Kungiyar Juventus na son ta taya mai tsaron bayan Manchester City, Eliaquim Mangala, bayan da ta sayar da Leonardo Bonucci.
An ce Juventus din na son taya dan kwallon kan fan miliyan 20.
An tsawaita hukuncin dakatar da Bailly
Dan kwallon Manchester United, Eric Bailly ba zai bugawa kungiyar wasa uku ba, sakamakon jan kati da aka yi masa a karawa da Celta Vigo a gasar Europa League.
Jordan Spieth ya ce bai fuskanci kalubale wajen lashe gasar kwallon golf da aka kammala a Royal Birkdale ba, inda hakan ya sa ya kara cin kofi bayan na kwararru da na US Open.
Southampton ba ta je Amurka da Van Dijk ba
Kungiyar Southampton ba ta je Faransa wasan atisaye da Virgil Van Dijk ba, bayan da ta bar shi a gida.
Ana alakanta cewar kungiyoyi da yawa na zawarcin Van Dijk kan kudi mai tsoka.
Wasu rahotanni na cewa Liverpool ta daina batun son daukar dan kwallon wanda ta fara zawarci tun da aka bude kasuwar bana, inda a lokacin ake cewa Southampton za ta yi karar Liverpool kan ta tuntubi dan wasan ta bayan gida.
Kocin Chelsea Antonio Conte ya tabbatar da cewar mai buga masa wasan tsakiya Pedro ya yi rauni a lokacin da ya yi taho mu gama da mai tsaron ragar Arsenal, David Ospina, a wasan sada zumunta da suka yi a Beijing.
Conte ya ce yana sa ran Pedro zai dawo atisaye nan da kwana 10 tare da fuskar roba da za a kera masa.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Mendy ne mai tsaron baya mafi tsada
Manchester City ta kashe sama da fan miliyan 200 wajen sayen kwallo a bana, bayan da Benjamin Mendy daga Monaco ya kammala komawa Ettihad a ranar Litinin.
Dan wasan tawagar Faransa da City ta saya kan fan miliyan 52 ya zama mai tsaron baya da aka dauka mafi tsada a duniya a bana.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Takaitattun Labarin wasanni na safiyar Litinin
Video content
Video caption: Takaitattun Labarin wasanni a safiyar Litinin 24072017Takaitattun Labarin wasanni a safiyar Litinin 24072017
Boxing
Video content
Video caption: Turmi uku suka dambata a tsakaninsu babu kisa aka raba suTurmi uku suka dambata a tsakaninsu babu kisa aka raba su
Dan Aminu ya buge Shagon Abata mai
Dambe 12 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja. Nigeria a safiyar Lahadi.
An fara sayar da tikitin damben Mayweather da McGregor
Sauran kasa da wata daya a dambata tsakanin Floyd Mayweather da Conor McGregor a karawar da masu son dambe ke son gani a duniya.
An fara sayar da tikitin kallon dambatawar a Intanet a ranar Litinin da wasu wuraren a Las Vegas.
Karawar da za a yi ta a cikin watan Agusta, za a kalli damben daga tsakanin dala 500 zuwa 10,000.
Haka kuma akwai tikitin dala 1,500 da 2,500 da 3,500 da 5,000 da kuma 7,500.
An kuma takaita cewar tikiti biyu za a bai wa gidan da suke da yawa domin kallon karawar.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Teburin gasar Firimiya bayan mako na 31
LMCNPFLCopyright: LMCNPFL
Sakamakon mako na 31 a gasar Firimiyar Nigeria
Mountain of Fire ta ci Katsina United 3-2 a wasan mako na 31 da suka karasa a safiyar Lahadi.
LMCNPFLCopyright: LMCNPFL
Ko Wilshere zai koma Turkiya kuwa?
Daily Mail ta wallafa cewar kulob din Turkiya Antalyaspor na kokarin daukar dan wasan Arsenal, Jack Wilshere, sai dai shugaban kulob din ya ce Arsenal ta saka buri kan dan kwallon.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Inter za ta dauki Vidal
Inter na son taya Arturo Vidal kan kudi fan miliyan 50 in ji La Gazzetta, koda yake Bayern Munich ta ce ba ta shirya sayar da dan wasan ba.
MarcaCopyright: Marca
Liverpool za ta sake taya Keita
Sky Sports ta ce Liverpool za ta sake taya dan kwallon RB Leipzig, Naby Keita tun farko anki sallama mata dan wasan kan tayin fan miliyan 70 da ta yi.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Koscielny zai ci gaba da wasa a Emirates
Zan ci gaba da zama daram a Arsenal - Koscielny
Quote Message: Ina da yarjejeniyar buga wa Arsenal tamaula shekara da yawa, kuma banga dalilin da zai sa na bar Gunners ba from Laurent Koscielny
Ina da yarjejeniyar buga wa Arsenal tamaula shekara da yawa, kuma banga dalilin da zai sa na bar Gunners ba
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Sanchez zai yi zamansa a Arsenal
Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce Alexis Sanchez bai nemi ya bar kungiyar a bana ba, saboda haka yana sa ran zai ci gaba da wasanninsa a Emirtaes.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Southampton ta bar Van Dijk a gida
Southampton ba ta sanya sunan kyaftin dinta Virgil van Dijk a jerin 'yan wasan da za ta tafi da su atisayi Faransa a wannan makon ba.
Kocin kulob din Mauricio Pellegrino ya fada a makon da ya gabata cewa Van Dijk na yin atisayi shi kadai saboda dan kwallon ba shi da tabbas kan makomarsa kuma hankalinsa a rabe ya ke.
Rahoto kai-tsaye
time_stated_uk
Wakar Jafaru - Hussaini dan mai kotso
Damben gargajiya
Video content
Ya kamata Martial ya jajirce - Mourinho
Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya bukaci Anthony Martial ya zama yana kan ganiyarsa a koda yaushe.
Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin
Juventus na son taya Mangala
Kungiyar Juventus na son ta taya mai tsaron bayan Manchester City, Eliaquim Mangala, bayan da ta sayar da Leonardo Bonucci. An ce Juventus din na son taya dan kwallon kan fan miliyan 20.
An tsawaita hukuncin dakatar da Bailly
Dan kwallon Manchester United, Eric Bailly ba zai bugawa kungiyar wasa uku ba, sakamakon jan kati da aka yi masa a karawa da Celta Vigo a gasar Europa League.
Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin
Spieth zai kara daura damara
Jordan Spieth ya ce bai fuskanci kalubale wajen lashe gasar kwallon golf da aka kammala a Royal Birkdale ba, inda hakan ya sa ya kara cin kofi bayan na kwararru da na US Open.
Southampton ba ta je Amurka da Van Dijk ba
Kungiyar Southampton ba ta je Faransa wasan atisaye da Virgil Van Dijk ba, bayan da ta bar shi a gida.
Ana alakanta cewar kungiyoyi da yawa na zawarcin Van Dijk kan kudi mai tsoka.
Wasu rahotanni na cewa Liverpool ta daina batun son daukar dan kwallon wanda ta fara zawarci tun da aka bude kasuwar bana, inda a lokacin ake cewa Southampton za ta yi karar Liverpool kan ta tuntubi dan wasan ta bayan gida.
Latsa nan don karanta labarin
Za a yi wa Pedro fuskar roba
Kocin Chelsea Antonio Conte ya tabbatar da cewar mai buga masa wasan tsakiya Pedro ya yi rauni a lokacin da ya yi taho mu gama da mai tsaron ragar Arsenal, David Ospina, a wasan sada zumunta da suka yi a Beijing. Conte ya ce yana sa ran Pedro zai dawo atisaye nan da kwana 10 tare da fuskar roba da za a kera masa.
Mendy ne mai tsaron baya mafi tsada
Manchester City ta kashe sama da fan miliyan 200 wajen sayen kwallo a bana, bayan da Benjamin Mendy daga Monaco ya kammala komawa Ettihad a ranar Litinin. Dan wasan tawagar Faransa da City ta saya kan fan miliyan 52 ya zama mai tsaron baya da aka dauka mafi tsada a duniya a bana.
Takaitattun Labarin wasanni na safiyar Litinin
Video content
Boxing
Video content
Dan Aminu ya buge Shagon Abata mai
Dambe 12 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja. Nigeria a safiyar Lahadi.
Latsa nan domin karanta cikakken labarin
An fara sayar da tikitin damben Mayweather da McGregor
Sauran kasa da wata daya a dambata tsakanin Floyd Mayweather da Conor McGregor a karawar da masu son dambe ke son gani a duniya.
An fara sayar da tikitin kallon dambatawar a Intanet a ranar Litinin da wasu wuraren a Las Vegas. Karawar da za a yi ta a cikin watan Agusta, za a kalli damben daga tsakanin dala 500 zuwa 10,000.
Haka kuma akwai tikitin dala 1,500 da 2,500 da 3,500 da 5,000 da kuma 7,500. An kuma takaita cewar tikiti biyu za a bai wa gidan da suke da yawa domin kallon karawar.