Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin

  Da fatan za ku tara a gobe domin jin wasu sabbin labarin wasanni

 2. Teburin gasar Firimiyar Nigeria bayan mako na 31

  Kai tsaye
 3. Rivers da Akwa sun tashi 1-1

  Gasar Firimiyar Nigeria kwantan wasan mako na 22

  Rivers United da Akwa United sun raba maki a tsakaninsu, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a kwantan wasan mako na 22 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria da suka fafata a ranar Laraba.

  Da wannan sakamakon Akwa United tana ta uku a kan teburin gasar da maki 51, ita kuwa Rivers United tana ta 12 da maki 41 da kwantan wasa daya da za ta yi da Kano Pillars.

  Har yanzu Plateau Uniteds ce a matsayi na daya, sai Mountain of Fire biye da ita.

  Kai tsaye
 4. Wilshere ba ya son ya bar Landan

  Independent ta ce Jack Wilshere na Arsenal bai son ya yi nisa da Landan, kuma zai so ya koma West Ham a bana maimakon ya bar buga gasar Premier.

  Kai tsaye
 5. Renato ya ce yana son ya bar Munich

  Jaridar Independence

  Renato Sanchez ya ce yana son barin Bayern Munich a bana, AC Milan da Manchester United na daga cikin kungiyoyin da ke son daukarsa, wanda aka yi masa darajar fan miliyan 43 in ji Independent.

  Kai tsaye
 6. Liverpool ba ta fargabar ta kashe kudi

  Daily Mail ta wallafa cewar kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba sa jin tsoron kashe kudi wajen sayo 'yan wasa a bana, kuma zai ci gaba da zawarcin dan kwallon Southampton mai tsaron baya Virgil van Dijk.

  Kai tsaye
 7. Coutinho ba na sayarwa bane

  Jaridar Daily Star

  Liverpool ta ce ba za ta sayar da Coutinho ko nawa za a taya shi, amma Barcelona za ta biya fan miliyan 80 idan za a sayar mata da dan wasan Daily Star.

  Kai tsaye
 8. Barcelona za ta sake taya Coutinho

  Jaridar Sports

  Barcelona ta tura wakilai zuwa Ingila kan batun Philippe Coutinho, duk da kin sallama tayin fan miliyan 72 da Liverpool ta yi kan dan kwallon mai shekara 25 in ji Sports.

  Kai tsaye
 9. Arsenal za ta biya kudin Lemar

  Jaridar The Sun

  Arsenal na daf da daukar dan kwallon Monaco, Thomas Lemar kan fan miliyan 45 in ji The Sun.

  Kai tsaye
 10. Madrid da Man City za su kece raini a Amurka

  Kungiyar Real Madrid za ta kara da Manchester City a gasar International Champions Cup a ranar Alhamis a Amurka.

  Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin za su kara a gasar, kuma a wasan farko da suka yi a Australia kaka biyu da ta wuce, Real ce ta doke City 4-1.

  Cikin haduwa hudu da aka yi tsakanin kungiyoyin biyu, Real Madrid ta ci wasa biyu sannan suka yi kunnen doki a karawa biyu.

  A gasar bana Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 2-0, sannan United ta yi nasara a kan Madrid a bugun fenariti, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1.

  Kai tsaye
 11. Dambe tsakanin Shagon Mada da Dan Aminu Langa-Langa

  Wata karawar da suka taba yi a baya a Abuja, Nigeria.

  Video content

  Video caption: Damben gargajiya da aka yi da safiyar Lahadi a Abuja, Nigeria
 12. Za a hana wasu kungiyoyin China wasa a badi

  An umarci kungiyoyin kwallon kafa na China 13 da su sauke bashin da ke kansu ko kuma a hana su shiga gasar tamaula ta kasar ta badi.

  Hukumar kwallon kafa ta China ce ta rubuta wasikar umarnin ga kungiyoyin da bashin ya yi wa katutu ciki har da manyan kungiyoyi uku da kanana biyar masu buga karamar gasar kasar.

 13. Barkley na son barin Everton

  Ronald Koeman ya ce Ross Barkley yana son ya gwada sa'a a wani kulob din kuma Everton a shirye take ta bar shi ya bar kungiyar a bana.

  Saura shekara daya yarjejeniyar Barkley mai shekara 23, ta kare da Everton, kuma bai saka hannu kan tsawaita zamansa ba.

  Haka kuma Koeman ya ce ya taya Gylfi Sigurdsson na Swansea City kan kudi fan miliyan 40, sai dai kungiyar ta ce za ta sallamar masa a kan fan miliyan 50.

  Kai tsaye
 14. Peaty ya yi mamakin rawar da yake takawa a Linkaya

  Adam Peaty ya ce ya yi mamaki da irin bajintar da ya yi a wasan linkaya.

  Dan wasan mai shekara 22 ya doke tarihin kammala tseren cikin ruwa da kirji da ya kafa da kansa sau biyu a gasar duniya da ya fafata a Budapest.

  Zakaran da ke rike da kambu James Guy da kuma Duncan Scott ba su kai bantensu ba.

  Kai tsaye
 15. Mourinho ya shirya wa gasar Premier

  Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce sun shirya kan yadda za su lashe gasar Premier da za a fara a cikin watan Agusta, kuma yana son ya daura damarar cin kofin Zakarun Turai.

  Kai tsaye
 16. Mbappe zai yi zamansa a Monaco

  Kungiyar Monaco na tattaunawa da Kylian Mbappe domin ta tsawaita yarjejeniyar dan kwallon ya ci gaba da wasa a Faransa in ji mataimakin shugaban kungiyar.

  Tun farko an alakanta kungiyoyi da dama na zawarcin dan kwallon mai shekara 18 , ciki har da Real Madrid wadda ake cewa za ta saya kan Yuro miliyan 180.

  Vadim Vasilyev ya ce Monaco ta samu kungiyoyi da dama da suke son daukar dan kwallon a bana.

  Kai tsaye
 17. Man City ba ta zawarcin Mbappe

  BBC ta fahimci cewar Manchester City ba ta taya dan kwallon Monaco, Kylian Mbappe ba, dan kwallon da ake cewa zai koma taka-leda a Real Madrid kan kudi Yuro miliyan 160.

  Sai dai har yanzu City tana son sayen Alexis Sanchez na Arsenal

  Kai tsaye
 18. Gasar tennis ta German Open

  Aljaz Bedene ya yi nasarar doke Jose Hernandez-Fernandez a wasan zagayen farko a gasar kwallon tennis ta German Open.

 19. Wadanda ke kan gaba a yawan cin kwallaye

  Gasar Firimiyar Nigeria bayan da aka yi mako na 31

  Kai tsaye
 20. Djokovic ba zai karasa wasannin bana ba

  Tsohon Zakaran kwallon tennis karo 12 na duniya, Novak Djokovic ba zai karasa sauran wasannin gasar kwallon tennis ta bana ba, sakamakon raunin da yake fama da shi a gwiwar hannunsa.

  Djokovic mai shekara 30, bai karasa karawar da ya yi da Tomas Berdych a ranar 12 ga watan Yuli a gasar Wimbledon sakamakon raunin.

  Dan wasan ya ce yana fama da ciwon sama da shekara daya da rabi.

  Kai tsaye