Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshem shirin

  Da fatan za ku tara a ranar Ltinin domin jin wani sabon shirin labaran wasanni

 2. Allardyce - Kudin da ake sayen 'yan wasa na sa matsi ga koci

  Tsohon kocin tawagar kwallon kafa ta Ingila Sam Allardyce ya ce tsabagen kudin da ake sayen 'yan wasan tamaula na kara matsi ga mai horar da kwallon kafa.

  Sama da fan miliyan 850 aka kashe wajen sayen 'yan kwallon da za su buga gasar Premier daga kasuwar da za ta daina ci a tsakar daren 31 ga watan Agusta.

  Allardyce mai shekara 62 ya yi murabus daga horar da Crystal Palace a watan Mayu, inda ya ce kungiyoyi na dora buri kacokan ga koci.

  Kai tsaye
 3. Har yanzu PSG na neman Neymar

  L'Equipe ta ce Paris St Germain nada tabbacin za ta kammala daukar Neymar daga Barcelona kan kudi fan miliyan 198 nan da kwana 15.

  Kai tsaye
 4. Allardyce zai dawo horar da tamaula

  Tsohon kocin tawagar kwallon kafar Ingila, Sam Allardyce ya shaidawa BBC cewar zai dawo horar da tamaula nan gaba.

  Allardyce ya yi ritaya daga jan ragamar Crystal Palace bayan da ya haurar da kungiyar daga siratsi.

  Kai tsaye
 5. 'Yan wasan da Chelsea ta dauka a bana

  Wadan da ta dauka: Willy Caballero (Manchester City,) Rudiger (Roma kan Yuro miliyan), Bakoyoko (Monaco, Yuro miliyan 40), Morata (Real Madrid, fan miliyan 60)

  Wadan da suka barta: Ake (Bournemouth, Yuro miliyan 23), Cuadradofalse(Juventus, Yuro miliyan), Begovic (Bournemouth, Yuro miliyan 11.5), Bertrand Traore (Olympique Lyon, Yuro miliyan 10), Atsu (Newcastle, Yuro miliyan 7.5), Solanke (Liverpool, yarjejeniya ce ta kare), Terry (Aston Villa, yarjejeniya ce ta kare), Abraham (Swansea, aro), Aina (Hull, aro), Loftus-Cheek (Crystal Palace, aro), Chalobah (Watford, Yuro miliyan 5.7), Van Ginkel (PSV, aro), Zouma (Stoke, aro)

  Kai tsaye
 6. Har yanzu City na son daukar Mbappe

  Daily Mail ta ce koci Pep Guardiola ya ce Manchester City tana da kudin da za ta kalubalanci Real Madrid kan daukar Kylian Mbappe na Monaco.

  Kai tsaye
 7. Za a ci gaba da Firimiyar Nigeria a ranar Lahadi

  Wasan mako na 32

  Kai tsaye
 8. Barca za ta maye gurbin Neymar da Coutinho

  Talksport ta ce Barcelona za ta dauki Philippe Coutinho daga Liverpool domin maye gurbin Neymar idan ya koma PSG.

  Kai tsaye
 9. Golan Watford ya tsawaita zamansa

  Mai tsaron ragar Watford, Heurelho Gomes ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu a kungiyar.

  Golan mai shekara 36 ya buga wa kungiyar wasa sama da 100 tun lokacin da ya koma kungiyar a 2014.

 10. Real za ta bai wa United Bale

  Jaridar Independence

  Independence ta ce idan har Real Madrid ta dauki Kylian Mbappe daga Monaco, za ta sayarwa da Manchester United, Gareth Bale.

  Kai tsaye
 11. Dan Moyi mawakin damben gargajiya

  Wakar da ya yi wa Shamsu Kanin Emi dan wasan Arewa

  Video content

  Video caption: Dan Moyi - wakar Shamsu kanin Emi
 12. Football

  Shugaban hukumar kwallon kafar Spaniya, Angel Maria Villar ya yi ritaya daga mukamin mataimakin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Turai da na mataimakin Fifa.

  A farkon watan nan jami'an tsaro suka damke Villar kan zargin almubazzaranci da rubuta takardun jabu.

  Sai dai kuma ya karyata zargin da ake yi masa, amma ba zai sake jagoranci hukumomin ba.

 13. Tottenham ba ta dauki dan wasa ba

  Bayan da Tottenham ta yi ta biyu a gasar Premier da aka kare, har yanzu kungiyar ba ta dauki dan wasa ko daya ba.

  Kungiyar za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai da za a yi a bana.

  Tottenham ta sayar da mai tsaron bayanta Kyle Walker ga Manchester City kan kudi fan miliyan 45.

  Kai tsaye
 14. Froome zai shiga tseren Vuelta

  Chris Froome ya tabbatar da cewar zai fafata a tseren kekuna da za a yi a Vuelta ta Espana, bayan da ya ci Tour de France ta shekarar nan ta uku a jere ta hudu jumulla.

  Kai tsaye
 15. Kalas ya tsawaita zamansa a Chelsea

  Tomas Kalas ya tsawaita zamansa a Stamford Bridge zuwa shekara hudu, sai dai kuma Chelsea ta sake bayar da shi aro ga Fulham.

 16. AC Milan na son daukar Costa

  Kungiyar AC Milan na son ta sayi Diego Costa na Chelsea, kafin ta dauki Nikola Kalinic daga Fiorentina.

  Sai dai Costa ya fi son ya koma Atletico Madrid.

  Kai tsaye
 17. Kun san 'yan wasan da Man City ta dauka?

  Manchester City ta kashe sama da fam miliyan 200 a lokacin bazarar nan domin tunkarar kakar wasa ta bana.

  'Yan wasan da City ta saya sun hada da:

  • Kyle Walker (fam miliyan 45)
  • Bernardo Silva (fam miliyan 43)
  • Ederson Moraes (fam miliyan 43)
  • Benjamin Mendy (fam miliyan 52)
  • Danilo (fam miliyan 26.5)
  Kyle Walker
 18. Za a raba jadawalin WAFU Cup 2017

  Za a raba jadawalin gasar WAFU Cup ta bana a ranar Alhamis a otal din Labadi beach da ke Accra, Ghana.

  Za a fara wasannin tsakanin 9 zuwa 24 ga watan Satumbar 2017 a filin wasa na Sekondi.

  Ga kasashen da za su kara a gasar:

  Benin

  • Burkina Faso
  • Cape Verde
  • Ivory Coast
  • Gambia
  • Ghana
  • Guinea
  • Guinea Bissau
  • Liberia
  • Mali
  • Mauritania
  • Niger
  • Nigeria
  • Senegal
  • Sierra Leone
  • Togo
 19. Rooney zai buga wa Everton gasar Europa

  Wayne Rooney ya ce a koda yaushe yana dokin buga wa Everton wasa a gasar Zakarun Turai ta Europa.

  Everton za ta buga wasan cike gurbi da MFK Ruzomberok ta Slovakia a Goodison Park a yammacin Alhamis.

  Rooney mai shekara 31, zai buga wa Everton karawar a karon farko tun bayan da ya bar kungiyar sama da shekara 13 ya koma Manchester United.

  Ya koma United da taka-leda yana da shekara 18 kan kudi fan miliyan 27 a shekarar 2004.

  Kai tsaye
 20. Takaitattun Labarin Wasanni

  Video content

  Video caption: Takaitattun Labaran Wasanni 27072017