Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin

 2. Ko mai Mahrez zai ce bayan da ya lashe kyautar?

  Riyad Mahrez on his award win: "Kyautar tana da mahimmaci a waje na, kuma kyauata ce mai girma ga dan kwallon Afirka kuma nayi murna dana lashe ta

  "A koda yaushe yana da kyau idan ka lashe kyauat kuma a matsayina na dan kwallon Afirka kyauat ce mai mahimmanci."

  Ko mai ya sa ka lashe kyautar: "Ina jin saboda na ci kofin Prewmier mun kuma taka rawa gani kakar bana ta yi mana kyau.

  "Ina tunanin 'yan Algeria za suyi alfahari dani daga Afirka na fito kuma suna alfahari dani kuma ina gode musu da dukkan iyalai na

  "Ina godiya da magoya baya, ina mai matukar murna da na karbi kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na bana."

 3. Riyad Mahrez

  Zakaran gwarzon kwallon kafa na Afirka na BBC na bana

  Kai ne magaoya bayan tamauala suka zaba a matsayin gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na bana. Yaya ka ji cewar kai ne ka lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na 2016?   

  Video content

  Video caption: Zakaran kwallon Afirka na BBC na 2016
 4. An bai wa Mahrez kyautar gwarzon BBC ta bana

   Kociyan Leicester Claudio Ranieri ya bai wa Riyad Mahrez kyauatar gwarzon BBC ta bana.  

 5. Riyad Maharez ne gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana

 6. Wa zai karbi kyautar bana tsakanin Mahrez da Mane?

  Afoty
 7. Daf muke da sanar da zakaran bana

  Peter Okwoche ne zai sanar da gwarzon dan kwallon Afirka na bana a BBC Focus on Africa a talabijin da radiyo.

 8. Mahrez ko Mane, wa zai lashe kyauatar bana?

  Saura 'yan takara biyu suka rage, sin wanene zai lashe kyautar bana, tsakanin Mahrez ko Mane?

  Afoty
 9. Wasu karin kyautukan da za a lashe

  Asisat Oshoala, 'yar tawagar kwallon kafar Nigeria ta mata mai murza-leda a Arsenal, wadda ta ci lambar yabo a matsayin wadda ta fi cin kwallaye a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Kamaru a bana, tana daga cikin 'yan takarar kyautar macen da ta fi yin fice a fagen tamaula a Afirka ta hukumar kwallon kafar nahiyar.

  Za a sanar da wadda ta lashe kyautar a ranar 5 ga watan Janairu a Abuja, Nigeria.

  Afoty
 10. Banda kyautra gwarzon BBC akwai wani bikin kuma

  Bayan kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na bana da BBC za ta karrama, da akwai kyau kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya ta Ballon d'Or. 

  Kyautar wadda hadaka ce tsakanin hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa da mujallar Faransa mai wallafa harkokin tamaula. 

  Tuni kuma suka raba gari inda a bana mujallar za ta bayyana gwarzon bana a fagen tamaula a duniya, inda 'yan jaridu daga fadin duniya ke yin zabe. Za a sanar da gwarzon bana da karfe 19:00 agogon GMT, kuma takara ce tsakanin Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi wanda ake hasashen daya ne zai lashe kyautar.

 11. Muhawarar da kuke tafkwa a BBC Hausa Facebook

  Usman Useey Unguwar Chabano: Allah ya bai wa mai rabo sa'a. 

  Nasir Ussein: Muna yi wa duk wanda ya yi nasarar samun na daya murna. 

  Abubakar Muhammad Abdul: Ni dai ina Goyon bayan Riyad Mahrez. 

  Aliyu Magaji Marabar Musawa: Dukkansu sun cancanta dan haka duk wanda Allah ya bai wa a cikinsu daidai ne.   

 12. Andre Ayew ya kuskure shekarar nan

  A watan Agusta West Ham ta kashe makudan kudaden da ba ta taba kashe irinsu ba a baya wajen sayen dan Ghana Andre Ayew daga Swansea, a kan kudi fam miliyan ashirin da dubu dari biyar.

  Ficen da Ayew ya yi a fagen buga kwallo, da kuma jimillar kwallaye 12 da ya ci a wasanni 35 a tsakanin shekarar 2015 da 2016, sun sanya shi yin fice a karshen kakar wasanni, inda ya samu kyautar gwarzon sabbin 'yan wasa a watan Mayu.

  Video content

  Video caption: Andre Ayew
 13. Yaya Toure bai samu damar lashe kyauata ta uku ba

  Toure dai shi ya sake lashe kofi a 2016 - a karo na 17 a rayuwarsa ta kwallo - lokacin da ya daga Kofin Gasar League ta Ingila da Manchester City, bayan ya sha kwallo a fanariti da suka yi nasarar kan Liverpool a wasan karshe.

  A wannan shekarar ne dan wasan tsakiyar mai shekaru 33 ya ce ya kawo kololuwar rayuwarsa a kwallo, duk da ya ce har yanzu da sauransa, kuma sanya shi da aka yi cikin wadanda za su buga wasannin shekara mai zuwa ya tabbatar da hakan.

  Video content

  Video caption: Yaya Toure
 14. Pierre-Emerick Aubameyang

  Dan wasan gaba gaban kuma dan kasar Gabon Aubameyangna da fitattun kwallaye 26 da ya sha wa kulob dinsa Borussia Dortmund a 2016.

  Aubameyang ya zamo dan Afirka na farko da aka bayyana a matsayin Gwarzon dan wasan shekarar, kuma dan Gabon na farko da ya lashe Gwarzon Dan Kwallon shekara na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka.

  Video content

  Video caption: Pierre Emerick Aubameyang
 15. Ban kwana ga 'yan wasa ukun da aka fitar

  Daga cikin 'yan wasa biyar da ke yin takara an fitar da guda uku saura biyu suka rage, bari mu yi waiwaye kan dalilan da ya sa aka zabi Pierre-Emerick Aubameyang, Yaya Toure and Andre Ayew suka kasance a cikin jerin 'yan takara tun farko.

 16. Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

  Rukaiyya Usman Fari Jebuwa: Gaba dai gaba dai Riyad Mahrez muna yi maka fatan alheri.. 

  Jafaru Garba: Mahrez ne gwani na a gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana  

 17. Shin waye zai lashe kyautar bana ta BBC?

  An fara lashe kyautar a shekarar 1991 kuma Abedi Pele na Ghana wanda a lokacin ke murza-leda a Merseille ta Faransa ne ya fara karbar kyautar.

  Aforty 2016
 18. Yanzu saura 'yan wasa biyu da za a bayyana gwarzon BBC na 2016

  Yanzu kuma 'yan wasa biyu da suka rage masu yin takarar gwarzon dan kwallon kafa na BBC na Afirka na 2016 sun hada da Sadio Mane da Riyad Maharez.

  Shin a cikinsu wa zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na 2016 ne?