Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Chelsea ta amince ta dauki Morata
 2. Aguero zai ci gaba da wasa a Ettihad
 3. Arsenal na neman Karim Benzema
 4. Conte ne koci mafi tsada a tarihin Chelsea
 5. Ross Barkley na son komawa Tottenham
 6. Shugaban Barcelona ya ce babu inda Neymar zai je
 7. Leicester na sahun gaba wurin neman Kelechi Iheanacho

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu da Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin

  Da fatan za ku tara a shirinmu na gobe domin kawo muku wasu labaran wasanni.

 2. Wasannin mako 30 a gasar Firimiyar Nigeria

  Wasan Enugu Rangers da MFM ruwan sama ne ya hana a ci gaba da fafatawar, an tsayar da gobe domin a karasa karawar.

  Kai tsaye
 3. Sakamakon damben gasar mota

  Bahagon Sanin Kurna ya kai wasan daf da karshe a gasar damben mota a ranar Laraba a filin wasa na Ado Bayero Square da ke birnin Kanon Nigeria.

  Bahagon Sanin Kurna daga Arewa ya buge Bare-bare daga Kudu.

  Shi kuwa Dan Ali Shagon Bata isarka daga Kudu ya kai zagayen gaba bayan da ya sasanta da shi da Sanin Shagon Kwarkwada shi ma dan damben Kudu.

  Sauran wadanda suka kai wasan daf da karshe sun hada da Ali Kanin Bello daga Arewa da Abdurrazak Ebola.

  Kai tsaye
 4. Wasan damben gargajiya da aka yi a baya can

  Video content

  Video caption: Turmi uku suka dambata a tsakaninsu babu kisa aka raba su
 5. Sakamakon gasar Firimiyar Nigeria

  Wasannin mako na 30

  • Wikki 1-0 ABS
  • Katsina 1-0 Pillars
  • Remo Stars 1-1 3SC
  • Enyimba 2-1 Lobi
  • Plateau Utd 1-0 FCIU
  • Gombe Utd 0-0 Tornadoes
  • Abia Warriors 0-0 Akwa
  • Nasarawa 2-1 El-Kanemi
  • Rivers Utd 0-1 Sunshine Stars
 6. 'Yan wasan da aka haifa ranar 19 ga Yuli

  Matt Miazga shekara 22

  Neto shekara 28

  Kevin Großkreutz shekara 29

  Nene shekara 36

  Josue shekara 38

  Ebbe Sand shekara 45

 7. Bolt zai yi ritaya bayan tseren Landan

  Usain Bolt ya ce zai fafata a tseren mita 100 da kuma ta 'yan wasa hudu a gasar da birnin Landan zai karbi bakuncin duniya a Agusta.

  Bolt din wanda ya lashe lambar zinare takwas a Olympic ya ce da zarar ya kammala wasa a tseren Landan din zai yi ritaya.

  Za a fara tseren mita 100 a ranar 5 ga watan Agusta, sannan a yi ta 'yan wasa hudu a ranar ta Asabar daga na Bolt ya rataye takalmansa.

  Kai tsaye
 8. Barcelona ta je Amurka da 'yan wasa 26

  Sabon kociyan Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 26 da ya tafi da su Amurka a ranar Laraba, domin buga atisayen tunkarar kakar bana.

  Barcelona za ta buga gasar International Champions Cup, inda za ta kara da Juventus ranar 22 da watan Yuli da Manchester United 26 ga watan da kuma Real Madrid a ranar 29 ga watan na Yuli.

  Ga jerin 'yan wasan Barca da ta je da su Amurkan: Pique da Rakitic da Sergio da Denis Suarez da Arda da Iniesta da Suarez da Messi da Neymar Jr. da Cillessen da Mascherano da Paco Alcacer da Jordi Alba da Digne da S. Roberto da Aleix Vidal da Umtiti da Semedo da Marlon da Douglas da Samper da Vermaelen da Munir da Ortola da Jokin da Ezkieta da kuma Alena.

  Kai tsaye
 9. Juankar ya koma Malaga zuwa 2021

  Juankar ya zama dan kwallon Malaga, bayan da ya buga mata wasa aro kakar wasa biyu.

  Dan kwallon ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu.

  Kai tsaye
 10. Takaitattun labarin wasanni

  Wanda muka gabatar a ranar Talata

  Video content

  Video caption: Takaitattun labarin wasanni na Talata 18072017
 11. Arsenal ta ci Munich a fenariti

  Arsenal 1-1 Bayern Munich

  Arsenal ta doke Munich 3-2 a bugun fenariti

 12. Arsenal ta farke kwallon da Munich ta ci

  Arsenal 1-1 Bayern Munich

  Kai tsaye
 13. Ana tauye hakkin kwararrun 'yan kwallon Afirka

  Video content

  Video caption: Ana tauye hakkin wasu 'yan kwallon Afirka
 14. A rana irin ta 19 ga Yuli..........

  A rana irin ta 19 ga watan Yulin bara Liverpool ta amince ta dauki Christian Benteke daga Aston Villa kan kudi fan miliyan 32.5.

  Kai tsaye
 15. Watakila Giroud ya koma Everton

  Everton na son sayen dan kwallon Arsenal, Olivier Giroud bayan da Borrusia Dortmund ta ce ba za ta sayar da Pierre-Emerick Aubameyang in ji Daily Telegraph.

  Kai tsaye
 16. Damben gasar mota ta Kano

  Zubar ruwan sama ne ya hana ci gaba da damben gasar cin mota a ranar Talata tsakanin Bahagon Sanin Kurna daga Arewa da Bare-Bare daga Kudu da fafatawa tsakanin Ali Shagon Bata isarka daga Kudu da Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu a gumurzun wasan daf da na kusa da na karshe.

  Muhukuntan gasar sun tsayar da ranar Laraba da yammaci domin ci gaba da wasannin a filin wasa na Ado Bayero Square da ke Kanon Nigeria.

  Kai tsaye
 17. Arsenal ta sauya Kolasinic

  Arsenal 0-1 Bayern Munich

  Arsenal ta sauya dan sabon dan wasan da ta dauka a bana Saed Kolasinic.

 18. Gasar Firimiyar Nigeria mako na 30

  Alkalan wasan Wikki da ABS

  Alkali: Imam M. Umar

  Mataimaki na daya: Shehu Saidu

  Mataimaki na biyu: Ibrahim Yusuf

  Mai jiran kar-ta-kwana: Musa I. Daura

  Kai tsaye
 19. Benteke zai buga wa Palace wasa

  Liverpool v Crystal Palace

  Crystal Palace za ta fara wasa da Christian Benteke a karawa da za ta yi da tsohuwar kungiyarsa Liverpool a Hong Kong.

 20. Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

  Sa'idu Gagiyo Katamma Ni Magoyin Bayan Manchester United ne kuma ina yi wa kungiyar fatan alkairi, ina bukatar kungiyar ta saya mana 'yan wasan tsakiya mai tare kwallon.