Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Watford 3-2 Everton
 2. Leicester City da Manchester City
 3. Real Madrid da Deportivo La Coruna
 4. Wasan damben gargajiya

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

A nan muka kawo karshen shirin na labaran wasannin kai tsaye

Wasannin Premier na ranar Lahadi

 • Chelsea v West Bromwich Albion 
 • Manchester United v Tottenham Hotspur 
 • Southampton v Middlesbrough 
 • Liverpool v West Ham United   

Leicester City da Manchester City

'Yan wasan da za su taka-leda

Premier
BBC Sport

Yadda teburin gasar Premier yake

Premier
BBC Sport

Sakamakon wasannin mako na 15 gasar Premier

Premier
Getty Images

Gasar Premier wasannin mako na 15

Premier
BBC Sport

Real Madrid da Deportivo

Real Madrid za ta karbi bakun cin Deportivo La Coruna a wasan mako na 15 a gasar La Liga a ranar Lahadi.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburi da maki 34, yayin da Deportivo ke matsayi na 16 da 13.

La Liga
Getty Images

Swansea 3-0 Sunderland

Yadda ake murza-leda

Premier
BBC Sport

GOAL Burnley 3-1 Bournemouth

Hull 2-2 Crystal Palace

Yadda ake gara wasa

Premier
BBC Sport

GOAL Hull City 2-2 Crystal Palace

Adama Diomande na Hull City

GOAL Hull City 1-2 Crystal Palace

Wilfried Zaha na Crystal Palace

GOAL Swansea 2-0 Sunderland

Fernando Llorente a minti na 54

Damben: Garkuwan Shagon Alabo da Mahaukaci Teacher

Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu ne ya buge Mahaukaci Teacher daga Arewa a turmi na biyu a damben da suka yi a Dei-Dei a Abuja, Nigeria. 

A turmi na biyu Garkuwan Shagon Alabo ya yi nasara

Fifa ta dakatar da wasu jami'an kwallon Afirka

Fifa ta dakatar da tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afrika ta Kudu Kirsten Nematandani, daga shiga harkokin wasanni tsawon shekara biyar, saboda an same shi da laifin kin bayyana almundahana da kuma kin bayar da hadin kai ga bincike.

Laifin ya danganci wasu wasannin sada zumunta ne guda uku na kasa da kasa da aka yi a Afrika ta Kudu kafin gasar cin kofin duniya ta 2010.

Haka kuma FIfa ta haramta wa wani tsohon jami'in hukumar kwallon Zimbabwe Jonathan Musavengana, da tsohon kocin Togo Banna Tchanile, shiga harkokin wasanni tsawon rayuwarsu sakamakon laifin cin hanci da rashawa.

Mista Musavengana yana da hannu ne a wata cuwa-cuwa da aka biya 'yan wasan kasar Zimbabwe kudi domin su bari a ci su, a wasanni a yayin wani rangadi na Asia a 2009.

African Football
Google

GOAL Hull 1-1 Crystal Palace

Christian Benteke na Crystal Palace

GOAL Swansea 1-0 Sunderland

Gylfi Sigurdsson a minti na 51

Watakila Mikel Obi ya bar Chelsea a Janairu

Hira da aka yi da Mikel kan yadda ba ya buga wa Chelsea wasanni

Yawan matan da ke wasanni ya karu a duniya

Yawan matan da ke wasanni akai akai a duniya ya kai yawan da bai taba kaiwa ba zuwa miliyan bakwai da dubu dari biyu da goma kamar yadda wani bincike ya nuna.

Binciken na kungiyar Sport England, ya gano cewa yawan matan da suke shiga wasanni ya karu da 250,000 tun lokacin da kungiyar ta kaddamar da shirinta na wayar da kan mata su rika shiga wasanni (This Girl Can) a 2014.

Bambancin yawan maza da matan da suke wasanni ya ragu kamar yadda nazarin ya nuna zuwa miliyan daya da dubu dari biyar da hamsin.

Haka kuma gaba daya an samu karin mutanen da ke wasanni akai akai maza da mata har 229,400, idan aka kwatanta da shekarar da ta wuce.

Women in sports
Mehr

GOAL Arsenal 2-1 Stoke City

Ozil

GOAL - Arsenal 1-1 Stoke

Theo Walcott

Arsenal 0-1 Stoke City

Yadda ake gara wasa

Premier
BBC Sport

GOAL - Arsenal 0-1 Stoke

Charlie Adam, a bugun fenariti

'Yan kasan teburin Premier bayan mako 14

Premier
BBC Sport

GOAL - Hull 1-0 Crystal Palace

Robert Snodgrass a bugun fenariti

Wenger: Za mu rike Sanchez da Ozil

Arsenal za ta yi duk abin da za ta iya domin ganin 'yan wasanta na gaba Alexis Sanchez da Mesut Ozil ba su bar kungiyar ba in ji kocinta Arsene Wengeri.

Ana rade radin 'yan wasan biyu za su koma wasu kungiyoyin, kasancewar saura wata 18 kwantiraginsu ya kare da Arsenal din kungiyar na tattaunawa da su kan sabuwar yarjejeniya.

A bana Sanchez dan kasar Chile ya ci wa Arsenal kwallo 11, kuma yana kan-kan-kan da Diego Costa a matsayin wadanda suka fi cin kwallo a Premier.

Premier
Rex Features

GOAL - Burnley 2-0 Bournemouth

ward

Watford ta doke Everton 3-2

Yadda aka murza leda

Premier
BBC Sport

Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Shu'aibu Idris Kofar-fada Bulangu: Gaba dai gaba dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, tabbas mu magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta arsenal a wannan wasa da zamu buga da Stoke City muna da kwarin gwiwar cewa sai mun yi musu ruwan kwallaye. Up Sanchez 

Umar Tijjani Yusufari: Allah ya sa a tashi babu kare bin damo, yadda kulob din Chelsea zai ba su tazara mai yawa idan suka doke West Brom a ranar Lahadi up Blues 

Murtala Ibrahim Zangon Daura: Ina fatan yan Stoke City za su lallasa Arsenal domin mukara tabbatarwa da yan Arsenal cewar yan kofi haram ne. 

Umar Alassan Kamaru: A gaskiya wannan wasa tsakanin kungiyar arsenal da Stoke City zai dauki hankali yan kallo musamman yadda arsenal take taka rawar gani a wasaninta dan haka zamuce Arsenal zata dauke Stoke City.

Barcelona ta ci Osasuna 3-0

Barcelona ta doke Osasuna da ci 3-0 a gasar La Liga wasan mako na 15 da suka kara a ranar Asabar.

Luis Suarez ne ya ci kwallon farko sannan Lionel Messi ya ci guda biyu a fafatawar.

La Liga
Getty Images

GOAL Osasuna 0-3 Barcelona 3

Lionel Messi

Osasuna 0-2 Barcelona

Lionel Messi

La Liga
Getty Images

"Alonso ba zai koma tuka marsandi ba"

Fernando Alonso ba zai maye gurbin Nico Rosberg matukin motar marsandi wanda ya lashe tseren motoci ta 2016 ya kuma yi ritaya. 

Manajan Alonso, Flavio Briatore ne ya sanar da hakan, bayan da shugaban tseren motoci na kamfanin marsandi Toto Wolff ya ce a ranar Litinin zai tuntubi Alonso idan zai amince ya karbi aikin. 

 Alonso dan kasar Jamus yana da yarjejeniyar aiki da kamfanin McLaren wadda za ta kammala a 2017.  

Formula 1
Getty Images

Wasannin gasar cin kofin Premier mako na 15

 •  Watford da Everton 
 •  Arsenal da Stoke City 
 • Burnley da Bournemouth 
 • Hull da Crystal Palace 
 • Swansea da Sunderland 
 • Leicester da Man City

Sharhin gasar cin kofin Premier a BBC Hausa radiyo

Arsenal da Stoke City

A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier kai tsaye da harshen Hausa. 

Wannan makon za mu kawo muku daya daga cikin wasannin sati na 15 ne a karawar da za a yi tsakanin Arsenal da Stoke City. 

Za mu fara gabatar da shirin da karfe 3:30 agogon Nigeria da Niger. 

Za kuma ku iya bayar da gudun mawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta a BBC Hausa Facebook da kuma gugul filas. 

Premier
Getty Images

Jama'a barkanmu da saduwa a cikin shirin labaran wasanni kai tsaye