Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Coutinho ba zai bar Liverpool ba - Klopp
 2. United ta kammala sayen Matic
 3. An dakatar da Phil Jones buga wasa biyu
 4. Barcelona za ta yi karar PSG
 5. Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji
 6. Sanchez zai fara atisaye ranar Talata
 7. Madrid za ta yi wasa shida a watan Agusta
 8. Arsenal ta lashe Emirates Cup na bana
 9. Hamilton ya yi na hudu a tseren Hungarian Grand Prix

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Rudisha ba zai shiga gasar tseren Landan ba

  Zakaran tseren mita 800, David Rudisha, ba zai buga gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya ba, sakamakon raunin da ya yi.

  Dan wasan na kasar Kenya mai shekara 28, ya ce a shafinsa na twitter ya yi matukar bakin-ciki da takaici, da ba zai halarci wasannin da za a fara daga 4 zuwa 13 ga watan Agusta a Landan ba.

  A shekarar 2012 ne ya lashe lamabar zinare a gasar Olympiccs da aka yi a Landan, da kuma wacce aka yi a Rio din Brazil a shekarar da ta gabata.

  Kai tsaye
 2. Uganda ta nada masu horar da tamaula

  Hukumar kwallon kafa ta Uganda (Fufa), ta nada Moses Basena da Fred Kajoba, a matsayin masu horor da tawagar kwallon kafar kasar a matsayin rikon kwarya.

  Masu horarwar sun maye gurbin Milutin 'Micho' Sredojevic, wanda ya yi murabus tun kafin kwantiraginsa ya kare kan rashin biyansa albashi a ranar Asabar.

  Hukumar ta tabbatar da cewa tsohon kocin dan kasar Serbia na bin ta bashin dala 54,000, kuma tace ta fara shirin biyansa.

  Sredojevic shi ne wanda ya ja ragamar tawagar kwallon Uganda tun daga 2013, inda ya kai ta gasar kofin nahiyar Afirka karon farko tun bayan 1978.

  Kai tsaye
 3. Dambe tsakanin Nuran Dogon Sani da Shagon Abata Mai

  Da suka dambata a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi

  Video content

  Video caption: Turmi biyu suka dambata babu kisa aka raba su
 4. Man United ta kammala daukar Matic

  Manchester United ta kammala daukar Nemanja Matic daga Chelsea kan kudi fan miliyan 40 kan yarjejeniyar shekara uku.

  Matic mai shekara 28, shi ne na uku da United ta dauka a bana, bayan Victor Lindelof daga Benfica kan fam miliyan 31 da Romelu Lukaku kan fam miliyan 75 daga Everton.

  Mourinho ya taba sayen Matic kan fan miliyan 21 daga Benfica a Janairun 2014 zuwa Chelsea.

  Kai tsaye
 5. An dakatar da Jones buga wasa biyu

  An dakatar da dan wasan Manchester United, Phil Jones daga buga wasa biyu, bayan da aka sameshi da laifin fadawa jami'an hukumar Turai bakaken kalamu.

  Hukumar kwallon kafa ta Turai ce ta samu dan wasan da laifin furta munana kalamai da kin bayar da hadin kai ga jami'an hukumar kula da gwajin shan abubuwa masu kara kuzari.

  Haka kuma hukumar ta ci tarar Manchester United fam 8,900 da kuma Jones mai tsaron baya da zai biya fam 4,450.

  Shi kuwa dan kwallon United, Daley Blind an tuhumeshi da laifin karya dokar kula da shan abubuwa masu kara kuzarin wasa, sai dai an ci tararsa fam 4.450 kawai.

  Hukumar ta hukunta Jones da tuhumar Blind a wasan karshe da United ta ci kofin Europa bayan da ta doke Ajax.

  Jones, ba zai buga Uefa Super Cup da Manchester United za ta kara da Real Madrid a ranar 8 ga watan Agusta ba. Haka kumaa ba zai buga wasan farko da United za ta yi a gasar cin kofin Zakarun Turai.

  Kai tsaye
 6. Fulham ta dauki Kamara

  Kungiyar Fulham ta dauki Aboubakar Kamara daga Amiens ta Faransa kan yarjejeniyar shekara hudu.

 7. Takaitatun Labaran wasanni

  Video content

  Video caption: Takaitattun Labarin Wasanni daga Sashen Hausa na BBC
 8. Ingila ta kai wasan daf da karshe

  Tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta ci Faransa daya mai ban haushi.

  Jordie Taylor ce ta ci kwallon kuma na biyar da ta zura a raga a gasar, wanda ya bai wa Ingila nasarar cin Faransa a karon farko tun shekara 43.

  Ingila za ta buga wasan daf da karshe da Netherlands a ranar Alhamis.

  Kai tsaye
 9. Mahrez zai koma Roma

  Jaridar Corriere dello Sport ta ce an cimma yarjejeniya tsakanin Leicester City da Roma a kan daukar Riyad Mahrez, inda dan wasan tawagar kwallon Algeria zai je can domin a duba lafiyarsa.

  Kai tsaye
 10. Teburin gasar Firimiyar Nigeria bayan mako 32

  Kai tsaye
 11. Har yanzu Tottenham ba ta sayi dan kwallo ba

  Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce an bar su a baya wajen sayen 'yan kwallo domin tunkarar wasannin bana, amma yana kokari domin ya sayo 'yan kwallo in ji Evening Standard.

  Kai tsaye
 12. Sakamakon Firimiyar Nigeria mako na 32

  Kai tsaye
 13. Everton ba za ta sallama Barkley ba

  Jaridar Daily Mail

  Jaridar Daily Mail ta ce Everton na shirin kin amincewa da tayin fan miliyan 35 da za ayi wa Barkley, duk da cewa kwantiraginsa zai kare kafin nan da wata 12.

  Kai tsaye
 14. 'Batun Sanchez ba zai shafi shirye-shiryenmu ba'

  Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce rashin sanin makomar Alexis Sanchez a kungiyar ba zai shafi shirin da yake na tunkarar wasannin bana ba.

  A karshen kakar da za a fara a bana yarjejeniyar Sanchez dan kwallon tawagar Chile za ta kare a Gunners, kuma kungiyoyi da dama na zawarcin dan kwallon.

  Kai tsaye
 15. Barcelona za ta yi karar PSG

  Barcelona na sa ran Neymar zai koma atisaye a ranar Laraba, amma a shirye take ta yi karar Paris St-Germain idan har ta biya Yuro miliyan 222 kudin ka'ida da ta saka ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan Brazil din.

  Ana alakanta Neymar dan wasan Brazil mai shekara 25, da cewar zai koma buga gasar kwallon Faransa, kuma a ranar Talata ya kamata ya koma Spaniya daga China.

  Rahotanni na cewa dan kwallon zai je Qatar a makonnan domin PSG ta duba lafiyarsa. A makon jiya shugaban kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya ce Neymar zai ci gaba da taka-leda a Camp Nou a bana.

  Kai tsaye
 16. Jesus zai sake komawa Sevilla

  Rahotanni daga Spaniya na cewa Sevilla za ta sake dawo da Jesus Navas kungiyar daga Manchester City kan yarjejeniyar shekara uku da sharadin za a iya tsawaita zamansa zuwa shekara daya kuma, amma idan ya buga wasa akai-akai a 2019/20.

  Kai tsaye
 17. Watford za ta kara sayo 'yan kwallo

  Hertfordshire Mercury ta ce kocin Watford, Marco Silva ya nuna bukatar a kara sayo 'yan wasa a kungiyar kafin a fara wasannin bana.

 18. Coutinho zai maye gurbin Neymar

  Jaridar Mundo Deportivo

  Mundo Deportivo ta wallafa cewar dan wasan Liverpool Philippe Coutinho shi ne zai maye gurbin Neymar a Camp Nou idan ya koma PSG, kuma Barcelona na duba yadda za ta sayo Ousmane Dembele da kuma Kylian Mbappe.

  Kai tsaye
 19. Mcllroy ya sallami mai masa hidima

  Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce Rory Mcllroy ya sallami tsohon mai masa hidima a filin kwallon golf J.P. Fitzgerald, wanda suka yi aiki tare har ya ci manyan kofi hudu da kai wa kololuwar wasan golf a duniya a shekara tara da suka yi tare.

  Kai tsaye
 20. Ko Ross Barkley zai koma Tottenham?

  Ross Barkley

  Dole dan wasan tsakiyar Everton, Ross Barkley, ya rage kudin albashin da yake nema domin ya koma Tottenham, wadda ba ta da niyyar biyan albashin fan 120,000 a ko wane mako da ya yi watsi da shi a Everton, in ji jaridar Daily Mirrow.

  Wasu rahotanni sun ce Everton na son ci gaba da rike dan kwallon duk da cewa wata 12 ne kawai ya rage a kwantiraginsa.