Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen kawo muku bikin bayar da kyaututtuka na shekarar 2016

 2. Christianao Ronaldo ne gwarzon kwallon kafa a 2016!

 3. Carli Lloyd ita ce macen da ta fi fice!

     Carli Lloyd wadda ta ci kofin duniya ita ce macen da ta fi fice a 2016.

 4. Ko wace ce macen da ta fi yin fice?

  'Yan takaran su ne:

  Nominees are:

  Melanie Behringer ta  Bayern Munich  da Germany.

  Carli Lloyd ta Houston Dash da United States.

  Marta ta FC Rosengard ta Brazil.

  FIfa award 2016
 5. Subri ya laye kyautar kwallon da ya fi kayatarwa

 6. Kwallon da aka ci mafi kayatarwa

  Dukkanmu muna son kyakyawar kwallo. Amma wane kwallo ne dan dama-dama kuma wanne ne ya fi kyau?

  Ba za ka samu komai daga Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo anan ba.

  Kwallayen da suka fi fice su ne:   

  Na Marlone, dan wasan tsakiyan  Corinthians, ya  sha kwallon a gasar  Copa Libertadores a 2016.

  Na Daniuska Rodriguez, 'yar  wasan tsakiyan , a Venezuela,  a shekarar 2016 a gasar cin kofin mata 'yan kasa da shekara 17 na yammacin America. 

  Na Mohd Faiz Subri, dan wasan gaba, na kungiyar  Penang a gasar Malaysia Super League.

 7. Claudio Ranieri ne kociyan da ya yi rawar gani a 2016!

  Fifa Award 2016
 8. Claudio Ranieri ne kociyan da ya fi yin fice

  Claudio Ranieri ya yi hannu da Diego Maradona a lokacin da zai karbi kyautar.

 9. Claudio Ranieri ne ya lashe kyautar gwarzon koci da babu kamarsa a 2016

  Diego Maradona zai bai wa Claudio Ranieri kociyan Leicester City kyautar kociyan da ya fi yin fice a 2016.   

 10. Masu takarar kociyan da ya fi yin fice a 2016

  Ko Ranieri zai yi nasara a kan Zidane ko kuma Santos

  Fifa Award 2016
 11. Kyautar wasa ba da yin gaba ba

  Tun a shekarar 1987, Fifa ta fara karrama dan wasa ko kociya ko mahukuncin wasan tamaula ko alkali ko magoya baya ko kuma mutun guda da kyautar wasa ba da gaba ba.  

  Fifa Award 2016
 12. Cristiano Ronaldo

  Fifa Award 2016
 13. Kyautar mai horar da tamaula da ta fi yin fice a 2016

  Jill Ellis, daya daga cikin masu takara mai horar da Amurka 'yar Portsmouth.

  Silvia Neid, wadda ta yi ritaya bayan da Jamus ta lashe lambar yabo a Olympic a Rio a karon farko,da kuma Pia Sundhage, wadda ta horar da Sweden har ta kai ga lashe lambar Azurfa a 2016 a wasannin Olympic.

  Fifa Award 2016
 14. Kociya da dan wasa sun hadu a Zurich

  Tsohon kociyan Manchester United Sir Alex Ferguson ya isa wajen bikin tare da tsohon dan kwallon United Dwight Yorke.

  Fifa Award 2016
 15. Antoine Griezmann ya isa dakin karrama 'yan wasa

  Fifa Award 2016
 16. Ronaldo ya isa wajen bikin karrama 'yan kwallon

  Ronaldo
 17. 'Yan takara:

  Ranieri yana takaran zama kociyan da ya fi fice a bara, daya daga cikin kyaututtukan da za'a bayar

  Dan kasar  Italiyan wanda ya jagoranci Leicester City yin wani abun almara inda suka lashe kofin Premier a 2016.

   Sauran 'yan takaran su ne kociyan Portugal wanda ya lashe kofin turai,  Fernando Santos, a 2016 sai kuma Zinedene Zidane, mai horar da Real Madrid wadda ta lashe kofin zakarun Turai a bara . 

  • 'Yan takarar gwarzon dan wasa (Cristiano Ronaldo da Antoine Griezmann da kuma Lionel Messi).
  • Macen da ta fi fice a fagen tamaula ( Melanie Behringer, Carli Lloyd and Marta)
  • Kociyan da ya fi fice ( Claudio Ranieri, Fernando Santos and Zinedine Zidane).
  • Kociyar da ta fi fice ( Jill Ellis, Silvia Neid and Pia Sundhage).

   Da sauran kyaututtuka

 18. Shin Ranieri zai samu karin kyauta?

  Ko Ranieri zai iya lashe kyautar kociyan da ya fi fice?

  Fifa awards 2016
 19. Sabuwar shekara, sabuwar kyauta

  Abokanan gogayya akan fili

  Fifa Award 2016
 20. Biyu daga cikin 'yan takara Ronaldo da Messi

  Fifa Award 2016