Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Manchester United da Middlesbrough
  2. Gasar cin kofin Scotland mako na 22
  3. Gasar kwallon tennis ta Mubadala Abu Dhabi

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin, sai mako mai zuwa

Liverpool da Manchester City

'Yan wasan da za su buga wa Man City

Man City XI: Bravo, Zabaleta, Stones, Otamendi, Kolarov, Fernandinho, Yaya Toure, Sterling, Silva, De Bruyne, Aguero

Masu jiran kar-ta-kwana: Caballero, Clichy, Sagna, Fernando, A Garcia, Iheanacho, Navas

gASAR pREMIER WASAN MAKO 19
BBC Sport

Liverpool da Manchester City

'Yan wasan da za su buga wa Liverpool

Liverpool XI: Mignolet, Clyne, Lovren, Klavan, Milner, Henderson, Wijnaldum, Can, Lallana, Mane, Firmino.

Masu jiran kar-ta kwana: Karius, Lucas, Moreno, Alexander-Arnold, Ejaria, Origi, Sturridge.

Gasar Premier mako na 19
BBC Sport

An kammala wasu wasannin Premier

Gasar Premier mako na 19
BBC Sport

GOAL Swansea 0-3 Bournemouth

Joshua King

GOAL GOAL - Manchester United 2-1 Middlesbrough

Paul Pogba na United

GOAL Manchester United 1-1 Middlesbrough

Anthony Martial

Tevez ya fi kowa albashi a 'yan kwallo

Tsohon dan wasan gaba na Manchester City da Man United Carlos Tevez ya zama dan kwallon da ya fi daukar albashi a duniya, da fan dubu 310, kwatankwacin naira miliyan 186 a sati, bayan ya koma Shenhua ta China.

Shanghai ta dauki dan wasan na gaba dan Argentina mai shekara 32, daga kungiyar Boca Juniors, amma babu wani cikakken bayani da aka bayar kan yarjejeniyar, amma an ce kwantiragin na shekara 2 ne.

Sai dai wasu rahotanni sun ce Shanghai wadda tsohon kocin Brighton Gus Poyet ya koyar, ta amince da kwantiragin a kan kusan fan miliyan 40 tare da biyan dan wasan albashin fan 310,000, kwatankwacin naira miliyan 186 a sati.

Gasar Premier mako na 19
BBC

Sakamakon wasannin Premier mako na 19

Gasar Premier mako na 19
BBC Sport

Serena Williams za ta auri Alexis Ohanian

Fitacciyar 'yar wasan kwallon tennis, Serena Williams, ta yi amfani da kafar sada zumunta ta Reddit wajen sanar da baikonta tare da Alexis Ohanian.

Williams ta sanar da baikon da tayi da Ohanian daya daga cikin mamallakin Reddit ta hanyar rubutacciyar waka.

'Yar wasan tennis din ta ce ya gayyace ta Rome, birnin da suka fara haduwa, inda ya bukaci ta aure shi, kuma nan da nan ta amsa masa.

Gasar Premier makop na 19
reddit/AP

GOAL Manchester United 0-1 Middlesbrough

Grant Leadbitter

Grant Leadbitter

Dambe: Mahaukaci Teacher da Garkuwan Shagon Alabo

Dambe da aka yi tsakanin Mahaukacin Teacher da Garkuwan Alabo

GOAL Burnley 3-0 Sunderland

Andre Gray na Burnley

GOAL Chelsea 2-1 Stoke City

Willian na Chelsea

Watford za ta sayo 'yan wasa a Janairu

Kociyan Watford, Walter Mazzari zai sayo karin 'yan kwallo idan aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula a watan Janairu. 

Kociyan na fama da rashin 'yan kwallo tara da suka ci karo da yin jinya ko wadanda aka dakatar daga wasa bayan da suka yi laifi. Cikin 'yan wasa sun hada da Roberto Pereyra da Valon Behrami da Adrian Mariappa da Isaac Success da kuma Adlene Guedioura. 

Haka shi ma Ben Watson ba zai buga wasa ba, yayin da aka dakatar da Miguel Britos.   

Gasar Premier mako na 19
Getty Images

GOAL Chelsea 1-1 Stoke City

Bruno Martins Indi na Stoke City

Chelsea 1-0 Stoke

Yadda ake gara wasan

Gasar Premier mako na 19
BBC Sport

GOAL Chelsea 1-0 Stoke City

Garry Cahill

GOAL Swansea 0-1 Bournemouth

Benik Afobe

GOAL Leicester City 1-0 West Ham

Islam Slimani

Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Sadi Energy Tandaari Potiskum: Wasa tsakanin Chealsea da Stoke City ba'a san maci tuwO ba sai miya ta kare, to amma ina fatan Stoke ta lallasa chelsea da 2 da nema up up up masu premier Arsenal. 

Umar Tijjani Yusufari: Hahahhaha ina fata kungiyar kwallon kafa ta Chelsea za ta yi kaca-kaca da takwarorinsu wato Stoke City, domin kara bada tazara ga yan hamayya da suke bayan mu, musamman idan Liverpool da Man City suka yi canjaras anjima da maraice. 

 Ashiru Ibrahim B Kabo: Haba Chelsea ta yaro kyau take bata karko kofin premier na Liverpool ne. Allah yaba Stoke City sa'a ameen 

Chelsea da Stoke City

'Yan wasan da za su taka-leda

Gasar Premier mako na 19
BBC Sport

An karrama Murray da lambar girma

An karrama zakaran kwallon tennis na duniya Andy Murray da lambar girma ta Sir, bayan da ya yi bajinta a shekara ta 2016, inda ya dare mataki na daya a jerin wadanda suke kan gaba a wasan tennis a duniya.

A shekarar ce ya ci gasar Wimbledon da lambar zinare a gasar Olympic da aka yi a Brazil a 2016.

Murray ya ce yana jin ya yi yarinta da ya samu wannan lambar girma yana da shekara 29, amma hakan ya nuna kwazon da ya saka a wasannin da wanda hakan zai sa a dunga tunawa da shi a koda yaushe.

 Sauran 'yan wasan da aka karrama sun hada da Mo Farah da Lee Pearson da kuma Jessica Ennis-Hill.   

Gasar Premier mako na 19
BBC

Wani kulob din China ya taya Ronaldo fam miliyan 250

Mai kula da harkokin wasannin Cristiano Ronaldo, Jorge Mendes, ya ce wata kungiyar kwallon kafa a China ta yi wa Real Madrid tayin fam miliyan 250 domin ta dauki dan wasan Portugal.

Sai dai kuma Mendes ya ce Ronaldo mai shekara 31, bai yi shirin komawa can da murza-leda ba, duk da tayin albashin fam miliyan 85 da za a dunga ba shi a duk shekara.

Kudin da kungiyar ta China ta ce za ta bai wa Ronaldo a kowacce shekara zai kai naira 33,019,516,585:00.

A cikin watan Nuwamba ne Ronaldo ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Real Madrid zuwa Junin 2021, har ma ya ce zai iya kai wa shekara 10 a kungiyar.

Gasar Premier mako na 19
BBC

Ko Stoke City za ta takawa Chelsea burki?

Chelsea da Stoke City

Stoke City tana da damar takawa Chelsea burki bayan da ta ci wasannin Premier 12 a jere. Stoke din tana da 'yan wasan da za su iya bai wa Chelsea mamaki, sai dai kuma a kakar bana kungiyar ba ta tabuka rawar gani a wasannin da take buga wa. 

Chelsea ta fara gasar bana da kafar dama tun lokacin da ta nada Antonio Conte a matsayin kociyanta. 

Da farko Conte ya fara salon wasan 4-4-2 amma ya kasa samun yadda yake so. Daga nan ne kociyan ya fuskanci kwarewar da 'yan wasansa suke da ita, saboda haka ya koma salon wasan 3-4-3. Tun da lokacin ne Chelsea ta gagara tsara har ma ta dare kan teburin Premier ta kuma ci wasanni 12 a jere a gasar.

Gasar Premier mako na 19
AP

Chelsea na fatan kafa tarihi a Premier

Chelsea da Stoke City

Kungiyar Chelsea na fatan kafa tarihin lashe wasanni 13 a jere a gasar Premier idan har ta doke Stoke City a karawar mako na 19 da za suyi a ranar Asabar.

Idan kuma har ta samu nasarar yin hakan za ta yi kan-kan-kan da Arsenal wadda ta fara yin bajintar lashe wasannin Premier 13 a kakar wasan 2001/02.

Premier League mako na 19
Getty Images
A kakar wasan 2001/02 Arsenal ta ci wasannin Premier 13 a jere

Gasar Premier kai tsaye a BBC Hausa

A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier kai tsaye da harshen Hausa. 

Wannan makon za mu kawo muku daya ne daga cikin wasannin sati na 19 a fafatawar da za a yi tsakanin Chelsea da Stoke City. 

Za mu fara gabatar da shirin da karfe uku da rabi na yamma dai-dai da agogon Nigeria da Niger.  

Gasar Premier mako na 19
Getty Images

Gasar Premier League wasannin mako na 19

  • Chelsea  da  Stoke City FC       
  • Leicester City  da West Ham United       
  •  Manchester United  da   Middlesbrough       
  • Southampton  da  West Bromwich Albion        
  • Burnley  da Sunderland 
  • Swansea City  da  Bournemouth          
  • Liverpool da  Manchester City 

Barkanmu da saduwa a shirin labaran wasanni kai tsaye