Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Watakila West Ham ta sayar da Valenci
 2. Shin ina makomar Sanchez a Arsenal ?
 3. Manchester City na son daukar Walker

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku sake tarawa a ranar Litinin,

 2. Mo Farah zai fafata a wasannin Birmingham

  Sir Mo Farah ya tabbatar da cewar zai fafata a gasar wasannin tsalle tsalle da guje guje da za a yi a Birmingham a cikin watan Agusta.

  Dan wasan zakaran tseren mita dubu biyar da na 10 ya ce ya maida hankalinsa a wajen atisaye domin ya taka rawar gani a wasannin.

 3. Martial zai taka rawar gani a bana - Silvestre

  Tsohon dan wasan Manchester United mai tsaron baya Mikael Silvestre ya shaidawa BBC cewar yana sa ran dan wasan tawagar Faransa da ke murza leda a Old Trafford, Anthony Martial zai kai kan ganiyarsa a wasannin bana,

  Martial ya ci wa United kwallo tara a wasa 45 da ya buga mata a kakar da ta kare, sai dai kuma Silvestre ya ce ya kamata dan wasan ya kara kwazo.

  Kai tsaye
  Image caption: Martial ya ci wa United kwallo tara a wasanni 45 da ya buga mata
 4. Selby zai kare kambunsa na IBF

  Zakaran damben boksin Lee Selby zai kare kambunsa na IBF ajin Featherweight a ranar Asabar.

  Selby ya rasa mahaifiyarsa wacce ta mutu a ranar Talata, sai dai hakan ba zai hana shi dambatawa da Jonathan Victor Barros a karshen makon nan ba.

 5. Venus ta kai wasan karshe a Wimbledon

  Venus Williams ta kai wasan karshe a gasar kwallon tenis ta Wimbledon, bayan da ta fitar da Johanna Konta a yammacin Alhamis din nan.

  Venus mai rike da kofin karo biyar ta yi nasarar fitar da Konta daga gasar da ci 6-4 da 6-2, wanda hakan ya sa za ta fafata da Garbine Muguruza a wasan karshe. Konta ta kasa kafa tarihin kai wa wasan karshe a gasar, wanda rabon 'yar Burtaniya ta kai wannan matakin tun a 1977.

  Kai tsaye
  Image caption: Sau biyar Venus ta lashe gasar ta Wimbledon
 6. Gurgun da ke buga kwallon Amurka

  An haifi Isaiah Bird babu kafafu, amma hakan bai hana shi buga kwallon Amurka ta zari ruga ba.

  Video content

  Video caption: An haifi yaron babu kafafu, amma hakan bai hana shi yin wasan kwallo ba
 7. Man City na daf da daukar Walker

  Manchester City ta kusa kammala sayen dan wasan Tottenham, Kyle Walker, bayan da ta amince ta biya fam miliyan 50.

  A ranar Juma'a ake sa ran Walker mai shekara 27 zai je Ettihad domin a duba lafiyarsa. Walker ya koma Tottenham da taka-leda daga Sheffield United a 2009, sai dai ba zai buga wa Spurs wasannin atisayen tunkakar gasar bana ba. Mai makon hakan zai bi Manchester City zuwa Amurka a ranar Litinin, inda za ta fafata a wasanni sada zumunta.

  Kai tsaye
  Image caption: Walker zai bi Manchester City wasannin da za ta yi a Amurka
 8. Dambe tsakanin Aminu da Garkuwan Shagon Alabo

  A cikin watan Disambar bara aka dambata tsakanin Aminun Mahaukaci Teacher daga Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu a gidan dambe na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

  Video content

  Video caption: Dambe da aka yi tsakanin Mahaukacin Teacher da Garkuwan Alabo
 9. Stoke ta ki sayar wa West Ham Arnautovic

  Stoke City ta ki ta sayar wa West Ham United, Marko Arnautovic. The Press Associatin ce ta wallafa cewar West Ham ta taya dan wasan kan kudi fam miliyan 28 a makonnan.

  Saura yarjejeniyar shekara uku ta kare tsakanin Arnautovic da Stoke City, wanda ya koma kungiyar daga Werder Bremen a 2013.

  Kai tsaye
  Image caption: Arnautovic ya buga wa Stoke wasa 145
 10. Petev da Zagreb sun raba gari Ivaylo

  Ivaylo Petev da kungiyar Dinamo Zagreb sun raba gari kwanaki biyu a fara gasar cin kofin Croatia.

  Kocin mai shekara 42 ya yi fama da kalubale tun lokacin da ya koma kungiyar a Satumba, yayin da Zagreb ta kasa cin kofi a kakar da aka kammala, wadda rabon ta yi hakan tun shekara 12 da ta wuce.

  Zegreb ta nada Mario Cvitanovic tsohon kociyan matasan kungiyar a matakin mai horar wa na rikon kwarya.

  Kai tsaye
  Image caption: Zegreb ta nada Mario Cvitanovic a matakin mai horar wa na rikon kwarya.
 11. Ebola ya buge Bahagon Audu a gasar cin mota

  A gasar damben cin mota da ake yi a birnin Kano Nigeria, Ebola daga Kudu ya doke Bahagon Audu Argungu daga Arewa a turmi na biyu a dambatawar da suka yi a ranar Laraba.

  Shi kuwa Ali Kanin Bello daga Arewa a turmin farko ya samu nasara a kan Custom daga Kudu. Wasan da ya bai wa 'yan kallo mamaki shi ne wanda Dan Ali Shagon bata isarka daga Kudu ya kai zagayen gaba maimakon shamsu Kanin Emi daga Arewa. 'yan damben biyu sun fafata har lokacin da aka ware na ka'ida babu kisa daga baya aka yi kuri' a Dan Ali ya yi nasara.

  Za a ci gaba da dambatawa a ranar Alahmis a filin wasa na Ado Bayero Square da ke birnin Kanon Nigeria.

  Kai tsaye
  Image caption: Dan Ali daga Kudu da Ali Kanin Bello daga Arewa sun kai wasannin gaba a gasar
 12. Murray na goyon bayan Konta a Wimbledon

  Andy Murray na goyon bayan Johanna Konta ta kai wasan karshe a gasar kwallon tenis ta Wimbledon.

  Rabon da 'yar Burtaniya ta kai wasan karshe a gasar tun a shekarar 1977.

  Konta za ta kece raini da Venus Williams a yammacin Alhamis a wasan daf da karshe. Tuni aka fitar da Murray mai rike da kofin gasar a wasannin maza.

  Kai tsaye
  Image caption: Murray ne ke kan gaba a iya kwallon tennis a duniya
 13. Swansea ta ki sallama tayin Sigurdsson

  Swansea City ta ki ta sallama tayin fam miliyan 40 da Everton ta yi wa dan wasanta Gylfi Sigurdsson.

  Ita ma Leicester City na son daukar dan kwallon kan kudi fam miliyan 40 din. Sai dai Swansea ta nace da cewar sai dai a biyata fam miliyan 50 ga duk kungiyar da take son sayen dan wasan.

  Kai tsaye
  Image caption: Gylfi Sigurdsson ya ci kwallo ya kuma taimaka aka zura 13 a raga a gasar Premier ta 2016-17
 14. Barcelona na zawarcin Semedo

  Mahukuntan Barcelona, Robert Fernandez da Javier Bordas sun isa birnin Lisbon na Portugal, domin kulla yarjejeniya da dan wasan Benfica, Nelson Semedo in ji Marca.

  Dan kwallon shi ne Barcelona ke son yin amfani da shi a baya daga gefen hagu.

  Kai tsaye
  Image caption: Semedo ne ake sa ran zai zama mai tsaron bayan Barcelona a bana
 15. Dani Alves ya yaudare ni - Guardiola

  Wasu jaridun Turai sun wallafa cewar kociyan Manchester City Pep Guardiola na fadin cewar Dani Alves ya yaudare shi.

  Tun farko Guardiola ya sa ran Alves zai koma City da murza-leda, amma sai ya ji cewar ya amince da yarjejeniyar buaga wa PSG tamaula, har ma ta bashi riga mai lamba 32.

  Kai tsaye
  Image caption: Guardiola ya horar da Alves a Barcelona
 16. Chelsea ta amince ta sayi Bakayoko

  Sky Sports ta ce Chelsea ta amince ta sayi dan wasan Monaco, Tiemoue Bakayoko

  Sky din ta kara da cewar dan wasan zai kai darajar Euro miliyan 45, kuma kafin karshen makonnan za a gwada lafiyarsa a Stamford Bridge.

  Kai tsaye
  Image caption: Tiemoue Bakayoko zai kai darajar Euro miliyan 45 a kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo
 17. An bai wa Chelsea damar daukar Aubameyang

  Jaridar Daily Mail ta wallafa cewar Borussia Dortmund ta bai wa Chelsea damar sayen Pierre-Emerick Aubameyang kan kudin fam miliyan 60.

  Tun farko kungiyar Tianjin Quanjian ta China ce ta so daukar dan kwallon mai shekara 28, amma yanzu ta ce ta janye daga zawarcin dan wasa.

  Kai tsaye
  Image caption: Dortmund ce ta lashe kofin kalubale na Jamus da aka kammala
 18. Jama'a barkanmu da saduwa a cikin shirinmu na yau

  Za mu kawo muku yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon Turai ke ci da sauran labaran da suka shafi tamaula. Za ku iya bayar da gudunmawarku kan shirin a BBC Hausa Facebook kai tsaye.