Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Aubameyang zai ci gaba da wasa a Dortmund
 2. Neymar zai ci gaba da wasa a Barcelona
 3. shin Perisic zai koma United?
 4. PSG na neman Alexis Sanchez
 5. Aguero zai koma Chelsea?
 6. Ko PSG za ta iya sayen Neymar
 7. Lukaku ya ci kwallon farko a United
 8. Mata zai yi jinyar mako daya
 9. Daniel Sturridge ya shirya tsaf - Klopp

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu da Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a shirinmu na gobe

 2. Leiva ya koma Lazio da wasa

  Dan kwallon Liverpool, Lucas Leiva ya kammala komawa Lazio domin ya taka mata leda kan kudi fan miliyan biyar. Lucas mai shekara 30, shi ne dan wasan Liverpool da ya fi dadewa a kungiyar, wanda ya koma Anfield a 2007 daga Gremio ta Brazil. Dan kwallon ya buga wa Liverpool wasa 345, inda ya fafata a gasar Premier sau 247.

  Kai tsaye
 3. West Ham United ta kammala daukar Hart

  Manchester City ta kammala bayar da Joe Hart aro ga kungiyar West Ham United.

  A bara ne kocin City, Pep Guardiola ya cewa Hart zai iya komawa wata kungiyar, domin ba zai yi amfani da shi ba.

  Mai tsaron ragar mai shekara 30, ya buga wasa aro a Torino a kakar da ta kare.

  Kai tsaye
 4. Arnautovic ya koma West Ham United

  West Ham United ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon Stoke City Marko Arnautovic.

  Tun farko Stoke City ta ki sallama tayin da West Ham ta yi wa dan wasan sau biyu, amma yanzu ta sayar mata da dan kwallon kan kudin da ake cewa ya kai fan miliyan 24.

  Arnautovic mai shekara 28, ya koma Stoke City daga Werder Bremen kan yarjejeniyar shekara hudu, kuma saura kaka daya ta rage masa a Stoke din.

  Dan wasan ya ci kwallo bakwai a wasa 35 da ya buga wa kungiyar a kakar da ta kare.

  Kai tsaye
 5. Aubameyang zai ci gaba da zama a Dortmund

  Daraktan Borussia Dortmund, Micheal Zorc ya ce Pierre-Emerick Aubameyang zai ci gaba da murza-leda a kungiyar.

  An yi ta alakanta Aubameyang mai shekara 28 da cewar zai koma gasar Premier da wasa ko Paris St-Germain ko kuma AC Milan a bana.

  Zorc ya ce Dortmund ta yanke shawarar ci gaba da amfani da Aubameyang a wasanninta, kuma shi a wajensa an kammala rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula ta Turai.

  A tsakar daren 31 ga watan Agusta za a rufe kasuwar cinikin 'yan wasan tamaula ta Jamus.

  Kai tsaye
 6. Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

  Shuaibu Adam Bagwai Hahaha to Arsenal dabara dai daman bata kai rakumi inda ake so har sai an hada da akala. Gara ma kufitar da makudan kudade kusayi 'yan wasan da zasu fitar daku kunya, domin ance "sayen nagari mai da kudi gida".

  Hashimu Waso cefane bane iya miya, 'yan Manchester United kuyi hattara akwai maza a gabanku up Chelsea.

  Hassan Musa Hadejia DW Gaskiya ina jin dadin shirinku, kuma yana kawatardani 100% kuma ina sanar da 'yan Manchester United mun yi shirin bugawa da kowa.

 7. Babu wanda ya taya Mahrez - Shakespeare

  Mai horar da Leicester City, Craig Shakespeare, ya ce har yanzu bai samu wata kungiyar da ta taya Riyad Mahrez ba.

  Sai dai kuma mai tsaron bayan Leicester City, Robrt Huth ba zai a fara gasar Premier da za a fara a cikin watan Agusta ba, sakamakon raunin da ya yi.

  Kai tsaye
 8. Trippier ya tsawaita zamansa a Tottenham

  Mai tsaron bayan Tottenham, Kieran Trippier ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a kungiyar zuwa shekara biyar.

  Dan wasan mai shekara 26 ya koma kungiyar da wasa daga Burnley kan kwantiragin shekara biyar.

  Kai tsaye
 9. Neymar zai ci gaba da wasa a Barcelona

  Neymar zai ci gaba da taka-leda a Barcelona duk da rade-radin da ake cewar zai koma Paris St Germain a bana.

  Mataimakin shugaban Barcelona Jordi Mestre ne ya tabbatar da cewar ba za su sayar da dan kwallon ba, zai kuma buga kakar wasan bana da za a fara a Spaniya.

  Rahotanni a Spaniya sun ce PSG na son sayen Neymar mai shekara 25, bayan da kungiyar ta dauki abokin wasansa a tawagar kwallon Brazil, Dani Alves.

  Neymar ya koma Barcelona a 2013, a kuma watan Oktoban 2016 ya tsawaita zamansa a Camp Nou kan yarjejeniyar shekara biyar.

  Kai tsaye
 10. Getafe ta dauki aron Bergara

  Getafe ta sanar da daukar Markel Bergara daga Real Sociadad domin ya buga mata tamaula aro a kakar da za a fara a bana.

  Kai tsaye
 11. Valencia zai ci gaba da yi wa United wasa a Amurka

  Mai tsaron bayan Manchester United, Antonio Valencia zai buga wa kungiyar wasan atisayen tunkakar gasar bana da take yi a Amurka duk da jan katin da aka yi masa a karawa da Salt Lake a ranar Litinin.

  A 2006 Paul Scholes da Wayne Rooney an hana su buga wa United wasa uku bayan da aka ba su jan kati a wasannin atisayen a Amsterdam.

  Mahukunta ne suka sauya dokar, inda suka ce sai anyi wani babban laifi ne za a dakatar da dan kwallo daga buga wasa, girman laifin da ya aikata.

  Kai tsaye
 12. Gasar damben Mota: Za a ci gaba da wasa

  Za a karasa wasan daf da na kusa da karshe a gasar damben cin mota a yammacin Talata a filin wasa na Ado Bayero Square da ke birnin Kanon Nigeria.

  Za a fara dambatawa tsakanin Bahagon Sanin Kurna daga Arewa da Bare-Bare daga Kudu.

  Sannan asa zare tsakanin Dan Ali Shagon Bata isarka daga Kudu da Sanin Shagon Kwarkwada daga Kudu.

  Kai tsaye
 13. Ramos da Marcelo sun ci kofi 15 a Madrid

  Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos da Marcelo sun lashe kofi 15 kowannensu a kungiyar.

  'Yan wasan biyu sun ci kofin Zakarun Turai uku da na Zakarun nahiyoyi biyu da La Liga hudu da Copa del Rey biyu da Uefa Super Cup biyu da na Spanish Super cup biyu.

  A kakar wasannin da aka kare Ramos da Marcelo suka lashe kofin La Liga da na Zakarun Turai.

  Wasu 'yan kwallon Madrid biyu da suke biye a yawan cin kofi a kungiyar su ne Karim Benzema da Cristiano Ronaldo wadanda kowannensu ya lashe guda 12.

  Kai tsaye
 14. Wenger na son kara sayen 'yan kwallo

  Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yana son ya kara sayen 'yan wasa kafin a fara kakar wasannin bana. Wenger ya ce a shirye yake ya kara karfin kungiyar, wanda tuni ya dauki Sead Kolasinac da kuma Alexandre Lacazette.

  Kai tsaye
 15. Ebola ya kai daf da karshe a damben mota

  Abdurrazak Ebola ya kai wasan daf da karshe a gasar damben cin mota a yammacin Litinin a filin wasa na Ado Bayero Square da ke birnin Kano, Nigeria.

  Ebola ya kai zagayen gaba ne bayan da ya doke Jirgi Bahago Guramada a turmin farko.

  Kai tsaye
 16. Ya ya batun komawar Perisic United ne?

  Jose Mourinho ya ce bai san me yake faruwa ba kan batun daukar Ivan Perisic na Inter Milan zuwa Manchester United.

  Ana alakanta cewar dan wasan tawagar Croatia zan koma Old Trafford da taka-leda kan kudi fan miliyan 48.

  Mourinho ya ce bai da masaniya a lokacin da aka tambayeshi batun dan wasan, bayan da United ta ci Real Salt Late 2-1.

  Kai tsaye
 17. Damben mota: Ali Kanin Bello ya kai daf da karshe

  Ali Kanin Bello ya kai wasan daf da karshe a gasar cin mota da ake yi a filin wasa na Ado Bayero Square da ke Kano Nigeria a yammacin Litinin.

  Ali kanin bello dan damben Arewa ya yi nasarar buge Ali Shagon Saiwa daga Kudu a turmin farko.

  Kai tsaye
 18. Shin ina Michu yake?

  Isah Sani Mai Arsenal Shin ina labarin dan wasan gabane swensea city wato michu? a wacce kugiya yake taka ledane yanzu?

  Amsa: Michu ya yi ritaya daga buga tamaula.

 19. Za a fara gasar kwallon golf a ranar Alhamis

  An raba jadawalin wasan zagayen farko a gasar kwallon golf ta 'yan wasa bibiyu, inda Henrik Stenson da Jordan Spieth za suyi wasa tare sai Dustin Johnson da Rory McIlroy a rukunin farko.

  Shi kuwa Sergio Garcia da Jason Day da Zach Johnson da Mark O'Meara da kuma Ryan Moore suna tare.

  Kai tsaye
 20. Ko za ku iya tuna dan wasa Michu?

  Shekara hudu da ta wuce Michu ya ci wa Swansea City kwallo 18 a gasar Premier a kaka daya ya zama na biyar a jerin wadan da suka fi cin kwallo a gasar ta Ingila, sannan ya ya jefa kwallo a raga a 2013 a League Cup wanda Swansea ta lashe kuma kofi na farko da ta dauka.

  Yanzu yana da shekara 31 ya kuma yi ritaya. Bayan da ya bar buga gasar Premier ya koma Napoli inda ya yi rauni a kafarsa daga nan ya koma Langreo da Real Oviedo a Spaniya, yanzu raunin ya hana shi murza-Leda.

  Kai tsaye