya hana shi shiga sabgogin tamaula har tsawon shekara shida.
Tun farko kwamitin na da'a ya haramta wa Blatter da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini, shiga harkokin wasanni har tsawon shekara takwas, daga baya kwamitin daukaka kara na FIFA ya rage hukuncin zuwa shekara shida.
An samu tsofaffin shugabannin na FIFA da laifin karya ka'idar aiki, inda aka biya Platini ladan aiki na kudi fam miliyan daya da dubu dari uku.
Dukkansu sun musanta aikata ba daidai ba a lokacin da suka gudanar da aikinsu a FIFA.
Wannan ce gasa ta 12 da ake yi a wasan cin kofin afirka a kwallon mata, kuma Nigeria ta ci kofin sau tara a 1991, 1995, 1998, 2000, 2002, 2004, 2006, 2010, 2014
Kamaru ba ta taba daukar kofin ba, ta kuma je wasan karshe sau uku, inda Nigeria ce ta doke ta a dukkan wasannin uku a 1991, 2004, 2014.
Super SportsCopyright: Super Sports
Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook
Man City 1 -0 Chelsea
Shu'aibu Idris Kofar-fada Bulangu: Duk da dai ni magoyin bayan Arsenal ne, fatana a wannan wasa shine kungiyar kwallon kafa ta Man City ta yi wuju wuju da Chelsea kamar da ci 2-0. Up Gunners.
Muttawakkil Gambo Doko: Toh mu dai fatanmu wannan wasan a yi canjaras mai ci ko maras ci, Up Gunners
Mubarak Sani Kankia Fadan da ba ruwan ka yafi dadin kallo. Amma ni nafiso aci Chelsea. Up Manchester United.
El Clasico: Watakila Iniesta ya buga karawar
Gasar La Liga wasan mako na 14
Watakila kyaftin din Barcelona, Andres Iniesta, ya murmure daga raunin da ya yi, ya kuma fara wasa a karawar da kungiyar za ta yi da Real Madrid a ranar Asabar.
Iniesta mai shekara 32, bai buga wa Barcelona wasanni bakwai ba, sakamakon jinya da yake yi, kuma daga cikinsu wasanni uku kungiyar ta ci.
Barcelona mai rike da kofin La Liga tana mataki na biyu a kan teburi, inda Real Madrid, wadda ke matsayi na daya, ta ba ta tazarar maki shida.
EPACopyright: EPA
Man City 0 - 0 Chelsea
Yadda wasan ke tafiya
BBC SportCopyright: BBC Sport
Man City 0 - 0 Chelsea
Kungiyoyin biyu suna taka rawa a Ettihad
PACopyright: PA
Nico Rosberg ya yi ritaya daga tseren motoci
Zakaran tseren motocin Formula 1 na duniya Nico Rosberg ya sanar da cewa ya yi ritaya nan take.
Dan tseren dan kasar Jamus mai shekara 31 ya ci babbar gasarsa ta farko ranar Lahadi, bayan ya doke Lewis Hamilton.
Rosberg ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa "Na kai kololuwar ganiyata don haka wannan matakin da na dauka shi ne ya dace."
Rosberg ya lashe manyan gasar tseren motoci tara cikin 21 da aka yi a bana, inda ya doke Hamilton wanda sau uku yana zama zakaran tseren.
AFPCopyright: AFP
El Clasico: Barcelona da Real Madrid
Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 14 na gasar La Liga--karon battar da ake yi wa lakabi da El Clasico.
Bayan da aka buga wasannin mako na 13 a gasar cin kofin La Liga ta bana, Real Madrid ce ke kan gaba a teburi da maki 33, yayin da Barcelona ke biye da ita da maki 27.
A cikin karawa 13 da kungiyoyin biyu suka yi a baya a gasar ta La Liga, a wasanni uku ne Barcelona ta yi rashin nasara.
Real Madrid ta ci Barcelona a karawa biyar a wasanni tara da suka yi gumurzu a gasa dabam-dabam.
Lionel Messi na Barcelona shi ne dan kwallon da ya fi cin kwallo a karawar ta El Clasico inda ya ci 21, daga ciki ya ci hudu a wasanni biyar da suka kara.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Ronaldo da Mourinho sun kauce wa biyan haraji
Rahotanni sun nuna cewa fitaccen dan wasa Real Madrid, Cristiano Ronaldo da wasu 'yan wasan sun zille wa biyan harajin miliyoyin daloli, ta hanyar boye kudadensu a kasashen da ake amfani da su don kauce wa biyan harajin.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar Der Spiegel ta kasar Jamus ya gano hakan ne ta hanyar bayanan da aka kwarmata, cikin su har da takardun hakika na kwangilolin da 'yan wasan suka sanya wa hannu da bayanan sirrinsu da kuma sakonnin imel.
Lauyoyin Ronaldo sun ce hukumomin da ke karbar haraji na Spain sun yi bincike sosai kan takardun harajinsa kuma ba su gano wata badakala ba.
Sauran masu ruwa-da-tsaki a harkokin wasannin da ake zargi da zille wa biyan harajin sun hada da kocin Manchester United, Jose Mourinho, wanda kamar Ronaldo, yake amfani da wani wakili mai suna Jorge Mendes wajen ajiye kudinsa a kasashen da ake kauce wa biyan harajin.
Kamfanin Mr Mendes, Gestifute, ya ce Mourinho ya cika dukkan sharudan biyan haraji na kasashen Birtaniya da Spain.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Gasar Premier mako na 14
Wasannin da za a buga a ranar Asabar
Man City vs Chelsea
Crystal Palace vs Southampton
Stoke vs Burnley
Sunderland vs Leicester
Tottenham vs Swansea
West Brom vs Watford
West Ham vs Arsenal
Wasan karshe a cin kofin Afirka a kwallon kafar mata
Kamaru da Nigeria
Yadda Nigeria ta kai wasan karshe:
Wasannin cikin rukuni: Ta doke Mali 6-1; Canjaras da Ghana 1-1; ta yi nasara a kan Kenya 4-0.
Wasan daf da karshe: Ta ci Afirka ta Kudu 1-0.
Yadda Kamaru ta kai wasan karshe:
Wasannin cikin rukuni: Ta ci Masara 2-0; ta doke Afirka ta Kudu 1-0; ta yi nasara a kan Zimbabwe 2-0.
Wasan daf da karshe: Ta yi nasara a kan Ghana 1-0.
Alex Grimm FifaCopyright: Alex Grimm Fifa
Shirin gasar Premier kai tsaye
Wanda muke kawo muku ta radio a BBC Hausa
A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier. Wannan makon za mu kawo muku daya daga cikin wasannin sati na 14 a karawar da za a yi tsakanin Manchester City da Chelsea.
Za mu fara gabatar da shirin da karfe 1:15 na rana agogon Nigeria da Nijar. Za kuma ku iya bayar da gudunmawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta a BBC Hausa Facebook da kuma gugul filas.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Jama'a barkanmu da saduwa a cikin shirin labarin wasanni kai tsaye
Rahoto kai-tsaye
Daga Mohammed Abdu
time_stated_uk
Nan muka kawo karshen shirin da fatan za a tara a mako mai zuwa
El Clasico: Barcelona vs Real Madrid
Kyaftin din Barcelona Iniesta yana kan benci, bayan da ya dawo dga jinyar makonni shida da ya yi.
Blatter zai ji sakamakon karar da ya daukaka
A ranar Litinin kotun daukaka kara ta wasanni ta duniya za ta yanke hukunci a kan karar da tsohon shugaban FIFA, Sepp Blatter, ya daukaka a gabanta.
Sepp Blatter ya daukaka karar ne yana neman a yi watsi da hukuncin da kwamitin da'a na hukumar FIFA ya zartar, wanda ya hana shi shiga sabgogin tamaula har tsawon shekara shida.
Tun farko kwamitin na da'a ya haramta wa Blatter da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini, shiga harkokin wasanni har tsawon shekara takwas, daga baya kwamitin daukaka kara na FIFA ya rage hukuncin zuwa shekara shida.
An samu tsofaffin shugabannin na FIFA da laifin karya ka'idar aiki, inda aka biya Platini ladan aiki na kudi fam miliyan daya da dubu dari uku.
Dukkansu sun musanta aikata ba daidai ba a lokacin da suka gudanar da aikinsu a FIFA.
El Clasico: Barcelona vs Real Madrid
'Yan wasan Barcelona: Ter Stegen, Roberto, Pique, Mascherano, Alba, Rakitic, Busquets, Gomes, Messi, Suarez, Neymar.
'Yan wasan Real Madrid: Navas, Carvajal, Varane, Ramos, Marcelo, Modric, Kovacic, Vazquez, Isco, Ronaldo, Benzema.
Man City 1-3 Chelsea
Hazard
Crystal Palace vs Southampton
'Yan wasan da za su taka karawar
Kwallon kafa ta mata wasan karshe
Kamaru vs Nigeria
Shin ko Kamaru za ta doke Nigeria