Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Hart zai koma West Ham United
 2. Romero ya tsawaita zamansa a Old Trafford
 3. Dambe: Ebola zai kara da Jirgi Bahago

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a gobe

 2. Watakila Morata ya koma Chelsea

  Gazzetta dello Sport ta ce watakila Alvaro Morata na Real Madrid ya koma Chelsea da murza-leda maimakon AC Milan ta Italiya.

  Kai tsaye
  Image caption: Kungiyoyi da dama na zawarcin Morata
 3. An ci kwallo 288 a gasar Firimiyar Nigeria

  Bayan da aka buga wasa 288 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria, an ci kwallo 575 a yayin da aka kammala wasannin mako na 29 a ranar Lahadi.

  Kungiyoyin da suka buga wasa a gida sun ci 446, yayin da wadan da aka karbi bakuncinsu suka zura 129. A ranar Laraba ake sa ran ci gaba da wasannin mako na 30.

  Kai tsaye
  Image caption: Stephen Odey na Mountain of Fire shi ne jagaba da kwallaye 17 a raga
 4. Hegazi zai buga wa West Brom tamaula

  West Brom ta dauki mai tsaron bayan tawagar kwallon kafa ta Masar, Ahmed Hegazi domin ya buga mata wasa aro. Hegazi ya koma West Brom daga Al Ahly wadda ya yi wa wasa aro, bayan da ya bar Fiorentina a 2015 sakamakon jinyar rauni da ya yi.

  Kai tsaye
  Image caption: Hegazi ya buga wa Fiorentina wasa, sannan ya koma Al Ahly
 5. Hamilton ya lashe tseren motoci ta Burtaniya

  Lewis Hamilton ya ce yana alfahari da ya shiga jerin kwararrun tseren motoci kamar Alain Prost da Jim Clark, bayan da ya lashe gasar Burtaniya karo na biyar a ranar Lahadi a Siverstone.

  Kai tsaye
  Image caption: Hamilton ne ya ci gasar tseren motoci ta Burtaniya kuma karo na biyar
 6. Liverpool za ta dauki 'yan wasan da suka da ce - Klopp

  Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce zai kammala sayen 'yan kwallon da yake bukata kafin a fara gasar kakar bana.

  Tuni Liverpool ta sayi Mohamed Salah daga Roma da Dominic Solanke, wanda yarjejeniyarsa ta kare da Chelsea a kakar da aka kammala. Haka kuma Klopp na zawarcin dan wasan RB Leipzig, Naby Keita.

  Kai tsaye
  Image caption: Liverpool za ta buga wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin Zakarun Turai
 7. Al Habsi ya koma Al Hilal

  Kungiyar Reading ta sanar da cewar mai tsaron ragarta Ali Al Habsi ya koma Al Hilal ta Saudi Arabia kan yarjejeniyar shekara uku.

  Kai tsaye
  Image caption: Al Habsi ya koma Reading daga Wigan
 8. Liverpool za ta dauki Van Dijk?

  Dan wasan Southampton mai tsaron baya, Virgil van Dijk zai iya komawa Liverpool kan kudi fam miliyan 60, bayan da dan kwallon ya ce yana son zuwa Anfield da taka-leda.

  Kai tsaye
  Image caption: Van Dijk ya ce yana son ya koma Liverpool da wasa
 9. Ebola zai kara da Jirgi Bahago

  Za a ci gaba da wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin mota a wasan damben gargajiya da ake yi a birnin Kanon Nigeria.

  A yammacin Litinin Ali Kanin Bello daga Arewa zai fara yin wasa da Alin Saiwa daga Kudu, bayan sun tashi a sa zare tsakanin Ebola daga Kudu da Jirgi Bahago Guramada.

  Ana yin damben ne a filin wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

  Kai tsaye
  Image caption: Ebola ne ya lashe motar farko da aka yi a bara
 10. Ko Dambele zai koma Arsenal?

  Arsenal za ta yi zawarcin dan kwallon Celtic mai shekara 21, Moussa Dembele idan har Alexis Sanchez ya bar Gunners in ji jaridar Daily Star.

  Kai tsaye
  Image caption: Daily Star ce ta wallafa cewar Dembele zai koma Arsenal idan Sanchez ya bar kungiyar
 11. Ba na son mu'amala da dangina- Emmanuel Adebayor

  Shahararren dan wasan kwallon kafa na Togo Emmanuel Adobayor ya ce ba ya son yin hulda da danginsa, amma kuma yana jin dadin mu'amala da abokansa.

  Video content

  Video caption: Ba na son mu'amala da abokaina
 12. Munich ta bar zawarcin Sanchez

  Bayern Munich ta ce ta bar zawarcin Alexis Sanchez na Arsenal.

  Shugaban kungiyar Munich, Kar-Heinz Rummenige ne ya sanar da cewar sun bar zawarcin dan kwallon Arsenal, za su mayar da hankali wajen atisayen tunkarar kakar bana da za a fara.

  Kai tsaye
  Image caption: Arsenal na sa ran Sanchez ya ci gaba da zama a Emirates
 13. Federer ya lashe kofi na takwas a gasar Wimbledon

  Roger Federer ya zama dan kwallon tennis na farko da ya lashe gasar Wimbledon sau takwas, bayan da ya doke Marin Cilica ranar Lahadi.

  Kai tsaye
  Image caption: Federer ya ci kofi na takwas a gasar kwallon tennis ta Wimbledon
 14. Jama'a barkanmu da saduwa a shirin mu na yau

  Za mu kawo muku yadda ake cin kasuwar 'yan wasan tamaula a Turai da wasu labarin wasanni