Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Arsenal ba ta je Austalia da Szczesny ba

  The Sun

  Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ba ta je atisayen da za ta yi a Austarlia da mai tsaron ragarta Wojciech Szczesny ba.

  Ana alakanta mai tsaron ragar mai shekara 27 da cewar zai koma Juventus ne da murza-leda.

  Arsenal
  Image caption: Szczesny ya koma Arsenal da murza-leda daga Legia Warsaw a shekarar 2006
 2. Arsenal na son taya Thomas Lemar a karo na uku

  Jaridar Daily Mirror

  Kungiyar Arsenal na fatan sake taya dan kwallon Monaco, Thomas Lemar kan kudi fam miliyan 45. Daily Mirror ta ce Arsenal ta fara taya dan kwallon fam miliyan 30 da kuma fam miliyan 45 amma aka ki sallama mata shi.

  Arsenal
  Image caption: Thomas Lemar ya koma Monaco da taka-leda daga Cean a 2015
 3. Chelsea za ta taya Alvaro Morata

  Jaridar AS

  Jaridar AS ta wallafa cewar mai rike da kofin Premier da aka kammala Chelsea na shirin taya dan wasan Real Madrid, Alvaro Morata kan kudi fam miliyan 70.

  Real Madrid
  Image caption: Kungiyoyi da dama na son sayen Morata na Real Madrid
 4. Dan kwallon da aka saya mafi tsada a tarihi a duniya

  • Fam miliyan 89 - Paul Pogba - Juventus to Manchester United, 2016
  • Fam miliyan 86 - Gareth Bale - daga Tottenham zuwa Real Madrid, 2013
  • Fam miliyan 80 - Cristiano Ronaldo - daga Manchester United zuwa Real Madrid, 2009
  • Fam miliyan 75.3 - Gonzalo Higuain - daga Napoli zuwa Juventus, 2016
  • Fam miliyan 75 - Luis Suarez - daga Liverpool zuwa Barcelona, 2014;
  • Fam miliyan 75 - Romelu Lukaku - daga Everton zuwa Manchester United, 2017
  Manchester United
  Image caption: Pogba ne ya fi kowanne dan kwallo tsada a kakar wasan da aka kammala
 5. Dan wasan aka saya mafi tsada a Ingila

  • Fam miliyan 75 - Romelu Lukaku - daga Everton zuwa Manchester United, 2017
  • Fam miliyan 50 - Fernando Torres - daga Liverpool zuwa Chelsea, 2011
  • Fam mliyan 47.5 - John Stones - daga Everton zuwa Manchester City, 2016
  • Fam miliyan 44 - Raheem Sterling - daga Liverpool zuwa Manchester City, 2015
  • Fam mliyan 37.1 - Juan Mata - daga Chelsea zuwa Manchester United, 2014
  Manchester United
  Image caption: Lukaku shi ne dan kwallon da aka saya mafi tsada a gasar Premier
 6. Manchester United ta kammala daukar Lukaku

  Manchester United ta kammala daukar Romelu Lukaku daga Everton kan kudi fam miliyan 75 kan yarjejeniyar shekara biyar.

  Dan kwallon ya buga wasa aro a Everton daga Chelsea a kakar 2013-14, daga baya ta dauke shi kan yarjejeniyar shekara biyar.

  Romelu Lukaku ya shafe shekara hudu a Everton, inda ya zira kwallo 81

  Manchester United
  Image caption: Romelu Lukaku ya shafe shekara hudu a Everton, inda ya zira kwallo 81
 7. Sevilla ta dauki Pizzaro

  Kungiyar Sevilla mai buga gasar La Liga ta sanar a shafinta na Intanet cewar ta dauki dan kwallon Argentina Pizzaro, har ma ta gwada lafiyarsa za kuma ta gabatar da shi a yammacin Litinin.

  Sevilla
  Image caption: A ranar Litinin Sevilla za ta gabatar da Pizzaro ga magoya bayanta
 8. Rooney ya sake komawa Everton

  Rabon da Rooney da Everton tun shekara 13

  Wayne Rooney ya sake komawa Everton kungiyar da ya bari shekara 13 da suka wuce daga Mancherster United.

  Rooney mai shekara 31 shi ne dan wasan da ya fi ci wa United kwallaye a tarihi, ya kuma koma Everton a matsayin wanda yarjejeniyarsa ta kare a Old Trafford.

  Dan wasan ya ci wa United kwallo 253 a wasa 559 da ya buga mata tamaula.

  Rooney ya ci kofin Premier biyar da na Zakarun Turai da na Europa da kofin Kalubale, tun komarsa United kan kudi fam miliyan 27 a shekarar 2004.

  Eveton
  Image caption: Rooney ya koma United a 2004 kan kudi fam miliyan 27
 9. PSG na son sayen Mbappe

  The Sun

  Kylian Mbappe na karbar albashin Euro 18,000 a kowanne mako a kungiyar Monaco, sai dai kuma PSG na son ta dunga biyansa Euro 225,000 a duk makno idan ya amince ya koma can da taka-leda in ji The Sun.

  Kungiyoyi da dama na son yin zawarcin dan kwallo, wanda tauraruwarsa ke haskakawa.

  PSG
  Image caption: Mbappe yana daga cikin 'yan wasan da kungiyoyin Turai ke zawarci a bana
 10. Leicester City na son sayen Iheanacho

  Jaridar The Mirror

  Jaridar The Mirror ta ruwaito cewar Leicester City na fatan za ta kulla yarjejeniyar sayen dan wasan Manchester City, Kelechi Iheanacho a cikin makon nan, kuma watakila City ta sayar da dan kwallon kan kudi fam miliyan 30.

  Leicester City
  Image caption: Kelechi Iheanacho baya buga wasanni akai-akwai a karkashin Pep Guardiola
 11. Madrid ta gwada lafiyar Theo Hernandez

  Real Madrid ta gwada lafiyar Theo Hernández a asibitin jami'ar Sanitas da ke La Moraleja, kuma dan kwallon ya ci gwajin da aka yi masa kafin ya rattaba yarjejeniya da kungiyar.

  Daga nan ne za ta gabatar da shi a yammacin Litinin a gaban magoya bayan kungiyar a Santiago Bernabeu sannan ya gana da manema labarai.

  Real Madrid
  Image caption: A yammacin Litinin Hernandez zai gana da magoya bayan Real Madrid da kuma 'yan jarida
 12. Barkanmu da saduwa a shirin kai tsaye a labarin wasanni

  Yadda ake cinikayyar 'yan wasan tamaula a nahiyar Turai.