Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Januzaj ya koma Real Sociedad
 2. Wasu labarin wasanni da suke wakana
 3. Everton ta sauka a Tanzaniya domin wasan sada zumunta
 4. Madrid ta fara atisaye a Amurka

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin sai kuma gobe za mu dora

 2. An gayyaci 'yan wasa 29 zuwa Super Eagles

  An gayyaci 'yan wasa 29 na tawagar kwallon kafa ta Super Eagles masu taka-leda a gida sansanin horo domin karawa tsakanin Togo ko kuma jamhuriyar Benin.

  Nigeria za ta kara da wadda ta yi nasarar tsakanin kasashen biyu da za su kammala wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke murza-leda a gida.

  Super Eagles wadda Salisu Yusuf ke jan ragama, za ta kara da Togo ko kuma Jamhurirar Benin a ranar 13 ga watan Agusta, sannan ta karbi bakuncin wasa na biyu a ranar 19 ga watan.

  Ga 'yan wasan da aka bai wa goron gayyatar:

  Masu tsaron baya: Ikechukwu Ezenwa (FC IfeanyiUbah); Theophilus Afelokhai (Enyimba FC), Okiemute Odah (Lobi Stars), Dele Ajiboye (Plateau United)

  Masu tsaron baya: Jamiu Alimi (Kano Pillars); Orji Kalu (Rangers International); Stephen Eze (FC IfeanyiUbah); Ariwachukwu Emmanuel (Akwa United); Elisha Golbe (Plateau United); Chima Akas (Enyimba FC); Nasiru Sani (Katsina United), Osas Okoro (Rangers International), Chinedu Ajanah (ABS FC)

  Masu wasan tsakiya: Hafiz Aremu (Akwa United); Emeka Atuloma (Rivers United); Raphael Ayagwa (Lobi Stars); Ifeanyi Ifeanyi (Akwa United); Rabiu Ali (Kano Pillars), Samuel Mathias (El-Kanemi Warriors), Alhassan Ibrahim (Akwa United), Chiamaka Madu (Rangers International)

  Masu cin kwallo: Mfon Udoh (Enyimba FC); Prince Aggreh (FC IfeanyiUbah); Sikiru Olatubosun (MFM FC), Thomas Zenke (Nasarawa United); Austin Oladapo (Gombe United), Stephen Odey (MFM FC); Kingsley Eduwo (Lobi Stars), SundayAdetunji (Abia Warriors), Ifeanyi George (Rangers International)

  Kai tsaye
  Image caption: 'Yan wasa 29 Salisu Yusuf ya gayyata zuwa sansanin horo na Super Eagles
 3. Barcelona ta dawo yin atisaye ranar Laraba

  Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dawo yin atisaye domin tunkarar kakar da za a fara a bana.

  Tun da sanyin safiyar Laraba ta fara duba lafiyar 'yan wasanta 18, kuma hudu daga cikinsu daga matasan kungiyar suke.

  A kuma lokacin ne sabon kociyan Barcelona, Ernesto Valverde ya fara aikin horar da kungiyar da ya koma a karshen kakar da ta kare, bayan da Luis Enrique ya yi ritaya.

  Kai tsaye
  Image caption: Barcelona ta lashe Copa del Rey a kakar wasan kwallon kafa da aka kammala
 4. An fitar da Murray a gasar Wimbledon

  An yi waje da mai rike da gasar kwallon tennis ta Wimbledon Andy Murray a wasan daf da na kusa da karshe a ranar Laraba.

  Sam Querry ne ya fitar da Murray da ci 3-6 6-4 6-7 (4-7) 6-1 6-1, hakan ya sa ya zama dan Amurka na farko da ya kai wasan daf da karshe a gasar bayan Andy Roddick a 2009.

  Idan har Novak Djokovic ya lashe wasannin da ake yi, zai maye gurbin Murray a matsayin wanda ke kan gaba a iya gasar kwallon tennis a duniya.

  Djokovic zai kece raini da Tomas Berdych a yammacin Laraba.

  Kai tsaye
  Image caption: Murray shi ne ke matsayi na daya a iya kwallon tennis a duniya
 5. Labarai da dumi-dumiDani Alves ya koma Paris St-Germain

  Dan kwallon tawagar Brazil, Dani Alves ya koma Paris St-Germain da taka-leda, bayan da yarjejeniyarsa da Juventus ta kare a bana.

  Alves wanda Manchester City ta dinga zawarci ruwa a jallo ya amince ya buga wa PSG, maimakon ya sake wasa karkashin Pep Guardiola wanda ya horar da shi a Barcelona.

  City ta so ta bai wa Alves mai shekara 34 kwantiragin shekara biyu, amma ba za ta iya biyan fam 230,000 da PSG ake cewa za ta dinga biyansa a duk mako ba.

  Kai tsaye
  Image caption: Alves ya lashe kofin Serie A da Juventus a kakar da ta kare
 6. Ra'ayoyinku daga BBC Hausa Facebook

  Ahmad Sulaiman Bajoga Agaskiya ni kungiyata ta FC Barcelona, ina son ta saya mana 'yan wasa masu tsaron baya. Saboda matsalar kenan.

  Salihu Abubakar Inason Manchester City ta sayi Walker daga Spurs da kuma Benjemen Mandy daga Monaco sai ta kuma dawo da Mangala daga aro da ta tura shi.

  Mahmud Salihu Kaura Namoda Ina son kulob din da nake goyon baya wato Arsenal ya sayi yan wasan tsakiya masu kyau, haka zalika da dan wasan baya.

 7. Konta ta kai wasan daf da karshe a Wimbledon

  Johanna Konta ta zama 'yar wasan Burtaniya ta farko da ta kai wasan daf da karshe a gasar kwallon tennis ta Wimbledon, rabon da wata 'yar kasar ta yi hakan tun 1978.

  Konta ta yi nasarar doke Simona Halep da ci 6-7 (2-7) 7-6 (7-5) 6-4, wanda hakan ya sa ta yi kan-kan-kan da Virginia Wades wadda ta kafawa Burtaniya tarihin a shekara 39 da suka wuce.

  Da wannan nasarar Konta za ta buga wasan daf da karshe da Venus Williams.

  Kai tsaye
  Image caption: Konta ta kai wasan daf da karshe za kuma ta kara da Venus Willaims a ranar Alhamis
 8. Gasar Firimiya ta Nigeria

  Za a karasa wasan mako na 28 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria tsakanin Rivers United da MFM a ranar Laraba.

  Kungiyoyin biyu za su kara ne a filin wasa na Yakubu Gowon da ke Port Harcourt.

  Kai Tsaye
  Image caption: Wasan karshen mako na 28 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria
 9. Gasar damben cin mota ta birnin Kano

  An samu karin 'yan damben da suka kai zagaye na uku a damben gargjiya na gasar cin mota da ake yi a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano a wasannin da aka yi a ranar Talata.

  Dambatawa hudu aka yi a gasar, inda Shamsu Kanin Emi daga Arewa ya samu nasara a kan Shagon Shaf Shaf Guramada.

  Shi ma Bahagon Audu Argungu daga Jamus ya samu nasara a kan Ibrahim Dan Kanawa daga Kudu.

  Sauran 'yan damben da suka kai zagayen gaba sun hada da Bare Bare daga Kudu da Shagon Babangida daga Guramada.

  Kai tsaye
  Image caption: Tun a ranar Litinin aka fara gasar damben cin mota a birnin Kanon Nigeria
 10. Gasar tseren motoci

  Shugaban kamfanin Red Bull mai tseren motoci, Christian Horner ya ce ya yi mamaki da Silverstone ya kawo karshen yarjejeniya karbar bakuncin gasar British Grand Prix.

  Mahukuntan Siverstone masu tsara gasar tseren motoci a Burtaniya sun ce ba za su iya karbar bakuncin wasannin 2019 ba, sai idan an sabunta yarjejeniyar da suka kulla a baya. Silversone ya ce ya yi hasarar sama da fam miliyan bakwai a shekara biyu da ya karbi bakuncin tseren motocin.

  Kai tsaye
  Image caption: Silverstone ne ke karbar bakuncin gasar tseren motoci a kowacce shekara a Burtaniya tun 1987
 11. Mc Gregor ya sha alwashin doke Mayweather

  Conor McGregor ya yi alkarin doke Floyd Mayweather a turmi na hudu idan suka hadu a karon farko a gasar damben boksin a ranar 26 da watan Agusta a Las Vegas.

  'Yan damben biyu sun hadu ne a gaban dubban jama'a a lokacin da suka gana da 'yan jarida a birnin Los Angeles din Amurka.

  Kai tsaye
  Image caption: 'Yan damben za su kara a Las Vegas a karon farko a ranar 26 ga watan Agusta
 12. Labarai da dumi-dumiOzil zai ci gaba da zama a Arsenal

  Mesut Ozil ya ce yana son ya ci gaba da taka-leda a Arsenal, kuma zai tattauna da mahukuntan kungiyar kan tsawaita zamansa.

  Dan kwallon ya ce da zarar Arsenal ta dawo daga wasannin atisayen da za ta yi a Australia da China za su zauna domin batun tsawaita yarjejeniyarsa a Emirates.

  Ozil mai shekara 28, yana da kwantiragi da Arsenal zuwa 2018, amma ana ta rade-radi kan makomarsa a kungiyar.

  Kai tsaye
  Image caption: Da zarar Arsenal ta dawo daga atisayen tunkakar wasannin bana, Ozil zai tattauna da mahukuntanta
 13. Ra'ayoyinku a BBC Hausa Facebook

  Umar Bulama Damasak Hakika Bbc hausa naji da wannan dama kungiyar mu ta Chelsea musamu dan wasan gaba mai kyau mai yawan cin kwallo da yawa kamar Morata ko Lewandoski ko Aubameyang muke bukata a klub din mu na Chelsea.

  Abubakar Chika Abdullahi Ni magoyin bayan Real Madrid ne, Don haka ina Bukatar Madrid taci gaba da rike matsayin dan wasanta na gaba wato Alvaro Morata, sannan ta sayo mana Klelian Mbappe daga Monaco don yan gaban mu su kara karfi da kyau.

  Isah Isah Kwafsi Asarara Ni aganina 'yan wasanda muke dasu a Manchester United a yanzu sun ishemu kawai jiran muke ranar tazo mu zuburbudesu UP Man U.

 14. Watakila Aubameyang ya koma Chelsea

  Watakila Aubameyang ya koma Chelsea

  Jaridar Metro ta ce an bai wa Chelsea damar sayen Pierre-Emerick Aubameyang daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 65.

  Conte na son sayen mai cin kwallo bayan da United ta sayi Romelu Lukaku da yake zawarci sannan ya ce ba zai yi amfani da Diego Costa a kakar wasanni da za mu shiga ba.

  Kai tsaye
  Image caption: Dortmund ce ta ce za ta iya sayae da Aubameyang
 15. Everton na son sayen Sigurdsson

  Everton na son sayen Sigurdsson

  Jaridar The Guardian ta wallafa cewar Everton na son sayen Gylfi Sigurdsson kan kudi fam miliyan 50 daga Swansea City.

  Sai dai Swansea tana son a sayi dan kwallon fiye da farshin da Everton ta yi masa.

  Kai tsaye
  Image caption: Sigurdsson ya taka rawar gani a kakar wasan da aka kammala
 16. Palace ta dauki aron Loftus-Cheek na Chelsea

  Crystal Palace ta dauki dan kwallon Chelsea, Ruben Loftus Cheek aro zuwa karshen kakar da za a fara ta bana.

  Dan wasan mai shekara 22, wanda ya yi wa Chelsea wasa 32, shi ne na farko da koci Frank de Boer ya dauka a bana.

  Kai tsaye
  Image caption: Dan kwallon ya buga wa Chelsea wasa 11 a kakar da aka kammala
 17. United ta nada Carrick kyaftin dinta

  Kungiyar Manchester United ta nada Micheal Carrick a matsayin kyaftin dinta.

  Carrick mai shekara 35, ya koma United a shekarar 2006, ya kuma maye gurbin Wayne Rooney wanda ya koma Everton da taka-leda.

  Dan kwallon ya koma United daga Tottenham kan kudi fam miliyan 18.6 ya kuma kulla yarjejeniyar ci gaba da zama a Old Trafford zuwa Junin 2018 a shekarar nan.

  Carrick ya buga wa United wasa 459, ya kuma lashe kofin Premier biyar da na FA da na Zakarun Turai.

  Kai tsaye
  Image caption: Carrick ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a United a shekarar nan
 18. An kammala gwada lafiyar Rodriguez

  Likitocin Bayern Munich sun kammala gwada lafiyar James Rodriguez wanda zai buga wa kungiyar tamaula aro daga Real Madrid shekara biyu.

  Madrid din ta bai wa Munich zabin sayen dan wasan ko akasin hakan bayan shekara biyun da suka kulla yarjejeniya.

  A ranar Talata dan kwallon ya isa Jamus, ana kuma sa ran Munch za ta gabatar da shi a gaban magoya bayanta da yammaci Laraba.

  Kai Tsaye
  Image caption: Rodriguez ya koma Real Madrid a 2014
 19. Januzaj ya koma Real Sociedad

  Manchester United ta amince ta sayar da Adnan Januzaj ga Real Sociedad kan kudi fam miliyan 9.8.

  Kociyan United, Jose Mourinho ne ya cewa dan kwallon zai iya komawa wata kungiyar idan ya samu dama.

  Januzaj ya koma United daga Sunderland wacce ya buga wa wasa aro, kuma baya cikin 'yan kwallon da za su buga wa United wasannin atisaye a Amurka.

  Kai tsaye
  Image caption: Yanuzaj ya ci kwallo biyar a wasa 63 da ya buga wa Manchester United
 20. Barkanmu da saduwa a cikin shirinmu na yau Laraba

  Za mu kawo muku yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta nahiyar Turai ke ci da wasu labaran wasanni.