
Bayanai kan wasannin da suke gudana a sassan duniya
Stoke 2-2 Leicester City
Got a TV Licence?
Find out moreTakaitacce
- Bojan da Allen sun ci Leicester
- An bai wa Vardy jan kati a karawa da Stoke City
- Negredo ya ci Swansea kwallaye biyu
- An jima West Brom da Man United
- Crystal Palace 0-1 Chelsea
Rahoto kai-tsaye
Daga Mohammed Abdu
time_stated_uk
Nan muka kawo karshen shirin.
West Brom da Manchester United
'Yan wasan da za su taka-leda
Sakamakon wasannin gasar Premier mako na 17
An yi watsi da shirin Fifa na kara kasashe a gasar kofin duniya
Hadakar manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai ta yi watsi da shirin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino, na kara yawan kasashen gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026, daga 32 zuwa 48.
Shugaban hadakar, ko kungiyar ta ECA, tsohon dan wasan Jamus Karl-Heinz Rummenigge, ya ce duk wani abu da za a yi a game da gasar kamata ya yi, a mayar da hankali kan wasan.
Amma ba siyasa ko kasuwanci ba, don haka bai kamata a kara yawan masu shiga gasar ba.
Kungiyar ta ce daman tuni yawan wasan da ake yi a shekara ya yi yawan da ba za a amince da shi ba.
A farkon watan nan ne shugaban na Fifa, ya gabatar da shawarar mayar da gasar ta duniya ta kunshi kasashe 48, da za a raba zuwa rukuni 16, kowanne da kasashe uku-uku.
A ranar 9 ga watan Janairu ne majalisar zartarwar Fifa, za ta tattauna kan shirin na Infantino.
GOAL Middlesbrough 2-0 Swansea
Alvaro Negredo
GOAL Middlesbrough 1-0 Swansea
Alvaro Negredo
Nadal ya nada Moya cikin masu horar da shi Tennis
Rafael Nadal ya kara tsohon zakaran kwallon Tennis na gasar French Open, Carlos Moya, a cikin masu horar da shi kwallon tennis.
Moya mai shekara 40, zai yi aikin horar da Nadal tare da Toni Nadal da Francis Roig.
Sakamakon damben gargajiya
Wasannin da aka yi a gidan damben gargajiya na Idris Bambarewa da ke Maraba 'Yanya a jihar Nasarawa, Nigeria a ranar Juma'a.
An biya 'yan Super Falcons kudadensu — NFF
Hukumar ta NFF ta samu biyan bashin ne bayan da gwamnatin Nigeria ta ba ta Dala Miliyan daya da dubu dari da saba'in domin ta biya ladan lashe kofi da hakkokin Super Falcons.
A ranar Larabar da ta gabata ne 'yan wasan na Super Falcons, wadanda suka lashe kofin kwallon kafar nahiyar Afirka na mata a watan Disamba a Kamaru, suka yi zanga-zanga zuwa Majalisar Dokoki da fadar Shugaban kasa saboda rashin biyansu kudaden da ya kamata a ba su.
Video content
An fara amfani da bidiyo a gasar Fifa
Kashima Antlers ta Japan ta zama ta farko da ta ci gajiyar tsarin amfani da hoton bidiyo a gasar, Fifa, inda ta samu bugun fanareti ta ci 3-0 a wasan kusa da na karshe na cin kofin duniya na kungiyoyi.
Alkalin wasa Viktor Kassai ya tsayar da wasan ne wanda ake yi a Japan, bayan da mataimakinsa mai lura da hoton bidiyon wasan ya ankarar da shi kan wani laifi da aka yi, inda ya bayar da fanareti bayan ya kalli bidiyon.
Kungiyar Kashima ta doke Atletico Nacional ta Colombia, wanda hakan ya sa ta zama kungiya ta farko daga Asia da ta yi nasarar zuwa wasan karshe na gasar.
A ranar Lahadi ne Zakarun na Asia za su kara a wasan karshe da Zakarun Turai Real Madrid ko Zakarun Amurka ta Arewa Club America.
West Ham United da Hull City
'Yan wasan da za su murza-leda
Middlesbrough da Swansea
Alvaro Negredo
Alvaro Negredo ya kasa ci wa Middlesbrough kwallo a karawa 13 daga cikin 15 da ya yi mata a bana.
Middlesbrough da Swansea
'Yan kwallon da za su taka-leda
Crystal Palace 1-0 Chelsea
Yadda ake murza wasan
Riyad Mahrez
Riyad Mahrez ne ya lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na 2016
Masoya kwallon kafa a fadin duniya ne suka zabi dan wasan tsakiyar na Algeria da Leicester a kan Pierre-Emerick Aubameyang da Andre Ayew da Sadio Mane da kuma Yaya Toure.
Video content
Crystal Palace 1-0 Chelsea
Fabregas ya shiga fili ya maye gurbin Willian
Crystal Palace 0-1 Chelsea
GOAL Crystal Palace 0-1 Chelsea
Diego Costa
Real Madrid da Kashima Antlers
Dan kasar Zambia, Janny Sikazwe ne zai alkalanci wasan karshe tsakanin Real Madrid da Kashima Antlers a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyi da za a yi a filin wasa da ke Yokohama.
Wannan shi ne karon farko da Sikazwe dan kasar Zambia zai alkaanci wasan da Real Madrid za ta yi.
Sai dai kuma a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyin a baya, Sikazwe ya busa fafatawar da Kashima Antlers ta doke Auckland City da ci 2-1.
Crystal Palace da Chelsea
'Yan wasan da za su murza-leda