Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu, Abdulwasiu Hassan da Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin

  Tare da fatan za ku tara a shirinmu na ranar Lahadi.

 2. Madrid ta gabatar da Ceballos

  Real Madrid ta gabatar da Dani Ceballos a gaban magoya bayanta a filin wasanta a Santiago Bernabeu na ranar Alhamis. A ranar 14 ga watan Julin 2017 Madrid ta sayi dan wasan daga Real Betis kan yarjejeniyar shekara shida.

  Kai tsaye
 3. An tuntubi Mbappe ta bayan gida - Monaco

  Monaco ta zargi wasu kungiyoyin nahiyar Turai da yin magana da dan wasanta Kylian Mbappe ta bayan gida.

  Kai tsaye
 4. CAF ta kara kasashen da suke buga kofin Afirka

  Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta kara kasashen da za su fafatawa a gasar cin kofin nahiyar zuwa 24 da za a fara a wasannin da Kamaru za ta karbi bakunci a 2019.

  Tun farko hukumar tana gudanar da gasar da kasashe 16, sai dai kuma ba ta fayyace ko za ta gusar da wasannin daga watan Janairu zuwa Fabrairu daga gudanarwa zuwa Yuni da Yuli ba.

  Kai tsaye
 5. A rana irin ta yau United ta taya Van Persie

  A rana ta 19 ga watan Yuli kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya tabbatar da cewar yana zawarcin Robin van Persie kyaftin din Arsenal.

  Daga baya ne dan wasan ya koma United ya kuma taka rawa a kakar da kungiyar ta lashe Premier a 2012/13.

  Kai tsaye
 6. Werder Bremen na son aron Martial

  Werder Bremen na son ta dauki aron dan kwallon Manchester United Anthony Martial.

  Kai tsaye
 7. Liverpool za ta sake taya Keita

  Jaridar The Mirror ta shirya taya mai wasan tsakiya na RB Leipzig, Naby Keita kan kudi fan miliyan 70, tun farko anki sammala tayin fan miliyan 66 da kungiyar ta yi wa dan wasan tawagar kwallon kafa ta Guine mai shekara 22.

  Kai tsaye
 8. Wa zai taka rawa tsakanin Morata da Lukaku da Lacazette

  Cikin manyan 'yan wasa uku da suke cin kwallo da aka saya a gasar Premier tsakanin Alvaro Morata da Alexandre Lacazette da kuma Romelu Lukaku wa zai fi taka rawar gani a bana?

  Kai tsaye
 9. Juventus ta sayi Sciglio

  Juventus ta kammala daukar Mattia de Sciglio mai shekara 24 daga AC Milan kan kudi fan miliyan 10.64.

  Kai tsaye
 10. AC Milan ta dauki Bonucci

  AC Milan ta dauki Leonardo Bonucci Kungiyar AC Milan ta dauki Leonardo Bonucci kan kudi da ake cewa ya kai fan miliyan 40 daga Juventus.

  Dan kwallon mai shekara 30, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku da Milan wadda ta kashe fan miliyan 160 wajen sayo 'yan wasa a bana.

  Kai tsaye
 11. Damben gasar cin mota wasan daf da karshe

  Za a fitar da jadawalin wasan daf da karshe a gasar cin mota wadda ake yi a Kanon Nigeria da yammacin Alhamis.

  'Yan wasan da suka kai wasannin daf da karshe sun hada da Ali Kanin Bello daga Arewa da Bahagon Sanin Kurna daga Arewa da Dan Ali Shagon Bata isarka daga Kudu da Abdurrazak Ebola daga Kudu

  Za kuma a buga wasan karshe da matsayi na uku a ranar Asabar a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Garin Kanon Nigeria.

  Kai tsaye
  Image caption: Dan Aliyu da Shagon Mada
 12. Yadda tebur yake bayan mako na 30 a Firimiyar Nigeria

  Kai tsaye
 13. West Ham na daf da daukar aron Hernandez

  West Ham na daf da daukar aron Hernandez West Ham United ta kusa dauko aron dan kwallon Bayer Leverkusen, Javier Hernandez domin ya buga mata wasa.

  West Ham tana da tabbacin son daukar tsohon dan kwallon Manchester United mai shekara 29, amma ba a fayyace kudin da za ta biya ba.

  Kai tsaye
 14. Takaitatun labarin wasanni na Laraba

  Video content

  Video caption: Takaitattun Labarin Wasanni 19072017
 15. United za ta taya Aurier

  Manchester United na son daukar matashin dan wasa mai shekara 24 dan wasan Paris St-Germain mai tsaron baya Serge Aurier, bayan da tattaunawa da United ke yi kan sayen Fabinho na Monaco ta ci tura in ji Independent.

 16. Yadda guragu ke buga kwallo

  Video content

  Video caption: Yadda Guragu ke buga kwallo
 17. Sakamakon wasan mako na 30 a Firimiyar Nigeria

  Kai tsaye
 18. Manchester City na neman Danilo?

  Danilo da Ronaldo

  Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ce Manchester City na son sayen dan wasan bayan Real Madrid Danilo, wanda dan kasar Brazil ne.

  Kudin cinikin dan kwallon ka iya kai wa fan miliyan 26 da rabi.

 19. Chelsea za ta yi murna da sayen Morata - Nevin

  Tsohon dan wasan Chelsea Pat Nevin ya ce magoya bayan kulob din za su zuba ruwa a kasa su sha bayan da suka sayi Alvaro Morata.

  Morata, mai shekara 24, zai tattauna kan yarjejeniyar da zai sa hannu sannan a gwada lafiyarsa a cinikin da zai kai fam miliyan 60.

  Alvaro Morata
 20. Neymar ba na sayarwa ba ne - Bartomeu

  Jaridu da dama na rawaito cewa Paris St-Germain a shirye suke su tattauna da Barcelona kan sayen Neymar a farashin da ka iya kai wa fan miliyan 196.

  Sai dai Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya shaida wa BBC cewa dan kwallon na Brazil, mai shekara 25 ba na sayarwa ba ne.

  Neymar