Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin.

 2. Damben boksin: De Gale da Badou

  Zakaran damben boksin ajin IBF super-middleweight James DeGale zai kara da zakaran kambun WBC Badou Jack a New York a ranar Lahadi.

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 3. Wasu wasannin damben gargajiya da aka yi a Marabar Yanya

  Video content

  Video caption: Dambe 11 aka yi a gidan damben gargajiya na Bambarewa da ke Marabar Yanya
 4. Gasar Premier: West Ham da Crystal Palace

  'Yan wasan da za su murza-leda

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 5. Gabon 2017: Wace kasa ce za ta lashe?

  Ivory Coast - Ta fito da sabbin 'yan wasa. 

  Ghana    -  Ana mata kirari da Jamusawan Afrika 

  Aljeriya - Na da 'yan wasan Afirka da aka fi ji da su a 2016. 

  Senegal - Ta ci duk wasanninta na samun cancanta.

  Masar - Ta yi rawar gani a wasannin cancanta kuma tana da nasibi.

  Zambia - Ta yi cikas ga burin wasu a 2012 inda ta lashe gasar

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 6. An tashi wasa Tottenham 4-0 West Brom

  03:20

  Kwallo ukun da Harry Kane ya ci ta taimaka wa Tottenham lashe wasanta na shida jere a gasar Premier, kuma za su matsa zuwa matsayi na biyu a kan tebur. Komai ya yi kyau a zagayen arewacin Londo.

 7. Sam Sunderland ne ya lashe Dakar Rally

  Sam Sunderland ya zama dan Burtaniya na farko da ya lashe gasar tseren babura ta Dakar Rally wadda ya ci a ranar Asabar.

  Dan wasan mai shekara 27 ya bai wa Matthias Walkner na Austria tazarar minti 32 a zangon karshen gasar a Argentina. 

  An fara gasar bana ta 38 a Asuncion zuwa Paraguay da Boliviasannan aka kammalata a Argentina.

  Gasar wasannin premier mako na 21
 8. Gasar Premier: Swansea City da Arsenal

  'Yan wasan da za su murza-leda

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 9. GOAL Tottenham 4-0 West Brom

  Harry Keine kwallo na uku da ya ci a karawar

 10. Murray zai kara kaimi a wasanninsa na tennis

  Andy Murray ya ce sai ya kara kaimi a wasaninsa idan har yana son ya ci gaba da zama a mataki na daya a jerin wadanda suke kan gaba a wasan kwallon tennis. 

  Dan wasan mai shekara 29 zakaran gasar Wimbledon ya maye gurbin Novak Djokovic a shekarar da ta wuce.

  Murray zai fafata a gasar Australian Open a mako mai zuwa.

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 11. GOAL Tottenham 3-0 West Brom

  Harry Kane

 12. Gasar Firimiyar Nigeria wasannin farko

  Karawar da za a yi a ranar Lahadi

  Bayan Kano Pillars ta fafata da Ifeanyiubah a ranar Asabar ne ake sa ran buha wasanni tara a ranar Lahadi.

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 13. Kano Pillars da Ifeanyiubah

  Kano Pillars ce ta doke Ifeanyiubah 2-0 a wasan da suka yi a bara a Kano, inda Prince Aggreh da Suleman Usman ne suka ci mata kwallayen biyu. 

 14. Gabon 2017: 'Yan wasan da za su taka rawar gani

  Baya ga Aubameyang, kallo zai koma kan fitaccen Dan wasan kwallon BBC na bana wanda ke tashe kuma Dan kwalon shekara na CAF Riyad Mahrez da kuma Dan wasan Afirka mafi tsada Sadio Mane

  'Yan wasa 23 ne daga gasar Premier Ingila za su je gasar cin kofin Afirka ta Gabon ciki har da dan wasan Manchester United na kasar Ivory Coast Eric Bailly, da dan wasan West Ham daga kasar Ghana Andre Ayew, da Islam Slimani dan Aljeriya da ke buga wa Leicester kwallo dan wasan  Crystal Palace da zai wakilci kasar Ivory Coast Wilfried Zaha.  

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 15. Yau za a fara gasar Frimiyar Nigeria

  Kano Pillars da Ifeanyiubah

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 16. Jadawalin gasar Copa del Rey

  Wasannin daf da na kusa da na karshe

  Real Madrid za ta fafata da Celta Vigo a wasan daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey.

  Madrid ta kai wannan matakin ne bayan da ta ci Sevilla 6-3 a wasanni biyu da suka yi, yayin da Celta ta ci Valencia 6-2.

  Mai rike da kofin bara, Barcelona, za ta kece raini da Real Sociedad, ita kuwa Atletico Madrid za ta kara ne da Eibar.

  Kungiyar Alcorcon wadda ita kadai ce ba ta buga wasannin La ligar Spaniya za ta yi gumurzu ne da Deportivo Alaves.

  Barcelona ce a kan gaba wajen yawan lashe Copa del Rey, bayan da ta dauki 28, sai Athletic de Bilbao mai 23, Real Madrid kuwa 19 ne da ita da Atletico de Madrid mai guda 10 a tarihi.

  Za a fara wasannin farko a gasar daf da na kusa da karshe a ranar 18 ga watan Janairu, sannan a yi karon batta a karo na biyu a ranar 25 ga watan Janairun 2017.

  Ga jadawalin wasannin da za a yi:

  • Real Sociedad da Barcelona
  • Alcorcon da Alaves
  • Atletico Madrid da Eibar
  • Real Madrid da Celta
  Gasar Premier wasannin mako na 21
 17. Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

  Asheerou Asabib Nasara Wannan wasa fatan a yi draw sannan ina fatan Liverpool ta lallasa Manchester Utd da ci 2 - 1.

  Mustapha Mohammed To! Gasar Premier in ta zo tsakiya ko masana wasanni ma sai dai a hankali. 

  Saleh Muhammed Saleh Damare To! Mu dai za mu iya cewa fadan da babu ruwanka, dadin kallo ne da shi. Up Barcelona! 

  Shuaibu Adam Bagwai Hahaha! Ta safe ta yaro, Tottenham 2 - 0 West Brom. A ci gaba da gashi suya sai ranar sallah. Up Liverpool!

 18. Tottenham sun mamaye wasa

  Yayin da West Brom suka iya taba kwallo sau 52 ana minti 33 da fara wasa, Tottenham sun taba kwallo fiye da sau 200.  

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 19. Gabon 2017: Yau za a fara gasar cin kofin Afirka

  Yau Asabar da karfe 5:00 agogon Nijeriya ne za a fara gasar cin kofin Afirka karo na 31, inda mai masaukin baki Gabon za ta buga wasan farko da Guinea-Bissau

  Shekara sittin kenan tun bayan fara gasar cin kofin Afirka cikin 1957 a Sudan, inda kasa uku ta fafata kuma Masar ta dauki kofi.

  Gasar a bana ta kunshi wasa 32 a tsawon kwana 23, inda kasa 16 - za su kara da juna cikin rukuni hudu. A ranar 5 ga watan Fabrairu ne za a buga wasan karshe, inda kasar za ta tafi da kofi wanda aka kere shi a kasar Italy da kuma tsabar kudi dala miliyan 4.

  Gasar Premier wasannin mako na 21
 20. GOAL Tottenham 2-0 West Brom